Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 23

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*23*

A hnkli yake tukin tamkar baya so haka suka cigaba da tafiya Babu Wanda ya sake magana cikinsu nan ya kunna wakar Maheer Yana sauraro Yana bi tamkar shiya rera wakar na assalamu alayka ya rasulullah , hajjo ta kauda Kai tana kallon window Yana kallonta ta gefen Ido can ya rage volume yace ” zaki hadu da inna ne yarinya ba Ina Miki magana kikayi banza dani bah ” gabanta ne ya Fadi sai ynxu ta tuna wajen waye zataje tabbas idan batayi sa’a ba har dukanta inna zata iya akan rashin dankwalin , nan ta juya ta marairaice tace ” don Allah Yaya muje ka Siya min hijabi ” bani da kudi ni ” Kai tsaya ya Bata amsa ba tare da ya kalli inda take bah , ” please ya Ayman ” ckn zuciyarsa yace dama tasan sunana ashe , a zahiri kuwa lumshe idanu yayi ya cigaba da driving nasa cikin kwanciyar hnkli. Ganin Bai kulata yasa tayi saurin dora hannunta kan nasa tare da cewa “please Yaya nah..” Yadda ta furta ga Kuma sanyi da laushin hannunta nan take ba shiri Ayman Yana Neman rasa saiti jikake kiii…ya taka Wani wawan birki, ya juya Yana kallonta itama shi take kallo a tsorace ” ya Salam! Me hakan, bakisan Muna kan titi bane” a hnkli yake magana ckn rashin son hayaniya, ta turo baki tace ” toh ni me nayi don kawai nace ka Siya min hijab , idan naje gida dukana inna zatayi wllhi ” ai gara ta dakeki ,Kuma sai na fada mata cewa har rike Maza kikeyi ” da sauri ta wara sai Kuma ta marairaice tace ” don Allah kayi hakuri wllhi ni bana rike kowa kaima…” Sai Kuma Kuma shiru ” ki karasa Ina ji ” nidai kayi hakuri karka fada mata Kuma muje ka siyamin hijab ” toh ke ynxu Baki da hijab a school din ne?” Ina dashi kawai ban dakko kayana bane ” me a ckin bag naki?” Books ne sai chocolate da wasu Yan kayayyaki ” Yan kayayyaki kamar me dame ” turo Baki tayi Bata ce komai ba, ” toh shikenan tunda bakison hijabin ” nidai kayi hakuri pls my yayah”! My yayah! Sunan ya tsaya masa a rai, lumshe Ido yayi sannan ya kunna motar suka cigaba da tafiya ya dauki hanyar area 10, tana kallon hanyar bayan like 20 mins yaje yai parking gaban old Sahad ya juya Yana kallonta ” muje ” a hnkli ta Bude ta sauka ya kulle motar suka fara tafiya a jere wajen a cike yake saboda kasancewar Weeknd ne nan fah aka zuba musu ido wato sunyi bala’in dacewa ga kyau na daukar hnkli ga Kuma kasaita, ganin kallon da Ake musu yasa ya rike hannunta suka fara tafiya da sauri har suka shiga cki. Kai tsaye bangaren kaya sutura suka haura nan suka fara Neman layin hijab ckn sa’a kuwa suka ci karo da layin jalbab dogaye masu kyau, hannu yasa ya dauki Wani pitch color ya Mika mata sannan ya sake daukan wasu guda 3, ta juya tana kallonsa da sauri tace ” my yayah Allah inna zata Gane Kai Ka siyomin pls ka barshi nagode” d’aga kafada yayi yace ” u r right, toh muje ” nan ya juya sukaje wurin biyan kudin Yana kallonta yace ” ko chocolate bazaki dauka bah” no thanks ” daga haka ya biya kudin suka fice . Cikin mota ta saka jalbab din yayi mata kyau sosai Amma tsayin ya mata yawa haka ta nadeshi ya tada mota suka dau hanyar AYA zuwa maraba.
