Adandi 34
*34*
Kallonsa takeyi cikin tsananin mamaki amma saita samu kanta dabin umarninsa ya riqe hanunta har suka isa gurin motarsa ya bude mata ta shiga shima ya shiga har ya tayar sai kuma ya tuna ya kashe ya fita ya shiga bangaren fulani Amina bai jima ba ya fito hanunsa dauke da wani kyakkyawan tea flast ya ajiye a gabansa ya shiga ya zuba mata ido ta hade kanta da gwiwa sai kuka takeyi me tsuma zuciya duk da yanda shassheqar kukanta yake cakar zuciyarsa amma bazaitaba sakacin rasa cikinsa ba haka yaja motar suka fita daga gdan sarautar har sukaje gda batace masa qala ba.
Suna isa gdan ta bude motar a fusace ta sanya key ta bude qofar parlourn ta shige ya bita da kallo har yanzu kuka takeyi shiga yayi ya mayar da qofar ya rufe saboda lkc yaja har anyi sallar Isha tea flast din ya haura saman da sauri.
A qasa ya tarar da ita saman center carpet din dake jikin gadon ta dora kanta a saman katifar gadon tana kukanta me ban tausayi cikin sanyi jiki ya matsa jikinta ya dago fuskarta ta kwace cikin kuka tace “ka qyaleni Mainah Abdu ka rabu dani banason kowacce kalma daga gareka me zaka fadamin me ka mayar dani kanason dole saika rabani da mahaifiyata akan me me tayi maka Abdu me mukayi maka da kakeson dole saika shiga tsakaninmu” toshe kunnensa yayi cikin tashin hankalin fassara da Aysha tayi masa a hankali ya matsa jikinta yace “bazan taba shiga tsakaninki da wacce kike kallo a matsayin mahaifiya a gareki ba kawai don son zuciya ki amince dani don Allah ki bani hadin kai zakiyi alfahari da hakan anan gaba kinsani Aysha inasonki bazan cutar dake ba” daga masa hanu tayi tace “ya isa haka Abdu ka ficemin daga daki amma na haqiqance kaiba mijin daya kamata na rayu dakai bane…” Cafkarta yayi da sauri yace “dawa zaki rayu idan baki rayu dani ba kada ki kuskura ki kawomin zancen wani banzan namiji a gdana wlh bana dukan mace amma tsaf zan dagargazaki wawuya kawai da batasan mesonta ba ke banda haukanki wannan har uwace da zaki nemi fadamin mgn akanta uwar da batason cigabanki uwar da take burin cutar dake dason ganin bayanki uwar da takeson hanaki haihuwa duk wani burinta da plan dinta akan yanda zata lalataki ta cutar dakene”
Dakatawa yayi yaja fasali sannan ya turata gadon yaci gaba da cewa “kawai saboda inason farin cikin abokan gaba sai na daukeki na kaiki gurinta ta lalatamin cikina dake jikinki to bari kiji banson Hajiya Lubabatu wadda take amsa sunan mahaifiyarki kuma bazan taba sonta ba saboda haka ki sani wasan yanzu muka fara kuma dole kiyimin biyayya domin nine mutum na farko daya zama wajibinki kiyiwa biyayya dagani sai mahaifinki wanda na tabbatar bazai taba barinki ki cutu ba kuma bazai taba cutar dake ba Aysha idan kikayiwa Dr Hasina biyayya ma bazanji komai ba saboda zuciyarta tanada tsarki kuma domin Allah take sonki amma bazan taba yarda ko lamuntar kiyiwa wannan matar biyayya ba wlh azeem Aysha Hajiya Lubabatu bata fara kuka ba indai akai nane”
Yana fadin haka ya juya ya fice ya ja mata qofar da qarfi zubewa tayi a qasa ta dora hanunta a kanta tace “nashiga ukuna wayyohhhh niya Allah na me kake nufi danine Allah wannan wanne irin miji ka hadani dashi ne Allah meye tsakanin mahaifiyata da mijina…” Tana mgnr tana kuka me ratsa zucciya ta jima tana kuka me shiga jiki kafin tayi qarfin halin miqewa ta fada bathroom tayi wanka ta fito ta shimfida sallaya ta fara nafilfili tana roqon Allah ya kawo mata mafita cikin wannan rikitaccen al’amari nasu ita Mainah Abdu gaba dayansa tsoro yake bata ta lura da takunsa ko qaramin motsi mutum yayi saiya fassarashi gashi shi kansa bai yarda da kansa ba ko fita yayi idan ya dawo kafin ya shigo cikin gdan saiya zagaye ko Ina na harabar gdan kuma tasha tashi cikin dare taji bayanan idan ya shigo ya ganta sai taga ya waske koda kuwa zata tambayeshi ce Mata zaiyi cikin aikinsa ne ko yace tsaron lfyrki nakeyi.
