Yar Zaman Wanka 35-36
Subhanallahi Abban twins lafiya” Cewar Sadiya lokacin da ta sakko idanunta a kan Imran. Kafin Imran da ke kukan zuci da sarari ya yi magana Inna ta yi karaf ta ce.
“Haba Halima yo kya yi maganar lafiya ma kina ganjn mijinki a wannan hali na durƙuso, ƙura’ani ni duk tunani na naƙuda yake ashe wai duk labarin ƙanzan kurege ne mutum a dudduƙe ya zo cewa yake Innarmu, Innata” Cewar Inna tana sakin dariya. Da mamaki Sadiya take kallon wani uban gumi da hawaye ratata a fuskar mijin nata.Ga miciji a cikin singlet ɗinsa sai wani nishi yake fitarwa kamar wanda aka biyo da gudu.
“Ya Allah ni dai ina ganin abubuwan da na kasa gane ko fahimtar inda suka dosa shin wai meye tsakanin Inna da Imran ne?” Sadiya ta jefawa kanta tambayar a zuciyarta tana miƙa hannu za ta fara ƙoƙarin cire masa Hassan ɗin.
“Haba Sa’adiyya wai me yasa kika raina ni ne ya za a yi in yi ta maza in bar baccina dan in taimaki mijinki kina can kina baccin asara, muka ƙayyade zai min rawa da amshi ina masa waƙa amma yanzu ki zo za ki cire masa micijin nan salin alin, so kike ki barni da haƙƙin rawar da ya mini ban cire masa micijin ba ai ni ya kamata na cire masa…
“Sadiya umarni nake baki idan kina son ki shiga aljanna ki cire min micijin nan dan Allah” Imran ya katsewa Inna maganarta dan ya ga jan maganar za take ta yi shi kuma numfashi ma dakyar yake iya yi dab komai yake da faruwa da shi.
“Ke dan Allan can bani wuri ni ɗin da ya rainawa hankali ni zan cire masa, in banda ma fallasa auren bashi ai da tuni ma an yi komai an gama ba tare da kin sani ba, amma saboda girman kai rawanin tsiya irin na Imirana ya ƙi taka rawa da kyau, saboda ya gama ganin makwancina wato ga ƙaramar danga me daɗin tsallaka shi ne yanzu kuma ya ce ki cire masa” Cewar Inna tana ture Sadiya gefe. Sadiya tana shirin magana amma Inna bata, bata dama ba, ta hana ta, hannunta ta kai bayan Imran ta daddage ƙarfinta cike da mugunta ta sanya faratanta ita ala dole singlet ɗin za ta cire tun daga farkon bayansa ta fara karta faratan ta har wuyansa tana ɗago singlet ɗin haɗe da farcen nata, ta kusa gama ɗago singlet ɗin wani uban raɗaɗi ya ratsa Imran na farcen da Inna ta karta masa amma haka ya daure dan burinsa kawai a rabashi da micijin.
Haka ta haɗo da micijin da singlet ɗin ta cire amma ko lokacin da ta zo cirewa daga wajen kunnesa sai da ta haɗa da kunnuwan duka biyu ta murɗe yadda zai ji a jikinsa ba tare d Sadiya ta lura ba, haka dai ya danne har wani ɗan daddaurewa yake.
” Yanzu na san na yi wai mahaukaci ya taka kashi, to Halima sai gareki kuma tun da an cire ai ta faru ta ƙare an yiwa me dami ɗaya sata, har a ce ina nan a bar Imirana cikin damuwa ai idan da kara akuyar gidan sirika ma iya ce da ke dashi ai duk ɗaya ne a wurina ba banbanci” Ta faɗa tana miƙawa Sadiya Hassan da singlet ɗin gabaɗaya.
Wata uwar ajiyar zuciya ya sauke yana jin raɗaɗin bayansa da Inna ta kartawa farce da kuma kunnuwansa suna zafi amma babu yadda zai yi sai dai ya ƙuduri wani abu da ban, sai yanzu ya gama fahimtar cewa babu makawa Inna ce ta kai masa micijin nan.
“Lallai tsuhuwar nan al’amarinta ya girmi tunani na “Ya faɗa a ransa yana mamakin irin ƙarfin halin Inna.
” Yau dai na ga abin da ya turewa buzu naɗi yo banda dalili mai sa a leƙe gindin sirika wai yau ni Imirana ke kira Innata” Ta faɗa tana dariya.
Wani takaici ne ya ziyarci Imran lokaci guda abubuwan da ya sha faɗa cikin gushewar hankali da tsananin tsoro suka rinƙa dawo masa haushin kansa ya rinƙa ji da kuma hashin nauyin baccin Sadiya ai da ta tashi da wuri da bai nemi taimakon Inna ba wanda hakan gashinnan ya zame masa abin gorantawa. Amma dama ya san duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa.
