Hausa NovelsMatar So Hausa Novel

Matar So 6

Sponsored Links

BOOK ONE*

*Page.6*

“Yau wani ya hucce gajiyarshi akan wata toh sannu Allah yasa kwallon ya faɗa raga, nan da watannin muzo cikin shinkafa.”  Duka Aman ya kai mishi yana murmushi dan dama Ahmad ya fito ɗan kazar kazar.

Related Articles

Kallon Agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunshi yayi, kafin ya ɗago kai taɓe baki yayi cikin nutsuwa yace.
“Wannan mutumin kome sai yasaka mana african time ne.”

Bai rufe baki ba, sai ga mai nasara ya turo hancin motarshi a haraban ma’aikatar, nima guri yayi ya parka sannan ya zuro kafar shi wanda yake cikin wani haf shoe, yafito sam bai cika damuwa da saka kaya kananu ba, duk kayan da zaka gani a jikinshi toh jamfane yau ma, jamfarce ruwa ashe sai takalmin shi haka ga baki ɗaya dai haɗin yau yayi tane fully, a hankali yake takowa fuskarshi a sake  ya shiga officer ɗin da sallama, amsawa sukayi  tare da mika mishi hannu musabaha yayi da Aman dan shi yake kusada, sai ya mikawa Ahmad suka gaisa tattaunawa sukayi  akan cigaban kamfanin da zasu buɗe,…

*****
Tunda muka ɗauko hanyar gida idanuna ya sauka akan mai saida ayaba, taɓa rahilah nayi cikin zolaya nace mata.
“Keee! Yaren novel can.”

Duka takaimin cike da jin haushi ta rausayar da kanta, dukda nikk’af ce a fuskarta sai da na hango murmushi akan fuskarta, a hankali tace.
“Insha Allah dakanki zaki kirani dan ɗaukar darasi, keee nifa mijina sai ya haukace akaina dan…”

Kasa tayi da muryanta dai dai kunnena tace.
“Babu abinda baxan iya mishi ba, ke har ɗaukar hotona zan natura mishi.”

Zaro Ido Rahimah tayi tace.
“Mun shiga uku, Rahilah wato baki daina ba ko?”

D’aga kafaɗarta tayi alamun oho, sannan tace.
“Ga wacce zaki tuhuma, bani ba ina zaman lafiyata ta kawo min maganar wai ga ayaba.”

Dariya nasaka har ina rike cikina, haka nayita tsokanar Rahilah ita kuma tana biye min har muka iso gida,..

Da dare kuwa muna zaune a tsakar gida muma shan iska, Malam da Umma da kuma Mama suna hira Malam yace.
“Ina son Allah ya kawo min mazaje nagari da zasu aure min, Yan ukuna dan na lura Rahilah ta ɗan fisu, rawan kai addu’a nake musu ba dare ba rana.”

… “Hmm Malam dama ina son magana dakai akan Maryam Sajida, Malam Mus’ab yayi min magana akanta nace sai na tuntuɓeka.” Inji Umma knn,

Shiru yayi na wani lokaci kaman bazai magana ba, ya kirani.
Jikina har rawa yake na isa gurinshi, nace.
“Na’am malam.”

“Kina son Malam Mus’ab ne?” ya jefa min tambayar,

A ruɗe kamar wacce akace tayi karya na shiga cewa.
“Wallahi na rantse da Allah ni bana kulashi ma, kuma malam ka tambayi su Rahilah babu ruwan da shi..”

Kuka na saka musu ina rantse rantse, “Ya isa Mamana ban ce zan miki dole ba, dama tambayarki nake shin kina sonshi ne ko A’a.”

Cikin sauri nace.
“A’a ni bana sonshi.”

“Tashi kije Allah yayi muku albarka,”
“Amin” su Umma suka ce suna min dariya,

Dakin Umma na shige na kwanta, take su rahila suka biyo ni, suna rarrashina.

Bayan tashinmu Umma take faɗawa Malam, “Na manta ban faɗa maka ba, Akwai Yar Amiran na da’awa zata aure yariman zazzau shine aka turo min da katin bikin, mi kagani akan tafiyar.”

Murmushi yayi sannan yace.
“Ba damuwa, Allah ya kaimu lokaci amma bake ɗaya zakiyi tafiyar ba ko?”

“Eh zan ɗauki Yan uku muje dasu dan zasu taimaka min sosai.” tace mishi.

