Nasarar Rayuwata 22
*Talented writers forum*
*22*
Hajjo tayi sati a gida ko shago inna taki barinta taje bare wata kasuwa saboda yanzu ta fara girma ga Kuma alamomin girma sun fara bayyana a jikinta ga Kuma fargaban zuwan Aman, harga Allah inna Bata son wata alaka ta shiga tsaknin Hajjo da Aman donhaka take Allah Allah hutun ya kare ta maidata makarantar sai Wani lokaci kafin ta Kara barinta tazo gidan. Duk yadda Ayman ya nace akan yazo suje tare inna taki amincewa haka ya hakura ya kyaleta.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inna taci gaba da gwagwarmaya tana faman hada kudin makarantar Hajjo duk da cewa da sauran lokaci Amma ance Mai zurfin Ido shike fara Shirin kuka da wuri, a bangaren Ayman kuwa sunyi resuming second semester results Nasu ya fito ba laifi dukkansu sunyi kokari don Babu me carryover cikinsu saboda haka Ammi tayi farin ciki sosai a nan ta amince da d’aga batun auren Aman da zee har sai sun kammala karatun nasu.
**********†**
*Bayan shekara biyu*
Abubuwa dayawa sunfaru ciki kuwa harda baikon Aman da zee angama komai saura sadaki da lefe , yanzu saura shekara d’aya su kammala karatun nasu ayi biki a Halin yanzu soyayya suke zubawa da zee Babu laifi zee ta samu Kansa yadda take so duk da cewa Wani lokacin Yana mata wulakanci Amma ko kadan Bata damu ba , gashi mamanta ta samu minister wato hnklin Ammi ya Kara karkata ga son Ganin sun shiga familyn masu naira donhaka take ta Kara karfafa zumunci da dangin Armani, Ayman kuwa hankali kwance yake karatunsa tunda baa Kara kawo masa zancen aure ko zancen sarauta ba, inna kuwa ta zame masa tamkar uwa domin kuwa a kullum sai sunyi waya takan Yi masa nasiha da bashi Yan shawarwari akan lamuran rayuwarsa, Hajjo kuwa ana jarabawar JSSCE wato zata kammala aji uku a secondary sun kusa zuwan gida wannan kenan .
Yau Inna ta dauki tsohon sim nata ta saka rabonta da sim din ya kwana biyu duk da cewa wasu lokutan takan sakan sannan ta cire ta ajiye, yauma haka nan ta dauka ta saka tana danna wajen Lambobi kenan kira ya shigo kamar jiranta Ake . Shiru tayi ta kurawa wayar Ido Sam Batasan wannan layin ba sabon number ne kamar bazata d’aga ba sai Kuma ta canza shawara ta d’aga tare da sallama ” assalamu alaykum” ” wa’alakissalam magira, don girman Allah karki kashe min kira please na rokeki ki saurareni ” tamkar wacce aka zarewa laka a jiki haka ta zauna numfashinta dakyar yake fitowa ga Wani sanyin da jikinta yake har tana Jin tamkar rike wayar zai gagareta ” Ameenah! ya furta cikin wata irin muryar dayasa tsigar jikinta ya tashi , ” kina jina, please talk to me ” a hankali tace” yah Yusuf ” Naam magira Tah, don Allah Ina Neman alfarma ki tausayamin ki bani daman ganinki Ameenah, don Allah ki taimaka ki bari mu Hadu mu tattauna nasan kina ckn Abuja , jiya na shigo saboda ke please ki bani dama please and please” shiru tayi tana sauke numfashi a jere tamkar wacce tayi Wani aiki ta gaji , ” magirah don Allah pls ” shikenan gobe zan kiraka ” daga haka ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya tare da runtse Ido, abunda take gudun dai Yana Shirin faruwa da ita , a hnkli ta furta ” Allah gani gareka ka min zabi Mafi alheri ” haka ta sulale ta kwanta tare da rufe idonta tamkar me bacci, maman Nana taji shirun yayi yawa ta shigo tare da sallama” malama lfy dai yau Kuma baccin yamma ” a hnkli ta Bude idanun tace ” mmn nana Wani alamari na Shirin faruwa dani” zama mmn nana tayi tace ” toh… Allah yasa dai lfy ” numfashi ta sauke ” maman Nana kedai ki tayani da adua sai gobe zakiji komai ” Allah ya kaimu ” Ameen ” daga haka mmn nana ta tashi ta bar mata d’akin saboda ganin tana bukatan kadaici.
