Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 51-52

Sponsored Links

5⃣1⃣&5⃣2⃣

*Alhamdulillah naga masoya na Asali, naga kuma masu mugun gajen hakuri, yau ba bawa mai hankali da zaiyi wa kanshi fatan ciwo, tsawon lokacin da nafara rubutu inba wani kwakkwran dalili ba bana kaunar infara typing in tsaya, na rubuta littafi bakwai wnn ne na takwas hakan bai taba faruwa ba, nafada nakuma nafada nabada hakuri mutanen da sukasan halin da nake ciki sunfito sunyi bayani, Amma wai duk da haka wasu zasu rika daukar waya suna tanbaya ta Ina posting dinmu Ina update sister kin ajiyemu kin kyale mu, kuma abin mamaki masu complain din duk wainda suka biya dari biyar ne, Allah sarki akwai sister da tabiya dubu uku Ana bata prvt wlh tun ranar da ta tanbaya nafada mata banda lfy bata kuma bina tace update ba, haka akwai masu dubu biyu dubu daya duk ba wadda tayi complain saboda lfy itace komai idan ba lfy ba Abinda bawa zai iya yi a rayuwa, kuma ciwo inba na Ajali bane yanada iyaka don haka masoya nagode sosai da sosai masu complain kuma Allah ya baku hakuri bazance komai ba*

08032252760
08175479641contact this numbers for more information

 

……………Bacci tasha sosai a kafadar shi, Wanda ya raba dare yana kare mata kallo, wani irin farin ciki yake jin shi a ciki, finally zai kasance tare da ita, zasu rayu su biyu ba wani shamaki ba Wanda zai hanasu sakewa.
Washe gari tunda safe sakon shi ya iso wurin Momy lokacin ta shirya fita aiki, cikin adonta na manyan mata, taci karo da manager din khaleel, yace “ga sako inji mai gida Hajiya. Ya shigo da motar tana sake da baki ya faka wajen Ajiyar motocin su, saurin bude takardar tayi taga Atm din Ahmed da nashi na gida tareda takardun gidan dana company, wani irin faduwa gabanta yayi, me wannan sakon ke nufi? Saurin kiran manager tayi ganin zai fita tace ” kai zo Ina mai gidan naka da yabaka wannan sakon?
“Hajiya ai tunjiya yabar Nigeria bai fadamin inda zaije ba tareda madam dinshi. Ya fita Abinshi domin shidai ya isar da sakon.
Dafe kai tayi tareda jan kafa takoma cikin gidan, tana shiga falon ta zube, ” shikenan ya tafi ya koma, Wayyo Allah na ni balkisu
Nashiga uku na. Tasa kuka mai karfi, Wanda saida masu aiki suka firfito a rude suna tanbayar lafiya?
“Duk ku wuce kubani wuri munafukai magulmata. Da gudu suka koma, Wanda yayi dai dai da shigowar salifa cikin wasu arnan kaya duk jikinta a bayyane, “yau kin tunada mutuwar Ahmed ne Momy? Tafada cikin izgili, “mutuwar ubanki natuna mai farar kafa, yakamata ingano cewa keba Alkhairi bace a rayuwar ya’yana Amma nakasa gano hakan saida nayi sanadin d’ana ya gudu yabarni, nashiga uku na ni balkisu.
Matsowa tayi a fusace ta shake wuyan Momy batareda duba girma ko shekarun taba, ” ubana sa’an iskancin kine? Eh, kuma yanzu ne kika gano cewar ni ba Alkhairi bace a rayuwar ki, kina tunanin don Allah na Auri d’an ki tunfarko? Dukiyar nan mukewa bawani Abu ba, tunda bazan samu kan mijin ba meye amfanin Auren. Dakyar ta kwaci kanta tana jan numfashi da kyar tasamu ya dai dai ta, Wanda lokacin har idon Salifa yakai kan takardun dake zube akasa, saurin kwashe wa tayi tana dubawa ” kawosu nan dukiyar ya’ya na ce bakida hakki a ciki. “Hhhh niko keda hakki da Dukiyar mazaje na, Ina tuminin takaba na na Ahmed? Yanzu shima wannan kisa kawai ya mutu domin bazai dawo miki ba, tunda nikuma nasamu wannan yanzu kinga gida ya zama nawa office company motoci.
Tashi tayi tareda kallon ta ” sharia kuma tazama banza kenan da zaki mallaki Dukiyar mijina da ya’ya na daga sama ni balkisu Ina kallon ki. “Watch and see Hajiya balkisu zan nuna miki inada manya asama, Wanda zai tsaya miki kinja ya gudu don haka bakida wani gata, kibini in labaki cikin gidan nan ko kina kuskure wa in watsaki waje couse this is all my property. Tafada tana juyi tareda kada jiki, ta fice Abinta, cikin kaduwa ta dafe baki “na janyo ruwan kashe kaina. ranar ba inda ta iya zuwa, koda ta Kira kawarta kin dagawa tayi domin Y’ar ta tashafa mata komai, don haka ta tattaro inata inata tayo gidan, suka baje a side din salifar suna y’an da sukaso batareda sanin momy ba. Domin kirjin ta ciwo yakeyi tana cikin tsananin tashin hankali, kanta har wani nauyi yake mata, waye zata fadawa ya taimake ta yadawo mata da Khaleel? Modu, tayi saurin mikewa tareda daukar key tayi waje cikin sauri, ta manta ranarda kafarta ta taka zuwa gidan shi Amma yau batada wani zabi dole taje.
Saida tafito taga motar kawar tata, batabi takaiba domin khaleel ne damuwar ta idan yana nan komai zai dawo dai dai don haka dole tasa yadawo kota halin yaya.

