Hausa NovelsMatar So Hausa Novel

Matar So 14

Sponsored Links

Page….14*

“Allah ki ajiye nik’af ɗin nan sai kace ba Yar kaduna ba,muje haka mana.”

Mai da shi nayi cikin hijab ɗina nabi bayanta kamar rak’umi da akala,

har gurin motarshi muka isa, suna tsaye shida wani matashi da alamun shine telan, kaina a kasa na gaidasu, telan ne ya amsa dan ko kallo ban isheshi ba, mika min album telan yayi yace.
“Madam gashi ki zaɓe kalar da kike so.”

Karɓa nayi jikina na rawa, ina satar kallon Mai nasara wanda ya juyar da fuskarshi wani guri daban, jan hannun Huda nayi muka koma gefe nan tayita nuna min, wasu style ni duk sai naji kayan sun bani kunya, sabida akasarinsu masu buɗaɗɗiyar kirjine ni kuma ina kunya sosai, da muka gama dubawa na mika mata album ɗin nace.
“Wai duk wannan na meye.”

Kallona tayi cike da mamaki sannan tace.
“Baki san za’ayi dinner bane.”

“Dinner gaskiya bazanje ba! Ki faɗa mishi asuke dinner dani.”

Shiru tayi, tabar gurina wajenshi taje tace.
“Daddy wai ita, bata son dinner ko za’a fasane sai a maidashi liyaffa, tunda haka ranta keso.”

D’ago kanshi yayi, akayi dace nima na ɗago muka zubawa juna ido, kauda kanshi yayi yana mi taɓe baki ya kalli tela yace.
“Ok kaji wai haka bai mata ba, zamu iya tafiya.”

Baya telan ya shiga huda ta shiga gaba, takowa yayi har gabana kaman ance na ɗaga kaina sai a fuskarshi, sunkuyar da kai nayi kasa jikina ya fara ɗaukar rawa, kallona yake daga sama har k’asa kamar wanda akasahi maganar dole yace.
“Kina da zaɓin abinda zaki yi ne? Dan matukar na tafi babu abinda zai dawo dani.”

Tsabar na dirirince ban taɓa tsayuwa haka ba, sai gabaki ɗaya jikina ya ɗauki rawa bansan ya akayi ba na fashe da kuka, ina ja da baya.
Mamakin halina yake, yanda kuka bai bani wahala, kallon yanda nake ja da baya har na kusan faɗawa lambatu, kawai sai naji an finciko ni bazata na faɗa kanshi tare da cusa kaina a kirjinshi.

Runtsa idanunshi yayi hannunshi ɗaya na bayana ɗaya hannun ya dunkule shi kamar zau zabga naushi, saukar zafaffan kwalla daga idanuwana zuwa kan chest ɗinshi yasa shi ɗagoni ya ture ni sannan ya juya motarshi, yanda ya ture ni kuwa zuɓewa nayi a kasa, tare da sake kuka haka yaja motar suka tafi, yana lura da yanda huda ta kafeshi da ido.

Dakyar na mike na shiga gida, abin mamaki ina zare hijab ɗina Aunty gausiya tace.
“A ina kika samu, turare mai karfi haka a tsorace na sunsuna hijab ɗin naji ai turaren mai nasara ne, ai kuwa nayi wurgi da hijab ɗin tare da zuba gwiwa na kasa nace.
“Don Allah ki rufa asiri wallahi tsausayine ya rufta dani ya taimake ni shine, jikinmu ya haɗu da juna amma ni ba Yar iska bace.”
Dariya tayi tace.
” Ni ban tambayeki ba, kamshin ne yayi min daɗi da zaki min dogon turanci.”

Tsabar ganin yanda na ruɗe dariya tayita min.

****
Tunda suka bar kofar gidan mu yake satar kallon inda kwalla na ya jika mishi, yanayin da abin ya faru yasashi faɗawa wani yanayi  na daban, sauke drvn yayi ya wuccw gida da huda..

****
Sati biyu ya rage ayi bikin muna zaune da dare sai ga Rahilah tazo, tsiya muka shiga mata tana dariya,

Dakin iyayenmu tashiga suka gaisa sannan ta faɗa musu abinda ya kawota, shiru Malam yayi kafin yace.
“Da fatan ba irin wanda akayi na watsewa zaku yi ba.”

“A’a malam cikin shiga mutunci da kima zamuyi, kuma za’a kawo muku hotonan ma.”

