Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 17

Sponsored Links

*talented writers forum*

*17*

*Birnin Sennar*

Gimbiya Fulani ce xaune can kuryan d’aki tayi jugum tana jimamin abinda ke Shirin faruwa ckn masarautar tasu a da can ita din ta kasance mace mara Maida hankali kan son Mulki Kuma tun asali ita mutum ce Mai saukin Kai da karfin Imani wacce ke karban duk kaddarar da ta sameta da hannu biyu wannan karon abin ya dan tab’a xuciyarta, tana tausayin Ayman kwarai saboda yawan hakurinsa gashi har yau Bai kammala karatu ba bare asa ran zai iya dogaro da Kansa duk da cewa suna da arziki amma muddin bai tashi ya tsayawa Kansa ba gaba abin zai zama abin gorantawa ga abokan gaabansu. Shiru tayi tana tunanin rayuwar d’an nata gashi Babu shakuwa tsakaninta dashi sai irin Wanda baa rasa bah, Gani take gara ya cigaba da rayuwa a can najeriya ya fita daga tsabgar masarautar tasu don Batason jefa rayuwarsa ckn hatsari, sallama akayi jakadiya ce nan ta Bata izinin shiga dama can Babu Mai shiga d’akin daga sultan sai ya’y’anta sai Kuma jakadiya, ” Allah ya taimaki uwar d’akina y’ar sarki jikan sarki matar sarki Kuma uwar sarki Mai jiran gado , yanzu na samu labari cewa maigirma sultan be amince da bukatar tasu bah amma har ynxu suna kan bakarsu, a takaice dai hukuncin sultan Ake Jira wasu ko sunce yarinyar tazo tana can bangaren an ajiyeta ana mata hudubar tsiya ” numfashi Fulani ta sauke tare da lumshe Ido ta rasa abin fada bakinta ya mata nauyi, dakyar ta budi Baki tace ” Allah shi kyauta,” cike da mamaki jakadiya ke kallonta tace ” haba ranki shi dade yanzu bazakiyi Wani abu akan Hakan bah, Babu Wani matakin da zaki iya dauka akai, me zai hana ki gana da Mai martaba sultan ki nuna masa rashin dacewar abunda suke Shirin aikata duk da cewa Babu Wanda yasan me a zuciyar sultan ” murmushi tayi ” kaiya… jakadiya bazaki gane ba nagaji da wannan masarautar taku, kullum Ayman kullum Ayman tamkar shi kadai ke ckn masarautar, gara su Yanke hukuncin ko Ayman zai samu ya inganta rayuwarsa yayi rayuwa irin na kowa Babu takurawa, shi yaron nan kullum cikin biyayya yake bashi da ra’ayin Kansa, Babu abunda zanyi akai face adua Allah yasa hakan shine Mafi alheri a rayuwarsa ” ” Ameen ya Allah Amma idan ya tabbata da nafi kowa bakin cki” kiyi hakuri jakadiya mu nemi zabin Allah shiyasan dai dai yafimu sanin abunda ya dace ” jinjina Kai jakadiya tayi tana Kara ganin girma da kimar Fulani a idonta lallai wannan duniya baya gabanta.

A can bangaren Gimbiya Suhail kuwa tana xaune ckn Wani rantsetsen falonta Wanda ba kowa ke shiga ba ga kayan marmari anjerasu birjik tana xaune ckn shiga ta alfarma gefenta kuwa sabreena ce kallo daya zaka mata ka tabbatar tana ckn bacin rai , Hanifah ce ta shigo da tare da masu mata hidima nan Gimbiya Suhail ta d’aga hannu suka juya suka fice falon ya rage daga ita sai sabreena da Hanifah , bayan ta gabatar da gaisuwa ta nemi waje ta zauna ” ranki ya Dade Ina fatan komai lafiya da wannan Kiran gaggawa haka” cike da bacin rai ta fara magana ” nasan kinsan komai so kike ki nuna Baki sani ba saboda Baki goyon bayan abunda nake so, toh ki sani ya xama dole ku bani hadin Kai dama ke da Failuzah ku kuke bani ciwn Kai amma wanna karon baxan lamunce bah, ya zama dole ku bani goyon baya muhada Kai mu cinma wannan buri namu saboda dama ku kukafi cancanta kawai dai kaddarace tasa Fulani ta rigani haihuwan d’a namiji Amma bisa al’adah ya’y’ana ne ya kamata su gaji wannan karaga donhaka ban amince ba Kuma baxan taba bari Ina raye wannan masarautar ta koma hannun wasu ko ince d’akin wasu ba nawa d’akin bah, ya zama dole Aseem ya gaji wannan masarauta idan ya mutu y’ayansa su cigaba ko y’ayan daya daga ckinku ” murmushi Hanifah tayi daman tasan zancen donhaka ta fara magana cikin nitsuwa” haba ranki ya dade ai kin riga kin gama magana tunda kikace kaddara tasa Umma Fulani ta rigaki haihuwan d’a namiji, toh meyasa bazaki bar kaddarar ta tafi ahakan bah, abunda kinfi kowa sanin cewa babban da namiji shike gadon karagar Mulki Kuma kinsan Hakan shin meyasa zaki biyewa son zuciya da….” Ke!…ki dakata haka, dama nasan bazaki amince ba donhaka ba shawarar ki nake nema bah ” tana magana cikin tsawa da bacin rai, Hanifah Bata Karaya ba tace ” Meyasa kike son raba kanmu, meyasa kinfi son…” Tass…ta ajiye mata Mari tana faman huci Hanifah ta tallabo kumatun cikin bacin rai ta tashi tsaye tace ” insha Allah burinki bazai taba cika bah ” fuu..ta juya Suhail na faman Kiran sunanta amma ko waigowa batayi bah ta fice daga bangaren nasu gaba D’aya. ran Gimbiya Suhail yakai kololuwa wajen baci duk cikin y’ayanta tafison Hanifah da Aseem amma kwata kwata raayinsu baizo daya bah saboda Hanifah kullum akan gaskiya take tana da matukar adalci da tsoron Allah gaba daya halayen mahaifinta ta dakko hatta yanayin halitta don tana tsananin kama da sultan Abu Hanifah donhaka ne yasa ake ganin kamanninta da Ayman saboda shi Bai debo hasken Fulani bah, sabreena kuwa ckn zuciyarta kamar ta shake Suhail take ji saboda Neman rabata da masoyinta da take kokarin Yi, bayan ta samu ta shawo kan matsalar har ansaka musu rana amma dare d’aya mahaifiyarta da Gimbiya Suhail suna neman wargaza mata farinciki akan nasu burin , Aseem da Babu abunda Yasa gaba irin Neman mata a hakan suke son ta rayu dashi a matsayin miji, tirr da hali irin na Gimbiya Suhail da son abin duniya da son Mulki. Batasan lokacin da taja tsaki har ya fito a fili bah, kallonta Suhail tayi cike da bacin rai tace ” mutuniyar banza ana nuna Miki hanyar lafiya kika kafe kika nacewa yaro kamar mayya, ana nema Miki zaman lfy da dan uwanki kina Nuna bacin rai toh nida ke ne a gidan nan kindawo kenan sai ranar auren naku da Aseem zaki bar nan ,Kuma kika kuskura kika kira wancan Mai girman kan tsiya sai na mugun bata Miki rai tashi ki bani waje mutuniyar banza kawai” tashi tayi ta koma masaukinta ta fada bisa gado tana rusa kuka Babu Mai lallashinta.

