Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 33-34

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*33&34*

 

…….bayan sallar isha’i Amaan na zaune kan sofa a bed room d’in Ammi “sai b’ata rai takeyi sbd tanta jiran sheriff yadawo daga masallaci Amma shiru be dawo ba”idanuwanta duk sun ciko da k’wallah tana jiran abu kad’an ta fashe da kuka”har teddy d’in tata ta wullar da ita gefe guda”Ammi dake lazimi bayan gama shafa’i da wuturi datayi duk tana Ankare da ita”tama d’auka ko wani Abinne shariff d’in yakoma yimata”can dai Amaan tace”Ammi ki kira hamma dan Allah “akan me Amaan?”yadawo gida haka nan mana”kinga dare yayi kar mugaye su kamashi….dariya Ammi tayi tace”insha Allah babu Abinda zai faru dashi”nasan wani uzurinne ya rik’eshi yazun kinga yadawo”to Amma Ammi basai ki kirashi ba?”shikenan kinga ga wayar can ki d’akko mun”batayi mgn ba ta tashi ta d’akko wayar dake saman bed ta mik’a ma Ammin…. shariff kuwa bayan yagama sallar isha’i kiran gaggawa ya riskesa hakan yasa ya nufi office “saidai besan dalili da tunanin Amaan ke mak’ale Acikin zuciyarsa ba”gaba d’aya yayi suku suku dashi”yau bbu wannan yawan d’aure fuskan dayake yawanyi”mus’ab duk yana lura dashi”har suka iso office d’insa zasu shigar da wasu baya nai Awani file haka shariff ya zauna yana dai Aikin kawai”can ya d’auki wayarsa da nufin yakira Ammi yace”Abama Amaan”saidai tunanin to meye zaice ma Ammin na dalilin kiran Amaan d’in yasaka ya Ajiye wayar”gashi beson yamata k’arya,kuma yasan halin mus’ab dayaga yakira yace”Abata iskanci zaita masa”Ahaka kiran Ammin yashigo cikin wayarsa”wanda yayi mamaki sosai”har gabansa yafad’i daya tuna ko ciwon Ammin yatashi?”sai kuma yaga Ai ga sadeeq dake likitah Agidan….ganin wayar na niyar tsinkewa yasaka ya d’auka”tun kafin yayi mgn yaji sautin siririyar muryarta”yad’an lumshe Ido yana fad’in uhmm”hamma Ina kaje tun d’azun baka dawo ba?”kofa bacci banyiba Ina jiranka”ko kana so irin wa’annan mugayen suka maka?….. tattausan murmushi yasaki yana k’ara mak’ala wayar gefen kunnansa yace”baki gajiya da shirme Amaan”Ina office nakusan dawowa karkiyi bacci saina dawo”to hamma zan jiraka”to fad’amun yaushe kikeso nadawo sai in dawo?”nidai yanzun nakeso”okay to shikenan “yafad’a yana yanke wayar”mus’ab da yayi suman zaune yana kallonsa da saurarensa”ya kauda kansa”yana k’ok’arin mgn yaga shariff ya mik’e tsaye yana fad’in Abokinah da safe mun Ida zan wuce gida”baki bud’e mus’ab yace”Akan wace matsala zaka koma gidan? yafad’a yana mamaki sbd yasan kan wannan Aikin shariff beji be gani koda wajen kasuwancinsa Ake kiransa be zuwa Amma gashi yanzun zai tafi sbd mace”macen ma k’aramar yarinyar da bata hayyacinta”kasancewar yaji wayar da sukeyi da Amaan dukda ba komai yajiba….banida wata matsala mlm”Amaan ce tasaka rigimar saina dawo yanzun, idan kuma bandawo ba tadinga fushi kenan”wai kana nufin gudun fushin Amaan yafi Aikinka mahinmanci kenan?”ya tab’e baki yana fad’in zancen kakeso”daga haka ya d’auki phones nasa yanufi k’ofa “mus’ab ya mik’e tsaye Aransa yace”yau da gobe kenan”saidai Ayanzun be shirya tsokanar saba sai Ank’ara kwana 2″sallama sukayi kowa