Hausa NovelsMatar So Hausa Novel

Matar So 17

Sponsored Links

Page….17
Tsaki yaja min tare da juyawa ya zabgawa Matanshi harara, na mi ya kawoku juyawa suka a birkice sabida ranshi na kara ɓaci. Wuccewa yayi ya shige ɗakinshi zama yayi a bakin gado tare da dafe goshinsa, kanshi na kara zafi.

…… A hankali Huda zo inda nake ta rungumeni, kuka ne ya kwace min wanda bansan iyarkashi ba.
Dakyar na mike na haura ɗakina dake sama akan kujera na zube na cigaba da kuka.

Kiran sallah azhar ya ɗaga ni nashiga bandaki, alola nayi fuskana na kalla a madubin ban ɗakin naga fuskana sun kumbura, musaman inda ya mare har hannunshi sun kwanta Girgiza kai nayi na fito na shimfiɗa abin sallah na fara, ina idarwa Huda na shigowa ta shirya tsaf cikin sanyi murya tace.
“Aunty Mom zan tafi, gidan aikine a gabanki kici ko ta cinyeki ba lallai bane na dawo amma kafin tafiyata zan zo.”

Tana gama faɗar haka ta fita da sauri, bin bayanta nayi sai na dawo na buɗe jakana na ciro kuɗi wanda nasamu a buɗan kai na sauko da gudu, tsabar karsu tafi ban bata wani abu ba,  duk hankali na yatafi da ita dan naji dirin motarshi.

Gummm naji bayan nasauko daga step, garin gyara rikon kuɗin naji nayi karo da abu baya nayi zan faɗi duk kuɗin suka watse, a kasa saura kiris na faɗi da baya sai ji nayi an rike k’uguna tare da tallafeni, a firgice na ɗago ina kallonshi nayi a tsorace.

Tunkuɗe ni yayi tare da buga tsak’i, tare da barina a gurin ajiyar zuciya na sauke tare da tattara kuɗin na sake fita a falon.

Har gurin motar na isa na kwankwasa glass ta buɗe tana murmushi nima mai da mata murmushin nayi sannan zuba mata, kuɗin cikin motar nace.
“Don Allah kafin tafiyarki, ki zo mana.”

Ƙallon uban tayi sannan ta juye gareni tace.
“Aunty Mom nagode amma..”

“Kuna ɓata min lokaci.”  baya nayi.ina kallonsu har suka bar gidan a hankali na koma ciki, kai tsaye falona na wucce naje na zauna ina tunanin gida gashi babu waya a hannuna.
……
Shiru motar tayi ko kallon inda yake takiyi tsakaninta da Allah take fushi dashi.

“My Queen am so sorry.”
“Daddy bani zaka bawa hakuri ba, Aunty ce zaka bawa hakuri kuma kasaya mata waya dan bata da waya tun safe take cewa tayi kewar Ummanta da Mamansu, kuma tana son kiran hajiyarku maganar gaskiya baka kyauta ba, mace ce fa kuma idan da adalci ai bincike ya kamata kafara a gaban kishiyoyinta ka ɗaga hannu ka mareta, kuma tq baka hakuri wallahi in nice bazan baka hakuri ba, nasan ni Yarinya ce amma bazan taɓa barin a cutar dani ba, matukar ina da gskyana.”

Shiru yayi yana nazarin maganar Y’arshi. A wani shago suka tsaya ya fita shi da ita, ita ta zaɓar min infinit Hot8 suna gama saya yaje ya saya min layin Mtn, ya saka a laida suka shiga motar,

A gida ya sauketa ya fita ko leka gidan baiyi ba, ya tafi gurinsu Aman.

****
“Wallahi naga makirci kiga fa marinta yayi amma ta nuna a shirye take da wasu hukuncin yarinyar ta iya makirci wallahi in watace kowa sai yasan an taɓa ta.”Inji Aneesah.
Taɓe baki fareeda tayi sannan tace.
“Gulma dai ko? Ina makirci anan koda yaran malamai haka suke bazaka taɓa gane ana cutar dasu ba tsabar an cusa musu munafunci a ransu.”

Shigowar Huda yasa suka fashe da dariya ” Yar amarya har an korokine.”
Banza tayi dasu bata kulasu ba.

……..
Daga Gidan Mamie Ahmad ya wucce ofishinsu ya zauna jagwaf, lokacin Aman na waya Rahilah wanda kusan duk hiransu na manyan ne, dakyar ya iya katse kiran.

Hira suka taɓa sama sama, can sai ga Mai Nasara nan suka buɗe pagen hira kowannensu da abinda yake damunshi, Aman matsalar Hindu na niman faɗa da Rahilah, ga matsalar Ahmad da Hafsa, shi har tsoron tun karan Rahimah da niman wani abu dan gani yake matsalar na nan dan har ynx y’ayan marenanshi na motse suke haka na nufin da sauranshi knn.

