Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 1-2

Sponsored Links

❤‍‍ MISKILI NE‍❤‍

 

Story & written
by mommyn fareesa

*GODIYA* Alhamdulillah!godiya ta musammun ga Allah S W A daya bani Aron rai da lafiyar fara wannan littafi lafiya,yah Allah yadda na fara lafiya Allah kasa na gamashi lafiya “tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi mohd S A W da Ahalinsa da sahabbansa

*GARGADI* kirkikirarran labarine banyishi dan wani ko wata ba aguji sauyashi ta kowace siga sbd hakkin mallakata ne

Dedicate to All my fans

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

Page 1&2

KD state
……….. wayayyun y’an mata ne su kusan 4 suna zazzaune A gaban wani table cikin wani had’ad’d’en garden na Alfarma”wanda sai d’an wane da wane ke iya zuwa wajen dan shak’atawa da d’ebe kewa”kowa na harkan gabansa Babu ruwan wani da wani….seerat ta kalli k’awarta dake daga tsakkiyarsu zaune tace “faree wai lafiya naga yau bakida walwala”ga shisha Ankawo ko kallo bata isheki ba??…..na kalli wacce aka kira da fareedah! doguwa ce marar jiki me mugun haske na bleeching”tayi kitso da gashin Doki Daya zubo saman kafad’arta”tana sanye da riga da wondo da suka bayyana Ainahin suran jikinta”yatsun hannayenta na dama guda biyu tana sanye da zobba na gold”yayinda ta dad’e da eye glass black”sai kamshi ke tashi Ajikinta”ba zamu iya kiran fareedah kyakykyawaba”kuma bazamu iya kiranta mummunaba”cost tanada aji,yanga ,dason gayu shiyasa ake mata kallon tanada kyau….muhibbah dake gefe tana taunar chiweengum tace”nima kusan Abinda na fahimta Atare da ita kenan”numfashi fareedah ta sauke ta zare eye glass nata ta Aza saman table d’in gabansu”d’aya bayan d’aya take binsu da kallo kafin cikin damuwa ta juya idanuwanta tana fad’in tunda na ganshi a super market jiya da yamma na kasa nutsuwa seerat”guy d’in yamun takowace fuska”irinsa nake da tsarin na mallaka Amatsayin mijin Aure nah”inason ingarman namiji me aji da iya d’aukar wanka”saidai wannan ya wuce iya tunanina friends”pls ku bani shawara taya zanyi bincike Akansa harna samu yasoni na mallakesa??”dukda nasan Aiki ne me wuyar gaske Agaba na”sbd jiya na tsorota da irin shan k’amshin daya dinga yi”na lura MISKILE NE na bugawa ajarida”tunda agogon daya d’auka ta fadi Ina gefe na d’auka na mik’a masa cikin jan hankali”Amma ko kallona be yiba “sai k’amshin turaren daya tafi yabarmun”Ina tsaye wajen Ina tunani cikin ma’akatan dake wajen suka zo suka Amshi Agogon”naso ace ko muryansa naji….Nadiya tayi murmushi tana girgiza kanta kafin anutse tace ” *Fahad Shariff* sanannan mutum ne kowa yasanshi sbd dukiyarsa a garin nan”kece dai da baki dad’e da dawowa Nigeria ba ke baki sanshi ba”wai dama shine take nufi?”cewar seerat”eh shine sbd ni naga sadda yafita tanata kallonsa”ku kuma kuna can layin da turaruka suke…pls Nadiya yanada mata?”dariyar shakkiyanci nadiya tayi tana girgiza kanta tace”yasin k’aton tuzuru ne! Amma karki damu zqn binciko miki duk Abinda kikeson sani game dashi kafin kisan yadda zakiyi ku Jone”karki manta kefa maza ke bi kina yarfasu fareedah?”to miye na damuwa?”karki manta kobai soki sbd Ajinkiba zai soki sbd matsayin mahaifinki…. gaskiya bakisan waye Fahad Shariff ba Nadiya!cewar seerat “yayinda fareedah tayi tagumi idanuwanta na hasaso mata kyakykyawar doguwar fuskar *Shariff* inaso ki bamu dama nanda 2days zamu zo miki da duk wasu baya nai Akansa insha Allah “saidai wlh inada labarin mugun MISKILE NE! harma wasu na zaton ko Aljannah ta Auresa sbd ko Ina yake baya mgn”idan kuma yayi maganar Bata wuce d’aya zuwa biyu”ga Rashin fara’a da bashida ita”gwabron numfashi