Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 32

Sponsored Links

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect Writers)_

 

*GARIN DAƊI……!*

 

*_NA_*

_*UMMI A’ISHA*_

PAID BOOK #500

*Wattpad:ummishatu*

{32}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Ban san tsawon lokacin da na ɗauka ina shaƙar baccin wahala ba domin lokacin da na tashi tuni har rana ta fito, a hankali na buɗe idanuwana, ni kaɗaice acikin ɗakin hakan yasa na maida hankali na wurin tunanin yadda zanyi in tashi har in kai kaina bathroom saboda gaba ɗaya ilahirin jijiyoyin jikina sun ɗaure sai uban tsamin jiki da nake fama dashi take na tuno hirarmu da Ƙawalli tun shekarun baya wai taji ance jijiyoyi 40 kuma duk sai an tsinka su, duk da ina fama da kaina hakan bai hanani dariya ba araina ina cewa ai wataƙila ma ni jijiyoyin da Samz ya tsinka sun kai 100 irin wannan azaba haka,

Samu nayi na yunƙura na tashi zaune, nan take idona ya sauka kan jinin da ya fita a jikina daren jiya faca-faca ai ban san lokacin da na ƙwalla ƙara ba wadda saida naji ƙasa na ya amsa sai kuma na fashe da kuka, ƙofa naga ya buɗe ya shigo yana sanye cikin blue black ɗin t shirt da baƙin trouser daga gani fita yayi ya dawo,

“am sorry baby…. Me ya saki kuka?” naji ya faɗa lokacin da yake hawowa kan gadon, da jajayen idona na kalleshi amma bance komai ba sai cije baki da nake yi, shima idanuwansa ne suka sauka kan jinin da na gani wanda shi dama already ya ganshi, kama ni yayi yasa a jikinsa yana rarrashi na amma na kasa yin shiru ni kaina ban san dalilin kuka na ba shin raɗaɗin da nake ji da zugi ko kuma farin cikin na kawo martaba ta inda ya dace, ko kuwa takaicin rabuwa da abin da na jima tare dashi,

“Baby….. Menene abin kuka wai? Dama ba ni kike yiwa tanadi ba?”

Kai na girgiza masa alamar shi nake yiwa,

“ok to ai idan nine farin ciki zaki yi tunda gashi kin bani abina kuma nayi farin ciki…. Kin sani cikin duniyar da ban taɓa zuwanta ba, banma san da ita ba sai jiya, thank you baby… Am grateful”

Duk da naji daɗin kalamansa amma hakan bai sa na daina kukan ba, daƙyar dai ya lallaɓa ni da taimakonsa na shiga toilet, saida na daure na shiga ruwan zafi sosai na gasa ko ina na jikina amma duk da haka jina nake kamar ba daidai ba kai anya mutumin nan aika aikar da yayi min ba sai na dangano da hospital ba? Wallahi jina nake kamar sai an ɗinke ni dan ina jina da banbanci sosai akan yanda nake da,

Wankan tsarki nayi da ruwan ɗumi sannan na fito ina ɗaure da towel har lokacin jikina banji ya gama warwarewa ba daga tsamin da yayi sai dai ya ragu da kaso mai yawa, baya cikin ɗakin dan haka na sake na shirya na saka kayana sannan nayi salla, ina idarwa na koma saman gado na kwanta dan tun kafin infito ya cire bedsheet ɗin yasa wani, ina nan kwance ina tunanin rayuwa da abubuwan da suka faru daren jiya wanda basu da maraba da duniyar mutuwa naji motsin shigowarshi, lumshe idanuwa na nayi har ya ƙaraso kan gadon,

“am soo sorry baby i left you alone….. Muna tare da yayanki ne wai your friend has made a yummy breakfast for us…. Tashi ki gani”

Sai lokacin na buɗe idona ina kallon farantin da yake riƙe dashi sosai abin ya bani mamaki jin wai yaya Abdul hakeem ne ya kawo mana breakfast ɗin da Ƙawalli tayi kuma wai harda zama su yi hira da Samz koda yake naga yayan ya sauko tunda jimawa amma ada kafin auren mu babu wanda ya tsana sama da Samz baki da baki ya faɗa min wai wallahi ya tsani wannan kafirin ɗan iskan saurayin nawa kuma idan ya sake ganina dashi sai ya targaɗa ni, kuma shine yayi kutun kutun ɗin da su Abba suka rabani dashi dan kusan kowa a lokacin kallon ɗan iska yake yiwa samz gani suke kawai yazo ne dan ya gurɓata min rayuwa, ni kaɗai na yarda dashi kuma na san ba ɗan iska bane,