“Allah ya nuna mana lokacin.” yace mata,

Haka suka cigaba da hira ni kuma su rahila suka shiga rarrashina, kar a ɗakin muna kwana wannan ɗabi’armu ce da zaran abu yasami ɗaya toh kaman ya sami saurane.

****
Yau alhamis muna tsakar gida wanki muke, malam ya shiga cikin raha yace.
“Yan uku gobe juma’a fa kar a manta da saukar da ake min.”

“Toh Malam Insha Allah zamuyi maka.”

Cikin ɗoki da muna muka gama wanki mun, kowacce ta ɗauki Alkur’ani muka fara karatu tun alhamis,

Kafin dare munyi kusan izu goma goma, zuwa juma’a kuwa muka sauke mashi, cikin jin daɗi ya kiramu ya bamu dubu uku uku, duk lokacin da mukayi mishi sauka sai ya bamu kuɗi, haka ba karamin kara mana kwarin gwiwa da kaunar mahaifinmu muke ba,

****
Kallon gidan Aman yayi tun ranar da ya gyara ko tsinke ba’a sake ko sharewa ba, tana can naɗe a gado tana chart  shiga yayi ciki ranshi na ɓace ya fincikota zuwa falo yace.
“Wallahi Hindu!!! Kina kure hakurana amma karki damu, idan nafita na samu gidan nan haka Allah zan baki mamaki.

Jin abinda yace yasa jikinta ya shiga rawa, take ta fara aikin ba ji ba gani.

Al’amarin matansu sai da buɗe wuta, ta ɓangaren Ahmad da sauki dan tunda taji batun kishiya ta shiga hankalinta. Mai Nasara ne dai ya tattara su ya watsa a kwandon shara har gara. Aneesah tana gane mishi dukda bata da lokaci tana kamanta mishi wasu abubuwan sai dai rayuwar gidan babu tsarin.Addini a ciki sabida kowacce mace bata san yaushe ne take da miji ba, balle ta sami lokacinta kamar yanda ya tsara musu, idan yana gari toh babu ruwanshi da bin ka’ida,

Ko tsarin Addini, bawai dan bai sani ba, a’a sai dai shi baxai ya dogon magana dasu ba, kawai idan ya zo miki toh yazo idan kuma kika kai kanki haka ma yayi, sam shi bai san mi ake cewa rarrashin mace ko biye mata tayita shirme ko ya san damuwarta, babu ruwanshi da haka idan kaga damuwar shi akan kasuwarcinsane ko an taɓa yaranshi.

(Nasan mi karatu zai so sanin waye ne Mai Nasaran nan da matanshi nan)

Yunus Muh’d Yunus  shine cikaken sunanshi, mai Nasara kuwa sunan Kakanshine ya ci wato Asalin Yunus mai nasara, Alhaj Muh’d Yunus tsohon sakataren gwanatine bayan wnnan matsayin ya rike shugaban zaɓe na kasa, sannan ya rike matsayin mai lura da kamfaninnikan gwanatin kasar naija,

Babban mutane da ya sanu a ɓangare aikin gwanati, da wasu fanoni na siyasa, mutane da dama sun so ya fito takaran governo ko sanata amma yaki yace shi baya ra’ayin siyasa.

Mai Nasara shine babba a gidan, Hajiya Hauwa itace uwar gida mi yara biyar uku Mata biyu maxa, Yunus shine babba sai Zainab tana aure a abuja, sai AbdulKadir yana aiki a kano, sai  Hajara, tana aure anan zaria, sau ɗan Autansu Abdullahi.

D’akin Mama kilishi kuwa kuwa yaranta uku ne, Safwan shine babba, sai  Zuwairiyya, da kuma Yar autanta Nana Aisha.

Kusan yaran gidan suna da haɗin kai dan Yaran Hajiya a hannun mama kilishi suka tashi, yayinda su Yunus suka taso a hannunta,

Yunus yana da degree uku ne a fanin kasuwanci, yana da ilimin Addini sosai ga kuma ilimin boko,  kuma dukda arzikin Mahaifinshi, baisa yayi karatu a wajen kasa ba, anan jami’ar A.b.u yayi karatunshi.

Anan ya haɗu da Ahmad da Aman wanda suma suka zo karatu, tun a shekaransu na biyu a jami’a suka fara haɗa karfi da karfe, domin kafa kansu,

Daga haka ne, fa suka mike da niman nakansu. Matarshi ta farko balkisu yar tsohon sarkin zazzau ce, kasancewar Mama kilishi mahaifiyarta yar cikin gidan sarautace kuma baban Balkisu Kawun Mama kilishine, kuma suna zumunci sosai, dan har balkisu tana zuwa gidansu mai Nasara.