Shikan shi Alhaji yayi mamakin ganin ta yau a gidan shi, saidai yanda ta saukar da kai yafi bashi mamaki” Baban yara shin ko kasan da tafiyar khaleel? Shine maganar ta tafarko bayan sun gaisa, yace mata “ya akayi Hajiya balkisu? Nayi matukar mamaki da na ganki gidana yau. “Nidai bashine matsala taba, Ina so inji in kasan inda yarona yaje? “Bansani ba toh, ai d’an ki ne kece uwar shi kinfini Iko da mulki akanshi don haka kike zuba sarautarki a matsayin ki na uwa, yau ya akayi kike neman shi a wurina? Kije ki nemeshi duk inda yaje. Wani irin takaici taji y’an da yake fada mata magana a kai kaice, ” toh ai kaima akwai hakki a wuyan ka tunda Amana d’an uwan ka yabar maka, don kasa ga rufemai idanu shine zaka bari zuri’ar shi ta watse, shi wancan ya tafi, wannan kuma ya gudu yabarni, don girman Allah nidai kafadamin inkasan inda yaje.
“Bansani ba kitashi kibani wuri, kedaman matsalar ki jahilci kije ki nemi ilimin addini kafin ki mutu cikin duhu domin kalaman ki Sam bana mai ilimi bane, da kinada kwakwal wa da kin gano mugun halinki duk shine ya janyo miki halin da kike ciki, kuma bakiga komai ba inda wainnan mutanen banzan da kike tareda sune, kije sune zasu cire ma Y’ar mutane hakki da kika tsana kika hanata sakewa da mijin ta tunfarko kuma Allah ya nuna miki Aya akan dole dai saita rayu da jinin naki da bakya kauna, meye laifin talauci ke kika bawa kanki Arziki? Ko ke cikin Arzikin aka haifeki, saboda kawai kinshigo cikin zuri’ar mu kin lashi jar miya kinfi uban kowa daga kafada….. Kuka tasa mai ciwo tareda mikewa ” basai kaci mutunci naba modu, basai katuna min da Asalina ba, nasan duk inda nafito Amma kasani inda sa hannun ka dana yabarni sai Allah yasakamin. Ta juya tafita tana kuka, a hanya ta Kira zarah tasa kuka, ko bayani takasa yimata, ” Aunty lafiya yada kuka kuma? ” Ina cikin masifa zarah khaleel ya dauke Naziya yabarmin kasar baki daya sannan yanzu wannan tsinanniyar itada uwar ta sun tare min agida….. Ta kora mata komai. tasa salati, tareda cewa Ina zuwa Aunty Anjima ki kwantar da hankalin ki.
Kuka takeyi sosai yanzu take nadama mara Amfani tunba aje ko Ina ba, domin babu abin tashin hankali a wurin ta sama ga tafiyar khaleel.