Misalin karfe 10 na safe inna ta sauka wajen gate din snake farm tafi yarda su hadu a nan saboda Babu mutane musamman a wannan lokacin da yamma akafi zuwa wajen , tana zuwa bakin gate zata Bada kudi security yace ” Wani Alhaji Yana ciki yayi booking din wajen yace baya bukatan kowa ” murmushi tayi tace ” shi nazo Gani ” Ya sunanki?” “Amina ” ok haka yace min wata Amina zatazo nemansa ” nan aka Bude mata ta shiga kanta na kallon kasa duk da cewa Hijab ne a jikinta me hannu light pink Amma Hakan Bai Hana asalin kyaunta dada fitowa ba, a hnkli take tafiya ckn nitsuwa gaba d’aya ya tashi tsaye ya kura mata idanu Babu ko keftawa ” magirah” ya furta a hnkli dai dai lokacin da ta karasa kusa dashi tare da sallama sai ynxu ta d’aga kanta idanunta suka fada cikin nasa hawaye ne suka taru a idanun nata ” magirah kece, ashe zan Kara ganinki a rayuwa nagode nagode da kika bani wannan dama I really appreciate ur concern towards me thank you…” Ya Yusuf! …nan ta fashe da kuka tana kuka a hnkli tare da sunkuyar da Kai, a karo na farko a rayuwarsa yakai hannu ya rike palm nata a hnkli ya jawota suka zauna bisa wasu kujerun da aka tanada a wajen lambun, runtse Ido tayi tana Jin Wani abu na sirga mata daga tsakiyar Kai har zuwa tafin kafa nan da nan ta lumshe idanunta tana tuna rayuwarsu na can baya, “karki gaji dani yanzu ma Wani alfarma zan sake nema a wajenki Ameenah, wannan karon bazan hakura ba bazan Kuma Baki damar ki zabi abunda ranki ke so bah, a wancan karon na rasaki bisa kaddara Amma wannan karon bana fatan sake rasaki har abada pls ki taimakawa rayuwata ki cika min wannan burin nawa magirah, kinsan shi kadai ne burin da ya ragemin a duniya pls n pls magira don girman Allah ki bani dama na cika wannan burin ” bugun zuciyarta ya dada karuwa numfashinta na fita sama sama kwakwalwarta cak! Ya tsaya ta kasa tunani ta kasa aiwatar da komai sai kallonsa take tamkar wacce taga sabuwar halitta, cikin zuciyar Alhaji Yusuf kuwa adua yake Allah ya bashi nasara , tabbas wannan karon yasan zaiyi sonkai tunda yasan cewa mijinta ya dawo Yana nemanta Amma bazai taba sanar da ita ba a wannan karon baya fatan sake rasata har abada , duk duniya Babu macen da ta shiga rayuwarsa irin Amina a wancan lokacin bashi da zabine Amma wannan karon dole ya mallaki abunda yake so. “Kinyi shiru magirah pls say something” shiru tayi ta rasa me zata ce masa ” don Allah ki bani last chance pls ” sauke numfashi tayi a hnkli ta fara magana ” Fav ka manta har ynxu da aurensa a kaina ” na sani fav na sani Amma for how long zaki cigaba da jiransa? , Shekara nawa ynxu haba fav kiwa kanki adalci kiyi abunda ya dace , ko addini ya Baki wannan dama, kiyi amfani da iliminki mutumin nan bakisan inda yake ba bakisan halinda yake cki ba maybe ya manta dake, dama can ke kika Fi damuwa dashi Amma….” Shhh…ya Isa haka , nasan komai nasani pls don’t remind me anything” nan