Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 2

Sponsored Links

©️ HASKE WRITERS ASSOCIATION.
_(Home of expert & perpect writers)_

 

*GARIN DAƊI…….!*

*_NA_*

*_UMMI A’ISHA_*

*Wattpad:ummishatu*

 

*2*

 

~~~Ganin na zurfafa wurin tunanin da baida wani alfanu ya sanya Maryam zungurata tare da faɗin,

“tunanin me kike yi ne kuma? Wai dan Allah menene damuwarki ƙawalli?”

Numfashi na ajiye ahankali kafin na kalleta ina sake gyara zamana bayan na jingina bayana da jikin gadona,

“kawai mamakin kalamanki nake ta faman yi, ta yaya ma zaki kwatanta zuciya ta da misalin mutanen da basa jin ƙamshi ko wari? Ni dai ina ji acikin raina kawai dan yaya faisal ba type ɗina bane shiyasa bana jin sonshi acikin zuciya ta”

“dan girman Allah kibar maganar nan ƙawalli, kawai muyi maganar abinda yadace muyi wurin karɓarsa, me kike ganin za mu shirya masa?”

Na san dan kawai abar maganar yasa ta faɗin haka, share maganar nima nayi nai tsam da raina sannan na bata amsa da cewa,

” nifa da snacks ma kaɗai zan haɗa masa ai ya isheshi kuma bamu wahalar da kanmu ba ”

Hararata tayi tare da jan ɗan ƙaramin tsaki,

“mtswww kina da damuwa wallahi, ta yaya zamu bashi snacks kaɗai? Gaskiya koda zamu bashi snacks ɗin to ya zama dole mu yi masa girki”

“nifa gaskiya agajiye nake kema kin sani, dama weekend ne kaɗai ranar hutuna to shima weekend ɗin gashi yazo min babu hutu”

“wallahi ko zakiyi me sai mun yi masa girkin nan, mutum zai taso tun gari igari ya Abuja yazo takanas saboda ke kice wai iya snacks za a bashi? Wannan ma ba zai yuyu ba”

“to naji, yanzu ke aganinki me da me yadace muyi masa?”

“yawwa yanzu kika yi magana, fried rice ma kaɗai ta isa da ɗan pepe chicken ɗinsa sai cream cocumber and apple salad inyaso sai ayi snacks ɗin da lemon kwakwa”

“shikenan to babu matsala zuwa goben da safe sai muyi”

“haka nake son ji, ko kefa, bari in tashi in je gida sai goben”

Mayafina na ɗauka na bi bayanta domin yi mata rakiya, muna tafe muna sake tattaunawa har muka zo daidai sashen samarin gidan mu wanda a halin yanzu iya yaya Abdul hakim ne kaɗai aciki domin yaya Abdallah yayi aure shi kuma yaya Abdurrahman ya tafi bauchi wani aiki, muryar yaya Abdul hakim muka tsinkayo yana cewa,

“idan kika sake kika fita ahaka sai jikin ki ya faɗa miki….”

Jikina na shiga dubawa amma banga aibun shigata ba sam domin kuwa riga da wandone ajikina masu taushi sai mayafi da na yafa,haushin hakanne yasani juyawa na koma ban ƙara bi ta kan Maryam ba dake tsaye suna gaisawa dashi, ina komawa ɗakina nayi salla bayan na idar na sake komawa wurin su Annie waɗanda ke zaune cikin wata runfa dake cikin farfajiyar gidan mu, zama nima nayi bayan na zubo abinci, nan na ɓata lokaci har zuwa lokacin da Abba ya shigo nan kuma muka rankaya muka bishi sashensa, Abba yana mutuƙar ji dani domin sunan mahaifiyarsa gareni haka kuma shine da kansa ya saka min sunan da ake yi min alkunya dashi wato widat. Ganin ƙarfe goma saura ya sani yi wa su Abba sallama na wuce ɗakina, miss called nagani guda biyu na yaya faisal, shirin bacci nayi ina tsaka da addu’a naji wani kiran yana shigowa, ɗauka nayi bayan na kwanta na nutsu ina saurarensa,

“Ko gimbiyar ta fara bacci ne na tasheta? Ni ɗinne akwai ni da rashin haƙuri in dai akanki ne….”