“Shi knn, kuje.”
Godiya tayi sannan tazo ta samu muka fita,   sai da muka fita har mun shiga motar Mijinta sannan take faɗa mana abinda zamuyi, aikuwa nace bansan da haka ba,

Share ni tayi muka tafi.

A can muka sami Mai nasara da Ahmad wani ɗaki aka ware mana, muka shiga aka shirya mu, ba gurin ɗaukar hoto bane gidan saukar bakinsune anan muka sami mai kwalliyar,

Bayan wasu lokuta muka fito aka fara ɗaukar hotonmu, munyi mu uku munyi sai wanda mukayi da mazajenmu kowa da kalar kayanshi, dake bana jure shagali haka dakyar aka gama abubuwan dani.

Duk wanan bidirin da muke ko kallon juna bamayi, asalima yakan ajiye gefe guda.

Sai da aka kusan gamawa yace.
“Ku bani guri a mana na karshe.”
A birkice na shiga kallonshi komawa gefe yayi sukayi magana da mi ɗaukar hoton, sannan ya dawo gurina harara na yayi yace.
“Sai nace ki tashi.”
Mikewa nayi ina daidaita zaman gyalena, ina ɗago kaina nayi an fincikoni haɗe goshinmu yayi, lokaci ɗaya na dafe kirjinshi ina runtsa idanuna.

Tare da rike rigarshi tam, ɗaukar hoton akayi a haka sannan ya tureni na faɗi kan kujera, haɗiye kukana nayi nasamu na bar gurinsu  wajen yan uwana naje na fashe da kuka,

Duk suka ruɗe harsu Ahmad ɗin yana fitowa suka tsareshi da tambaya ɗaga musu hannu yayi dan sun cika mishi kunne yace.
“Ku tambayeta mana”

Yana faɗar haka yabar gidan muma gida aka dawo damu. Kallona,Rahimah tayi a nutse ina jan hancina tace.
Wai mike haɗaki da shine? Na lura duk zuwanshi sai yasaki kuka, kema sanin kanki iyayenmu bazasu taɓa zaɓa mana abinda zai cutar damu ba, amma mi yasa kike kuka ko baki sonshine tunda kika rahilah itama ba son Aman amma yanzun kiga yanda suka koma kamar zasu cinye kansu, kece baki lura ba, amma kiga yanda yake ɗawainiya da ita kamar zai maidata cikinshi, tsabar so ki kwantar da hankalinki don Allah kar iyayenmu su fahimci halin da kike ciki.”

Dafata yayi idanuna na kara cikowa da kwalla nace.
“Rahimah wallahi tsoron shi nake ji, kuma duk zuwanshi sai ya min mugunta, ɗazun a can ɗin nan fisgoni yayi ya gwara min kaina da nashi, kinga gurin.”.

Na nuna mata kwalla nasake cika idanuna.

“Wannan ba hujja bane, idan kika auna yanayinshi ba mai yawan kwaranniya bane haka Abban Chuchu ya faɗa min, suma suna son ganin yana walwala kamar kowa, amma haka ya tsarawa kanshi, ɗabi’arshi ce miskilanci ke ya dace ki shiga jikinshi ba shi zai shiga naki ba, ajiye wannan haukar zakiyi a gefe ki fara koyawa kanki rashin kunya, da wayewar dole, ki rage tsoro ki koyi tsiwa da wasu halin irinsu shagwaɓa, shirme kan ai nasan kece karshe a cikin gidanmu amma dole ki ajiye wannan sakarcin, ki zama jan wuya ki koyi iya kallon cikin idanunshi da rigimar dole yanda zaki canza mishi rayuwa amma ba ki xauna kina zare manyan idanu kamar mayya ba, idan yayi miki ki ɗauka ko ki ajiye a gurin. Ko gidanshi kika je matanshi suka ga baki da hikima da dabara zaki sha wahala dasu balle kuma shi namiji wanda ake kamashi ta hanyoyi da dama, ba yau Umma ta fara faɗar haka ba amma nayi mamakinki da kike zauna kina zubda kwlla akan namiji yana cusa miki bakin ciki tun awaje kenan kin nuna mishi baki da karfin kwatar kanki kenan hmm gwara ki ajiye tun wuri.”

Tana gama faɗar haka ta juya min baya abinta, dan har ta gama ban daina kuka ba asalima kaman kara min kaimi akayi.

……..Rike hannunshi tayi tana murmushi tace.
“My Man kaje AuntyNa tana jiranka karmu shiga hakkinta.”

