Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 16

Sponsored Links

16…..
A nutse Mami tayi ma Kawu na lado bayanin abinda ke tafe dasu kmr ynda tayi ma Ammi, na lado yyi tsit yana kallonta, ganin shirun yyi yawa yasa Mami tace “ya kuma naga kayi shiru….” yyi wata shegen dariya yace “to me kuwa xance maki baiwar Allah ae xancen naki ne naji sa wani iri, idan yarinya kike so kije gidan marayu mana, duk yaran garin nn baki ga na dauka ba sae yar kanina,” Mami bata kuma cewa komai ba, shi ko sae fama da waran sa yake, Aliyu ma dae kasa cewa komai yyi, can Mami ta mike tace “to malam mun gode ssae” ko kallonsa Aliyu bae yi ba ya fice, Mami ta bi bayansa, da sauri Shatu tace “to wae Hajiya yar aiki kike nema ne? Ga Hinde nn bbu abinda bata iya ba wllh, tun daga kan shara wanke wanke kai har girki” mami ta juya tana kallonta tace “A’a ni ba aiki Ikram xata yi man ba, tsakani da Allah nake son riketa in bata ilimi idan Allah ya yrda” shatu tayi tsaki ta koma cikin dakinta, Mami tayi murmushi ta fita daga gidan, Na lado yyi tsaki yace “hka kawae sun shigo sun katse min cin wara na,” shatu ta fito da sauri tana kallonsa tace “to malam don me ma baxa mu ce su dauketa su dinga biyanmu ba, sae dae kuma kar suje su walakanta rayuwarta don yawanci idan yara suka shiga Abujan nn da ciki ko cutar kanjamau suke dawowa, to ma ina ruwan wani don Allah je ka tsayar dasu malam kila karshen talaucinmu ne ya xo….” da sauri Na lado ya mike yyi waje da gudu har Aliyu yyi reverse ya dinga daga masu hannu yana cewa “ku tsaya ku tsaya” Mami ta sauke glass ya karaso da sauri yace “Hajiya idan banda abunki ina kika taba jin anyi hka, kawae ca xakiyi min kina son daukar ikram ta dinga maki aiki kina biyan iyayenta, ba wae kice mu baki ita ba kmr bamu san ciwon haihuwanta ba” Mami tayi shiru tana kallonsa snn ta sauke ajiyar xuciya tace “to in
samu iyayen nata in fada masu hka knn?” yace “A’a ae ba
sae kin je gun su ba kuma, nima nn ubanta ne, sauko mu
koma ciki muyi ciniki” Aliyu ya kauda kansa yana murmushi
hade da girgixa kai, Mami ta fita ta bi sa, suna shiga gidan
na lado yace “to nawa xaki dinga biyan iyayen nata duk
wata” Mami tace “ku dae xaku fada” Shatu tace “ae Ikram
ba baya ba wajen aiki, yarinyar akwae shegen kokari bbu
abinda bata iya ba” Na lado yace “to dae kin ji, duk wata ki
dinga biyan iyayenta dubu ko uku ne” Mami tayi murmushi
tace “to xan dinga baku dubu ashirin duk wata” Shatu da
mijinta suka yo waje da ido a tare hade da cewa “iyyee” Na
lado ya washe hakora yana murxa tafin hannunsa yace
“Allah sarki Hajiya, kmr kuwa kin san talauci yyi ma iyayen
nata katutu” Mami bata ce komai ba ta bude jakarta ta kirgo
dubu ashirin ta mika masa tace “to ka kai ma iyayen nata”
kasa karba Na lado yyi sae kallon kudin yake yana kikkifta
ido, Shatu ta karbe ta saka cikin rigar nononta tace “to bari
in kai masu Hajiya, amma yau xaki tafi da ita ko” Mami tace
“idan sun bani ita” Shatu ta figi mayafi tace “bari ina xuwa
ynxu yanxun nn, ae ya xama dole ki tafi da ita yau kar a
shiga hakkin ki” tana kai wa nn ta fice, kmr xata tashi sama
ta isa gidansu Ikram, Ammi na wanki tsakar gida, tayi
mamakin ganin shatu, shatu na kirkiran murmushi tace
“wanki kike Aisha” Ammi tace “sannu da xuwa maman
Hinde daga ina hka” Shatu tace “wllh daga gida daxu Na
lado ke gaya min abinda ya faru jiya, shine naxo jaje, ina
Ikram din ynxu” Ammi tace “tana can gidan yakumbo tun
jiya wllh” Shatu tace “kai gskya kam gwara ki bar ta can
kawae, to bari in koma Aisha ynxu na gama suyan wara
nace bari in xo dae” Ammi ta rakota har kofar gida tayi
mata gdya snn ta koma ciki, da gudu da gudu Shatu ta isa
gidan yakumbo, yakumbo na bayan gida ta shige dakinta ta
ga Ikram xaune tana ta faman xare tabarma du ta tsiyace
tabarman, Shatu tace “Ikram, maxa xo muje mamarki tace in
kawo ki” Ikram tace “A’a yakumbo tace baxan sake fita ba,
baki san jiya saura kadan kai na ya fita ba” Shatu tace “lah,
in ji wa ya gaya maki kai na fita maxa tashi muje gun
Amminki tana nemanki kinji Ikram” bata jira me Ikram xata
ce ba ta daga ta sama, ta ja ta suka fice daga gidan, Ikram
sae kuka take tana cewa “ni ki kyaleni baxan je ko ina ba”
janta ta dinga yi kmr dabba tana kunduma mata xagi har
suka iso anguwarsu, Aliyu na xaune cikin mota ya hangosu
ya fito da sauri, ikram na ganinsa ta fixge hannunta daga
na shatu tayi gunsa da gudu tana kuka ya durkusa gabanta
ya dafa ta yace “me ya faru Ikram wa ya dokeki” tana kuka
ta nuna masa Shatu tace “ita ce ta dauko ni daga gidan
yakumbo tana son Anty ta yanka min kai” yace “wace
Antyn?” tace “me bani Ayaba mana wnn mamar taka,
Yakumbo tace min kan yara take yankewa a bayan gidanta”
Shatu tace “oho ga ta nn dae mun fita hakkinku mu dae, ae
dama yakumbon nn tsinanniya ce dole ta kitsa maki karya”
ta yi cikin gida tace “to Hajiya gata can kofar gida” Mami
tace “iyayen nata sun yrda knn?” Shatu tace “da gudu ma”
Mami ta mike tayi masu gdya snn tayi masu sallama ta fita,
Shatu da Na lado na biye da ita a baya suma sae gdyan
suke.

Back to top button