Nasarar Rayuwata 18
*Talented writers forum*
*18*
Ammi ta kura mishi idanu gab’a da’ya tausayinsa take yaro karami amma anbi ansakashi gaba da kiyayya ana son tauye masa hakkinsa Wanda anhalatta masa ana Neman haramta masa , Kansa a sunkuye yake Yana jiran yaji dalilin Kiran da ta masa , numfashi ta sauke sannan ta kira sunansa ” Ayman!.. ” Ammi nah ” ya amsa Kai tsaye
“Ayman kayi hakuri ka dauki komai bisa kaddara , Ina matukar tayaka bakin cki d’ana ni Kuma nayi alkawarin nema Maka wacce zata maye gurbinta cikin kankanin lokaci, mutanen masarautar ku akwai son Kai da danne hakki Ayman,” shiru yayi Yana sauraronta tamkar Bai gama fahimtar me take nufi bah, ta cigaba da cewa ” yanzu sai maganar Mulki ne bamusan wane hukuncin sultan ze Yanke bah, amma a halinda Ake cki zancen aurenka Babu shi ita yarinyar ta koma tace Aseem take so ba Kai bah” aure nah Ammi, kina nufin anfasa maganar aurena da sabreena” ya tambaya a dimauce , Ammi wacce take tausayinsa tace ” kayi hakuri Ayman Allah zai hadaka da wacce ta fita insha Allah ni nan na Maka alkawarin samo Maka jinin sarauta nan ba da dadewa ba kayi hakuri kaji” murmushi ne ya subuce masa wannan shine labarin da yafi kowane labari dadi agaresa , Ammi ta kura masa Ido tana Jin tausayin Ayman da sonsa na Kara shigarsa yaron akwai hakuri ga ladabi da biyayya, yanzu da a ce Aman ne da Allah kadai yasan dramar da zaa kwasa amma shi wannan har murmushi yake ” shikenan Ammi nagode amma ni zancen auren nan da anbari sai na kammala school before ” au yanzu ka fara son karatun kenan ja’iri ” murmushi yayi ya sunne Kai ” toh shikenan tashi kaje sai munyi magana da Umma duk halinda ake ciki , amma yanzu haka rikici ake a masarautar taku kan wannan Batu da zancen nadin sarautar yarima ita wancan Suhail din so take a bawa d’anta Wanda Hakan bxai taba faruwa ba bazamu xuba mata Ido tayi abinda taga dama bah ” tabe Baki yYi ya tashi ya mata sallama ya wuce part nasu Kai tsaye, Wani farinciki ne ya ziyarci zuciyarsa lallai Allah Mai iko kenan yau sabreena ce tace Bata sonsa sai Aseem , koma menene dai yayi murna da wannan lamarin take yayi sujudush shukur na nuna godiya gun ubangiji ya tabbata wannan din zabin da ya nema a wajensa ne , inna ce ta fado masa a rai cike da zmudi ya dauki waya ya fara Neman layinta har ya katse Bata d’aga ba nan ya ajiye ya tuna yanzu haka tana Wani aikin ne saboda yamma tayi sosai.
Aman ne ya fada d’akin tamkar anjefosa ” Kai man ya haka, me kayiwa yarinyar nan ta koma gun kaninka” murmushi Ayman yYi ” me Kuma zan mata, kasan shi so tsuntsune so Ina ga ya tashi daga kaina ya fada kan Aseem ” mtsww..anyi banza wllhi, ynxu ko kunya bakaji budurwarka ta koma gun kaninka ai wannan ma is a slap on the face I swear ” lumshe Ido yayi Aman da gaba da’ya haushin lamarin yake yace ” Koda yake Kai bakasan hakan ba tunda baka soyayya ba, yanzu ko dan kishin Aseem bakaji don Allah?” Haba kishi Kuma kamar mace ” tirr… wllhi Kai matarka tayi asara zata Sha fama da mijin da is not romantic ” hmm .Mr Romeo shiyasa naji ansaka muku rana da wannan yarinyar koh” take fuskar Aman ya canza zuwa bacin rai ” mtsw.. shegiya kamar mayya take wllhi nidai ka cuceni saboda Kai ta fara bibiya har Allah ya hadata da Ammi aka like min kamar gum, yanzu da kuruciyata zaa min aure tsakani da Allah am just 24 fah ” murmushi Ayman yai ba tare da yayi magana bah, ” ni na manta ma ban fada Maka ba , wannan beb din da nake so ashe ta koma yola tana school wllhi naji haushi ba kadan ba, but shaa..zata waye ai tunda school ne ta tafi, ai da sun gayamin sai na saka a Nemo mata Turkish na nan Abuja wllhi ” tabe baki Ayman yayi haushi ya kama Aman yace ” why am I even telling you this..mtsww banza miskili ” ya tashi ya fice Ayman yabi bayansa da murmushi nan ya koma ya gyara kwanciya.