Sun sauka lafiya Wanda cab ke jiransu already a filin jirgin, tayi matukar gajiya tayi bacci harta gaji, tundaga filin jirgin take baza idanun ta domin tasan wannan kasa tanada cigaba sosai a fadin duniyar nan, domin ta hada al umma daban daban yare Kala Kala, dafa kafadar ta yayi tareda cewa ” welcome to bangkok madam. Fuskar shi dauke da murmushin farin ciki, kallon gajiya tayimai ya ce ” sorry muje ga mota. Ya bawa driver umarni ya kwashe kayan su suka shige baya yana kwakume da ita, kallon bakin shi takeyi Wanda take mamakin y’an da yake zuba yaran Japanese da driver kamar yaren da aka haifeshi dashi, saida yaga tana kallon shi yayi murmushi tareda cewa ” zankoya miki different language anan Chinese Japanese harma Hungarian language Wanda duk sun tattara a wannan kasa, kuma idan bakin sani ba bazaka banbance suba domin kusan duk kalar idanun su daya da. Dora kanta tayi a kafadar shi domin wata irin kasala takeji wadda bata taba jin irin taba a jikin ta.
Yasaka hannu tare da rungume ta, ba Abinda yakai mai wannan dadi a rayuwar shi, ganin shi tareda ita a wannan kasa da yake mafarkin ganin ta a ciki, burin shi yagama cika a rayuwa, sai Ajiyar zuciya yake yi, ita kuwa kallon hanya takeyi tana shakar iskar wannan kasa mai matukar burgewa, ko Ina tsab tsab har suka isa unguwar da yake zama, gidajene kamar quarters ba wani hayaniya sai kukan tsuntsaye, cab din na tsayawa ya saketa tareda bude kofar yace ” let go madam we are home our small world. Fitowa tayi tana kallon KO Ina, gidan ba wani kato bane akan gidan su dake kano, Amma tasani a irin wannan kasar wannan gidan kudin shi sai yafi karfin wancan, gashi yaji fulawoyi masu bansha’awa da furanni,
Masu sanyin kanshi, fitowar wata mata Y’ar China ne daga cikin gidan zata iya kaiwa kimanin shekara arba’in tana sanye da afron na girki, fuskar ta sake tana mai welcome da yaren sinanci ya amsa tareda nuna mata madam dinshi, da gudu ta Kara so tana rungume ta tareda zuba mata yaran da ko zo inkasheki bazata jiba, kayansu ya shigar ita kuma ta rakota har ciki jikinta na rawa, kamar rakumi da akala haka ta bita,
Kamar yanda kasashen na waje suke basa cika tarkace a cikin gidajen su haka shima nashi simple ba wani hayaniya sai sai dai kasan koma meye kudi ne a ciki, saida ya shigar da trolley da Jakar shi ta laptop ya dawo tareda cewa ta hado musu Abinci madam is hungry yace ta shigo bedroom ta yi fresh up su rsma sallolin su, dama akagare take da wanna Matar me shegen zuba da bata gane komai, tuni ta cire hijabin jikinta suna shiga ta ga kujera ta zube kwance domin tayi mugun gajiya jikin ta kamar anyi mata duka, kwabewa shima yayi tareda daura towel ya juyo, yaga yanda ta kwanta tana shirin yin bacci, murmushi yayi mai d’an sauti, ya matso tareda tsugunawa gaban ta, ya dukar da kanshi dai dai bakinta ya bata light kiss, tayi saurin bude idanun ta, murmushi ya sake mata kafin yace ” bacci? Wani irin lumshe idanun ta takeyi gwanin sha’awa, Abun ya burgeshi sosai yaji tsigar jikin shi na Tashi Wanda ya dade yana controlling tareda Addu’ar neman dama, yau gashi gata a cikin gidan su sukadai, harshen shi ya Dora saman girar ta ya lasa tareda matsawa har kan hancin ta ya gangara lips dinta ya rike na kasan gam yana Ajiyar numfashi, bajewa yayi zaune akasan tareda rungumota zuwa jikin shi, zare bakin ta