fareedah ta sauke tana mik’ewa tsaye tace”kutashi muje driver ya maidamu gida”zuwa jibin pls ina son jin komai kansa”wlh ba wasa nake muku ba Ina bala’in SON Shariff pls”karki damu faree baby”suka fad’a cikin tausayawa suna tashi tsaye”sai zuzutata sukeyi da wasa kyawunta ai bazai k’ita ba”wanda Abinda suke fad’a ba shine gaskiya Aransuba”suma suna tare da ita ne sbd dukiyar mahaifinta da matsayinsa da kuma kasancewarta wayayya”kasancewar fareedah dake jigon tafiyar batayi walwala ba kocin wani abu awajen shiyasa suma gaba d’aya sai basu ci komai ba suka bita kawai”sai wulakanci take yiwa driver d’inta ,shidai yayi shiru inda sabo yasaba da wulakancinta Dana k’awayenta”wanda duka watan ta guda da sati biyu da dawowarta k’asar….kai tsaye G R A yanufa dasu”adaidai katafaren gidan me girma deputy governor yayi horn”get man yabude musu get”sai da securities suka duba mutanan dake cikin mortar sannan suka wuce ciki………
Dan Allah Abokinah ka Amince da gayyatar nan taka da akayi kaje ku tattaunah da manyan mu pls”kasan gaba d’aya bbu wani da muke tunk’aho dashi garin nan da sauran wasu garuruwan kamar kai Acikin y’an CID! kuma wannan Aikin daza kayi wlh ba k’aramin taimakon mutanan garin nan zai yiba ya kuma karesu dayin shugaba mugu”wlh danine nike da kamalarka bazan ma rok’i ka Amince kaje kasanya hannu ka Amshi wannan Aikin ba”da nine kai tsaye zan Amsa naje nayi” wlh ! wlh!! konayi rantsuwa bazanyi kaffara ba,na tabbatar sai kayi nassara dan nasan duk girman kanta dole idan tayi Arba dakai ta rikice ta k’yasa”ta haka kai kuma zakayi Amfani da wannan dama kamana bincike yadda yaka mata”sbd haka dole ka Ajiye duk wannan MISKILANCIN naka my man”cewar mus’ab yana kallon kyakykyawar fuskar Abokin nasa *Fahad Shariff*! pls say some thing mana my guy…..Masha Allah! shine Abinda na furta dana kalli fuskar *Fahad Shariff* wato *miskilin namiji* ko gezau beyiba yanata danne danne a laptop d’insa”Babu wata Alamar dake nuna yasan wani abu wai fara’a ko dariya”kamarma bbu shi Acikin office d’in”ko kuma da bango mus’ab ke mgn”irinsu sharif sune mazan da akema lak’abi da one in million…..lolx”sbd guy d’in yahadu ta ko Ina ya had’a abubuwa da yawa”sanye yake da farin kaya irin na y’an CID”Wanda ba k’aramin haska choco skin nashi sukayiba”red lips nasa gaba d’aya suna cikin bakinsa yana tauna”yayi nda ya tsare laptop d’insa da manyan fararen idonsa da Alamar wani abu me mahinmanci yakeyi Aciki”duk wanda ya shigo cikin katafaren office d’in nasa daya k’awatu bazaiso ya fitaba kodan sbd irin daddad’an k’amshin dake tashi Aciki”wanda asalin k’amshin na mamallakin office d’in ne”dan ko yaya ya zauna waje sai Anji k’amshin turaren sa me Dadi da kashe gangar jiki” *fahad Ibrahim Shariff* dogone wankan tarwad’a”shiba fari ba ,ba kuma bak’i ba”yanada murd’add’en jiki”hade da manyan k’wanji”da suke sakama marar gaskiya jin shakkarsa….lolx! kanafa jina sheriff?kaga yamma tayi sosai bana so nayi latti noory tayi fushi dani(matarsa)”ni aganina goben kaje Abujan kuyi mgn”saidai kasan dole saita mota bata jirgi ba”sbd tsaro ba tsoro ba!idan kadawo mayi mgn zan saka asamomin contact nata da duk wani bayani game da yarinyar”saidai ka fara koyon firan masoya da zafafan kalamai na soyayya daga yanzun ko?”yafad’a cikin tsokana yana mik’ewa tsaye,sai kallon agogon dake manne jikin bango yakeyi”yayinda Shariff kamar bbu shi a office d’in”mus’ab be kuma damuba sbd yasan halin Abokin nasa”bakin k’ofa yanufa ya murd’a handle d’in k’ofar……kasan A tsarina na tsani karya dame yinta”for what reason da zanyi soyayyar k’arya da wata?bayan samun mafitar mu