yashiga mota yanufo gida…. Amaan kuwa bayan sun gama wayar tafara gyangyad’i , Ammi tace taje saman bed ta kwanta”babu musu taje ta kwanta”bata jima da kwanciya ba bacci yayi Awon gaba da ita”wajen k’arfe 9:7 pm shariff yashigo cikin parlourn”sadeeq da Abdallah na zaune suna kallo”gabansu saman center table kayan ciye ciye ne irin na y’ay’an gata masu dashi”duk sannu suka masa ya Amsa yana k’arema cikin parlourn kallo yaga bbu Amaan “beyi mgn ba directly yanufi k’ofar bed room d’in Ammi”knocking yayi sau kusan biyu Amma shiru”hakan yasa yaturo k’ofar yashigo”ya sauke numfashi yana kallon farar kyakykyawar fuskarta tanata bacci rabin gashin kanta zube saman pillows”ta takure jikinta waje guda da Alama sanyi takeji”motsin ruwan da yaji Abath room yasaka ya fahimci Ammi na ciki”kai tsaye wajen ward d’in gefen dama yanufa yabud’e “sbd nan yafahimci kayanta suke ciki”safa da hula sabuwa ya d’akko ,kafin ya rufe ward rope d’in yana tunanin tayaya zai saka mata?”yabi y’an dumur dumur d’in k’afafuwanta da kallo jajir dasu”wanda tunda yake da ita be tab’a tsayawa ya kalli k’afafuwanta ba sai yau”socks d’in ya Ajiye gefen k’afafuwan nata”kafin ya matsa ya d’ago kanta ya gyara mata gashin kanta ,kafin yasaka mata hular ,hucin numfashinta na sauka saman damtsan hannunsa”karan hancinta yaja d’an murmushi na sub’uce masa”hakan yayi daidai da Ammi ta turo k’ofar bayin”da sauri ya janye hannunsa cikin basarwa”yayi tsaye yana shafa kansa “tun kafin tayi mgn yace”Ammi ga socks d’inta nan nizan je na kwanta saida safe”to shikenan Allah yakaimu”daga haka yajuya yafita”ta zauna gefen bed d’in tana girgiza kanta tasaka ma Amaan safar”kafin ta wuce ta shirya ta kwanta itama…..duk irin sanyin da Akeyi saida shariff yayi wanka kafin ya kwanta, tunanin Amaan ya masa sallama har bacci ya d’aukesa”saidai yau yayi mafarkin yarinyar daya jima be koma mafarkin taba “tana tsaye gabansa da eye glass tanata murmushi tana fad’in *salfad* daga yau bazaka koma ganina ba zan koma inda na fito”ta fad’a tana masa bye bye tana matsawa nesa dashi”sai tsaida ita da hannu yakeyi Amma bata saurareshiba”yana ganin ta kusan b’acema ganinsa yayi saurin tashi zai bita”saidai wayam bbu ita….karki tafi! karki tafi!! shine Abinda yake nanatawa yana juye juye saman bed d’in harya bud’e manyan fararen kyawawan idanuwansa “da sauri yatashi zaune sbd ganin gari yayi haske”yaduba Agogon dake manne jikin bango “6:38am”Ahanzarce ya sauka daga saman bed d’in yanufi bath room”be jimaba yafito yasaka jallabiya ya kabbara sallah”k’arfe 7:45 am yafito cikin zazzafan wanka ya sakko k’asan “ya Aza suwaita saman k’ananun kayan dake jikinsa yana zuba wani irin fitinannan k’amshi”yayi kyau matuk’a “Abdallah yabishi da kallo Aransa yace”dama nine yaya! yana sakkowa Amaan na fitowa daga d’akin Ammi”tana sanye da riga da wondo na kanti , ta Aza suwaitar daya barmata Asama “ta sanya pasincap d’insa daya bata kwanaki”gashinta tuli guda data d’aure ya tsaya iya dokin wuyanta”hannayenta duka na zube cikin Aljihun suwaita d’in”tana sanye da plate shoes da sock”tanata zuba sanyayyan k’amshi “ba k’aramin kyau Amaan tayiba”kallonta kawai Abdallah keyi sbd tunda tazo gidan be tab’a ganin tayi irin wannan kyawun ba…..Atare itada shariff k’irjinsu yabuga! suka kafe juna da Ido”ta kwab’e fuska tana kawar da kanta ta nufesa”shi kuwa be fasa kallontaba ,saidai yak’i yin mgn”da Alama y’an miskilancin na’a kai….hamma shine jiya baka dawo ba saida nayi bacci ko?