Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 28

Sponsored Links

*PAGE* 2⃣8⃣

ko da jakadiya tadawo tatsugunna, gimbiya tattare nutsuwarta tayi tamaida gareta tace bakomai yasa nakirakiba sai dan naga alamun zaki iya taimaka min, inaso kirik’e min sirrina Indai kikayi haka toh zaki ji dad’ina ammah duk ranar da kika nemi kitona min asiri. murmushin mugunta gimbiya sumayya tayi sannan tace kinsan wacece ni

jakadiya duk’ar da kanta tayi tace ranki yadad’e kar kidamu a kodayaushe ina tare da ke zanyi duk abinda kikeso.

jinjina kai gimbiya sumayya tayi tace shikenan zaki iya tafiya

zarah ko da takoma part d’inta zama tayi saman cushin cikin ranta duk sai taji bataji dad’in abinda tayi ma sumayya ba dan tasan hakan da tayi bai daceba, ko da daman tayine dan tanuna mata talakka ma daidai yake da kowa, kuma duk saboda haka take daurewa tana nuna ma yarima kulawa dan har a lokacin batajin sonsa a cikin ranta, jikinta taji duk yayi sanyi cikin ranta tace insha Allahu bazan k’ara shiga hurumin da banawa ba dole inje inbata hak’uri dan bansan yanayin da zata shiga ba.

sawa tayi aka fara kira mata kuku nan tayi masa bayani tace yakoma bakin aikinsa ammah banda ranar girkinta, dan bata buk’atar mijinta yaci girkin wani ranar girkinta, nan yayi mata godia sannan yatashi yafita cike da jin dad’i.

zarah tashi tayi tanufi part d’in gimbiya sumayya daidai lokacin sumayya tafito daga bedroom d’inta, cikin 6acin rai sumayya tace me kikazo yi min nan munafuka? ko munafuncin da maitan akazo yimin nan?

toh bari kiji Indai kin shanye yarima toh ni kurwata fes take duk wani maita da asiri bazasuyi tasiri akainaba.

zarah k’wallah ce tacika mata ido ahankali tace dan Allah kiyi hak’uri da abinda yafaru wlh…… A fusace sumayya tace wlh me munafuka? toh bari kiji wlh dole kirabu da mijina duk wani zak’ewarki daman ku ‘ya’yan talakkawa haka kuke baku iya samun wajeba ina gargad’inki da kifita harkar mijina inko ba hakaba zan fiddo miki halina a fili zakisan wacece gimbiya sumayya,

zarah k’wallar da take cikin idonta tanemi tazubo dasauri tagogeta tace dan Allah kiyi….. ke! ni fice kiban waje tun kan in karyaki a nan wajen, matsiyaciya kawai.

zarah da mamaki take kallonta ahankali tajuya tafita tabar d’akin kwata-kwata bataji dad’in yadda gimbiya sumayya takasa fahimtarta ba.

 

tun daga lokacin zarah tadaina shiga sabgar yarima indai ba ranar girkinta bace.

 

_*Bayan Sati ‘Daya*_

zarah tana zaune saman cushin hannunta rik’e da wayarta tana operated d’inta, kiran da yashigo wayartane yasa tabi wayar da kallo cike da mamaki ganin mai kiranta, ahankali tayi picking tare da yin sallama, daga chan 6angaren ciki-ciki yarima ya amsa mata sannan yace kizo inason ganinki, yana fad’in haka yakashe wayarsa.

zarah cike da mamaki tabi wayar da kallo cikin ranta tace ko me zanyi masa, mik’ewa tayi taje tad’auko veil d’inta tayafa sannan tafito tanufi part d’insa.

sumayya da bata dad’e da shiga ba zaune take gefensa tace sweetheart kiran me kakemin a wannan lokacin ko akwai abinda kake buk’ata? banza yarima yayi yakyaleta, har ta bud’e baki zatayi magana shigowar zarah yasa tafasa a wulak’ance tad’aga kai takalleta cikin tsawa tace me kikazo yi mana nan kuma uwar shishigi? zarah d’an rissinawa tayi tace barkanku da hutawa, sumayya tace kifita kibamu waje tun kan ranki ya6aci.