“Yo kuma ai sai ka tashi daga tsugunnen ka tafi masallaci tun da dai ka yi abin kunya yau” Cewar Inna.
“Dama tashi zan yi” Cewar Imran yana ji kamar ya kwaɗe Inna.
“Ba niyya ango ya kwana da wando, yo kana durdurƙusar da kai alamun kunya ka kasa tashi za ka ce wai dama tashi za ka yi, ai fa ka sanyawa zuciyarka dangana Imirana faɗan da ya fi ƙarfinka kake midashi wasa sai ka zauna lafiya da mutane, ai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki”
“Wai kamar ya Inna” Cewar Sadiya da ta fara fuskantar wani abu kenan dai Inna ce ta haddasa komai.
“Abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro, wato ke uwar ƴan son miji shi ne kike bin ƙwaƙƙwafi, kawai ki barni da Imirana dan kura ce kaɗai ta san gidan mai babbar sanda” Ta faɗa tana niyyar fita daga ɗakin.
“Sadiya miƙo min riga a drower” Ya faɗa yana jin haushin Inna na ƙara azalzalashi a kan ƙin yin da na sani a kan abubuwam da ya aikata mata a baya da ma wanda zai aikata mata nan gaba, duk da dai ya san ramin ƙarya ƙurarre ne, kuma rana dubu ta ɓarawo ɗaya ce tak ta me kaya.
“Maza miƙo masa rigar ya tafi masallaci kar ya yi saki na dafe, na ga sai wani hararata yake abin da na masa bai gode ba yo Allah na tuba ban da dai abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma dukansa ake duk taimakon da nake yiwa Imirana a gidan nan ba ya gani kawai dan na sa ya min rawa na ce yake ɗan zazzakuɗa mazaunai yana kaɗa kai shi ne laifin da na masa” Cewar Inna tana kallon Imran fuskarta da alamar dariya, wata uwar harara ya doka mata.
“Wai tsohuwar nan ni za ta yiwa kissa, amma ba komai ki dai bi a hanakali kar tura ta kai bango, dan wanda bai ji bari ba zai ji hoho” Ya faɗa a ransa. Sadiya kuwa Hassan ta mayar kan gadonsa ya ɗakkowa Imran rigar dan gabaɗaya kanta ya kulle da abubuwan nan ko kaɗan Inna da Imran babu wanda ya ke tunanin halin da Hassan ke ciki, wai yana cikin halin ne ma har ya zama ana ɗaukansa dan cika wani buri, gashi kullum cikin ka ce suke ta ka gane dalili musamman ma shi Imran da, ko damuwa da bai yi ba da yawan magana amma yanzu sai take jin har magana yake yadawa Inna a wayance ta kasa gane bakin zaren.
Inna dai juyawa ta yi ta fice daga ɗakin ta je ta ɗauro alwala. Ta dawo tana ɗakko abin sallarta daga cikin jakarta sai ga Imran ya fito daga bedroom ɗin.
“Masallacin ne Imirana sauka lafiya” Ta faɗa tana ƙushe dariyarta ganin ya fito sai muzurai yake. Bai tanka mata ba ya cije leɓe ya sanya kai ya fita ya ɗaura alwala ya tafi masallaci dan zuwa lokacin ma har an kusa kaiwa raka’ar farko.
*HAJIYA*
Tun da ta baro gidan Imran bata zame ko ina ba sai gidan wani Malam Isuhu mai almajira ta daɗe tana jin labarinsa to da yake ma babu nisa sosai daga gidanta amma can sama da su yake. Tana zuwa ta tambaya aka ce yana cikin gidan da sallama ta shiga gidan bayan sun gaisa da matan aka faɗa masa ya yi baƙuwa, bayan an mata iso ta nufi ɗakin nasa tare da matarsa uwar gidansa ita ce ta raka ta har turakar Malam ɗin. Ɗakin cike yake da manyan qur’anai da littattafan addini a gefe guda, ga wasu carbuna manya manya da ƙanana hawan hawa. Zaune yake a kan darduma ya sanya gabansa gabas ga wani ƙaton carbi yana ja. Matar da ta rako ta tana shiga ɗakin ita kuma ta koma. Malam kuwa da ke ɗaura rubutu a leda rubutun cikin bokitin fenti babba, wanda ruwa ne kawai aka zuba tawada a ciki sai a ƙulla a leda ana baiwa mutanen da suka bayar da kuɗi a musu rubutu.