Lumshe idanunshi yayi cike da jin wani iri, janye hannunta yayi yakai kan Maranta da ya fara tasowa, ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.
“Ina matukar son abinda ke kwance a nan da wacce take ɗauke dasu, Allah ya inganta min rayuwarsu nima nayi alfahari da nawa.”

“Amin Ya Allah, ai da uwar da abin cikin duk nakane bana wani ba, kasan wani baya haihuwan ɗan wani, don Allah tashi kaje tana jiranka.”
Dakyar da suɗɗin goshi ta tadashi yafita ɗakin, side ɗin Hindu ya nufa ko ina kace kace ba’a magana, haɗiye ɓacin ranshi yayi ya shige ɗakinta, a saman gado ya sameta tayi tagumi tana share kwalla,

Dakyar ya zaunaa bakin gadon yana kallonta cikin nutsuwa, bawai baya son hindu bane tsabar kazamtarta yasa yake kinta, janyota yayi jikinshi ganin haka yasa ta fashe da kuka bai wani damu ya dakatar da ita ba, saima zuba mata ido da yayi mikewa yayi ya ɗagata zuwa ɗakinshi,

Taimaka mata yayi tayi wanka ta gyara jiknta, sosai dan shi ya bi lungu da sako ya tayata cire gashin gurin da dattin sannan tayi wanka da taimakonshi, duk sai yaji yana jin ba daɗi dan tunda suka dawo taki barinsu a zauna lafiya, duk ranar girkinta a ɗakinshi yake kwana, taki ta nutsu ta gyara kuskurenta.

Koda suka fito ba laifi da yajata suka raya daren abin takaici ko jimawa ba’ayi ba ta fara mita ta gaji,

A take rahilah ta faɗo mishi a rai cike da bakin ciki ya sauka bao ida abinda yayi niyya ba.
…….
Tunda ya fita rahilah ta fashe da kuka, tare da rungume pillow haka take fama da matsanancin kishin Aman, dukda haka bata taɓa nuna mishi tana da zafin kishi ba, asalima da zaran ta ganshi take niman kishin ta rasa, kuka tayi mai isarta sannan ta mike ta shiga bayi tayi alola tazo ta fara sallah, ta jima tana kaiwa Allah kukanta da ya yaye mata kishin dake damunta.

Karshe a gurin ta kwana.

…….

Kwanaki sun gangaro har saura kwana biyu bikinmu, ranar laraba Rahilah tazo da katon akwatinta kowa yaganta yaga mai ciki dukda bai fito ba amma tayi wani jaaa, sai kwaɗayin azaba musaman Ayaba dan tazo mana dashi yafi cikin laida bai baki da fari, kuma irin manyan nan ba kanana ba,

Tunda ta warewasu Umma ta shige ɗaki da sauran ko kallon yaran Yayunmu da suke ce mata Auntƴ zamu ci. Batayi ba asalima gyara kwanciyarta tayi ta ɓare ɗaya tana kallonmu ta shiga lasar ayabar. Sam bamu fahimcin iskancin da take nufi ba sai da ta mike zaune tace.
“Kunga Yaren novel, duk ranar da kuka zama iskanka haka zakuyiwa mazajenku.”

Zaro idanu mukayi da cewa.
“Kamar Ya???”

Dariya tayi sannan tace.
“Ku jakuna ba’ayin XxX ba tare da amotsa jiki ba dole kisan hanyar da zaki tadda mishi hankali, ko ce muku akayi kamar yanda bunsuru ke bin akuya haka ake abi…..”

Allah bamu ji karshen maganarta ba, muka samfeee dan mun lura Rahilah ta lalace idanunta yayi mugun buɗewa, dama ya-ya lafiyar giwa..

*****
Gidan Mai nasara, a fakaice suka hura mishi wuta ta hanyar daina mu’amala dashi sai huda, sam bai wani damu ba dan ya bawa kowacce dama tayi haka,

Ana bikin saura kwana biyu ya shiga ɗakin Balkisu, ta zaune sanye da doguwar riga mai huda, shan y’ayan itace take, tunda ta amsa mishi sallama bata kuma ɗagowa ba, zama yayi kusada ita ya amshi bowl ɗin ya fara shan y’ayan itace hankalinshi kwance,