Shigowar inna kenan daga gidan tana sanye da Wani hadadden abaya me shegen kyau ya Kara fito da kyaunta tana zaune mmn nana na mata sannu da zuwa ta zauna bisa tabarma tace ” wai har yanzu yaran nan Basu iso bah ” mmn nana tayi murmushi tace ” kinsan go slow din maraba Nyanya bare yau asabar sai a hnkli” Kuma fa hakane don yanzu na wuce hanyar Baki Gani ba baya tafiya Sam wllhi ” sannu malama kinsha hanya kamar da wasa kin wuni a can ” hmm..kedai bari wllhi gaba d’aya jikina yayi sanyi mmn nana inayi Ina tuna sulei nace idan ya dawo kwanan nan Kuma ya zanyi ” dariya mmn nana tayi tace” sai a sake daurawa man tunda naga kin damu dashi, Allah na tuba malama ai Koni yau na samu mijin aure zuwa zanyi a raba wannan kaddararren auren dake kaina bare ke da tun farko shi zaki aura Bai nufa ba sai yanzu Allah ya kawo Kuma kina wasa da damar ki ” shiru inna tayi ta buga tagumi, mmn nana ta cigaba da cewa ” karki manta akoda yaushe ke kike min nasiha akan cewa na yarda da kaddara duk yadda tazo min toh ke bakiyi tunanin cewa kema kaddarar ki kenan, wata kil ma shine Nasarar rayuwarki malama ki duba lamarin nan dai, wannan bawan Allah hakika masoyinki ne na kwarai duk da bansan tarihin rayuwarda kukayi a baya ba Amma na tabbata Yana tsananin kaunarki” inna ta gyara zama tace ” insha Allah yau zan Baki tarihin rayuwata Amma Kuma mmn nana kinsan me, yanzu da mukaje a raba auren sun bukaci waliyai sannan zasuyi bincike nan da sati biyu toh shine gaba d’aya nake ganin bamu kyauta ba, shine hnkli na ya kasa kwanciya Gani nake tamkar naci amanar Sulei hakkinsa zai kamani ” girgiza kai mmn nana tayi tace” tabbas! Tunda nake ban taba ganin mace me tsananin biyayya da bin dokokin aure irinki ba malama, kinsan a raina Ina kiyasta irin zaman da kikayi da baban hajjo, toh ki duba ynxu da Baku tare ma kina rike da mutuncin aurenki da martabarsa bare a ce Yana kusa. Lallai ranar da ya dawo ya samu kin auri Wani lallai yai babban asara a rayuwarsa, wato duk namijin da ya sameki yaji dadi sai ya godewa Allah, Amma ni Ina ganin Babu laifi tunda dai baban hajjo ya tafi yau shekara 6 Bai nemi inda kuke ba Koda yake bamusan ko Yana raye ko ya mutu bah, zamanki haka nan akwai cutarwa cki malama Kuma ke kika gayamin irin ni’imomin addininmu sauki gareshi Babu tsawwalawa donhaka kije kiyi aurenki Allah yasa Hakan shine Mafi alheri da Nasara a rayuwarki ” Amin ya rabbi nagode Mamn nana yanzu dai anraba auren yace Ina gama idda zamu saka rana ni Kuma nace ya bani lokaci” Allah ya Sanya alheri ya nuna mana lokacin, gara da kk ce masa haka Kinga a hnkli sai ki fara shiri koh, iyye malama amarya ” ta karasa maganar cikin zolaya murmushi inna tayi tana Jin Wani iri a cikin zuciyarta. Sallama akayi hajjo ce ta shigo a guje saura kadan ta Fadi ga jalbab din ya mata yawa a guje ta fada jikin inna tana dariya ” kaji Wani rashin hankali kamar wata yarinya ke bakisan kin girma bane kk wannan guje gujen , Ina yayan naki ” mmn nana na dariya tace ” sanyin idaniya yau angama makaranta kenan Masha Allah ” nifa ban gama ba mmn nana nadai Yi rabi” Ayman ya shigo da sallama Yana rike da bag nata Yana tafiya a hnkli nan suka