tayi cikin kasalar da yasakar mata tace ” bacci nakeji, kuma bamuyi sallah ba. “Uhmm. Kawai ya iya cewa tareda saka hannu ya dago doguwar rigar dake jikinta ya zare ta ya wurgar, jikinshi har wani irin mazari yakeyi kamar mayunwacin zaki, ” zakiyi bacci letter baby sallah kuma zamuyi yanzu, na matsu da yawa I can concentrate idan ma nace zanyi alwala bazata zauna ba yanzu… Yafada muryar shi na sarkewa, “please nagaji my body is weak, bari inyi wanka tunjiya fa banyi wanka ba muna cikin jirgi. ” kamshi kikeyi baby ke mai tsaftace ko zaki shekara baki yi wanka ba I don’t mind I can leak your body in and out right now. Yafada yana dora bakinshi a wuyan ta yafara lasa tareda karasa maganar shi, ” yaushe rabon da inyi baby sau daya fa nayi testing kika lasa min Zuma ai nayi namijin kokari ko ke kinsani.
Ganin fa da gaske yakeyi tace ” OK wait muje gado jikina zaiyi ciwo a nan please. Tashi yayi da sauri zai dagata tace “zan iya, yana bin hips da kirjinta dake cike tam da kallo wani irin shanyewa idanun shi keyi, tafara takawa cikeda tsokana da daukar hankalin shi domin taga duk duniya jikinta na mugun daukar hankalin shi, saida tabashi tazara tayi hanyar da taga ansa washroom da gudu tana cewa ” nayi maka wayau. tareda yimai gwalo ta kulle kofar ta ciki.
Da baya baya yayi tareda dafe kai ya fada gadon yana juyi, ” zaki shigo hannu yarinya you must pay for it. Yafada yana murmushi mai cikeda farin ciki.
Tana shiga ta jingina da ginin tana kallon kanta ta katon mirror din dake bathroom din kallon jikinta takeyi, ” yes dole zata rikita namiji domin tasan ita kanta bata gajiya da kallon kyakkyawar kirar jikin ta, a ce namiji kamar khaleel mai matukar aji da girman kai yau shine ke nuna mata so da naci haka, ita tasan mai sa’a ce domin tasamu miji na fita a nuna ma kawaye Ajin farko,
Ta dade kafin ta murje jikinta tsab da sabulai masu kamshi da kuma turarukan wanka, ta tsane jikin ta ta dauro d’an karamin towel tareda nade kanta da wani saboda ta jika gashinta da ruwa domin small touch from him yanzu zata fara tsiyayo ruwa don shidin namiji ne na karshe,
Murmushi tayi ko yanzu za ayi daga idan ta fita, don haka ta d’an daure fuskar ta kadan ta bude kofar tareda fitowa batareda ta kalli gefen shi ba, Wanda shikuma yana nan a kwancen tana bude kofar ya bita da kallo yana bin mulmulallun kafafun ta har zuwa rabin cinyar da ke bude, dogon numfashi yaja tareda saurin tashi zaune ” zata kuma rikita ni, yafada a bayyane har tajishi, tayi saurin daukar katon hijab dinta ta zura tareda ganin dadduma a gefe, yayi saurin mikewa ” wait for me bari nima inyi infito. Ya wuce badon hakan yaso ba sai dan ganin rashin walwalar fuskar ta data sosa mai rai kadan, farin cikin ta yake son gani ba bacin ranta ba, bayason ya takura Rayuwar ta, he love her, ganin ta a karkashin shi kawai is enough for him don haka bazai taba takurata akan Abinda bataso ba koda zai cutu. tuni ya saita kanshi ya zura jallabiya tana nan inda take ya ja musu sallah, duk saida suka rama wainda ake binsu duka, ta d’an kishingida idanun ta a rufe tana Azkar, mikewa yayi ya fita, yaga cook din ta shirya musu komai a dining, yadawo tareda cewa ” let go and eat food is ready. Ya juya ya fita, kafin ta ce komai kamar walkiya ya fice, wani iri taji, why ya canja yanzu yanzu kuma?