sai nayi yaya da ita kenan??ya furta cikin tsayayyar murya, me d’auke da nagarta da dad’in Amo….kafin ya shafa zagayayyen b’akin sajensa zuwa katuwar sallayar dake tsakkiyar goshinsa yana sauke numfashi anutse”yafara kokarin tattara tarkacensa da nufin yatafi gida”Wanda kuma bashida niyar koma kula mus’ab “shi kuwa mus’ab dariyar shakkiyanci yasaki yana kallon sheriff yace”girmanka ne Abokinah kayi yadda kaga dama”idan buk’atarmu ta biya sai kayi mata Jan Ido ,kayi kuma blocking nata ba shikenan ba?”in kuma ta maka saiku Jone musha biki kawai”dukda ni kaina yanzun al’amarinka yafara bani tsoro kanada 38-40 yrs Amma baka damu da y’a mace ba”kodai da gaske baka lafiyar ne kamar yadda wasu ke fad’a??mitsuww! idan wannan zancen banzan yakawoka pls you can go…dariya mus’ab yadinga b’abbakawa yana rike ciki”yayinda Shariff yatabe baki yana mik’ewa tsaye”mus’ab ya tsagaita da dariyarsa yana fad’in bazanso ku Jone da y’ar mugun mutumin nanba sbd baku dace da itaba”dukda ni sau d’aya na tab’a ganinta”naji dai Ance bbu tarbiya ,ga girman kai data azawa kanta”sbd haka nidai Ina ganin ta wannan hanyar ne kawai zamu iya kamo bakin zaren”sannan kuma wannan itace damarka daka samu bana so kayi sakaci da ita”inaso kaje kayi tunani”kuma kasan dai zuwanka Abuja dole tunda manyanmu keson ganinka “kuma dole ka Amsa kiransu”daga haka mus’ab yabude k’ofar yafita”sharif yayi shiru yana nazarin kalamansa”kusan shudewar mintina 4 yaja gajeran tsaki ya d’auki breaf case nashi da safar fuska yasaka ya fito haraben wajen ya shiga cikin wata had’ad’d’iyar mota”wacce kudinta zasuyi 40 million…… kasancewar yana yin Aikinsa na sirrine shiyasa beson kowa yasan meye aikinsa na gwabnati”yafiso kawai Aci gaba da masa kallon d’an kasuwa kawai”kai tsaye Anguwar sarki ya nufa”inda gidansa yake”yana yini acan Amma gidan Amminsa yake kwana…..gidane me kyau irin na wayayyun y’an gayu”komai na more rayuwa da Amfani akwai Acikin gidan”bayan yayi parking ya cire safar fuskar ya fito daga cikin motar”me gadinsa nata yimasa kirari”hannu kawai ya d’aga masa yayi gaba”kasancewar akwai ma’akata guda biyu maza dake kula dako Ina na cikin gidan”illah dakin baccinsa ne kawai basu shiga su gyara, sbd Akwai sirrikansa dake Aciki”hakan yasa shine ke gyara Abinsa”ko Ina k’al fes dashi Amma uban gayyar sai yatsina fuska yakeyi sbd shifa yadda aka gyara main parlour d’in be masa ba”kasancewar Allah yayishi da wata irin masifaffiyar tsabta ta tashin hankali”kai tsaye master bed room nasa yanufa”wow Aljannar duniya ! komai na cikin d’akin milk colour ne”gefen bed d’in ya zauna ya Ajiye wayoyinsa gefe da brief case nasa”anutse yafara zare takalmin k’afarsa sawu ciki”Atake santala santaln dogayen k’afafuwansa jajir suka bayyanah tamkar na jinjiri sbd yadda suke shek’i da daukar Ido”kamar baya taka k’asa”gaba d’aya fuskar Nan tasa a had’e take musammun idan yatuna bbu hanyar da zaibi yayi bincike gidan ” *Alh isah tafashiya* saiya kullah soyayyar k’arya da y’arsa”bayan shi mgn kota mintina biyar ce tunda yataso yasan kamshi bata tab’a hadashi da wata y’a mace ba idan aka cire family nasa”haka Nan tun kafin yaga yarinyar yaji mugun tsanarta Aransa”Agogon dake daure a damtsan hannunsa ya duba 6:35pm”ya mutsa fuska yayi yana Jan tsaki sbd ganin yashiga lokacin wankansa Dana zuwa gidan Amminsa ya ganta”dukda idan yaje da b’acin rai yake dawowa”Amma mahinmancinta da matsayinta awajen sa ya wuce na yayi biris yaki zuwa dubata”kasancewar yana bama lokaci matuk’ar mahinmanci Arayuwarsa”Agaggauce ya mik’e tsaye cikin nutsuwa ya nufi bath room…….kimanin shud’ewar mintina 20 yafito d’aure