Garin Dadi 12
©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
_(Home of experts & perfect writers)_
*GARIN DAƊI….!*
_*NA*_
_*UMMI A’ISHA*_
From the writer of
KAMAR DA WASA
KUMALLON MATA
MIJIN MATACCIYA
SO DA ALAƘA & Rest…..
*Wattpad:ummishatu*
*12*
~~~Kamar kullum cikin shiga ta alfarma na shirya nasha turare nayi breakfast sama sama sannan na fita, wayar Hashim nake ta kira amma no answer baya ɗauka hakan yayi mutuƙar bani mamaki domin a iya sanina baya ƙin ɗaukar waya inda yana kusa, canja shawara nayi nace da mai napep ya sauya akalar napep ɗin a maimakon hanyar office mu kama hanyar gidan su Hashim,
Da fara’a tare da sakin fuska Iya ta tarbeni muka gaisa banji motsin kowa ba sai nata ita kaɗai da alama gidan babu kowa,
“Iya su Amiran basa nanne?” na buƙata kaina na ƙasa,
“Amira ta tafi makaranta Maimunatu…… Shi kuma Hashimu yana ɗaki ina jin bai tashi ba bare in duba shi in yi masa magana kin zo”
Wani ɗan ƙaramin ɗaki mai ɗauke da wani tsohon koɗaɗɗen labule ta shiga, yana kwance yana lallatsa sabuwar wayar iPhone ɗin sa yana hira da hajja Sharifa wacce ke sanar dashi wai da kwaɗayin wainar gero ta tashi irin wadda ake saka garin ƙuli ƙuli aciki a ina zai samo mata?
“Au Hashim dama idonka biyu? Ai na ɗauka bacci kake yi?”
“wallahi idona biyu Iya….”
“ehh ai gashi na gani, baka ji shigowar Maimunatu ba?”
“naji mana”
“Haka fa, to amma kaji zuwan nata shine ba zaka fito ku gaisa ba?”
“Iya ai ke ta zo gaisarwa, ba fa danni ta zo ba”
“Eh lallai, to wai tsaya wannan dalleliyar wayar ita kuma daga ina? A ina ka samota?”
“Iya wani abokin kasuwanci nane ya bani, yanzu ma muna sake tattaunawa ne game da yanda kasuwancin zai gudana, dan Allah kice kawai ta tafi idan na samu lokaci zan nemeta yanzu inada abun yi”
“Yayi maka kyau Hashim, yau kuma Maimunatun za a cewa ta tafi? Ashe baka da kirki ban sani ba? Yarinyar ta tsallake gida fiye da dubu tazo namu amma kake furta irin waɗannan maganganun? To idan ka gadama ka fito, idan kuma baka gadama ba karka fito kayi zamanka ”
Daga haka ta fito daga cikin ɗakin cike da ɓacin rai, duk abubuwan dake faruwa a kunnena ne kuma naji komai domin ɗakin bai da wani tazara da inda nake zaune,
Iya ƙokarin ɓoye ɓacin ranta tayi ta ce min wai yana zuwa amma abun takaici saida ya shafe mintuna 15 bai fito ba, miƙewa nayi ina sake duba agogon hannu na saboda lokaci yaja,
“Iya zan ƙarasa wurin aiki na makara sosai kar makarar tayi yawa” cike da damuwa da ɓacin rai naji tace,
“to shikenan Allah ya bada sa’a ta tsare sai kin dawo”
“amin Iya” na faɗa ina ɓoye damuwa ta dan har ga Allah naji haushi sosai ba kaɗan ba.