“Baby….. Tashi mana” ya sake faɗa cikin sigar rarrashi da kwantar da murya, a hankali na tashi na zauna ina kallon abincin da ya fara buɗewa, wasu ƴan ƙananan food flasks ne gwanin sha’awa daidai cikin mutum biyu har guda huɗu,

Na farko soyayyiyar awara da ƙwai ne aciki sai ɗayan mai ɗauke da soyayyen dankali da ƙwai, ɗayan kuma sos ce aciki sai na Ƙarshen wanda aka zubo farfesun kayan ciki, ai tunda naga awara naji yawuna ya tsinke ai ni da Ƙawalli mun san ta kan kwaɗayi lokacin da muna yara gaba ɗaya kuɗin mu wurin masu awara take tafiya, ta san ina bala’in son awara shiyasa ta yimin shi kuma oga tayi masa dankali, hannu na miƙa zan ɗauki awarar ya ɗauke, ɓata fuska nayi zanyi masa kuka,

“My crying baby……..” da kansa ya fara bani ina ci, awarar tayi daɗi danma babu yaji sai sos, ganin ina shirin cinyewa shi bai ci ba ya sani kallonsa nace,

“kai fa?”

“No… Wannan ai na baby ne, ki ci kawai”

Sai da na ƙoshi dam sannan shima yaci dankalin ya ɗauko min ruwa na sha duk ina zaune saman gado kamar wata sarauniya, kwanciya nayi a jikinsa atare muka yi bacci har wurin azahar dan bugun da ake yiwa gate ne ma ya tashe mu dan duk wayoyinmu suna kashe, shi ya fita jimm kaɗan sai gashi ya dawo wai abinci aka kawo mana daga gidanmu su Anty na amma sunƙi shigowa wai sauri suke akwai inda zasu je, murmushi nayi na tashi na shiga toilet nayi alwala na fito, shi kam masallaci ya fita, bayan na idar na rakuɓe jikin gado ina tasbihi har ya dawo,

“Baby wai lafiya kuwa?”

Girgiza masa kai nayi nace “Ji nake kamar na yage fa”

Zaro ido yayi kafin ya kama ni na mike tsaye muka zauna gefen gado,

“baby kin yage kamar wata paper…. Let me see”

Babu musu na kwanta na buɗe masa ƙafafuna ya duba,ɓoye firgicinsa yayi yace,

“anjima sai muje clinic a duba ki….”

“ka yaga ni ko?” na faɗa ina ƙoƙarin yin ƙwalla,

“no baby…. Babu komai fa” ya faɗa cikin sigar kwantar da hankali, tashi nayi muka fita falo muka ci abinci ya kunna mana zee world ni dai a kwance na wuni dan duk jina nake a gajiye tunda na tashi yau banyi komai ba sai ci sai kwanciya har magriba lokacin ne yace in shirya ya rakani clinic a duba ni, shiryawa nayi kafin ya dawo daga salla cikin wani c green ɗin lashi mai ɗigon silver da adon stones ajiki, dama ƙamshi yanzu ko ban shafa turare ba fatata ƙamshi take yi, hijabi na saka na ɗauko sabon takalmi flat na saka na zauna a falo ina jiran sa kuma har lokacin ban kunna wayata ba araina inata tunanin dalilin da ya hana ƴan gidanmu zuwa yau dan hatta Bishra ma da nasa rai da zuwanta itama ɗin bata zo ba kamar ta san abin da ya faru, a haka ya dawo ya same ni muka fita yana tambayata ina ya dace muje, tunawa nayi da wani ɗan ƙaramin asibiti da nake raka anty idan ta zo Dr ɗin mace ce kuma likitar mata, napep ya tare mana muka hau har zuwa asibitin,babu wani ɓata lokaci ya buɗe min folder muka shiga wurin Dr Aziza dama inata addu’a kar Allah ya haɗani da idon sani, tare dashi muka shiga dan shi yayi mata bayanin ma matsalata ni kunya bata barni ba, kan ɗan ƙaramin gadon da aka tanada saboda duba patient ta umarceni in hau zata duba ni, saida ta cajeni tsaf sannan na sauko na koma mazaunina na zauna itama ta dawo kan kujerarta,

“Ango na dubata ba wata matsala bace…..Illa rashin sabo, sannan size ɗin is too much for her dan haka dole sai ka rinƙa bi da ita a hankali….. Ba sai nayi mata ɗinki ba kawai zan bata wani ɗan ƙaramin cream da zata rinƙa shafawa but kaima sai ka ɗan ɗaga mata ƙafa for some days Koda kwana biyar ne zuwa 1 week, kafin sannan raunukan dake wurin sun warke dan ta ɗan jijji rauni…. ”