Danne abinda nake ji nayi na ƙirƙiro murmushin dole nayi wanda har shi saida ya jiyo sautin fitarsa, sau da yawa bana jin daɗin hirar da yake yi min kawai dai ina daurewa ne in danne in saurareshi amma ba wai dan yana burgeni ba,

” ba bacci nayi ba, ina wurin Abba ne kuma na bar wayar a ɗaki sai yanzu na shigo”

“ƴar gatan Abba, ai najima da sanin dama Abba ya naji dake, duk gidan nan babu wanda ya kai mu gata”

“har da kai a tsokanar?”

“a’a ba tsokana bace, na san bacci kike ji kin dawo daga aiki kin gaji, dan haka bari na barki kiyi bacci kafin mu haɗu gobe”

“shikenan nagode”

“kiyi bacci lafiya, bye bye”

Kashe wayar nayi na turata can ƙasan ɗaya pillow na dake gefen kaina domin dama baccin nake ji kamar ya sani shiyasa lokaci ƙanƙani bacci yayi awon gaba dani. Misalin ƙarfe 11 saura na tashi daga baccin da na koma bayan sallar asuba ganin yanda lokaci ya tafi ya sani zaro ido a raina ina cewa,

“har yanzu ƙawalli bata zo mun ɗora girkin nan ba”

Brush kaɗai nayi na fita amma sai dai me? Tun bayan fitowata nake jiyo wani lafiyayyen ƙamshi wanda ya tsinkar min da yawu, kitchen ɗin mama na shiga wanda daga can ne nake jiyo tashin ƙamshin, ina shiga na iske ƙawalli tanata cin uban aiki kuma ita kaɗai, ta sauke fried rice tana kwashewa cikin warmer sannan ga samosa tana soyawa gefe ɗaya kuma tana yin chicken pepe, sakin baki kawai nayi na tsaya ina kallonta gaba ɗaya ma na rasa abinda zan furta,

“yan mata sai yanzu aka tashi? Barka da fitowa”

“haba dan Allah ƙawalli, yanzu maimakon ki tasheni muyi aikin tare sai ki zo kiyi ta wahala ke ɗaya? Oya tashi in ƙarasa”

Murmushi tayi sannan ta miƙa hannu ta ɗauko plate guda ɗaya na tangaran ta soma zuba fried rice ɗin aciki,

“na san kina jin yunwa to ga taɓi kije kici idan kin gama kiyi wanka ki shirya dan babu mamaki ya taho…. Ki duba cikin fridge salad ɗin da na haɗa na ciki sai ki ɗan ɗibi kaɗan dan na baƙo ne kawai dai na sanmiki ne….”

“dan Allah kibar shi in ƙarasa kema kije ki huta” na faɗa ina marairaicewa,

“zancen kike so, nifa na gama aikina malama, idan ma zaki karɓa kije kici gara ki karɓa idan kuma baki karɓa in mayar abuna in juye dama albarkacin yaya faisal kika ci….”

Murmushi nayi na karɓa ina harararta,

“har wani ma albarkacin sa naci? Shi awa”

Bata kulani ba ta maida hankali wurin soye soyen da take yi ganin haka ya sani wucewa falon mama na ɗebi salad ɗin kamar yadda tace sannan na zauna na fara ci ina sake jinjina halacci da mutunci irin na Maryam duk da na san nima ɗin idan nice zanyi mata fiye da haka to amma a ƙawayen yanzu a wannan zamanin ba lallai asamu waɗanda suke ƙawance tsakani da Allah kamar yadda muke yi ba, ina ci ina duba lokaci ta agogon bangon dake kafe cikin falon ahaka na kammala na wuce ɗakina, saida na buɗe wayata sannan na fara shirin shiga wanka, massage ɗin yaya faisal ne ya shigo nan na buɗe naga yace min ya taho yana hanya harma ya wuce Kaduna, reply na mayar masa cewa Allah ya kawo shi lafiya, daga nan na shiga wanka a raina ina cewa gara inyi inyi in fito dan nasan yanzu zan ganshi ya ƙaraso saboda bala’in gudu gareshi a mota sam bai iya driving a hankali ba. Bayan na fito daga wanka ina shiryawa ƙawalli ta shigo riƙe da plate tana cin fried rice,