Sai bayan da na fita sannan Hashim ya fito daga cikin ɗaki daga shi sai singileti da gajeren wando,
“Da kyau butulu, ai na zaci ko zaka yi butulci bai kamata ka yi wa wannan Yarinyar ba haka bai kamata ka yi wa Allah butulci ba…. Tunda ka samu ido ka daina zuwa makaranta, ka daina zuwa majilissin ɗaukar karatu, ka daina zuwa masallaci, ka daina tashin asubah, anya Hashimu ka ɗauko hanya mai ɓullewa? Yanzu abin da ka yi wa Yarinyar nan kayi daidai kenan? ”
” Iya nifa banyi komai ba, ba gashi na fito ba, tana ina? ”
“Zama zatai tayi tana jiranka sai kace dan kai aka halicce ta? Wallahi tun wuri ka maida hankalinka, baka da aiki sai yawo, wuni zaka yi kana yawo na ba gaira bare ɗan dalili, ba zaka dawo gidan nan ba sai dare kuma daren ma ba na kusa ba, to wallahi ka san inda yake yi maka ciwo…. ”
” Iya nifa ba ko ina nake zuwa ba wurin abokaina nake zuwa muke zama muyi hira ”
” Kunci gidanku kai da abokan naka, abokan da sai yanzu ka same su asama ta kumfa bayan da duk basa tare da kai lokacin da kana makahon ka, wato yanzu ido ya buɗe har ka samu wanda suka fi mu, ada babu mai zuwa gidan nan da sunan yazo wurinka sai Yarinyar nan Maimunatu ita kaɗai amma yanzu wuni za ayi ana yi min sallama a gidan nan mata da maza da sunan an zo wurinka…. To wallahi ba a gidan nan ba, bazan yarda da wannan ba ”
Jin Iya ta isheshi da faɗa ya sake komawa ɗaki yayi kwanciyarsa ya cigaba da chaten ɗinsa ya barta nan tana ta kumfar baki.
Ni kam idan nace bana cikin damuwa ƙarya nake yi, dagaske bada wasa ba naji haushin abin da Hashim yayi min, wai kamar ni intaka ƙafa da ƙafa inje har gidansu wurinsa amma ya watsa min ƙasa a ido yaƙi fitowa ya bar ni nan har in gaji da zama in tashi, ai ko faɗa muka yi ko kuma wani laifin nayi masa bai dace yayi min irin wannan wulaƙancin ba,
Raina aɓace zuciya ta cike da damuwa na hango farida da alama daga masallaci take domin lokacin sallar azahar yayi tun tuni, waving ɗinta nayi nan ta taho wurina tana latsa wayar ta, zama tayi tana faɗin,
“Widat ya ne, you looked some how today, what’s happening?”
Murmushin yaƙe nayi wanda yafi kuka ciwo kafin na kalle ta,
“Wallahi babu komai, kawai dai wata friend ɗina ce ke neman shawara nikuma na rasa abin da zan faɗa mata shine duk abin ya dameni, wai saurayinta ne da suke tare yayi mata wulaƙanci…..” kwashe duk abin da ya faru tsakanina yau da Hashim a gidan su nayi na faɗawa farida amma na ɓoye cewar nice nace ƙawata ce, ajiyar zuciya farida ta sauke ta kalleni,
” wallahi maza basu da kirki wasun su….. Allah dai ya kyauta amma bai kyauta mata ba sam, wataƙila yanzu ya daina son ta ko kuma wani laifin tayi masa yake fushi, shi dai yasan abin da yake going soo it’s better kawai ta tuntuɓeshi taji abin da tayi masa ”
” hakane kam, bari infaɗa mata hakan ” na faɗa ina ɗaukar wayata, cikin sa’a kuwa na ganshi online, saƙo na tura masa kamar haka,
_Hashim kenan, sanin kanka ne ba wai maula na zo wurinka ba balle ka ajiye ni zaune ina faman jiranka, ai ko laifi nayi maka bai kamata kayi min haka ba gara ka fito fili ka sanar dani abin da ke cikin ranka._
Duk da yana online bai buɗe saƙona ba bare ya bani amsa hakan ya sake ƙular dani amma na danni zuciya ta ban sake ce masa komai ba, har zuwa lokacin da ya buɗe ɗin ya karanta nan ma bai tanka ba duk da naga alamar ya karanta ɗin saboda saƙon ya nuna min blue akan layika biyun dake ƙasanshi, sauka nayi daga online damuwa cunkushe fal raina ɓacin rai danƙare cikin zuciya ta, yau dan takaici wuni guda ban sha koda ruwa ba bare inci abinci, rabona da abinci tun breakfast ɗin da nayi a gida shi ɗinma iya ruwan tea ne sai soyayyen ƙwai ko bread ban ci ba, haka na wuni cikin damuwa duk raina babu daɗi har 5 tayi lokacin na tashi daga aiki na fito na hau napep don komawa gida,