ta Kara fashewa da kuka, gaba d’aya ya rude ya rasa ya zaiyi da ita bayason ganin hawayenta ” is ok pls am sorry ki daina kuka ya Isa haka, Amma pls kizo muje a raba wannan wahalallen auren kowa ya huta , ki bani dama na cika mana burinmu na tabbata His highness da Kansa zaiyi tsananin farin ciki idan ya samu wannan labarin duk da cewa ba ynxu na shirya sanar dasu komai ba, Yakumbo da kanta zatayi farin ciki magirah ke kinsan da hakan” Jin an ambaci yakumbo yasa Wani murmushi ya subuce mata tace ” Allah sarki yakumbo nah tana nan lfy koh, Ina su Bilkees dasu Jawahir I missed them all” kowa nan lfy sai kewarki, a kullum sai an ambaci sunanki a wannan gidan gaba d’aya kin tafi da farin cikin iyalan kin zabi son ranki ” runtse Ido tayi ta budesu tana Jin zuciyarta na mata Kuna ” ba son zuciya bane Kai Kafi kowa sanin abunda zuciyata ke so kawai dai kaddara ce tazo min a haka da tsananin rabo ” wai Ina yarinyar ne ? ” Sai ynxu ya tuna , murmushi tayi kafin tace ” tana makaranta” that’s cool..ynxu pls muje muyi abunda ya dace Fav ” a hnkli ta zame hannunta daga ckn nasa yayi saurin d’aga Ido Yana kallonta ” kayi hakuri ka bani lokaci ” ya Allah! Wane irin lokaci Kuma fav, ” ckn kwantar da murya tace ” kasan gaggawa aikin shedan ne so pls I need time” fine! Na Baki zuwa gobe yau kije ki gama duk tunanin da zakiyi gobe zan taho muje ayi abunda yafi dacewa da rayuwar ki, u can’t continue dis way haba! So kike ki cigaba da rayuwa ke kadai kina struggling bayan kina da gata da family Amma kizo kina Shan wahala haka, Kinga yadda kika koma kuwa??” Shiru tayi ta sunkuyar da kanta kalaman nasa sun shigeta tabbas! Bazata dawwama haka ba yau shekara 6 kenan Babu sulei Babu labarinsa …” Magirah! Ki newama kanki mafita ko saboda wannan yarinyar, idan baki so na fine zan hakura amma dole zamu koma gida tare bazan Kara barin ki a nan garin ba ” hawaye ne ya fito mata ckn rawar murya tace” ka manta da abinda Baba yace min, idan kowa ya manta ni ban manta bah har abada kalamansa na yawo a kwakwalwata ” good .. shiyasa nazo da mafita na tabbata kowa zai yafe miki zasu karbeki idan har komai ya tafi yadda ya kamata pls ki amince da wannan bukatar tawa ko don martabar family dinmu pls ” shiru tayi tana nazari daga bisani tace ” shikenan Allah ya kaimu gobe zanyi tunani Akai ” Wani murmushi ne ya bayyana a fuskarsa ” thank you so much, Allah yasa ki bani good news n thanks for honoring my invitation” murmushi tayi batace komai ba, shiru sukayi kowa da abunda yake kullawa a zuciyarsa. Bayan sun sauke inna a under bridge bundle na kudi ya cire ya damka mata a hannu yace ” gobe Ina son ganin Magirah da na sani a da can baya kamar yadda nasanta pls ” daga haka driver yaja mota suka wuce inna tana tsaye tayi Jim sai daga bisani ta tuna cewa maraba fah take Wani zai iya fisge kudin donhaka ta cusasu ckn purse nata ta shige ckn kasuwar maraba.
