Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 1

Sponsored Links

Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy ,yabani iKon gamawa lfy,
Ameen.

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci

____________________________________________

Page 1️⃣

wata karamar yarinyace dabazata wuce shekara 5yrs ba tashigo gida tana fadin mama,mama, mama, wata kyakyawar mata nagani wacce bazata wuce shekara 40 ba aduniya da sauri mahaifiyarta tafito daga kitchen auta meyafaru irin wannan kira haka, cikin kuka da yarinta tafara magana mama Kinga kin aikeni Khalid yakwace kudin yaki bani. Meya hadaki dashi bana hanaki wasa dashiba bayan kisan yagirmeki ko,mama tagama magana tana kallon autarta Dake kuka. To shikenan Yi shuru bari in kira antynki kuje tare kukarbo kinji auta cikin jindadi auta tace to shikenan mama.

Wucewa direct falo mama tayi tahau kwala kiran FANAN wannan baccin naki ya Isa haka kitashi kizo kisameni awaje, lekawa dakin nayi Dan inga wacece wannan FANAN din. Dakine Dede namasu matsaqaitan karfi masu rufin asiri, ganin wata kyakyawar yarinya nayi wacce aqalla bazata wuce shekara 18 ba tana sanye da wando boom short dariga me karamar hannu gashin kanta kuwa yasauko har gadon bayanta, mikewa tayi tsaye SE anan ne nasamu damar kare mata kallo chocolate color ce,tanada manyan idanu wayanda suka kasance farare, tana da hanci dogo, ga bakinta Dan karar Rami dashi, libs dinta red ne kamar tashafa mishi janbaki, tana da tsawo Dan bazaa sata sawun guntaye ba , kirjinta cike suke da boobs kamar zasu fito waje sannan tanada hips sosai Masha Allah domin yanda take da jiki mekyau da sura bazakayi tunanin shekarunta kenan ba kyakyawace ta ajin farko.

Tafiya tafarayi domin tashiga toilet ta watsa ruwa ko baccin ze saketa, bayan kamar 10mints tafito tana tsane jikinta da wani karamin towel, tunawa datayi mama nakirantane yasa tafara shiryawa da sauri, lotion tashafa ajikinta. wata dogon Rigar material tadauka tasaka kafin tadauki man gashi tashafawa kanta ta taje gashinta din tadau ribom dakyar ta iya hade gashin tadaure. Perfumes tafesa ajikinta tadauki hijab Daya wuce gwuiwanta tasa Masha Allah, ta hadu iya haduwa.

Fitowa tayi tasamu mama na gyara shinkafan dazaayi tuwon dare dashi, cikin sanyin murya tace mama gani dago kanta mama tayi cikin zuciyarta tafurta Masha Allah yata allah yakawo miki miji nagari, yauwa dama dazun na aiki auta shine komeya hadata da Khalid yakwace kudi a hannunta Dan Allah jekijimin baasi kikarba kudin kisiyomin kayan Miya dashi karki Dade Kinga yamma tayi ko cikin murmushinta dayake Kara mata kyau tace to mamana bari inji.

 

Ga wannan kufara dashi se mun hadu gobe

 

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

‍⚕️‍⚕️NIDA PATIENT DINA Story written by (MRS ISHAM )

Da sunan allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy Ameen.

 

Wanann littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci .

 

____________________________________________

 

Back to top button