Dan haka ba ya rubutun tawafa kawai yake zubawa a ruwa yana ƙullawa jin an ce ana masa sallama shi ne ya rufe bokitin ya ɓoye wanda ya ƙulla ɗin. ya koma ya zauna a darduma ya fara jan carbi yana mismis da baki.
Sai da ya kai ƙarshen carbin Hajiya tana zaune sannan ya juyo gareta ta fara gaishe da shi tana masa ya fama da kuma ƙoƙari da jama’a, nan ya masa komai lafiya.
“Malam dama wani aiki ne nake so ka min a kan iska…
“Ai mun gama sanin me yake tafe da ke, duk na gani cikin mafarki tun jiya na san da zuwanki, dan haka indai ƙwanƙwamai ne babu abin da ya gagaremu ku da su sai dai ku ji ana labari” Ya katse Hajiya daga abin da take son faɗa masa a kan Hassan da take so ta ce ya je ya masa addu’a ko za a dace ya dawo mutum amma kuma shi sai ya nuna ya san komai ya hana ta ta masa bayani.
” To babu komai nawa ne abin sadaka?”
“Ai abin sadaka sai mun je muke faɗa, kuma yau ina da baƙi ba zan samu zuwa ba sai gobe da yamma”
“To babu damuwa, Allah saka fa alkairi”
“Amin” Cewar Hajiya, tana jin daɗi za a yiwa jikan nata magani.
“Ai kar ki damu mu nan fitar da mutsa mutsai ba komai bane indai muka karanta ayoyin qur’ani to tabbas Allah zai amsa”
Sosai ta ji daɗin maganar tashi, sai da za ta tafi ya ce
“Baki faɗa mini gidan ba”
“Yo ai na ɗauka har gidan ma ka sani a mafarki ”
“A’a ki faɗa kawai an za a faɗa min gidan sai na falka daga bacci kin ji dalil”
Nan ta shiga masa kwatance daga ƙarshe ma dai sai ta gane ya san gidan Imran ɗin, dan ya faɗa mata wani gida da ke maƙotaka da gidan Imran ɗin dan haka sai ta ce masa maƙota ne da gidan da ya faɗa mata, sai da ta tabbatar ya gane sannan ta mas sallama ta tafi abinta.
” Wa ya ga taɓɗi ai ban da kin ce iska babu abin da na sani game da zuwanki amma yanzu ai na kama ki a hannu” Ya faɗa a zuciyarsa bayan fitar Hajiya yana janyo leda da bokiti ya cigaba da ƙulla maganin, rubutun, yana murnar samun aikin nan, kuma ma ya ce mata sai gobe yau yana da baƙi ne dan kar ta raina shi ta ce ba a kawo masa aiki.
Hajiya haka ta koma gida tana ta farincikin samun mafita dan haka ma sai ta ja bakinta ta yi shiru ko su Imran ba za ta faɗa wa ba sai gobe.
Wajen ƙarfe ɗaya da wani abu Inna tana zaune a ƙasa a falon tana cin abinci dan yau ita ra dafa abincin ma Ashrof bata zo ba, wai kanta na ciwo ko haka ne ko kuma saboda tsoratar da ta yi Allah kaɗai ya sani. Imran da ya ci abinci a bedroom ya fito jin ƙaran wayarsa da take caji a falo.
“Assalamu alaikum barka da rana Hajiya” Ya faɗa lokacin da ya kara wayar a kunnensa.
Amsawa ta yi tana tambayarsa mutanen gidan bayan sun gaisa, nan kuma ta ce.
“Imran na je wajen wani Malami Malam Isuhu zai zo da yamma. Shiru ya yi bai ce komai ba Inna da fa kasa kunne tana iya jiyo maganar da ake daga cikin waya, ba handsfree take ba amma dai volume ɗin a ƙure yake.Shiru ya yi yana son gama jin abin da take so faɗa masa.
“Gwara dai ya zo kam Amina dan yau ma micijin nan a wajen Imirana ya kwana a cikin rigarsa” Hajiya ta jiyo muryar Inna ta cikin waya hakan ne ya ƙara tada mata hankali. Wata harara Imran ɗin ya jefawa Inna da ke gatsina mas gefen hanci, haushi ma ya sanya bai ce komai ba jin Hajiya na faɗa a kan me yasa ya kwana da miciji kuma zuwan Malam Isuhu babu fashi dan haka sai ya zo. Hajiya na gamawa ta kashe wayarta ta bar Imran riƙe da wayar sai muzurai yake ya maida cajinsa ya koma ɗaki ya kwanta yana ta nazari tabbas ficewa zai yi daga gidan dan ba zai zauna a maida masa twins ba.A a zo wani maida masa ɗa miciji bayan Allahn da ya baiwa yaron baiwar zai dawo dashi a duk lokcin da ya so ita kuma mahaifiya ce a wajensa babu yadsa zai yi da ita. Sadiya da ke zaune tana shayar da Husaini ta kalli Hassan da ke kan gadonsa rufe da bargo, tana jin tausayin yaron har cikin ranta.
