Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 49-50

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*49&50*

 

 

…….. k’arfe 12:15 shariff yayi parking a compound d’in gidan mus’ab”be fitoba yazaro wayarsa yakirashi”bugu biyu ya d’auka yana fad’in hamman Amaan sai dubu ta taru”Amamakin mus’ab sai yaji sautin sanyayyan murmushinsa”hmm !da Alama Abokinah bakinka da mgn ko?”kaga gani nan a compound d’in gidan ka pls kasameni Ina sauri zamuyi mgn “be jira cewar saba ya kashe wayar…. ba’a fi cikakken minti ukku ba mus’ab ya iso gaban motar yana sanye da jallabiya Ajikinsa”sharif ya kallesa yana yatsina fuska yace”me kakeyi har 12 ta wuce bakayi wanka ba??dariyar rainin wayo mus’ab yasaki kafin yace “karka manta ba tuzuru bane ni irinka?”yawanci week end haka nake zama sbd gani ga muradin raina “Allah yataimaka Ina kammalawa na fito daga wanka ka kirani da kafin nan ne bazan iya d’auka ba….banza d’an iska! saika fad’ama wanda beda muradin ran nasa”yo gaka nan “uhmm kake gani ko?”Eh mana tunda miskilancinka ya hanaka kula mata so kakeyi saika tsofe ta yadda bazaka moru ba….naushin daya kaimasa yasaka yayi shiru yagoce yana dariya”kafin yace”meke damunka duk kayi y’ar rama ga k’asumba tacika maka fuska??shariff yatab’e baki murya bbu wasa yace”pls jeka shirya muje ka rakani wajen Amaan”na mana booking d’in jirgin dazai tashi k’arfe 2 na rana….da kallo mus’ab yabishi har yayi shiru “Aransa yace” Anzo wajen”Afili sai yace”Amaan d’in duka yauba satinta guda ba da komawa shine zakaje??kaga pls idan zakaje kaje zan jiraka 15 minit kasaka kaya muje muyi Azahar sai mu wuce”uhmm zance zakaje kenan?”Eh shi zanje d’an sa Ido”Ada na d’auka shak’uwace nayi da Amaan sai yanzun na fahimci shak’uwa daban SO ma daban”sati guda ka duba kaga yadda nayi sbd rashinta”tabbas mus’ab idan babu Amaan bazan iya rayuwa ba”wlh ko kallonta wani namiji yayi nine kawai nasan menakeji Azuciyata”na shirya tararta na fad’a mata Abinda ke raina”banaso mu baro garinsu batare dana san nan gaba kad’an zan zama mijin taba….shafa idanuwansa dake waje mus’ab yayi sbd ya tabbatar shariff miskilin daya sani shine ke cewa idan babu mace bazai rayuba??wata dariyar shakkiyanci yasaki yana rik’e ciki…. mutumin naku Atake ya had’a rai cikin jin haushin mus’ab yace”look mus’ab! Akan me zaka tasani gaba kana mun dariya kamar wani me tab’in hankali”sbd nace maka ka rakani?”idan bazaka jeba shikenan fita na wuce…..matsalata dakai kenan Abokinah”shine saurin hassala”da raina da lafiyata dole nayi dariyar murnan wai yau kaine ka Ajiye zafin kai kake cewa kana son wata”Aidama ni tuni nasan son Amaan kakeyi wlh “na kuma gane hakanne sbd zafin kishinta dakake nunawa k’arara”k’aramin misali kan Dr mansoor,gashi nan sbd ita baka shiri dashi”tsaki shariff yaja yace”mus’ab pls jeka kabani waje”mansoor kuma muddin be dena sontaba wlh na saka arufesa k’aramin Aikina ne….ah ah hakan bazai faruba”tuni yajima da hak’ura da ita sbd ya fahimci sonta kakeyi”fatanmu Allah yasa itama ta soka”sbd nasan dai Abokinah me irin kamalarka da wuya yayi kwantai”yak’are maganar yana fita daga cikin motar yana dariya”shariff ya sauke Ajiyar zuciya yana danne danne