Wani zuwan da tayi gidan taga mai nasara, shi knn ta haukace sai gashi duk sati sai taxo gidan dan taga mai nasara, shi kuma bai san tanayi ba, dan shi mace bata gabanshi dan yafi yarda da kasuwanci da yarda da hidimar mace.

Idan tazo gidan haka zata takuwa Mama sai ta mata hiran mai nasara, tun tana ɗauka dan burgewa take sata a gaba, sai Mama ta lura da cewa, ai balkisu ta hau bishiyar kace, akan son Mai nasara Mama batayi kasa a gwiwa ba ta tambayeta nan kuwa ta amsa, da eh.
Haka ba karamin daɗi yayiwa Mama ba, har ta labartawa Hajiya karɓan alamarin hajiya amma kasan ranta bata so wannan haɗin ba, sabida Hajiya burinta mai nasara ya sami macen da zata sauya mishi rayuwa ba wacce zata sake dulmiyar dashi ba, amma ganin girman Mama yasa ta amince.,

Lokacin da maganar ya isa kunnen Maza, basu ɗauki alamarin da sauki ba, suka kambamata har mai nasara yazo hutu, nan iyayenshi suka tunkare shi da maganar,  shiru yayi  kaman ba dashi ake ba, sai da takaici yasa hajiyarsu bar falon tana sababi tace.

“Tsabar ka rena mutane ana maka magana kayi banza da mutane, sabida rashin kunya, Wallahi Rukayya da Alhaji karku sake sakani a cikin maganarshi.”

Tana fita ya bita da ido, jikinshi a sanyayye, sake mai maita mishi maganar Alhajinsu yayi, ɗago kai yayi yace.
“Hmm shi knn.”
Mama kilishi tace.
“Babana shi kenam din na amincewa ne .”

Mikewa yayi dakyar yace mata.
“Eh” sannan ya fita murmushi mahaifinshi yayi yace.
“Miskili kafi mahaukaci ban haushi duk yaran gidan nan a sake suke amma Babana kaman wanda aka takureshi”

Hira sosai mama sukayi da alhaji, akan sha’anin.
Koda ya koma makaranta bai fadawa abokanshi ba, dan lokacik suna matakin masters ne, dake ba mutum mai yawan magana bane shi yasa abin ya barshi iya shi kaɗai..
Bayan wata uku akafara hidiman biki tsakanin Balkisu da mai nasara basi taɓa haɗuwa ba, sai da Mama kilishi ta tura Abdul kadir yaje har makarantar yayi mishi terere a gaban abokai su kuwa suka sakashi a gaba da tsokana, haka  suka zo yaje gidansu balkisu ya koda suka je dan bashi ɗaya bane, Aman da Ahmad sune suka tsarata amma gogan naku nan make, a gefe yana jinsu da suka buwayeshi ya mike ya barmusu gurin()

Koda suka dawo gida Mama ta samesu da maganar take suka ware akan shagalin  sabida daga Aman har Ahmad kowannensu yana da rawan kai, haka sukayi ruwa sukayi tsaki suka ajiye ango a gefe,

Biki anyi na garari dukda ango baisan anayi ba, sai dai gurin dinner akasa shi dole sai da yaje, sai ɗaurin aure da, kuma hawan doki aka je gaida sarki.

A cikin gidansu aka ware musu, side ɗinsu.

….. “Ahmad wallahi wannan auren da aka mishi cutar yarinyar zaiyi, dan nasanshi sarai babu abinda zai iya sauke mata, shi yasa nasayo tablers ɗin nan zan jefa mishi a coca an jima, toh daren Amarci zai tabbata, dan na lura shi ɗin sai du’a’i.”

Dariya Ahmad yayi, sosai yace.
“Miskili kenan kafi mahaukaci ban haushi.”