Imran ko da aka fara kiran sallar la’a sar sai gashi ya fito zai tafi masallaci, ya sunkuya zai ɗauki wayarsa daga caji Inna ta ce.
“Wai ni Imirana wannan uban lemukan robar da ka kawo aka jibge ba za a ɗauka min wanda idan Aminiyata Tsahare ta zo gobe ba zan bata da kuma wanda zan bata saƙo ta kaiwa jama’ar garinmu ƴan uwa da abokan arziƙi, ni kuma in yaso idan na gama ZAMAN WANKA zan tafi sai in tafi musu da namn sunan da zan sanya shi a kitse” Ta faɗa tana kallon Imran da ya ɗago riƙe da wayarsa tsabar mamaki ma ya rasa bakin magana, wai ashe har wata aminiyarta ce za ta zo suna lallai tsohuwar nan da ɗora hau take a gado baki kawai ya taɓe bai ce komai ba ya juya ya fice zai yi alwala.
“Uban shegen mugun halin tsiya, yo Allah na tuba meye a lemon roba ban da tsiya ma abu da bai fi a bani sinƙi biyar (cartoon biyar)ko shida ba in bayar a mini bajinta da shi a ƙaunyen kafin in koma” Ta faɗa tana kallon lemon da aka jibge wasu kan wasu.
“Haba Inna wai ke dai bakya ƙi ko gudun abin magana, yanzu lemon da za a raba na ƴan suna shi ne za a baki har katan biyar kuma ma maimakon ki tambayeni sai kika tambayi Abban twins, sannan Inna har Iya Tsahare kika gayyato”
“Halima wallahi ba na son kinibibi ki fita idona in rufe, kuma ni nan Azumi wallahi ban iya munafurci ba shi yasa kika ga ina tambayar abu kuma abin da yasa na tambayi Imirana na ga dai shi ya siyo ba ke kika siyo ba, in tambayeki in tambayi wofi, kuma nawa sinƙi biyar yake da har za a ce na yi zari, sannan Tsahare kuma kamar ta zo sunan nan ta gama dan takanas ta kano na tura ɗan acaɓa ya faɗa mata na tafi Kano kin haihu ta sameni a nan”
“To shikenan Inna amma ai dai kin ga yadda wurin kwanan ma yake aiki ne a gidan nan amma kika gayyato ta”
“Na shiga aljanna na maƙale saboda na ga wurin zama babu fitowa, yanzu Sa’adiyya ni Azumi da na haifi ubanki kike faɗawa wannan magana wurin kwanan banza da wofi wallahi a kan Tsahare za mu ɓata da kowa saboda ita ce ta gaban goshi kuma sai ta zo ta kwana dan wallahi ban gaji rashin arziƙi ba da zan ruge ido in ce ta koma inda ta fito a ranar da ta zo dan rashin tausayi ta yi doguwar tafiya ta koma a ranar to ba da ni ba gaɗa a hurumi, kwana daram sai dai mijinki ya nemi akurkin kaji ko ma zabbi ke wallahi ko na tattabaru ne sai dai ya je ya kwana in ba haka ba mu haɗu mu uku mu kwana a gadon ni ke da kuma aminiyar tawa, in ba za ki kwana damu ba sai ki je wajen mijinki ku kwana a falo, dama burinsa kenan ya jiki a kusa dashi, ko yau ya ɗauka Hassan ke ce baki ga yadda ya ƙwaƙumeshi ba kamar mayunwacin zakin da ke jin yunwa ya samu abinci kai ai wannan yaro da jaraba yake”
“Inna ya aka yi kika sani ke da ya tasheki a bacci ta yaya kila san ya rungumi Hassan ɗin” Cewar Sadiya tana kallon Inna da mamaki.
Imran kuwa da ya taho zai wuce masallaci bayan ya yi alwala ya jiyo Inna na wannan bayani hakan ya ƙara bashi tabbacin ita ce ta kai masa Hassan kai kawai ya gyaɗa ya sanya kai ya fita abinsa.
Inna kwa yatsina fuska ta yi ta taɓe baki ta sanya hannu ta turo ɗankwalinta gaban goshi tare da kauda kai, babu yadda Sadiya ta iya sai ƙyaleta ta yi.
*Masu fitar min littafi ku sani haƙƙina ne, kuɗin karatu kawai kuka biya, ke ma da kike karantawa baki biya ni ba haƙƙina ne duk ina so ku san da haka!*
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA’IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134