da farin towel iya k’ugunsa”wani na rataye saman wuyansa yana goge ruwan jikinsa”turaruka kawai ya shafa yasaka milk d’in gogaggiyar jallabiya yafita”sbd befi saura 2 minit ba Atayar da sallar magrib…..yajima a masjeed d’in yana Azkhar har akayi sallar isha’i dashi”sannan ya koma gida ya d’auki mota yanufi Anguwar rimi….yana driving d’in ne cikin nutsuwa wayoyinsa biyu nata ringing Amma yayi Biris dasu dan yanzun ba lokacin d’aga wayarsa bane”Ammi ce kawai idan ta kirashi ko meye yakeyi zai Ajiye ya d’auka”horn yayi Akatafaren gidan mahaifinsa *Alh Ibrahim Shariff* k’aton gidane na Alfarma Anguwa guda, ya tsaru ya kuma k’awatu da kayan more rayuwa da jin dad’i”parking d’in motarsa yayi anan ma securities nata masa barka da zuwa be Amsaba saidai ya d’aga musu hannu ya nufi interest d’in shiga cikin gidan”Azuciyarsa yana tunanin idan su Abdallah basu dawo gida yanzun ba zasu sani”da wannan tunanin yayi sallama muryar can k’asa ya shigo”fuskarsa bbu wani Annuri ko fara’a,koma had’e rai yayi sbd yadda iftihal ke washe baki tana masa sannu da zuwa had’e da gaishesa”Arzik’in ya kalleta bata samu ba balle harya Amsa mata gaisuwar tata….. Ammi ta bishi da kallo tana girgiza kanta ta amsa sallamar tasa tana tsaresa da ido ,sbd ganin zai wuce be gaishe da mijintaba ,ga kuma y’arsa daketa gaishesa yamata banza”fahad ne? sannu da shigowa”cewar Abba dake zaune gefen Ammi hamshakiyar mace ,kuma dattijuwa da jin dad’in rayuwa yab’oye shekarunta”da k’yar sheriff ya iya had’a harrufa ukku wajen furta! nine ,ina ,wuni?”lfy qlau ya Aiki?”Alhmdllh ya furta agundure yana nufar bed room d’in Ammi”ta mik’e tabi bayansa”yana zaune kan sofa yana danna waya ta shigo da sallama”yad’ago ya Amsa fuskarsa bbu walwala yanata cin magani da k’yar kamar Ammasa tilas ya furta “Ammi meyasa wai any time mutumin nan yana nan ne?ban sani ba”na rasa me bawan Allan nan da y’arsa suka kashe maka arayuwa sheriff?”ta nuna tana sonka kace baka sonta”meyasa bazaka Amsa gaisuwar taba?”kasani bazan maka tilas ba domin kayi Aure”sbd mahaifinku yabani wasiyar karna tursasaku Akan Abinda ba dole bane”nasan kuma Aure lokaci ne” Amma kodan sbd matsayinka yaka mata ace ka Ajiye iyali”kamar yayi kuka yayi shiru sbd yatsani Amasa zancen Aure”ta zauna gefen bed tanata kallonsa mutum har mutum Amma bashida iyali “ita kanta addua takeyi masa kullum Allah yasa ya had’u da wacce zai so ba wacce zataso shi ita kad’ai ba”dan tanada tabbacin idan ya Auri wacce ke sonsa baya sonta zatasha wahalarsa”musammun Akan wannan miskilancin nasa da rashin fara’a da yake dashi”kimanin mintina 5 da shigowar Ammi d’akin kansa na ak’asa yace”Ammi bana son ganinki cikin damuwa ko son wani yasaki Adamuwa, inada hujjojin k’in sonki da mutumin nan Amma baki fahimta”ina rok’onki duk dad’in fira karki sake kisanar dashi labarin daya shafeni koya shafi mahaifina”gobe insha zan tafi Abuja da Asuba…iya nan yayi shiru sbd maganar ta masa tsawo”ta sauke numfashi tana nazarin kalamansa Ahanakali tace”Allah yakaimu lafiya”ubangiji yabaka nassara ,ya kuma tsareka da tsarewarsa sheriff”Allah ya jik’an mahaifinku”ta fad’a murya na rawa ta mik’e tsaye ta fita”sbd duk idan ta ganshi saita tuna Abbansu”kasancewar sheriff yafi sauran y’an uwansa kama dashi”shi kuwa tabe baki yayi Aganinsa inda tadamu da mutuwar mahaifinsu da bazata k’ara Auren wani ba…..kansa yad’ago sbd jin muryar Abdallah (autansu) ya shigo yana wak’ar music”yasha Aski irin na samarin zamani wad’anda kejin kansu Asama…..saidai Arba da yayi da babban yayansu yasaka jikinsa yafara b’ari da sauri ya fita yadawo yayi sallama”shi kuma ya amsa