Haka sukayita tsara yanda zasu kai Mai nasara ɗakin Balkisu, ai kuwa hakansu ta cima ruwa dan jefa mishi kwaya, Aman yayi suka barshi yasha, ba tare da ɓata lokaci ba suka rakashi ɗakim Amarya, akayi ɗan hira sama sama, sannan suka sayi baki suka ajiye musu kome, sannan suka musu sallama rakosu yayi sannan ya koma, a falo ya baje rigar ya zauna yayi crossing leg, yana hutawa,

Bayan kamar mintuna ashirin kwaya ta jika, nan ta fara aiknta tun yana sharewa yana wani basarwa, har ya fara jin zufa na karyo mishi ta ko ina, shi bai taɓa shiryawa kanshi haka ba, asalima shi ba me yawan sha’awa bane balle yace ai itace ra motsa mishi a daddafe ya shige dakinta dan har ta kashe wuta ta kwanta ko cire kayan jikinta batayi ba,

Hayewa gadon yayi ya,zare kayanshi daga nan ya fara bin amaryanshi da zafi(Bance kome ba dan kar na lalata virgins ɗin Yan mata),

Jin bakon yanayi yana bin jikinta, ga ɗan gyaran da Iyaye suka mata, take ta biye mishi sai da akazo sabonta kwanturaki nan ne idanunta ya rena fata, dan duk tarun da yayi na shekara da shekaru ya juye mata, hot milk ɗinshi, me ɗauke da seed na musaman, yana  gamawa ya koma gefe sai baccin gajiya da zazzaɓi me dan zafi ya rufeshi sabida energy ɗin ba iya nashi kaɗai bane har da na drugs,

Allah sarki  Balkisu taci kuka har ta godewa Allah, ga ciwon jiki, dakyar ta mike ta shiga ban ɗaki ta wanke jiknta fess, ta fito tasamu har yayi bacci itama gefe ta kwanta sai bacci.

****
Bayan sati biyu kana ganin Mai nasara kaga ango dan har wani kiba ya ajiye, duk inda ya ratsa sai an bishi da ido toh ya aka iya akuya taji daɗin manda()< tunda ya gane darajan babban gida ba ruwanshi da miskilanci sai ya gama ya shiga tsare mata gida()

Itama mulki ya satakota a gaba, dan daga gidansu aka kawo mata masu aiki har mutum biyu,

……Shekaransu ɗaya ta haifi huda takwaran Mama, nan ya tattaro soyayyar duniya ya ɗaura mata, dake a gaban iyayenshine sai kula da yarinyar ya koma kansu sabida itace jikar ɗansu na fari dukda kanenshi mata sun haihu,

Rashin samun kulawar Uwa da huda take fama dashi yasa su hajiya suka ɗauketa, nono kawai Balkisu ke iya ba,

Huda nada shekara uku, Balkisu tasami wani cikin kamar zatayi hauka, dan bata farɗaɗo daga hidimar Huda ba sai ga wani cikin, ana ne ta gane waye mai nasara dan kwayance mata yayi dole ta hakura da kudirinta.

A bangare kasuwanci kuwa har sun fara fita dubai sayo kaya, wani tafiyarshi suka haɗu da Fareeda, wacce ta tsinci lalitarshi a cikin kasuwan zamani, duba cikin lalitar tayi taga passport ɗinshi anan ta shiga nimanshi dakyar tasameshi ya zo niman lalitar(wallet) mika mishi tayi ya karɓa, yayi mata godiya. Nan take faɗa mishi ai tasan alhajinshi dan Abokin Babantane, murmushi kawai yayi suka rabu,

Koda Fareeda koma gida nan ta labartawa iyayenta ita fa taga miji, nan tsohuwar abokantaka ya motsa, Alhaji Ibrahim gusau, ya tafi har zaria ya bawa mai Nasara auren Fareeda dan akara dankon abota,()  koda maganar ya isa kunnen balkisu ko ta kula, ita bata da damuwa, dan kowacce da gindinta zata zauna ko irin haukar kishin babu.

Wata biyar tsakani akayi auren, wannan karon ma, dai bawani tuntuɓarshi akayi ba dan sunsan karshe yace hmmm shi kenan ko Ehh,

Zuwan fareeda da wata biyu, Balkisu ta haihu, a lokacin ya gama gininshi na Unguwar sarki kaduna,.

Bayan suna suka dawo baki ɗaya, nan kowacce ta cigaba da zama, sai dai dukkansu basu da lokacinshi dan fareeda na gama amarci ta cigaba da kasuwancinta, bata zuwa dubai amma duk lokacin da zai tafi shi ke mata aikanta.