amsa masa inna tana salati tana tafa hannu ” yau naga rashin kunya, shi bawan gidanku ne da zaki bar masa jaka ya dakko Miki, Maza tashi ki karba kafin makeki kaji min shashanci ” murmushi yayi ya karasa kusa da inda suke mmn nana ta shimfida masa darduma ya zauna, hajjo kuwa Bata rai tayi ta karbi jakar nata ta wuce daki tayi kwanciyar ta. Bayan sun gaisa yace zai tafi inna tace ka bari a kawo Maka ruwa man ” no inna nagode ana kirana a gida ” “nagode sosai dan gidan inna , bari a kawo Maka mutumin naka kunun aya ” tana gama magana ta tashi Bai tafi ba ya tsaya don Yana matukar son kunun aya a rayuwarsa da can baisan dashi ba sai da yazo Nigeria yasan dadinsa, inna ta zuba masa dayawa a Leda ta fito ta Mika masa Yana godiya ya karba tare da musu sallama ya tafi. Hajjo ta fito rike da zobo tana karewa inna kallo cike da mamaki tace ” inna wai biki kika je ne wannan kwalliya haka ” tabe Baki inna tayi batace komai ba ta tashi ta shiga d’aki, ta juya gun mmn nana suka gaisa nan suka fara hiran yaushe Gamo har aka kira sallah sannan suka tashi.
Ayman ne gaban Ammi ya sunkuyar da Kai kasa yana kallon teburin cin abinci Aman kuwa galala yayi Yana kallon Ayman gani yake tamkar a film wai Ayman ne ya fara soyayya harda rike hannun mace, a karo na biyu Ammi ta sake tambayarsa ” y’ar gidan waye a fadin Abuja” shiru yayi still ” Bada Kai nake magana bah prince” kiyi hakuri Ammi bansan sunan mahaifinta bah ” toh me tsakaninku ” Babu komai Ammi ” Babu komai amma ka iya rike mata hannu cikin jama’a ko kunya bakaji, shin ka manta Kai din wayene? Ko ka manta cewa duk inda kuke idona na biye daku, so kake sultan ya tada maganar auren naka koh Ayman ” runtse Ido yayi a hnkli yace ” am sorry Ammi insha Allah Hakan zakai sake faruwa bah” shikenan zan baka last chance tunda baka taba aikata hakan ba maybe u have a reason, amma Ina son tunasar da Kai cewa koma y’ar gidan wayene a kasar nan matukar ba jinin sarauta bace forget it , ka fini sanin rules na masarautar taku donhaka u have to be very careful” daga haka ta tashi a fusace tabar dinning room din. Numfashi Ayman ya sauke tare da ajiye fork din dake hannunsa ya tura plate din abincin gefe, Aman ya kallesa Yana murmushi yace ” Mr Romeo so bro u r dis romantic ashe bansani bah ” tsaki yaja Yana Shirin barin wajen Aman ya make murya yace ” sorry Sweetie” girgiza kai Ayman yayi yabar wajen Aman na dariya ya tashi yabiyo bayansa don Neman tsokana. a falonsu suka zauna a tare Ayman na rike da Kansa dake Sara masa nan kuwa Fauzan ya fito rike da cup da pain killer a hannu ya Mika masa Babu gardama ya karba ya hadiye tare da sipping na ruwan kadan ya maido masa cup din tare da gyada Kai alamar godiya Wanda Babu Wanda yasan hakan sai Fauzan din kadai, Aman yace ” nazo ka bani labarin yarinyar, u know am amazed wllhi wai har Kai zaka iya kula mace da wannan uban girman kan naka ” murmushi Ayman yayi tare da lumshe idanu ya jingina da jikin sofa din, Aman ya kallesa Yana jiran amsa Fauzan ne ya sake shigowa ya nemi waje ya zauna ” wai kana Ina lokacin da ya tafi zancen Fauzan ” murmushi Fauzan yayi yace ” ni bansan ya fita bah “

Back to top button