be koma mgn ba”k’asa Abdallah ya duk’a ya Aza kansa saman cinyoyin sheriff ya shagwabe fuska kamar d’an yaro yana fad’in yaya pls inata nemanka tun dqzun,na kuma kiraka sai kaki d’auka”pls kayi mgn mana”banza yamasa yature masa kansa yasan dama idan Abdallah na masa haka kud’i yakeso wajensa”Abdallah na kok’arin koma yimasa mgn yaji k’arar shigowar message awayarsa”da sauri yazaro wayar yana hasashen kud’i ne yayan nasa yatura masa”Aikuwa sune 500k”ihun murna yayi”sheriff yaja gajeran tsaki yana nuna masa k’ofa “Alamar ya fita”shi kuma ya matsa jikin bango yana turo baki yace”yaya kayi mgn mana pls”Abdallah yaushe na fara wasa dakai?”kasa mgn yayi ya juya ya fita dan sun saba da halayen yayan nasu….
washe gari misalin karfe 5:11 pm”me taksi ya Ajiye fahad shariff Atasha “sbd ya hau motar zuwa kd yadawo gida”dukda yamma tayi besan yayi dare Ahanya”Amma be gama Abinda yakaisa garin da wuri ba”sanye yake da riga amlace ash colour da jeans dark blue “saiya Aza jibgegiyar rigar sanyi dark blue yasaki hularta abaya”yadad’e da b’akin glass da face mas” fararen kyawawan idanuwansa kawai ake iya gani”kasancewar yau Antashi da wani irin sanyi”kuma dama yakanyi hakan duk lokacin dazai shiga cikin mutane mabanbanta yakan b’adda kama”simple dress ne yayi amma ba k’aramin kyau yayi ba”ga wani irin kamshi me dadi da jikinsa keyi”ko ina ya wuce saiya bar musu daddad’an k’amshin turaren sa”sai duba agogon fatar dake daure a damtsan hannunsa yakeyi”yanufi wajen wata k’aramar mota me kyau da lafiya da yaji wani na fad’in motar kaduna ce mutum goma takeci”saura mutum ukku ta cika”kok’arin yafito mutumin sheriff keyi da nufin yamasa mgn zai kama sit d’in mutum biyu”kawai yaji wani abu me kamshi ya rufe masa fuska harda saman lallausan sumar kansa datake yawan cika”hannunsa guda yasaka yana janye abun”sai yaga Ashe mayafi ne siriri me sharara pink colour”d’ago kansa yayi cikin rashin saa suka had’a ido da ita”da Alamar mayafinta da iska yaja ta biyo”kuma da alama motar itama zata shiga”haka nan yaji kirjinsa ya buga! had’e rai sheriff yayi dukda idanuwansa kawai ake gani saiya yar da mayafin”yana mamakin duk sanyin da ake tsulawa take yawo d’an wannan mayafin”sai kuma yaja tsaki sbd ganin ina ruwansa?……”kema kaduna zakije ne?yaji muryar yaron motar Abayansa yana tambayar yarinyar data duk’a ta d’auki mayafinta”wacce bazata wuce 18-20 yrs ba”tana sanye da pink d’in lace riga da siket”fuskarta bbu make up”daga ita sai mayafinta ko hand bag bbu a hannunta sai plate shoes Ak’afarta”tayi daurin d’an kwalin daya fito mata da gashin gaban goshinta”kyakykyawa ce Ajin farko”tanada gogaggiyar fata ja”ko ba’a fad’a maka ba kallo d’aya kayiwa yarinyar zaka fahimci jinsin fulanice ita”tanada wata iriyar surar jiki mejan hankali”kusan gaba d’aya mazan wajen ita suke kallo”da wuya duk wani namijin me lafiya yayi Arba da ita beji wani abu game da ita ba….saidai babu wanda tayima mgn”hasalima koda yaron yatambayeta kd zataje batayi mgn ba”kawai dai ta tsintsi kanta da shiga cikin motar”fahad shariff kuwa bema lura data shiga ciki ba”illah kawai da k’yar ya iya cewa”zan zauna sit na mutum biyu sbd bana son takura”yafad’a cikin izzah!to shikenan Alh dama saura mutum biyu”sbd haka zaka iya shiga saimu wuce”banza sheriff yamasa ya zagaya ya bude k’ofar”maza hud’u ne zaune”sai yarinyar dake rakub’e agefe ta takure jikinta gu d’aya kamar tana jin tsoron mutane”yamutsa fuska yayi sbd gaba d’aya haushi yaji tana bashi”gashi beson zama kusa da ita”kuma beson zama su sakashi A tsakkiyar su……..✍️ Tofa koya zasuyi wannan zama kuma wacece wannan y’ar beauty??