Sai da ya koshi sannan ya ajiye abin shiru ya ratsa tsakaninsu, riko hannunta yayi yana murza yatsun hannun tare da kallon fuskarta, ganin yanda take karɓan sakonshi yasashi fara wucce iyaka, bata wani damu ba ta mika mishi wuya suka kashe arna sosai, kallon fuskarta yayi a hankali ya shafa gefen fuskar yace.
“Bansan ta inda zan fara faɗa miki ba, dukda na faɗa miki kwanaki zan kara aure kuma naga baki damu ba, shin mi yasa baki ɗabakka al’amurana a matsayin miji, baki tunanin wata ta shigo rayuwata ta sauya min ɗabi’a da halayata, karshe na karkata gareta zaki ji daɗi haka ko? Bana fatan tauyeku amma kuna wasa da hakkina, akala wata biyu zuwa uku knn da wata ta bani hakkina sabida kowacce ku tana busy, kowacce ka taɓa tana da abinyi yaushe zan kira kaina da magidanci, amma ba damuwa duk yanda kukayi ɗaya ne.”

Shiru tayi ta rasa bakin magana, sai ma narkewa da tayi a jikinshi tare da kara rungume shi, ɗago kai tayi cikin nutsuwa suka kurawq juna ido, ajiyar zuciya suka sauke kafin, ta janye idanunta tace..
“Duk matanka ban taɓa jin kishin kowacce su ba, sai wannan da zata shigo, dan tunkafin zuwanta muka ga sauyi daga gareka, abin da na lura kuwa nan gaba zamu iya rasaka ma, nidai don Allah dan soyayyar da nake maka karka juya min baya, ina sonka.”

(Hmmm cinibibi inji yara humm daga baya knn.)

Sam bai wani ji farin ciki ba, sai ma mamaki da tabashi sun jima a gurin kafin ya mike ya shiga ban ɗakinta yayi wanka ya fito, bai tsaya ba sai ɗakinshi kwanciya yayi yanata juyi, can ya lalubo wayarshi gallary ya shiga ya fara duba hotunan da suka ɗauka na bikin da zai gabato,

Yana zuwa kan namu ya tsaya cak zooming yayi, sannan ya taɓe bakinshi sannan ya kashe wayar.

****
Ranar alhamis muka gabatar da taron lakca na mata, wanda yana cikin tsarin hidimar bikin wanda Manyan malamai na kungiyar da’awa suka gabatar a harabar makarantarmu, Ranar juma’a Yayunmu suka shirya kamu dan ban sani ba, sai da aka kawo min kayan nan na buga tsalle nace bazan saka kayanda rabin jikina a waje yake ba, karshe dai sai da aka ɗauko min alkyaba na ɗaura akan gown ɗin, haka suka gama shirmensu bansan mi sukayi ba,

Muna dawowa aka fara mana kunshi, tunda na kifa kaina nake kuka, har aka gama min ban ɗago ba dake jan lalle aka mana,

Gashinmu a gida aka gyara mana dan bamu cika saloon ba amma an gyara manashi sosai.

Ranar asabar da karfe tara aka gabatar da walima, sha ɗaya saura aka ɗaura aurenmu Maryam Sajida Omer tare Yunus Muh’d Marafa.
Sai Rahimah Hassana Omer,tare da Ahmad Zailani Bature,

Ɗaurin auren da ya haɗa mutane da dama, ciki da wajen kasa dan har da abokan kasuwancinsu duk sun zo ɗaurin auren, baka iya gane hak’ik’anin gaskiyar abinda ke fuskar mai nasara sabida sanye yake da madubi,

Ana gama ɗaurin Aure aka ɗaukemu Zuwa ɗanki Malam murmushi yayi sannan yace.
“Toh mi zance musu bayan dai sunsan iyaka ta hakurin da na koya musu shi zance suyi bani da abinda yafi hakuri dan haka shi zance suyi tunda suka taso sun taɓa ganin wani abunda yafi hakurine a gidan nan dan haka suyi hakuri su zauna a ɗakin mazajensu lafiya.”

Iya abinda yace knn aka fito damu,

Rahimah zuwa ɗakin Mama ni kuma zuwa ɗakin Umma, ina shiga na zuɓe a jikinta, kallon yayunmu tayi tace.
“Ku fita mana a ɗaki.”

