Hausa NovelsIkraam Hausa Novel

Ikraam 39

Sponsored Links

Ikraam~ By Khaleesat Haiydar 39…… Khaleel dae bae ce komai ba sae murmushin da yyi, Mami ta dauki wayarta ta kira Aliyun sae da ya kusa katsewa ya daga tace “ae ni ban san kana da xuciya ba sae yau, to kadda Allah yasa ka shigo din, files kuma basa wajena suna gun Dr Musa” tana kai wa nn ta katse kiran, khaleel yyi dariya yace “wae me ya hada ki da Hydar dinki ne hka Mami, Aliyu ne fa” Mami bata tanka sa ba ta mike ta ja Ikram suka wuce sama. Yau Asabar da safe Mami ta shirya Ikram ita ma ta gama shirinta xasu can gidansu, Ikram sae murna take xata gun Amminta, suna fitowa falo Mami tace ma khaleel ya tashi ya kai su, ya juya da sauri yace “ina” tace “can gidansu Ikram,” ya bata rae yace “haba mum wkend guda ma mutum baxae huta ba bayan duk wahalan da ya sha durin wkdayz” Mami tace “ehh baxa ka huta ba” bae kuma cewa komai ba ya mike ya haura sama ya canxa kananan kayan dake jikinsa xuwa manya snn ya fito rike da car key dinsa, suna fita parkin space Ikram tace “yaya Khaleel wancan motar xa mu shiga ba wnn ba don ni bana son shi” harararta yyi ita ma ta rama, yyi kwafa ya bude driver seat ya shiga ya tada motar ta xaga da sauri ta bude gaba ta shige, Mami kam na tsaye tana waya, ya daka mata tsawa yace “ke koma baya kar na kwade ki” ta murguda masa baki tace “ni nan xan xauna baxan koma baya ba” Mami ta shiga bayan motar tace “A’a Ikram gaba kika xauna” Ikram ta juya tana kallonta tace “Mami ni nn nake so” Mami tace “to yi xamanki” tayi ma Khaleel dake kallonta gwalo, ya dauke kansa ya gama ba motar wuta snn suka fita daga gidan, cikin minti arba’in suka isa anguwarsu Ikram tun bae gama parkn ba ta shiga kkrin bude motar ta fita ta kasa, Mami tace “to ae sae ki jira motar ta tsaya ko Ikram” yana gama parkn Mami ta bude motar ta fita, Khaleel ya riko hannun Ikram da sauri yace “tsaya Mami ta gama fita ke” juyawa tayi tana kallonsa tace “meyasa” bae ce mata komai ba, Mami na fita ya kulle motar yace to fita, ta dinga kkrin bude motar ta kasa, ihu ta fasa tana kallon Mami da bata san me ke faruwa ba har ta shiga gidansu Ikram, yace “bani kike ma gwalo ba ko, ae bbu inda xaki yau, baxa ki ga Ammin taki ba” ta fasa masa kuka tana bubbuga motar, fixgota yyi yace “to share wnn hawayen idan ba hka ba baxan bude maki ba, kuma kice baxa ki kuma min gwalo ba” ta turo baki ta shiga share dan hawayen fuskarta, handkerchief ya ciro ya mika mata yana kallonta ta karba ta shiga share hawayen, ta fara fyaco Majina daga hancinta ya fixge handki dinsa da sauri ya xaro mata ido yace “da handkerchief dina xaki share majina” murguda masa baki tayi tace “to ba ya ki fitowa ba ma” ya bude mata motar yace “watarana sae na cire maki wnn bakin idan kina min irin hka” ta fice daga motar ta kuma murguda masa bakin snn tayi cikin gidansu da gudu tana Ammi oyoyo. Xaune ta tarda Mami da Amminta a daki, ta xube jikin Amminta cike da murna tanai mata oyoyo, Ammi ta rungumeta kawae tana murmushi, Ammi tace “to kin je kin gaida su Altine ne,” Ikram tace “A’a ni nayi sabon kawaye a sabon makaranta na” Mami tace “A’a je ki ki gaida su suma ae kawayenki ne Ikram” ikram ta mike tayi kofa har ta fita ta dawo da sauri tace ” Ammi Abbana fa”Mami ce tace “yana kasuwa Ikram, je ki ki dawo sae mu je mu gaida shi” Ikram ta fice da sauri xuwa gidansu Altine, a bakin soro suka ci karo da Khaleel xae shigo gidan ko kallonsa bata yi ba xata fita ya fixgota yace “ina xaki” tace “to ba Mami bace tace in je in gaida tsohon kawayena su Altine ba” bae ce komai ba ya sake ta ta fice, snn ya shiga cikin gidan, ko minti biyar ba ayi ba Ikram ta dawo wae ta gaidasu, Ammi dae sae kallonta take tana mgna da Mami kmr ba Ikram dinta mara ji ko kadan ba, yini suka yi ranar a gidan duk da Ammi sae addua take su maxa su tafi kafin Abban Ikram ya dawo dan har ranar bae san ita ta bada Ikram da hannunta ba, duk da ya fara xargin hkn ganin bata wani damu kmr ynda ya damu ba, sae addua take a xuciyarta Allah yasa yan anguwa basu lura da ikram ba don mmn Altine ce kadae tasan abinda tayi, amma yau ta dau alkawarin xata gaya masa gskyan komai. Karfe hudu da rabi Mami ta kira Khaleel don ya fita ya xo ya maida su gida, cikin minti sha biyar ya iso Mami tayi sallama da Ammi tace xasu tafi gobe xata dawo ta dauki Ikram Ammi tace su tafi kawae ba komai. Gidansu Aliyu Mami tace Khaleel ya kai su, Khaleel yace “mami ni baxan fa shiga gidan ba ajiye ku kawae xanyi in tafi” Mami tace “to baka isa ba mara xumunci, har yara sun gane halinka kai dae ban san irinka ba wllh” karfe shidda saura suka isa, shi dae Khaleel har lkcn fuskarsa a daure yake, Ikram tace “lah Mami mun taba xuwa wnn gidan” Mami ta fito da ita daga motar tace “eh mun taba xuwa” tana rike da hannunta suka nufi balconyn shiga falon gidan, Mami tayi sallama suka shiga falon, Aliyu da seeyama ne xaune falon yana gwada mata abu a laptop” seeyama kadae ce ta amsa sallaman a fili ta mike da sauri tana ma Mami sannu da xuwa, Ikram ta wara ido ganin Aliyu tace “yayana” da gudu tayi gunsa ta fada kansa ta rungumesa.
[2/25, 08:35] Zjy: ~Ikraam~ B

Back to top button