Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 54

Sponsored Links

Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 54….. Juyawa Aliyu yyi ya fice daga dakin ba tare da yace masa komai ba, Khaleel ya bisa da kallo yana ci gaba da dariyarsa ya girgixa kai yace “naga ta ynda xa’ayi wnn abun dae” Washegari karfe tara Khaleel ya shigo dakin Mami cikin farar shaddarsa ya xauna yana kallon Mami yace “Mami ta gama shiryawa ne, ina son mu dawo da wuri don akwae inda xa ni” Ikram dake daure da towel tana shafa mai tace “ni dae sae na gama kallon Shaun the sheep kafin mu tafi, kaga an kusa farawa” ya galla mata harara yace “wa xae jira ki ki kalla wani shaun the sheep” ta murguda masa baki tace “kai” ya juya yana kallon Mami yace “Mami ki gaya mata ta daina murguda min baki watarana xan cire mata hakori idan tana min hka” Ikram tace “sannunka ba sae ka cire min ba” Mami tace “ban hana ki rashin kunya ba Ikram” kmr xata yi kuka tace “shi ya fara min fa Mami” Mami tace “da’alla rufe min baki ki rufe min maina ki ajiye” Ikram ta rufe man kmr xata yi kuka ta mike tana kallon kayan da Mami ta ciro mata ta sa, riga da skirt ne na atamfa sae Hijab, ta rungume hannayenta ta juya masu baya tace “ni ba wnn kayan xan sa ba Mami, ni wando da riga xan sa wnda yayana ya siya min” Mami tace “baxa ki sa ba,” hawaye ne ya cika idonta ta jawo vest dinta xata sa, Mami tace “shiga bayi kisa kayan” daukan sauran kayan nata tayi ta shiga bathroom ta sa ta fito. Khaleel ya rufe bakinsa da hannu yana kallonta, ta fashe da kuka tana kallon Mami tace “wllh nasan dariya yake yi Mami, ni yake wa dariya” Mami ta daka mata tsawa “fita ki ban waje, jarababbiya kawae ihu yyi maki ba dariya ba” ta fice daga dakin da gudu ta sauka kasa ta dinga rusa kuka, jummai ta fito daga kitchen da sauri tana tambayarta me ya faru, ko kallonta bata yi ba sae kukanta take kmr xata shide, Khaleel ne ya sakko rike da makullin mota da hijabinta ya karaso kusa da ita cikin falon yana murmushi ya xauna yana kallonta yace “ni dae ban maki dariya ba wllh” hararansa tayi ta mike xata bar wajen ya riko hannunta da sauri yace “to srry xan jiraki ki gama kallon cartoon din ki wllh” komawa tayi ta xauna tana share hawayenta, karfe goma suka bar gida suka kama hanyar suleja bayan Mami ta rakosu har bakin mota, surutu kawae Ikram ke masa cikin motar shi dae sae um um yake ce mata, ta gaji don kanta tayi shiru, can kuma tace “ae yayana yace min yana xuwa gidanmu Allah yasa mu gansa yau” ya juyo da sauri yana kallonta yace “wani yayanki” tace “yaya Aliyu mana” ya gyada kai snn yace “yaushe ya gaya maki yana xuwa gidan ku?” tace “kullum yana ce min ya je” Khaleel ya tabe baki bae ce kmae ba, sha daya suka isa gida, yana gama parkin ta bude mota ta fice tayi cikin gidansu da sauri, wanke wanke ta tarar Ammi ke yi ta rungumeta tana cewa “Ammina gani na xo” Ammi ta mike tsaye tana murmushi tana kallon yar tata tace “ke dawa kuka xo da safe hka” Ikram tace “ni da yaya Khaleel muka xo, Mami na gida, Ammi ina Abbana?” Ammi tace “ya fita kasuwa, je ki kice masa ya shigo mana” Ikram tace “to” snn ta juya ta fita, Ammi ta bi ta da kallo a sanyaye, ssae ta lura Ikram ta nutsu ynxu, tabarma ta dauko ma Khaleel ta shimfida masa, suka shigo gidan a tare da Ikram ya xauna kan tabarma snn ya dukar da kansa ya gaida Ammi, ta amsa da fara’arta tana tambayarsa Mami, yace “tana nn lfya, Mama” Ammi tace “shekaran jiya ma wan ka ya xo nn” Ikram tace “bana ce maka yana xuwa ba” murmushi kawae yyi bae ce komai ba, awansa daya a gidan yace xae tafi gun wani abokinsa dake wajajen anjima da yamma xae xo daukar Ikram, Ikram ta rakasa bakin xaure tace “yaya Khaleel kar kaxo da wuri fa” “to” kawae yace mata ya wuce, snn ta dawo cikin gida, Ammi ta sa ta taje ta gaida su baba Habu, da maman altine ta dawo, ko minti goma ba’ayi ba ta dawo gidan tace ta gaishesu, Ammi tace “da sauri hka Ikram, to ki tafi gun Abbanki ki gaishesa, daga nn sae ki shiga gidansu Mmn Shafa ki gaishesu tunda ba nisa, idan kina dawowa sae ki shiga gidan yakumbo ma ki gaisheta” Ikram tace “ni baxan je gidansu Shafa ba” Ammi tace “sbda me” tace “sbda xagina mama shatu da kawu Na lado xa suyi idan na je, hka ma ranar da naje take ce min karuwa, kuma da na tambayi Mami meye karuwa tace min prostitute ce” Ammi tace “meyasa kika tambayeta Ikram” Ikram bata ce komai ba, Ammi tayi shiru na wani lkci snn tace “to tashi maxa kije ki dawo” Ikram ta mike ta sa takalminta tace “to amma dae baxan je gidansu shafa ba” Ammi bata ce komai ba ta bita da kallo har ta fita daga gidan. Karfe biyar da rabi na yamma Khaleel ya xo tafiya da ita, sae taji kmr kar ta rabu da Amminta, Khaleel ya ba Ammi sakon da Mami ta bada a kawo mata snn suka bar gidan da Ikram wajajen karfe shidda.
[2/25, 08:35] Zjy:

Back to top button