Sai shida suka bar ofishin, kowa ya nufi gidanshi unguwar sarki Mai nasara ya nufa tun daga falo yaga babu kowa, kokarin leka ɗakunarsu yayi ya ɗauki abin ɗauka ya bar gidan.

…….
Ina kitchen girki nake haɗawa, kamshin miyar kuka ne ya daki hancinshi, amma dake namijin duniya ne sa kai yayi ya wucce.
Haka na gama tuwo miyar kuka, wanda na gani a cikin kayan jerena, tuwon semo nayi banyi tsamanin ko zai ciba na jera a kan dinne table na ɗauki nawa na wucce sama,
Wanka nayo da alola sannan na gabatar da salla, ina idarwa na zauna na ci abincina kewar Umma da gida ya dameni ina zaune a gurin ga ba waya a hannuna duk sai naji ni, daban dukda wayarmu ta haɗaka ce .

Tashi nayi na sauko kasa zan wucce, yana falonshi a zaune, tun da ya ɗaga kanshi ya kalleni bai kuma kallona ba labarai DW ya cigaba da kallonshi.

Kitchen na shiga na tattara kayan da na ɓata nawanke tass sannan nagoge gas ɗin na juye sauran miyar a wani kwano silver nasaka a firij,

Kashe wutar kitchen ɗin nayi na fito, har zan gotashi yace min.
“Keee!”
Cak na tsaya kirjina na bugawa kamar wacce aka kamani da wani abu, tsaki yayi yace.
“Dalla kizo ki ɗauki abarki.”

Juyowa nayi jikina na rawa, kamar wacce aka tsoma a ruwa a hankali na taka inda ya ajiye farin ledar mai tambarin Abul Hanif communication… D’auka nayi bakina na rawa nace.
“Nagode.”

Shiru yayi min, da sauri nabar falon zuwa ɗakina zazzage ledar nayi na shiga ɓare kwalin wayar na ciro naga gefe ga katin Mtn da Airtel kamar mahaukaciya na fasa ihu ina faɗin.
“Alhamdulillah.”

Yana kallonshi yaji ihuna ɗago kanshi tsaki yayi, ya cigaba kallonshi a ranshi yace.
*Ji shirme waya aka bata fa, take ihu da yarinta idan kuma aka bata wani abu sumewa zatayi* girgiza kanshi yayi yana kambama girman yarantata, tuna karon da mukayi yayi ya dafe goshinsa,” Wallahi  an gama dani nasan nan gaba cewa zatayi na mata wani abu.” haka yayiya hasasho abubuwan da zan iya saka shi.

Jona wayar nayi a chaji bayan nasaka layukana mtn ɗine har da kati dubu da biyar har kati uku, kwanciya nayi a gurin ina yi ina leka wayar(sabon Waya) dakyar nayi isha na ɗauki alkur’anina na fara karatu sai takwasa na ajiye nasake leka wayata,() a gurin na ɓingire da barci, karfe hudu na farka nayi alola na fara nafila har akayi sallar asuba, sallah nayi na cigaba da azkar har garin ya fara haske sai lokacin na tuna ashe ina amarya fa.

Matsawa nayi nazaro wayar a jikin chaji, zama nayi na kunna wayar yana sittings na mike zuwa gadona jakana na janyo na shiga niman takardun nomber mutane, ina ɗauka, Hajiyarshi na kira har zan katse ganin yayi safiya lokacin sai naji ana cewa.
“Waye ne.?”
Cike da jin kunya nace.
“Umma nice maryam sajida.”
Murmushi tayi cike da jin daɗi tace.
“Allah yayi miki albarka, Kinsami wayarce dan Yarki tace min baki da waya.”
“Hmm eh jiya aka kawo min, ina kwana , ya gida dasu Mama.”

“Duk suna lafiya,da fatan babu matsala dai ko.?”
“Eh babu komi, dama nakirakine mu gaisa.”

“Allah yayi miki albarka ya baku zuri’a ɗayyiba, ayita hakuri wata rana sai labari nagode sosai Allah ya baku zaman lafiya.”

Can kasar makoshi nace.
“Amin” sai anjima na mata, nayi saved nomberta da Sweetmom, sai Nomber Mama kilishi itama mun jima tana min nasiha, ina gamawa nayi saved ɗinta da Our mom.