…ya d’auki kusan second 10 cikin shan k’amshi yace”babu gaisuwa balle yanatashi sai k’orafi zaki faramun dashi ko?? turo baki tayi tak’i yin mgn “saiya shareta yana danna waya yanufi d’akin Ammi da nufin ya gaidota”yana k’ok’arin shiga sadeeq yafito”rungume juna sukayi suka gaisa”shima Abdallah yataso ya gaisheda shariff”Amaan kuwa taji haushin sharetan dayayi sai kawai ta nufi wani d’aki da ake sauke bak’i tayi kwanciyarta”saida ta daidaici shariff yatafi sannan ta fito ta dawo parlourn”shi kuwa tunda yabaro d’akin Ammi yaketa baza ido Ina zai hangota? Amma bbu Alamar ta”saiya fita sukayi waya da mus’ab”bayan sun gama wayar har zai wuce parking lot kawai zuciyarsa ta umarcesa daya koma cikin parlourn”Anutse ya shigo da sallama”k’irjinta yabuga ta kauda kanta “gashi ita kad’aice zaune cikin parlourn”kinajin Ana sallama kinfi k’arfin ki Amsane?”wai meyasa idan baki bani wahalaba bakyajin dad’i ne Amaan?”yak’are maganar yana zama gefenta”tayi sauri zata tashi tana jan zuciya”ya rik’e gefen rigarta yana fad’in koki nutsu kona mareki”nika cikani mana”tunda baka damu dani ba”nid’in ai damuwar kikayi dani ko?”yafad’a yana tab’e baki ya zaunar da ita gefensa da k’arfi “har saida ta saki k’aramar k’ara “shareta yayi ya had’e rai yak’i yin mgn “sai ta sassauta murya tana fad’in hamma kayi break fast?”Amaan wai bazaki gaisheni ba da gaske?”ya canza topic d’in”cikin shagwab’a tace bafa hakane”sai kuma ta sakko k’asa tace”ina kwana?lafiya qlau “kai hamma bbu murmushi kawai ka Amsa Ahaka?”kin rainani ko? k’in mgn tayi ta koma ta zauna”hamma! uhmm”kasaka Amun lalle naga wata dashi cikin TV “kibari sai next week”ni Allah yau nakeso”tafad’a tana kuka had’e da shure shuren k’afafuwa kamar y’ar 5 yrs na rigima”besan lokacin dayace ya isaba zan yiwa Ammi mgn jummai takaiki Anjima “yana fad’in hakan ya mik’e tsaye”itama saita tashi tsayen”hamma nah Allah yatsare yabaka sa’a”Amma tunda baza kayi break ba nima haka”bece komai ba yanufi dining area d’in”itama sai biyosa tayi”bayan sun zauna itace da kanta ta zuba musu komai”suna ci tana masa surutu”shidai yana sauraronta Amma yak’iyin mgn”suna gab da kammalawa sadeeq yashigo cikin parlourn shida wani Abokinsa suka zauna kan kujerah suna mgn”shariff ya kalli Amaan murya bbu wasa yace”bana so kije parlourn can sai wancan yaron yafita”to hamma zanje wancan d’akin nayi wasa da y’ata na goyata ko?”kansa ya gyad’a mata”yana d’aukar tissue yagoge bakinsa itama ya goge mata nata”hankalinta nakan zobban daya bata”tashi muje”bbu musu ta mik’e tsaye suka baro dining area d’in”har bakin k’ofar d’akin yarakata,sai bayan ta shiga yanufi cikin parlourn da nufin ya wuce”Annan Abokin sadeeq ya gaishesa”ya Amsa tare da cewa sadeeq biyoni”to yaya”yafad’a yana tashi tsaye yabi bayan sa”suna fitowa shariff ya had’e rai murya Akausashe yace”daga yau