“sannu da aiki, nagode madalla Allah ya bar zumunci…”

“wannan yarinyar…. Kina abu kamar wata tsohuwa wadda ta shekara ɗari a duniya, shegen manyance”

“daga godiya shine manyance? Ai shikenan, ya kusa ƙarasowa”

“Allah ya kawoshi lafiya…”

“amin” na amsa ina ƙoƙarin ciro wata doguwar riga ta wani yadin material milk colour dama kusan irin shigar da nafi yi kenan doguwar riga dan zai yi wahala ka ganni da riga da skirt ko zani, daga doguwar riga sai riga da wando, turaren Arabian oud nayi amfani dasu sannan na saka kayan na yafa baƙin sirrin gyale, ina zaune kusa da Maryam muna hira naga kiran yaya faisal ya shigo,

“Kinga har ya ƙaraso ba” na faɗa ina ɗaga wayar ai kuwa ina karata a kunnena naji yace “madam gani na zo”

“ok to ina zuwa” na bashi amsa kafin na cire wayar daga kunnena na miƙe tsaye ina sake duba fuskata a mirror, ni na fara yin gaba ita kuma ƙawalli zata biyoni daga baya.

Kamar koda yaushe a sashen su yaya Abdurrahman na iskeshi ɗakin yaya Abdul hakim, ya sha gayunsa cikin wani sabon lallausan yadi fari kansa sanye da hula, ganina na shigo yasashi yin murmushi yana kallona,

Zama nayi ɗan nesa dashi na fara gaidashi fuskata a sake duk da saida nayi namijin gaske kafin hakan ta kasance. Muna zaune muna ɗan taɓa hira wacce mafi yawanta ta aikina ce ƙawalli ta shigo hannunta ɗauke da babban faranti wanda ta ajiye agabansa itama suka shiga gaisawa, ta ɗan jima sannan ta fita ta tafi, nikam har saida lokacin sallar azahar yayi sannan na samu na fito na nufi sashen mama tun daga nan ban sake komawa wurin sa ba har sai bayan da aka yi sallar magrib duk da massage ɗin da naga ya tutturo min akan wai in zo in ɗauki kayana da ya kawo min, sai da na bari ƙawalli ta dawo sannan muka je tare bayan na sake caɓa ado cikin wata doguwar riga ƴar kanti mai santsi, nan ta kwashi kayan ta fita dasu ta kai cikin gida, tare dashi muka shiga gidan suka gaggaisa dasu mama sannan ya shiga wurin Abba, tun daga nan nikam nayi sallama dashi na wuce ɗakina, kayan da yaya faisal ya kawo min nagani saman gadona ƙawalli ta ajiye min su nan na zauna na soma dubawa, turaruka ne yan ubansu designers sai kayan ciye ciye su chocolate kala daban daban sannan sai kwalin sabuwar waya ƴar yayi mai shegen tsada. Kinkimar kayan nayi na nufi wurin mama dasu domin nuna musu amma koda naje sai naji tace ai tuni Maryam ta kawo musu sun gani dan itace ma ta umarceta da ta kai min kayan ɗakina suma ga irin tsarabar da ya kawo musu, fruits nagani kaya guda tun daga kan lemo, ayaba, abarba da apple, apple ɗin na ɗauka guda ɗaya na wuce ɗakina na ajiye kayan na soma shirin bacci bayan na gabatar da sallar ishah lokacin misalin ƙarfe tara da rabi (9:30) na dare, kishingida nayi akan gado na na ɗauki apple ɗin da na shigo dashi na fara gutsira ina ci, wayata na hannuna ina duba posting ɗin da aka yi a Instagram dan yau gaba ɗaya ban hauba sai yanzu, kiran da ya shigo cikin wayar tawa ne ya katse min kallon da nake yi, “yanzu zai katse min jin daɗi” na ayyana hakan acikin raina ina ƙoƙarin ɗaga kiran,

“albishirinki….. Abba yace in turo magabata na……” iya abinda na iya ji kenan sakamakon silmiyewar da wayar tayi ta faɗi………………. ✍

 

 

*_Ummi Shatu_*

Back to top button