Umma naso kira sai nakira Mama Amarya, mun jima muna hira da ita sannan tabawa Umma nan na fasa ihu, sai da ta cire wayar a kunenta tace.
“Uwata yaushe zaki girma.”
Dariya nayi nace.
“Ummana i miss you,””

Wallahi zama nayi nasata a gaba shiriri, sam namanta kaina dan na cire hijab ɗina da kuma zanin sallah fitowa nayi duk jelar kitsona ya sauka kafaɗa ita kanta rigar jikina ta wofice dan hannun bra gareta, kuma iyakarta gwiwa, ina zubawa Umma taɓara son raina, na manta gidan bani ɗaya bace.
Haka na sauko ina mita, tare da bubuga kafana a kasa, shi kuma yafito zai bar gidan ya sauke idanunshi akaina, cikin sauri ya kauda kanshi tare da barin falon da wani irin sauri gamm naji an rufe kofar falo, sai lokacin na tuna yanda na fito ai a 360 nayi sama har ina haki, kashe wayar nayi baki ɗaya, kunyace ta ɓoyeni a ɗaki har rana….

…….
Tunda Ahmad ya shigo gidan ɗakin Rahimah ya nufa, inda ya sameta rike da alkur’ani, zama yayi har takai aya, karɓa yayi ya rufe tare da ajiyewa.

Janyota yayi yana sunsunar wuyarta cikin sanyi murya yace.
“Mi kika tanadar min, ina jin yunwa.”
D’ago kai tayi tana murmushi, tace.
“Coconut rice da veg soup , na tanadar maka.”

Kanshi na wuyarta yana sumbatarta cikin shakar turarenta yace.
“Saura kee kin tanadar min da kanki.”

Dif ta ɗauke wuyata tare da rike hannunshi da tajisu a cikin rigarta yana murza abinda yake kauna daga mace, tsigar jikintane ke tashi a hankali ta zare hannunshi kanta na sunkuye tace.
“Ina Off, kayi hakuri.”

Matseta yayi cikin sanyi murya da tausayinsu yace.
“A miki hakuri my Preety.”

Shima abinda yasa bai damu ba sabida baiji wani motsin daga abubuwan aikinshi bane, ruwan wanka ta haɗa masa tare da cire mashi kayan sawarshi sannan tafita ta haɗa abincinshi da zai ci…

Koda ya gama masalaci yafita yaje bai dawo ba sai bakwai, sider ɗin Hafsa yaje ya kalleta gani yayi babu nadama a fuskarta sai ma wani farin ciki da take, bai zauna ba ya fita daga gurinta.

Komawa gurin Rahimah yayi, abinci ta gabatar mishi yaci suna hira har kusan goma ta rigashi tashi, taje tayi wanka, yanda ta barshi anan tasame shi yana barci dakyar ya tashi zuwa ɗakinshi, itama ta wucce ɗakinta tana mamakinshi.

Washi gari kuma ta rigashi tashi, ita ta tasheshi zuwa masalaci.
…….
Dakyar nafito nimawa cikina abinda zanshi ci, har dare banji ɗuriyarshi ba, ganin nasaka abinci yaki ci sai banyi tunanin girkawa dashi ba, ina kwance bayan isha muna hira da Rahilah ta Whatsp sai gashi ya shigo a fusace, hantsilawa nayi tare da komawa  can kuryan kujera ina kerma, cikin fusata yace.
“Ina abincina?”
“Hmm kayi hakuri naga jiya bakaci bane shine ban saka mak…”

“Dalla yi min shiru kazama dake ma, maza tashi ki girka min wani abincin ko na miki shegen duka.” ya buga min tsawa da sauri na mike nazo na raɓa gefenshi doguwar rigace na material kaina babu ɗan kwali nayi kasa aguje garin sauri na zame tare da faɗuwa, ihu na tsala da sauri ya biyo ni, ranshi na kara ɓaci cike da sabon masifa yace.
“Ki wucce ki min girki dan ko karyewa kikayi  bazan ɗaga miki kafa ba ”

Ina kuka haka namike dakyar na shige kitchen, jollop ɗin macaroni nayi mishi, ina gamawa na juye masa yana zaune akan dinne table,ina ajiyewa ya buɗe abincin da renin hankali yace.
“Keee zo nan.”
Gabanshi naje ina haɗiye kukana yace.
“Bashi zanci ba, kisake girka min wani abincin.”

Kuka na fasa mishi ina yarfe hannuna nace.
“Don Allah daddyn Huda kaci wannan kafana na min ciwo.”

Buɗe baki yayi yana kallona kafin ya mikewa , na shiga ja da baya har muka kure bangon gurin kallin fuskana yayi, sannan ya take min kafar da takalminshi, kasss naji kafar tayi, bansan kuka ko ihu rahama ne, sai a lokacin ajiyar zuciya na sauke tare da zuɓewa a jikinshi………
[8/25, 3 PM] Real Mai Dambu:
*MATAR SO*

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER’S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai….

Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So….
Dedicater To Hafsat Abubakar

_Wannan buk ɗin hakk’in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

*BOOK 1*

Back to top button