karka koma shigowa da kowane namiji a main parlour “idan parlourn bak’i ko naka zaka kaisa ka kaisa Amma banda na cikin gida…. Akan me yaya?akan haka naga dama ko bazabi bane? ni banceba”naga dai koda zasu gaisa da Ammi fa?”wai sadeeq ni kakema musu?”kayi hak’uri yaya zan kiyaye”banza yamasa ya wuce yabar masa k’amshin turarensa “sadeeq fuskarsa babu walwala yakoma ciki”bayan tafiyar Abokin nasa yashiga d’akin Ammi tana zaune gefen bed tana shan magungunan ta”yanayin yadda taga fuskarsa tasan yanada damuwa”kusa da ita ya zauna yana fad’in dama Ammi bayan bani gidan nan yaya shariff yakafa dokar kar wani namiji yashigo?”bangane ba?”bayani yamata”kafin yace”wlh raina yabani sbd wannan Amaan d’in yasaka dokar nan “ni wlh Antakurani sbd wata”kasan dai bana son haka ko?”idan kasab’awa shariff tamkar nika sab’amawa ko Alh”dan yanzun shine matsayin mahaifinku”shikenan Ammi kiyi hak’uri”Amma ni Aganina tund….shiru yayi sbd shigowar Amaan cikin d’akin saima yatashi tsaye yafita……
Kwanci tashi Asaran me rai”sadeeq yasha hutunsa yafara Aiki cikin nassara A sabon Asibintinsa da shariff yagina masa”yayinda Amaan itada mutumin nata Ayi tsiya Ayi dad’i”yanzun suna mgn sama sama da Dr Mansoor Amma ba kamar daba”kuma har yanzun be dena son Amaan ba”Amaan kuwa watanta hud’u kenan cif da had’uwarta da shariff “tuni mlm yagama rubuce mata Alkur’ani me girma ta shanye, Ana kuma cigaba da bata magungunan neman tsari da karya sihiri”Amma har yanzun shiru”batun kishinta da shariff ke nunawa sai Abinda yayi gaba zamuce….. Ayau take juma’atu babbar rana! tunda Amaan ta tashi takejinta sukuku kamar marar lafiya”ga yawan tsoron mutane tanaji”koda mgn aka mata saita furgita”ga wani irin ciwo da kanta keyi tun safe har la’asar be dena ba”taci uban kuka ta k’oshi”Ammi da shariff sunyi rarrashin duniya har sun gaji”daga k’arshe kunsan halin mutumin naku yayi fushi ya k’yaleta”Ammi ta kira sadeeq ta waya bayan fitar shariff yazo yadubata yamata Allurai”tana kwancen ta tsiri fitinar sai Ammi ta kira mata shariff ta waya”Ammin tace”bazata kirashiba”shine ta dinga uban kuka”Ammi ta girgiza kanta kawai domin itama tafara bata haushi”saita shareta”dak’yar Amaan tayi shiru”bbu jumawa bacci me nauyi yayi Awon gaba da ita…..gab da magrib shariff yashigo fuskarsa bbu walwala”ya zauna yana yima Ammi sannu da gida”saidai bata masa zancen Amaan ba”yaga kuma ta d’aure fuska”yanaso yace tana Ina yana jin shakka”ba masallaci zaka jebane?”Eh Ammi “yafad’a yana sosa k’eya”can ya mik’e tsaye yace”ya jikin Amaan d’in?”da sauk’i bacci takeyi”bara naje natasheta tayi sallah ba’a son baccin magrib”beyi mgn ba yana dai tsaye yanata jin fad’uwar gabar da baisan dalilin jintaba”sai kuma gefen girarsa ta dama ta dinga fat !fat!!…… Ammi na tura k’ofar Amaan natashi zaune a furgice tana furta innalillahi wa inna ilaihir raju’un!! mommy kina Ina?nayi wani irin mugun mafarki…..✍️

zazzafan sharhi ko aji shiru

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
Vip grp 1000
via 2230373842 NABILA ALIYU UBA BANK

Ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

Idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button