Awaya,can ya lalubo vedio d’in da yayiwa Amaan “k’uri yayima wayar yanata kallonta besan lokacin daya furta”yarinya me d’an k’aramin baki surprise d’in ki zanyi, saidai ki ganni gudanku yau insha Allah “yafad’a yana murmushi lokacin datake yin gwalo cikin wayar”Adaidai lokacin kuma vedio d’in yak’are”ya lumshe idanuwansa yana dafe saitin zuciyarsa”Afili yace”kece babyn nan ta mafarkina Amaan”kece kike kirana da *SALFAD* yanzun na gano Hakan….sabbatu kawai yakeyi shikad’ai har mus’ab ya iso cikin shirinsa zazzafa dake nuna sud’in wayayyun y’an boko ne kuma masu ji da kansu”motsin shigowarsa cikin motar yasaka shariff nutsuwa ya maida wayar Aljihun wondonsa”mus’ab yace”kaga na jima ko?”Ina can Ina fama da noory da k’yar nasamu ta yadda”Amma ni gobe zan dawo gaskiya”Nima Ai haka”saidai ko idan Amaan tak’i yadda nadawo”dariya mus’ab ya k’yalk’yale da ita yana fad’in wlh kana burgeni Abokinah “wato ba k’aramin dacewa kukayi da mutuniyar ba”uhmm! kawai shariff yafad’a yana bama motar wuta suka fice daga cikin get d’in gidan “saida suka tsaya a hanya sukayi sallar Azahar sannan suka wuce Airport”sai wajen k’arfe 2 da y’an mintinah jirginsu yatashi bayan driver d’in Ammi yazo yatafi da motar shariff”suna cikin jirgin Amma hankalinsa na wajen Amaan sai yaji fargaba”sbd yana gudun ya zubba Ajinsa da girmansa yace”yana son k’aramar yarinya kamarta ita kuma tace bata sonsa”wanda yanada yak’inin saida ya balaga Aka haifi Amaan”, Amma ga ikon Allah ita yakeso”idan kuwa yatuna had’uwarsa da ita a tashar motar Abuja saiya k’ara girmama ikon Allah”shidai mus’ab na kallonsa”sai wajen hud’u saura suka sauka”directly wata had’ad’d’iyar hotel shariff yaka musu suka sauka”mus’ab ne kawai yaci Abinci Amma shi beci Abinci ba “sbd ba Abincin bane Agabansa”suma Acan sanyi Akeyi sosai”sai waya yakeyi da body quards nasa yana musu masifa basu isoba shi har ya iso”shidai mus’ab d’an kalllone yana gani yana kuma darawa”sai wajen biyar saura sannan suka iso shima sbd gudun da suka dinga zubawa”da motoci ukku suka zo manya kuma na gani na fad’a”cikin wacce tafi kowace tsada da kyau Anan sharif da mus’ab suka zauna a back sit”driver yafara jansu”yayinda motoci biyu ke biye dasu Abaya…duk inda suka gifta sai An kallesu,wasuma na zaton ko wani shugaba ne”directly Anguwar su Amaan suka nufa”sosai tsarin Anguwar yaburge sharif dayake kallo ta glass”bugawar zuciyarsa tayi daidai da lokacin da driver d’in yatsaya gaban get d’in gidan su Amaan yana danna horn”sai Akayi sa’a yusuf na kusa”fitowa yayi yana kallon manyan motocin”Atake ransa yabashi shariff ne”yana wannan tunanin body quards d’in shariff su shidda suka fito da bakak’en suit Ajikinsu suka bud’e masa k’ofar motar….cikin nutsuwa yazuro dogayen santala santalan k’afafuwansa Awaje ya fito cike da aji had’e da shan k’amshi “yusuf yasaki murmushi yakaraso yana fad’in” yaya shariff kune tafe haka?”wannan zuwan bazata,k’ilanma waccan rigimammiyar bata san da zuwanku ba ko?”yafad’a yana k’ara girmama matsayin shariff Aransa”dan inda be sanshiba zai d’auka wani shugabane ke tafe”gaba d’aya d’aid’ai kun mutanan dake layin suka bisu da kallo”sharif yak’araso gaban yusuf yabashi