Fita sukayi ina kwance a jikinta shafa kaina tayi sannan ta ɗago min kai tace.
“Auta ina ganin ai nagama miki bayani tun a auren Rahilah kuma nasan zaki iya kome dan kare martaban gidan nan, auta wata rayuwa tana can tana jiranki gwargwadon hakurinki gwargwadon kimarki a ido mijinki, auta bani da haufi akanki amma ina da shakku aksn ɗabi’arki ta tsoron bak’in fuska, ki jajjirce ki zama jaruma kema aure ya kaiki ba tsoron wata ba, bance ki rena su ba, amma ban yarda wata ta nuna miki yatsa ki zauna kinakuka ba, koda wasa karki nunawa Kishiyoyinki bakya shiri da mijinki da zaran kika nuna musu baki shiri dashi da wannan abin zasu yake ki har kibar rayuwarsu, Auta so nake kizama fitar numfashin Yunus ki xama bugun zuciyarshi, so nake ki zama nutsuwarshi, ki zame mushi haske rayuwarshi autana ina son ki zama bango yayinda yunus ya ɗibo gajiyarshi ya jingina a gareki ina tsorataki da lalaci, ragonta, rashin iya magana, rashin ɗa’a, ban baki shawaran rabashi da kowa nashi ba, Maryam ki zama adila karki saka ido akan abin hannunshi idan yabaki ki nuna mishi godiyarki, sannan kice ya kara yawa Iyayenshi hidima, Auta bari na baki wani sirri karki taɓa yin sati baki nime wani abu kin bashi ya kaiwa Iyayenshu musaman Mahaifanshi da matar babanshi, auta kannen shi da sauran danginshi ki kyautata musu nina faɗa miki wannan da kanki zakice Umma abinda kika sani ga tukwaicinsa, ki daidaita rayuwarku sannan idan ya karkata ki dawo dashi kan hanya, Kiyi imani da Allah zai baki mafita da nasara akan komi Maryam Sajida ga wannan alkur’ani ne sai hisnul musulim, sune iya abinda zan baki, ni bana boka bana malam amma nayi imani da Allah Maryam Sajida ban umarceki da shan maganin mata ba, dan bai gyara komi sai ɓata aure kiyi tattalin kanki da lafiyarki musaman alauranki baya bukatar wani abu bayan ruwan zafi, Maryam! Maryam! Maryam! Sau uku nakiraki ki nutsu dan akwai lokacin da bazan iya taimakonki ba, juriyarki da hakurinki sun isa su karɓeki, karki taɓa bijire mishi, matukar kinsan ba hakkin wata ya tsalaka ya kawo miki ba, ni dai na umarceki da ki zauna lafiya da kowa, banda saurin fushi da fusata Allah yayi miki albarka, yasa nan da wasu watanin an kawo minke ce dan sunan wanka Autana tayi girma ta zama mace koda yake da sauranki dan bakisan Waye zaki zauna dashi ba, aikin gabanki ki sannan waye Yunus.”

Kuka nake tare da kamkame Ummata ina cewa.
“Umma don Allah karku kaini na fasa zuwa ina son zama daku.”..

Shafa kaina tayi sannan tace.
“Hakuri zakiyi dan zaria za’a wucce dake, kuma ana jiranku Auta keda zaki zauna a garin nan miye na kuka kuma, idan kika samu kulawar mijinki mantawa zakiyi da Ummanki, maza tashi ana jiranki karki ɓata musu lokaci kinji autana.”

Kiransu Shema’u tayi suka fitar dani, sannan aka kawo mata Rahimah kamar yanda tayi min haka ta mata, ashe mama amarya kan babu abinda ta iya cewa, sai Allah ya baku zaman lafiya kinga halin da nake ciki ki zauna lafiya da mijinki nima shine nawa kwanciyar hankalin tashi kuje ana jiranku.”

Aunty Asma’u da Aunty Hamdiya da gausiya suka tawo min, Aunty Shema’u da Aunty Shukrah da Matar Ya hayat, suka raka Rahimah, katsina.

Rahilah kan bata bisu ba zaria ta biyo mu, dakyar aka rabani da jikin Umma aka sakani a mota……..

*Ina taya dukkanin musulmin faɗin duniya murnan Sallah babba, Allah yasa’ayi lafiya ya bamu lafiya da zaman lafiya……Barka da Juma’a ayi shagalin sallah lafiya ina jiran ɗaukanina*

#HWA…….
#MATARSO……..
#Mai_Dambu…….
#Danban nake da sauran…….
[8/25, 2:59 PM] Real Mai Dambu:
*MATAR SO*

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER’S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai….

Dedicater To Hafsat Abubakar

_Wannan buk ɗin hakk’in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

*BOOK 1*

Back to top button