Tana idar da sallar ta tashi tasa doguwar rigar baccinta ta fesa turare ta dauki ribbon ta daure gashinta tunawa tayi da kunun da surukar tata ta dama mata ta nufi qasan da sauri ta shiga kitchen ta dauki cup ta fito ta tsaya a dinning din ta bude flast din ta tsiyaya kunun ta lumshe idonta qamshinsa yanayi mata dadi harta dauka zatakai bakinta taji yace “karkisha” cak ta tsaya cike da tsananin mamaki ya tako ya zagayo ta bayanta ya sanya hanunsa ya karbi cup din ya ajiye a saman dinning din ya sanya wani dan qaramin abu me kama da rariya akai ya danna wasu numbers yakai minti biyu yana haska kunun sannan yayi murmushi ya dauka yakai bakinsa yasha itadai tana binsa da kallo saida yasha sosai sannan ya sake tsiyaya mata wani yakai mata bakinta ta dauke kanta tare da juyawa zatabar gurin yayi saurin riqota yace “dan tayin babyna yanaso saboda haka dole ki bashi abinda yakeso” bai jira cewarta ba ya dauki cup din ya janyota jikinsa ya matseta ya buda bakinta ya fara dura mata tana kuka tana komai haka tasha kunun saida ta shanye tsaf sannan ya saketa yayi murmushi ganin tayi taga² zata fadi ya tarota ya dagata cak ya nufi dakin qasan da ita ya kwantar da ita a qatuwar katifar dake dakin six by six megida sauko mu gaisa yabita ya danne inda ita kuma takebin dakin da kallo duk tarkacen na’urori ne adakin tako ina sai wata qatuwar TV flasmah manna bakinsa yayi a kuncinta yace “baki taba shigowa dakinnan ba ko My Aysha bari kiga wani abu” wani remote ya dauka ya matsa cikin second talatin saiga hoto ya bayyana wayarsa ya dauka ya jorner da cable ya ajiye ya dawo ya kwanta ta zubawa TV ido kawai sai taga hoton parlourn fulani Hadiza ya bayyana kafin tayi wani tunani saiga lkcn da ta rungumeta da lkcn da take qoqarin shafa cikinta qasan mararta stop yasa a guri ya kira sunanta tare da zooming din hoton yace me kika fahimta a hoton nan?”
Shiru tayi batace komai ba saida ya qara maimata tambayar ta dago ta sauke dara² idanunta akansa ya mayar da kallonsa kan TV yace “ki kalli TV ki bani amsa” zubawa hoton ido tayi tace “bqn fahimci komai ba” ajiyar zuciya yayi ya saki videon yaci gaba da tafiya har zuwa lkcn da fulani Hadiza ta shiga dakinta abunda ya gigita tunanin Samha kawai saiga hoton dakin fulani Hadiza wai harda mgnr da takeyi tace “nayi qoqarin shafa mata maganin nan a qasan mararta amma nakasa saboda makirin yaronnan yana gurin wlh bakiga yanda ya kafeni da ido ba duk motsinta akan idonsa amma fa tabbas akwai shigar ciki a jikinta ki nutsu ki kama kanki ki tareta da salon dana tareta ki zuba mata maganin nan a lemo ta shanye mgn ta qare wlh ko batan wata bazata kumayi ba” gaban Samha yabada wani rasss ta tureshi daga jikinta da sauri tace “me hakan yake nufi? dawa take waya?? Menene ma’anar ko batan wata bazan kuma yiba” lumshe idonsa yayi ya janyota jikinsa yace “wannan shine dalilin da yasa na hanaki zuwa gurin Mamynki kiyi hqr a hankali zaki fahimceni My Aysha duk bangaren dana shiga baa sirri saboda inada Contact da ko Ina matsawar da wannan abar a gurin wato waya kuma da ita zaayi amfani”……….
*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/17, 6:29 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*
*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*