____________
Yau Hajjo sai murna Ake angama jss3 zasu tafi gida , tunda safe kowace daliba ke faman hada kayanta musamman Wanda bazasu dawo next term ba, idanun Hajjo sun kumbura don sabar kukan rabuwa da sis khairiyya wacce tayi candy , sun shaku matuka sun koma tamkar ya da kanwa a nan khairiyya ta hada hajjo da wata cousin nata Ummeey wacce take Ss1 su zasu shiga SS2 , Hajjo Bata dauki Wani kayan kirki ba Wani school bag kadai ta dauka ta rataya a baya tana sanye da uniform dinsu Riga da short skirt Wanda kadan ya wuce guiwa sai long sleeves shirt da suit navy blue a sama , tana sanye da boots nata sai ankle socks kitson kalba ne akanta Wanda ta maidashi kamar ibada , kanta Babu dankwali gashinta na Lilo a baya ga hasken fatarta ya Kara fitowa ga girma ynxu she is 16 , ga qamshin emergency dake tashi a jikinta duk Wanda yasan tsohon perf din emergency toh yasan qamshin akwai lasting. Yan gidan sis khairiyya sunzo daukarta nan suka Kara rungumar juna suna kuka dakyar aka rabasu, zuwa tayi ta jingina kanta da flag nasu tana jiran zuwan inna saboda Mrs Juliet tace ta sanar da ita zaazo daukarta duk abunda take idon Ayman na kanta tun lokacin da suka fito daga hostel suke kuka tare da sis khairiyya Yana ckn mota Yana kallonsu sai murmushi yake Yana son ganin iya gudun ruwar hajjo sai Kuma ya hango jingine da pole din flag ta kulle Ido nan ya kura mata idanu tayi Wani kyau me daukar hnkli nan yaji Wani kishinta ya rufesa dubeta ko dankwali Bata saka ba tabar gashi a waje. Aman yayi parking wajen parking lot na school din ya juya Yana kallon zee yace ” pls karki b’ata min Lokaci akwai inda zani ” murmushi tayi tace ” angama Habibi nah ” kashe masa Ido tayi ta Bude kofa ta fice murmushi yayi Yana girgiza kai, zee ta addabesa lallai dole sai sunzo daukar sister dinta dake makaranta a nan Babu yadda ya iya dole ya kawota . Zee sai faman raba Ido take ko zata hango Ummeey gashi Babu waya bare ta kirata , tsaki take faman ja tana raba Ido can taji an rungumeta ana dariya ko baa fada ba tasan Ummee ce “mstww… shegiya duk kinbi kina wahalar dani , don tsabar naci da wahalar dakai ki rasa school din da zakije duk fadin Abuja sai wannan clamzy school din” turo Baki ummee tayi tace ” kinfara koh, ni ki barni ai dad yace kowa yayi abunda yake so ni Kuma nan din ya min ” ba gwara Miki ki karasa a inda kikayi junior section naki ba , ynxu me abin burgewa a nan ” nidai sisy muje gida yunwa nake ji n i missed home ” tsaki Zee ta karayi sannan ta juya ta fara tafiya, Kamar a mafarki Aman ya hangota dam! gabansa ya Fadi” Amma dai wannan idan ba Hajjo bace toh duk yadda akayi suna da dangantaka saboda kamannin yayi yawa, dole yaje ya tambayeta ko tasan Hajjo ” Yana Bude kofar mota zee ta iso tana cewa ” sorry I kept you waiting koh…muje gata” ganin Aman ya fara tafiya tace ” Ina Kuma zaka my man, gata nan fah let’s go home pls ” 2 minutes pls ku shiga Ina zuwa ” ya hangota can tana magana da wata , dai dai nan Ayman yayi parking gaban hajjo tayi sallama da Bless ta Bude front seat ta shiga saboda Mrs Juliet ta tura Bless ta fada mata Ayman ne zai kaita gida. Aman na karasowa a wannan lokacin Ayman yaja mota suka kama hanyar fita harabar makarantar, ” shitt…” Aman ya fada da karfi cike da bacin rai ya koma haka yaja tashi motar ummee na gaishesa dakyar ya amsa suka fice daga school din. A hnkli ta furta ” Ina wuni ” kallonta yayi ya dauke Kai yace ” where is your scarf? ” Shiru tayi ta sunkuyar da Kai tana wasa da yatsun hannunta , shiru ne ya biyo baya