**************
Inna tana bisa sallaya wayarta yayi Kara ta tashi ta duba Mrs julliet ce ckn murna ta d’aga wayar ska gaisa ta Bata Hajjo suka Sha hirarsu sukayi sallama ta kashe wayar fuskarta dauke da murmushi tana Kara mikawa Allah godiya bisa yadda rayuwar ta ke tafiya cikin sauki da rufin asiri tabbas Allah Yana tare da masu gaskiya da masu hakuri har ila yau tana nan tana yiwa mijinta adua Allah ya bayyana shi tasa a ranta cewa sai ranar da Hajjo ta samu mijin aure a ranar zata koma gida saboda gudun gori da Neman asalin tarihinsu, tana ajiye wayar ta duba call log taga missed call din Ayman nan ta fara Neman layin nasa ashe Babu kati a wayar ta Maida ta ajiye kenan sai ga kiransa ya shigo, ta amsa suka gaisa take tambayarsa ya exams yace ” alhamdulillah komai normal innarmu Kuma Ina Miki albishir da cewa anfasa auren ” ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa ” Masha Allah Ina tayaka murna Allah yasa Hakan shine Mafi alkairi ” Ameen nagode innarmu kece kika bani kwarin guiwa da gudumawar adua nagode” Babu komai Ayman Ina son ka Adana wannan aduar duk abunda kake bukata ka roki zabin Allah shine dai dai kada ka biyewa son zuciyarka ” nagode inna insha Allah zanyi aiki dashi ” uhmm..na manta ban fada Maka bah, Aman yazo Neman Hajjo ” “ya fadamin inna Amma don Allah kada a fada masa inda take saboda Hakan zai iya janyo matsala Kuma zai raba mata hankalinta gida biyu, a bari ta gama karatun idan ta dawo…” Ayman bana bukatar auren Hajjo da Dan uwanka kayi hakuri, bayan zuwan nasa na fuskanci abunda kake boyemin wato mahaifiyarku Bata son muamalar tasu donhaka nidai bazan Bada goyon baya bah, nagode da dawainiyar da ka mana amma auren nasu ba Mai yiwuwa bane ” Wani abu ya hadiye dakyar ya Bude Baki yace ” kiyi hakuri inna na boye Miki ne saboda gudun tashin hnkli Amma insha Allah Babu wata matsala”
“Ah ah Ayman akwai matsala babba ma kuwa ni …” Inna ki mana adua, Abar wannan zancen kin manta yanzu kika gama gayamin cewa komai a barwa Allah zabi, donhaka na rokeki kada ki dauki maganar da muhimmanci kawai aduarki suke bukata” cikin sanyin jiki tace shikenan insha Allah zanyi ” yawwa innarmu toh yaushe zan kawo Miki ziyara, na kusa kammala jarabawata Kuma idan na gama zan danyi tafiya ne inna ”
Murmushi tayi tasan dara kawai yake son ya mata Yana Neman Wani hanyar taimakon da zai musu ita Kuma kunyarsa takeji dawainiyar tayi yawa ga kudin makarantar Hajjo ya biya na shekara 3 jss1_3 sai ss1 zasu Kara biya shiyasa ta dage da sana’a tana son ta biya kudin ss1 din da guminta… ” Inna ”
“Naam dan gidan inna ” murmushi yayi Yana Jin dadin hira da ita tana matukar debe masa kewa, ” shikenan inna tah sai da safe”
“Allah ya tashemu lafiya ya Bada sa’ar jarabawa” Ameen nagode ” dif..ya kashe wayar, inna ta kurawa wayar Ido tana Jin Ayman a ranta tamkar Wani jininta Yana tuna mata da Wani , lumshe Ido tayi tana Jin kewarsa sosai a rayuwa tasan duk duniya Babu Mai kaunarta irinsa hatta iyayensu ta tabbata yafisu kaunarta Amma kaddarar da Allah ya tsara mata kenan a rayuwa Babu yadda ta iya, zuciyarta na tunxurata akan Kiran layinsa Wani sacen zuciyarta kuwa na hanata, hannunta sai rawa yake ta danna wajen karban bashin kati zuciyarta na azalzalarta donhaka Babu Bata lokaci ta danna nambobin da ta haddace tun shekarun baya, bugun zuciyarta na dada qaruwa Allah yasa dai Bai canza layin bah tana wannan tunanin taji wayar na ringing da alama layin na tafiya, gub..gub..gub.. zuciyarta na harbawa har Kiran ya katse baa d’aga ba daga dayan bangaren Babu Bata lokaci ta sake kira har ya kusa katsewa aka d’aga tare da sallama Wani murya Mai dadin sauraro da tsantsar nitsuwa da haiba ya sake maimaita sallamar Jin baa amsa masa bah, shiru tayi a yayinda take Jin muryar har cikin kogon zuciyarta nan hawaye ya cika mata idanu Babu shiri kukan da take dannewa ya kubce mata har sautin sheshekar ya fara fitowa , har abada bazai manta da ita ba ” magirah! ” Ya ambaci sunan saura kiris ya Suma daga xaune, ckn muryar kuka tace ” ya Saif! “Magirah! Magirah kina Ina ne, magirah an aiko mana cewa kin Bata dake da y’ar ki , kina jina magirah! Magirah ”
Kitt…ta kashe wayar ta kasheta gaba daya ta cigaba da kuka Mai tsuma zuciya.