Cikin napep ɗinma cikin ƙunci nake dan abubuwan dake ta faman kai kawo acikin raina masu nauyi da sanyawa zuciya damuwa, ina zaune nayi tagumi da wayata a hannuna danger ta tsayar damu muna tsayawa naji an daki bayan napep ɗin da ƙarfin gaske wanda yayi sanadiyyar da muka tafi muka daki na gaban mu, nidai abin da zan iya tunawa kenan sai buɗe idona nayi na ganni kwance kan gadon asibiti ƴan gidanmu na kewaye dani, kan anty Khadija na fara sauke idona wato babbar yayarmu sai Bishra tana zaune kusa da ita sai Anty Salaha gefe ɗaya kuma Yaya Abdul Hakim ne sai ƙawalli na zaune kusa dani,
“Sannu Widat….. An auna arziƙi” Anty Khadija ta faɗa tana tsotsar farar ƙasa dama duk lokacin da take laulayin ciki ba a raba ta da shan farar ƙasa,
“Sannu ya kike jin jikin?” anty Salaha ta tambayeni tana tasowa zuwa kusa dani,
“Da sauƙi” na faɗa ina riƙe kaina wanda ke yi min azababben ciwo, duk sannu suke ta faman yi min, jikina in banda ciwo babu abin da yake yi min domin na kukkuje na daddauje amma anyi sa’a babu karaya ko ɗaya, ganin ƴan gidanmu da irin hirar da ake yi ta sani na ɗan ware dan har wayata na ɗauka nima na hau online,
“Ohh ni Dije waya ta shiga ran bayin Allah ba kaɗan ba ana gadon asibiti ma chaten ake” Anty khadija ta faɗa tana kallo na,
“Ai abun ba a cewa komai, kin san har a maƙabarta ana chaten? Wai mutum yaje maƙabarta kai mamaci amma ya ɗauko waya yana chaten ko amsa kira….” Yaya Abdul Hakim ya faɗa,
“Last time da naje umarah abin ya bani mamaki Hakim wai har a ɗakin Allah sai ka ga mutane da waya a hannu ana chaten ko wani abu me kama da haka, wanda ya je ibada dan Allah me ya haɗa shi da wannan?” Anty khadija ta faɗa tana jijjiga kai alamar ɓacin rai,
” Anty kin manta yanda rayuwar duk ta taɓarɓare ne? Ai abin sai addu’a kawai ” Anty Salaha ta faɗa tana duba takardar dake maƙale a jikin gado na,
Nikam status nayi da cewar ina gadon asibiti na samu accident jiya da yamma ina buƙatar addu’ar ƴan uwa da abokan arziƙi, nan take aka fara yi min fatan samun lafiya tare da kyakkyawar addu’a, gaba ɗaya contacts ɗina kowa yayi min addu’a da sannu wasu ƙafa da ƙafa ma suka zo suka dubani musamman ƴan office ɗinmu da friends waɗanda ke kusa amma banda Hashim duk da ya duba status ɗin nawa ya gani amma ko uffan bai ce ba, hatta Yaya Faisal sai da ya kirani ya dubani dan har yanzu muna ganin status ɗin juna duk da yayi aure watanni huɗu baya da suka wuce amma har gobe muna ɗan gaisawa ko ta chat ne dan har yana ce min so yake ya samu leave zai kawo mana matarshi gida mu gaisa,
Wannan abu da Hashim yayi min shi ya sake ɓata min rai dan confirm yaga status ɗina amma ko sannu maimakon haka ma shi sai status yake ta sakawa a wani katafaren boutique na zamani wanda ya haɗu ƙarshen haɗuwa ya sha decoration shi kansa Hashim ɗin ya haɗu cikin wasu arnan jeans da t shirt baƙaƙe abin ka da farin mutum ya haska sosai idanuwansa sakaye cikin baƙin glass, gefensa wata farar mata ce kyakkyawa itama idanuwanta rufe ruf da baƙin glass wanda ya amsheta sosai da wasu mutane zagaye suna yanka cake da gani bikin buɗe wannan boutique ɗin ake yi kuma ko tantama babu wannan matar itace mamallakiyar wurin domin naga wani hoton nata na daban Hashim ɗin ya ɗora yana cewa “the C. E. O”, shiru nayi na gama kallon status ɗinsa tsab sannan na ajiye wayata acikin raina ina saƙa abubuwa da dama……..
*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*
_*Ummi Shatu*_