Hijabin ta cire tareda bude trolley din da yazo dashi taga iners dinta danashi ne kawai sai wasu dogayen riguna dake cikin akwatin da ya hadawa Ahmed rugunan sunada kyau sosai da matukar tsada dayar ja ce daya kuma blue sunji stones da beads suna daukar ido gasu roba irin masu kama jikin nan ko hannu dayar batada daya kuma hannun ta guda daya anyi crossing dinshi daga wannan kafadar zuwa dayar,
Mai hannu din ta zura bayan tasa iners, saida tasa taga rigar dogon tsagu gareta tundaga kasa har kusan cinya, gata doguwa, tsaki tayi tana cewa wannan wace irin rigace, asarar kudi.
“Ba Abinda zan siya miki ya zama asarar kudi domin nasan zaiyi kyau da jikin ki. Taji muryar shi a bakin kofar, Wanda ya dade a wurin yana kallon ta yana murmushi saida tayi magana ne yabata amsa, tafito kamar wata model a cikin rigar, sumar kanta dake jike ta nannade gwanin sha’awa ta kwanta kamar style ya kalla, yace “zomuje food is waiting.
Kanta ta taba tana waige waige ya matso tareda dukawa ya sunkuceta bridal style, “you look pretty like that, suna fitowa mai aikin na shirin tafiya, tayi mai sallama batareda ta damu da Yanayin da suke ciki ba Wanda su ba wani Abu bane a wurin su, saida ya zaunar da ita ya duko tareda daga kanta zuwa saitin bangon dake dining din, zare idanun ta tayi ganin tangamemen hoton ta dabatasan ma lokacin da ya dauketa ba, kur ta kurawa hoton ido tanaso ta gano wane lokacine?
Muryar shi taji,
“Ranar da kika kusa sa zuciya ta ta buga saboda kishin ki, Wanda bansan me yasa kikabi Yaya na part dinshi ba, kinsan cewa nashiga cikin mummunan yanayi because of your love, zagayawa yayi tareda tsugunawa gaban ta ya riko hannun ta gam, kece macen da nafara yiwa kuka a duniya, kin san irin fanfon da shedan ya rika yimin saboda soyayyar ki? ranar da kika shigo dakina kuwa kikayi ten minutes, Hmm ko yaya na ranar da kyar na danni zuciya ta na iya yimai magana, and because of that bankuma kwanciya a gadon ba, impact ban kuma samun natsuwa ba saida na canja gadon, duk a tunsni na kunyi making love ne a kai,Hmmm you want understand my pain at that time nikadai nasan halin da nashiga, bantaba mafarkin zan mallake ki ba sai gashi Abinda Allah ya tsara, Ashe zanyi rashin wani gefe ne na rayuwata kafin insamu wani gefen da zai ragemin zafi da radadin rashin yayana mai sona,
Dagowa yayi ya zauna a kujerar gefen ta ya zuba mata ido ” why bakyason mu? Tanbayar tayi mata wani iri, ta kalleshi cikeda tuhuma. ” yes nasan momy nada nata kason na hana yayana samun farin ciki daga gareki like he dream, but what about me? I try alot domin ganin na baki lokaci domin Ina matukar bukatar kulawar ki Amma naga kamar Ina takuraki ko? Yafada cikin kwantar da murya kamar mai lallashi, “mata biyu bayan ke idan sha’awa yasa nake like miki dana bisu suma, do you know fauziya har cikin gidan nan tana zuwa? kinsan mata nawa nake gani tsirara? I love only you Naziya, I want only you by my side forget about Auren gado koda yaya na bai bar wasiyar in Aureki ba, I want let you marry another man, I must marry you Naziya because I truly love you, kuma zanci gaba da nuna miki son gaskiya ba wai sha’awa kawai nakeji naki ba, let eat. Yafada yana bude plate plate din manya dake dauke da different dishes kaza roasted fish da kuma his fevourite, kallon shi takeyi magan ganun shi sunyi mugun tsuma ta tareda sanyaya mata zuciya,,wani irin kallon nayi sa’a take yimai har yafara cin Abincin shi.