somun tab’ine wannan miskili ne yazo da abubuwa masu saka zuciya nishadi da kuma ban tausayi”uwa uba kuma zazzafar soyayya ❤️hanzarta biyan naki dan adama dake

wannan book d’in na kudine

regular grp 300
vip grp 1000
special group 2k wato 3pages in a day

zaku biya kud’in ku ta wannan acc number2230373842 nabila aliyu uba bank
kituro shaidar biyanki what’s app number d’ina 08100084251

300 kawai ake turo kati idan bakida acc amma sauran payment d’in ta acc ne

banason transfer d’in kati ko vtu photo d’in katin mtn zaki d’auka saiki turo dan allah banda kira❌

y’an nijar kutuntub’i wannan n +227 88 01 90 50
normal grp 500f
vip grp 1000f
special people 2000f

dan girman allah da darajan iyayenki karkimun mgn idan baki shirya biyaba

 

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/BZShHmdyI8pEEUcGSaYZAd
Assalamu Alaikum
Kindade kina neman wajen dazaki sayi Kaya amintattu masu kyau da quality cikin farashi mai sauki da rahusa.
Muna maraba daku zuwa MOM ANNOUR COLLECTION AND MORE
domin samun damar sayan Kaya masu kyau da aminci muna maraba da masu siyan daya ko sari delivery nationwide

Back to top button