Huda nada shekara bakwai Lokacin Mufida nada shekara uku fareeda ta haifi ɗanta namiji aka samishi Muh’d,
Wanda suke kira da sameer,  haka zaman gidan mai nasara ya kasance ahangunce dan kowacce abinda tayi niyya take, babu rabon kwana,

Ganin irin rayuwar gidan da Yan uwanshi suke magana akai hajiyarshi ta nima mishi auren Yar kaninta Aneesah, nan ma ba laifi, anyi hidima lafiya, sai dai Aneesah tayi kokarin janyoshi jikinta,  dukda ma’aikaciyar bankine haka bai hanata samun ɗan lokacinshi ba,

Da tafiya yayi nisa sai ta watsar ta ɗauki halayar manta gidan, abu guda dake fasa kan Aneesah shine kyau, Sabida uwart sadaka yalla ce ga kyau ga gashi, amma bata da damuwa, fitinanniyar kenan Fareeda matsalar fareeda guda ɗaya ne bata son haihuwa ita tana son yara amma gani take matukar ta haihu kyanta zai dakushe, shi yasa tun farkon auren da tayi ɓari, bata zauna ba taje aka saka mata roba a bakin mahaifa.

Gidan mai nasara kenan.

****
Aman Mohmud Mandara yan jahar barno ne, daga uwarshi har ubanshi, shine babba a gidan sai kanenshi guda Uku khalisat da Sakina da Nafisa, sun taso cikin gata da soyayyar Iyayensu ga uwa uba tarbiya, Khalisat tans aure a maiduguri,

Rayuwar Aman mai saukine dan shi mutum ne mai bawa kowa hakkinshi, baya son shiga hakkin wani,  yana phd ɗinshi a Computer engeering ya haɗu da Hindu, sun buga soyayya na bugawa a jarida dan iyayen hindu suma suna da rufin asiri sai dai matsalarta bata iya kome bane. Dan su a gidansu basa aiki,  mahaifinta bakano ne, mahaifiyarta yar Chadi ce, amma ma zauna garin kaduna, soyayyarsu takai har manya sun shiga maganar,

Lokacin da maganar aure ya taso ansha biki, da farkon Auren Aman shi yake mata komi, sabida yasameta yanda bai tsamani ba, ga kyaututtuka da yake mata na kuɗi da kayan kawa na mata, ganin haka yasa ta mike kafarta duk lokacinda yazo nimanta sai ya biya ta da wani abu, a hankali suka ɗauki lokaci dan ko shekara basuyi ba, ta tsirfo da halayar da ya fara gunduranshi, amma dake yana matukar sonta sai gashi ya shanye kome, har yana biye mata,

Bayan shekara biyu kazantarta tayi muni, babu masu zuwa gidan, duk mai aikin da yakawo sai ta gudu, dan kome ita zatayi ga wulakanci sai ya daina ɗauƙar masu aiki ya zuba mata ido,  har zuwa ynx da ya fara ikirarin saketa…..

****
Ahmad Zailani Bature, Mahaifinshi ambasane kuma tsohon Ma’aikancin banki duniya, yayi aiki a gurare dq dama, ciki da wajen kasar, shekaranshi uku knn da rasu,

Ahmad nada kanen maza biyu mata biyu, matan sune kananu, mazan kowanne yana da aikin yinshi, Fahad yake binshi sojan ruwa ne, sai Faisal wanda shi likitane, a kaduna ya haɗu da Hafsat a gurin bikin wani abokinshi, nan suka mannewa juna, Hajiya firdausi mahaifiyar ahmad tasa aka bincika mata halin Hafsat yar babban gidane amma matsalar uwarsu itake juya gidansu har da ubansu ga rashin tarbiya, danginsu yawo rayuwar karya da sauransu sannan dangin Ubansu basu isa zuwa gidansu ba,

Da haka Hajiya firdausi tayiwa Ahmad hannunka mai sanda amma fir yaki fahimtarta asalima sai yake ganin kamar sukar  niman aka kawo mata, ganin idanunshi sun rufe yasa tabishi da fatan alkhairi aka sha biki,

Ba laifi hafsat tana kokarin kyatatta rayuwarsu sai dai matsala ɗaya a gurin rayuwar aure, duk abinda zai mata kar ya taɓa mata boons,() anyisune dan kwalliya badan aji………

Kuyi hkr wallahi yau an wuni ana ruwa kuma bani da chajine…..A fuwa.
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu:
*MATAR SO*

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER’S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai….

Dedicater To Hafsat Abubakar

_Idan kinsan baki saya karki karanta sabida na kuɗine, idan kika samu an sato toh karki faɗa min maganar banza dan zan iya miki Allah ya isa, duk wacce ta fitar min Na barta da Allah_

*BOOK ONE*

Back to top button