zarah kallon yarima tayi da yake kallon TV ammah hankalinsa yana wajensu, ganin baida niyar yin magana yasa tajuya zata fita,
muryar yarima tajiyo yace umurninta zakibi ko nawa?

ahankali zarah tajuyo takallesa har a lokacin kallonsa yana ga tv, ahankali yajuyo yakalleta tare da nuna mata kujera tazauna,

key d’in mota yad’auko yamik’a ma sumayya yace ga wannan key d’in motarki ne da nasiya miki,

sumayya kar6a tayi tana juya key d’in tace dagaske tawa ce yarima? cike da Jin dad’i tarungumesa tace nagode sosai gaskiya naji dad’i, Allah yabarmu tare d’an bak’in ciki kuma saidai yamutu.

murmushi zarah tayi tace Allah yasa alkhairi Aunty gaskiya natayaki murna, sumayya harararta tayi tace inma bak’in ciki kike toh saidai kimutu.

yanayin yadda tayi maganar taso taba yarima dariya, d’ayan key d’in da yake hannunsa yamik’a ma zarah yace kekuma ga naki, zarah da mamaki take kallonsa ji take kamar a mafarki ahankali tace ni kuma?

yarima yace kikar6a mana, zarah tasowa tayi tad’an rissina takar6a tace nagode Allah yasaka da alkhairi Allah yak’ara girma da d’aukaka,

sumayya da tunda taji yace ga ta zarah yasa tacanza fuska, cikin 6acin rai tace ban fahimcekaba? ya naga kaba wannan d’iyar talakkawan kana nufin matsayinmu d’aya da ita ko me?

yarima shuru yayi yakyaleta, sumayya a fusace tace gaskiya yarima baka kyautamin akan me zaka dinga had’ani da wannan ‘yar ma….. kallon da yayi matane yasa takasa k’arashe maganarta, maida kallonsa yayi ga zarah da kanta yake sadde k’asa sannan yace motocinku suna parking space zaku iya zuwa kugansu, ke za’a fara koya miki taki ko da ace ba fita zaku dinga yi ku kad’ai ba na mallaka mukune abisa ra’ayin kaina.

zarah ce kawai tace toh mungode Allah yasaka da alkhairi Allah yak’ara bud’i, mik’ewa tayi tace nabarku lafiya sannan tafita tabar d’akin takoma part d’inta.

sumayya kallon yarima tayi tace haba yarima gaskiya banajin dad’in abinda kakeyi min.

yarima da mamaki yake kallonta yace sumayya me nayi miki?

shuru sumayya tayi batace komai ba,
kifad’a min abinda nakeyi miki Wanda ba daidai ba, cewar yarima.

Jin batada niyar yin magana yasa yamik’e yashige bedroom d’insa yabarta nan parlour, cike da 6acin rai sumayya tatashi takoma part d’inta.

tun daga ranar yarima yasa aka fara koya ma zarah mota kasancewar sumayya da dama chan ta iya.

*Bayan kwana biyu*

gimbiya sumayya ce tafito daga part d’inta zataje turakar mahaifiyarta, tsaye tayi tana kallon zarah da tanufi part d’in yarima bayanta kuyangarta ce d’auke da tray.

gimbiya sumayya kallon kuyangarta mairo tayi tace ya kike ganin ya dace inyi inaso kar yarima yaci abincin,

murmushi mairo tayi tare da d’an rissinowa ahankali tayi ma sumayya rad’a nima kaina bansan abinda take cewa ba saidai gani nayi gimbiya sumayya tayi murmushi tare da jinjina kai tace hakan kuwa za’ayi yanzu nasan yarima bai dawoba, mukoma ciki nafasa fita.

Bayan sun koma gimbiya sumayya sawa tayi aka duba mata fitowar zarah daga part d’in yarima, Bayan anzo anfad’a mata mik’ewa tayi tanufi part d’in yarima fuskarta d’auke da murmushi.