_____*Abuja Nigeria*____

Karon farko a rayuwarsa ya Maida hankali kan karatunsa ya dage sosai Yana karatun jarabawa abunda Bai taba ba a tarin rayuwarsa, kamar yadda inna ta fada mishi haka ya dage da adua kullum sai yayi istihara akan Neman zabin Allah dangane da lamarin auren nasa nan kuwa yaji saukin bacin rai da damuwar dayake cki a kwanakin baya , Yana Maida hankali sosai sai gashi kuwa Yana Jin dadin jarabawar duk lokacin da ya shiga hall haka zai rubuta ya fita ckn kankanin lokaci har ila yau bashi da aboki ko budurwa fauzan shine abokinsa inna kuwa ta zame masa Wani bangare na rayuwa saboda akoda yaushe Yana Jin dadin nasihar da take masa Yana karuwa sosai da ita ta bangaren zaman duniya da wasu abubuwan da suka shafi addini, Yana matukar ganin girma da darajarta duk da cewa yaso Kai mata ziyara amma ta hanashi yadau alwashin wataran dole yakai mata ziyara baxata . Gobe Yana da exams donhaka Yana rike da handout nasa Yana nazari da yamma Yana xaune a harabar gidan bisa kujerun da aka tanada saboda Shan iska, Mal sule ne tare da maigadin suke zaune can bakin gate suna hirarsu ta nuna kamar yadda suka Saba, Mal sule yace ” ni kuwa da zan samu wataran na dan fita na zagaya garin nan ko Allah zaisa na Hadu da iyali nah” ” Mal sule ai Ina ganin kokarinka wllhi, gaka da mota a hannu Kuma anbi an nuna Maka gari bazaka fita kullum kana Neman iyalinka ba ka tsaya zance kullum sai faman hawaye idan ka tunosu ” murmushi yYi yace ” haba Kai kuwa..kar ka manta wannan mota amana ce agareni idan ba tsabgar alhaj ba Babu abunda zai aikata da ita face Allah ya tambayeni..” Allahu Akbar! Kaji masu gaskiya da rikon amana, toh Allah na tuba yanzu don…” Ah ah ban tari numfashinka ba malam, amma ai Amana amana ce Kuma a ce na dauki mota na tafi Allah ya kiyaye Wani tsautsayi ya auko laifin waye kenan? , Kagani koh saboda haka gara dai na cigaba da hakuri sai idan Allah yasa Alhaji baya gari ko yayi tafiya haka sai na shiga motar kasuwa na dan zagaya ko Allah zaisa a dace ” dariya maigadin yayi yace ” Kai gaskiya samun mutane irinka sai an tona” ” suna nan kuwa dayawa a doron kasa, haka nan matata haka halinta yake mutuniyar arxiki ga tausayi da sanin darajar dan Adam, wllhi saboda halin tausayi irn natane yasa ta auren ta rabu da danginta da kowa nata..” girgiza Kai maigadin yayi Yana jimami Mal sule ya cigaba da share hawaye ” Allah sarki Hajjo uwata yanzu nasan ta girma , ko Yaya take oho sai Allah, ”
“Hajjo! Ayman ya maimaita sunan nan ya juya ya kurawa mal sule Ido Yana son yin tunani akan hiran nasu nan da nan ya rufe littafinsa , Wani bangare na zuciyarsa na cewa kawai kaje ka sameshi ku tattauna, zumbur ya tashi tsaye ya fara tafiya zai tunkari inda mal sule yake yana ckn tafiya kenan “Ayman! Cak..ya tsaya ba tare da ya juya ba, ” kazo Ina son ganinka yanzu ” Ammi ce ta fito daga cikn gida fuskarta Babu walwala ciki ko kadan daga haka ya juya yabi bayanta.

*Muje zuwa wasa farin girki*

Back to top button