hannu sukayi musabuha”bayan sun gaisa suka gaisa da mus’ab dake tsaye gefen shariff “Anutse cikin cool voice yace”bata san da zuwana ba surprise d’inta zanyi”okay muje ciki mommy na nan daddy ne yad’an fita”yafad’a yana yin gaba shariff da mus’ab suka biyosa Abaya”yana ganin body quards nasa zasu biyosu yadakatar dasu da hannu….. Amaan na sanye da riga da wondo na wani orange d’in material me zanen bak’i da red”ta Aza suwaita d’in da shariff yatab’a bata da pasincap d’insa “tana rik’e da teddy d’in ta tanata zuba k’amshi na irin turarukan da shariff yasiya mata,ba k’aramin kyau tayiba dukda fuskarta batada walwala” ta biyo hamma sadeeq tana kukan shagwab’a sbd ya d’auki wayarta zaije wajen wani party sbd yayi ruba da wayar….wani irin bugawa taji k’irjinta yayi”hakan yasa ta dakata da tafiyar datakeyi”sadeeq na kallonta yace”kima koma ciki duk wata rigimarki bazan bakiba”d’an Aramun d’in da zakiyi shine baki iyawa…..numfashin Amaan yanemi tsayawa cak !sbd daddad’an k’amshin turaren Fahad shariff da hancinta yashak’o mata”ta zaro idanuwanta waje lokacin data hangosu abayan hamma yusuf”sakin teddy d’in hannunta tayi ta zura Aguje ta wuce interest d’in shiga cikin gidan “mommy!! Mommy!! lafiya sarkin hankali kike k’walamun kira haka?”ta fad’a tana fitowa daga cikin kitchen”Amaan na murmushi tace”hamma shariff ne yazo shida Abokinsa”da gaske kikeyi?”wlh kuwa”maza kije kitchen ki had’o ruwa da lemo da snacks d’in nan kikai musu sit room”tana fad’in hakan ta wuce cikin parlourn “Amaan na k’ok’arin shiga kitchen taji sallamar mus’ab”gabanta ya tsananta bugawa ta waigo batare data kallesuba ta Amsa murmushi na kok’arin sub’uce mata”ranki yadad’e irin wannan tarban Abokinah zai samu?”cewar mus’ab yana kallonta yana murmushi “yayinda hamma yusuf yanufi k’ofar parlourn yace”bissimillah ku shigo”Amaan kuwa kasa mgn tayi jikinta sai b’ari yakeyi tasaci kallon shariff”Amamakinta ya kasheta da wani killer smile yana mik’a mata hannunsa”ta janye idanuwanta tana nok’e kafad’arta”had’e da nuna masa wai ga yaya mus’ab nan yana ganinsu”shidai mus’ab kallonsu kawai yakeyi”babu kunya shariff yatsaya gefenta yana fad’in kinsan Allah koki kalleni kona koma inda na fito”kasa mgn Amaan tayi”dan yau yabata mamaki dataga yana walwala sosai”mus’ab shidai dayaga Abin yafi k’arfinsa saiya wuce yabi bayan yusuf”Ahankali tace”kaida kake fushi dani shine kazo kuma?”yabi d’an bakinta da kwallo Anutse yace”laifinkine Amaan kinaso kawai ki dinga mun wasa da zuciya ko?”d’ago kanta tayi ta kallesa ya d’age mata gira guda”ta kauda kanta da sauri tana sunkuyyar wa”nida nazo gaba d’aya na Amsheki kidawo wajena shine hardamun tunin Ina fushi dake?”da sauri tace”da gaske hamma zaka tafi dani?”sai kin kalleni na baki Amsa “yafad’a yana matsowa dab da ita murya can k’asa yace”muje ciki *salfad* da sauri ta maimaita salfad tana kallonsa”ya matso da fuskarsa saitin tata ya hura mata iskan bakinsa”ta rintse Ido da sauri sbd jin kasala da mutuwar jiki”shi kuwa cikin sanyayyar muryarsa yace”muje ki rakani mu gaisa da mommy”saiki dawo ki fad’amun meyasa kike son wahalar da zuciyata salfad? yafad’a yana k’ok’arin duk’awa da nufin yazare takalmin