Wani daɗi naji da naji tace ya barni na huta na ƴan kwanaki, dan kamar ta shiga zuciya ta taga abin da ke raina, haka muka baro ofishin Dr Aziza tana ta tsokanata bayan ta bani ƴan shawarwari kan in dimanci tsarki da ruwan ɗumi hakan zai taimaka min sosai sannan kullum in rinƙa shafa wannan cream ɗin har can ciki sau biyu zuwa uku. Sai da muka fara tsayawa ta pharmacy ya siyi maganin sannan muka fita,ta wani restaurant muka biya yayi mana take away na dinner sannan muka wuce gida, sallar isha muka yi sannan muka ci abincin da muka taho dashi, ni dai yau da wuri nayi wanka dan bacci nake ji, a falo na barshi yana kallo yana waya da ƙannenshi wanda ko sau ɗaya bamu taɓa gaisawa dasu ba, ina zaune gaban mirror ina shafa haɗaɗɗiyar humrar da anty ta siya min tun daga garin Maiduguri ya shigo, sanye nake da farar night gown ɗina marar nauyi da kauri, yana riƙe da maganin da muka siyo wanda bai da wani girma dan dududu girmanshi bai wuce na ɗan ƙaramin Maclean ba amma cikinsa kamar Vaseline bai da wata maraba dashi,

“Kamar kinyi shirin bacci ko?”

Kai na ɗaga masa,

“yau baza a jirani ba?”

“Bacci nake ji…”

“ok…. Zo in saka miki maganin”

“uhmm uhmm….” nace dashi ina maƙale kafaɗa, hannuna ya kama ya zaunar dani gefen gado,

“Ba kya son ki warke da wuri? Ki tausaya min mana”

Murmushi nayi araina nace nima ai jiya ba tausaya min ɗin kayi ba, kwanciya nayi ya shafa min maganin sannan na kwanta shi kuma ya tashi ya fita falo, babu ɓata lokaci bacci yayi gaba dani, shi kam dama idan da sabo ya saba kwarabniyar dare, kallo ya tisa a gaba har wurin 1 sannan ya shigo yayi wanka yazo ya kwanta kusa dani tare da jawoni jikinsa, jikina yana haɗuwa da nashi na farka,

“am sorry bada niyya na tashe ki ba…” ya raɗa min a hankali,

“wai sai yanzu zaka kwanta?” na tambaye shi bayan na kwantar da kaina cikin ƙirjinsa,

“yanzun ma ba bacci nake jiba kawai na gaji da zama ni ɗaya ne ina son inji ɗumin jikin ki….”

“Nima tun ɗazu nake son ka shigo, ka barni inata jin sanyi”

“shine kuma ba zaki faɗa min ba, to koma baccinki”

“No, muyi hira”

“No,ina son in ganki kina bacci…. Bacci na yi miki kyau”

“nidai a’a nima ina son ganin baccin ka”

“OK to bari muga waye zai fara baccin”

Hira muka cigaba da yi har bacci yasamu nasarar saceni shi dai ban san lokacin da yayi ba kuma duk da haka ya rigani tashi.

Haka muka kasance cikin so da ƙaunar juna har tsawon kwanaki biyar koda yaushe cikin riritani yake da bani kulawa sannan har lokacin ban fara girki ba take away yake iyo mana kullum da zarar nayi maganar girki kuma sai yace ba yanzu ba in bari in huta in sake warwarewa, iya kawaici yayi wurin bin dokar Dr dan cewa yayi a maimakon kwanaki biyar zuwa shidan da tace shi ya hakura sai bayan kwana goma lokacin na gama warkewa, shaƙuwar da muka yi yanzu ta musamman ce fiye da ta baya shiyasa yau da ya sanar dani wai zai koma aiki jibi dan haka gobe da yamma zai tafi Kaduna zai kwana acan washe gari ya ƙarasa Abuja sai naji duk hankali na ya tashi, wuni muka yi yana rarrashi na tare da yimin alƙawarin wai ranar Friday zai dawo muyi weekend tare wannan dama shine dalilin da yasa bai so zamana a Kano ba dan zamu yi nesa da juna sannan su aikin su babu ɗaga ƙafa dama 2 weeks ya nema kuma daƙyar ma aka bashi 10 days, ni dai daƙyar na saki raina muka kwana cikin farin ciki amma da zarar na tuna tafiyar nan tasa sai inji ƙwalla, da kansa ya kira Bishra akan tazo ta tayani zama zuwa lokacin dawowarsa duk da haka raina bai yi fari ba, ƙin tafiya yayi har sai da yaga ƙarasowar Bishra lokacin ƙarfe 4 saura na yamma, rungume shi nayi na ƙara sannan na barshi ya tafi na koma ciki wurin Bishra ina goge hawayen dake bin kuncina……………..✍

 

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

 

*_Ummi Shatu_*

Back to top button