 

yarima ba shi yadawoba sai around 3 o’clock, zarah saida ta daidaici daidai lokacin da tasan yadawo sannan tatashi tanufi part d’insa kasancewar itace take da girki ranar.

tana shiga part d’insa daidai lokacin yafito daga bedroom d’insa hannunsa rik’e da waya yanayi, kallon zarah yayi da take murmushi sannan yawuce yanufi dining ko da yazauna zarah serving d’insa tayi sannan tazauna kusa da kujerar da yake zaune tana jira yagama waya.

gimbiya sumayya tana ganin wucewarta murmushi tayi tace munafuka yau zanso inga yadda zaki kwashe da yarima bari ma inbi inga yadda za’ayi wannan dramar.

lokacin da gimbiya sumayya tashiga part d’insa daidai lokacin yarima yagama wayar da yake, ganinta yasa zarah tamik’e tsaye fuskarta d’auke da murmushi tace ranki yadad’e sannu da zuwa,

murmushi gimbiya sumayya tayi tace yauwa gimbiyar yarima,

da mamaki zarah takalleta dan wannan ne karo nafarko da taga murmushi a fuskarta gimbiya sumayya,

yarima d’aukar spoon d’in yayi yad’ebo abincin zai kai bakinsa, kallon sumayya yayi da tazuba masa ido yace inzakici kizo kizauna kici.

gimbiya sumayya jayo d’aya daga cikin kujerun tayi tazauna nan zarah tayi serving d’inta, yarima ahankali yakai lomar farko a bakinsa, yana fara taunawa dasauri yazubar da abincin yana yamitsa fuska, zarah da mamaki take kallonsa tace yarima lafiya?

mik’ewa yayi dasauri yashige bedroom yanufi toilet, zarah kallon sumayya tayi itama sumayya kallonta tayi tace me yake faruwa?

zarah tace nima ban saniba ammah bari inje ingani dasauri tatashi tabisa a toilet tajiyosa yana ta kakarin amai, dagudu tabisa tarik’osa a rikice tace me yake faruwa please kafad’a min?

kuskure bakinsa yayi yafito yabud’e freezer yatsiyayi hollandia yasha, kallon zarah yayi da take tsaye yawurga mata harara yace wannan wane irin iskancine?

daidai lokacin gimbiya sumayya tashigo tace wai sweetheart me yake faruwa?

zarah tace me nayi maka?

harararta yayi yace au kina nufin bakisan abinda kikayi ba?

zarah tace wlh ban saniba.

yarima fizgota yayi yanufi dining da ita, kallonta yayi yace d’ibi abincin kici,

zarah d’iba tayi takai baki wani irin gishiri da yaji taji dasauri tazubar, cikin tashin hankali tace nashiga ukku ya akayi hakan takasance?

harararta yarima yayi yace kitambayi kanki, kwashi kwanukanki kifitar min daga d’aki,

zarah kwallah ce tacika mata ido tace wlh bansan yadda akayi hakan yakasanceba nidai lafiya lau nayi girki na dan Allah kayi hak’uri bari toh inje indafa ma mai d’an sauk’i.

hanya yarima yanuna mata yace kwashi kayanki kifita,

gimbiya sumayya tana tsaye duk dad’i ya cikata, ahankali tatako inda yake tace sorry sweetheart bari inje insa akawo maka abinci, kallon zarah tayi da take kwashe kwanoni tace ammah dai baki kyautaba wlh ya dai kamata kigyara halinki.

murmushi zarah tayi tad’auki tray zata fita, yarima kallon gimbiya sumayya yayi yace kema bita.

gimbiya sumayya tace haba yarima ni kuma me nayi?

hararar da yawurga matane yasa tawuce dasauri tafita cikin ranta tace tunda dai naci nasara ai bazan damu da kowane wulak’anci zakayi min ba….

 

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_*Wannan Page d’in nakune my Facebook fan’s ina ganin sak’onninku nagode sosai inaso kusani nima inaji da ku irin sosai d’innan*_

Back to top button