k’afarsa sawu ciki….hamma muje basai ka cireba”bece komai yashigo da sallama cikin parlourn, Amaan na bayansa”mommy dake zaune kan kujerah da hijab Ajikinta ta Amsa da fara’a tana masa sannu da zuwa “yaduk’a k’asa ya gaisheta “ta Amsa tana tambayar ya Ammi “bayan ya zauna kan kujerah mommy ta harari Amaan tana fad’in haka Ake tarban bak’i?”babu komai mommy Aimu ba bak’i bane cewar mus’ab”hakane Amma dukda haka aka muku ruwa ko? “hamma yusuf ya mik’e tsaye yace”muje can parlourn bak’i “Amaan ta mik’e tsaye tana turo baki ta fita”bata jima da fitaba suma suka fita”lemon roba da ruwan roba masu sanyi ta zuba cikin tray”Aranta tana Addu’ar Allah yasa shariff yasha sbd tasan lemon kwali kona gwangwani yakesha”suma wannan An Ajiye sune sbd bak’i “snacks kuma sana’ar mommy ne harda dambun nama tanayi na biki ko suna”kuma Ana shigowa gida Asiya”komai duk ta Aza saman tray d’in ta d’auka ta nufi parlourn bak’i”shariff ne kawai tasamu zaune kan carpet ya jingina bayansa Ajikin kujera”da Alama yafi buk’atar zama hakan”bayan tayi masa sallama ta Ajiye tray d’in Agabansa”sannu salfad”dawo nan kiji wata mgn “Ina wai yaya mus’ab d’in?”yafita zaiyi waya da matarsa”oya zoki zauna”nidai babu ruwana dakai”sbd Allah hamma shine zan kira sau 12 kak’i d’auka ko?”har kuka nayifa….ni kuma na zuci nayi Amaan “nok’e kafad’arta tayi tak’i zuwa tana duk’e gaban tray d’in”wato yanzun gudun zuwa wajena kikeyi kome?Allah idan kika bari nataso baki zoba d’aukarki zanzo nayi…ta d’an d’ago kanta da mamaki”yes! keda bakida wanima nauyi”kasa mgn tayi sbd canjin data gani yana mata”ga sabon suna daya saka mata, wanda sai yanzun ta fahimci meye ma’anar *SALFAD* lura datayi zai tashi tsaye yasaka da sauri ta tashi tsaye tazo ta zauna gab dashi tanata zuba masa shagwab’arta son ranta”shidai yana zaune yanata kallonta yana jin kamar ya janyota jikinsa saita masa shagwab’ar da hujja”can kuma sai tayi shiru”menene yasa kikayi shiru?”bakai bane kak’iyin mgn”kuma bakaje Aka maka Aski ba,bayan idan Aka maka gyaran fuskan kafi yin kyau” fushin da kikeyi dani da wanda nakeyi dake duk yahana naje Agyaramun”k’in mgn tayi sai ta jawo tray d’in ta zuba masa ruwa a cup ta mik’a masa”ya Amsa yana fad’in thanks “bud’e bowl d’in dake cike da dambun kaji tayi”k’amshin yadaki hancinsa”ga snacks suma cikin wani plate me d’an girma”bayan yasha ruwan ya kalli Abinda ta Ajiye masa yace”kamar dama kinsan da zuwanmu”ta d’an turo baki tace”shine baka sanar munba ko hamma?”inaso nayi surprise nakine da Abu guda biyu shiyasa”nayi na farko saura na biyu”to miye na biyun?”d’okin me kikeyi zakiji soon”Ina Ammi nah da fatan tana lafiya?”lafiya qlau tana gaidaki”Ina Amsawa sosai”yaya sadeeq da Abdallah basuce agaidani ba?basu ceba, sbd basusan inda na tafi ba”sadeeq kuma daga yau na haramta miki ce masa yaya sbd yanzun k’aninkine”ban ganeba?”beyi mgn yasaka spoon ya d’ebi dambun naman yakai bakinsa kafin ya tsareta da mayatattun idanuwansa cikin husky voice yace”sbd Ina fatan na zama miji Agareki SALMAHHHHHHH! shiyasa na soke daki kirasa da yaya”I love you so much my Amaan”pls do you love me???

Sharhi

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button