Yanda aka gasa gazar yasa taji miyanta ya tsinke tuni taji yunwar duk ta taso domin rabon ta da wani kwakkwaran Abinci tun jiya don haka janyowa tayi tafara yanka da wuka da fake takai bakinta, ya mutse fuska tayi domin ba test Sam don haka ta ture ta janyo cup ta tsiyayi fresh milk ta fara sha, ” what? Yace, domin yana kallon duk Abinda takeyi. ” if you can eat muje indafa miki wani Abun, yafada yana ture plate din gaban shi. ” no Ina ne kitchen din inje? Mikewa yayi ya nufi hanyar tana biye dashi, saida ya nuna mata store da komai, ta ciro indomitable kuda biyu kanana da kwai, yaja kujera ya zauna yana binta da adorable look. Komai nata abin burgewa ne a wurin shi, saida ta ciro carrot dasu green beans ta yanka, dasu albasa ta daka pepper a wani d’an karamin turmin dake wurin na sinawa mai kyau, kafin ta kunna gas tasa pan da ruwa duk yana kallon ta, ta fita ta dakko kazar ta dawo, saida ta yanka dai dai kafin ruwan ya tafasa ta saka indomie da naman kazar ta zuba komai domin batada wahalar dahuwa domin su kayan lambun suma su dahu, saida taga ya kusa dahuwa ta fasa kwai biyu akai ta juya, ta zuba albasar ta,
Cikin minti biyar kamshi duk ya gama cika shi, yakasa daurewa ya matso inda take yana kallon Abincin ta murfin glass din, tareda lumshe idanun shi yace “am very lucky, a zuciyar shi, juyewa tayi a plate ta saka fake daya, “nagama. “Hmm muje. Yafada, suka koma dining, duk ture plate din gaban shi yayi ya zauna tareda daukar fake batareda ya kalleta ba Yasaka yafara ci yana lumshe idanun shi, kallon shi tayi irin ya haka? Ya kashe mata ido, ” ga girkin matata why zanci na wata, kuma irin wannan kamshi I can’t resist gaskiya.
Tare suka ci yana faman sakin layi, har suka gama ya kwashe komai yakai kitchen, ta biyoshi da niyyar wankewa yace mai aikin zata dawo tayi suje su huta.
Dama ta gaji don haka ba musu ta nufi dakin saida ta dauki comb ta taje kanta tsab ta nade da band domin ya bushe, in so samu ne ta tube wannan rigar domin ta matse ta gaskiya, amma tasan me zai biyo baya, d’an juyowa tayi taganshi kwance dai ya idanun shi Alamar a rufe suke, tasan bacci shima yakeji don haka taja Ajiyar zuciya ta daga rigar ta cireta a hankali ta matsa tareda kashe hasken dakin sai hasken waje kawai dake haskowa, Wanda tuni ya bude idanun shi dama ba wani bacci lamo yayi yana shayar da idanun shi, gyalen jallabiyar ta ta nade jikinta dashi ta matso cikin sanda kamar wadda zata yi sata ta kwanta a hankali, duk yana kallon ta tareda sakin murmushi, yaki ko motsawa saida ta kwanta tafara tunanin kalaman shi na dazu, wani irin shauki da natsuwa tareda wani irin feeling dinshi taji she also love him and missed his magical touch, runtse idanun ta tayi tana cewa ” were is your promise Naziya? Bakyason ya Kara sonki ne? Gashi ya yi bacci ya kyaleki zakiyi wa kanki tsakiyar da ba ruwa idan salifa ta mallake miki shi ki tsaya sanya yagaji da jan Ajin ki ya koma mata. Wani irin mashin kishi taji ya caki zuciyar ta, she can let that happen because itama tanada matukar kishin shi fiyeda yanda taji akan Ahmed, juyowa tayi yana rigin ginen har yanzu kirjin shi a bude dagashi sai short idanun ta suka sauka akan kyakkyawan kirjin shi mai dauke da suma kwantacciya,………. 🖊

 

 

Back to top button