Auren Gado Hausa NovelHausa Novels

Auren Gado 49-50

Sponsored Links

 

……….. Ko waya bai iya kiran Naziya ba wadda ta cika tayi fam saboda yanda baida wani lokacin ta yanzu bayan yamata sabo mai wahalar mantawa, she is missing him, salon shi mai rikita ta Mata kwakwal wa da gangar jikinta, duk lokacin da ta tuna dashi sai taji tsigar jikin ta na tashi, Kwana tayi juyi har garin Allah ya waye, Wanda gefen shi kuwa da bakin ciki da takaici ya Kwana, a afarko yana dayasanin shirya tafiya ya bar Momy ita kadai, Amma yanzu baida wani choice sai na yabar musu garin kawai kowa ya huta he is going batareda wani regret ba, yana son jin muryar ta Amma yasan zata gano yana cikin damuwa domin zafin da yakeji bazai iya boye shiba zata gano shiyasa kawai ya hakura, Amma baiyi bacci ba Sam, sallah yayi tareda yiwa d’an uwan shi Addu’a har Asuba, jirgin su sai karfe shida na yamma zai tashi don haka bai fita da wuriba sai kusan karfe takwas, ya kirata lokacin tagama kunbura, saida ya Kira sau uku tayi picking tareda yin shiru kamar ruwa ya cinye ta, ” yau jan Aji akeyimin bama gaisuwar? ” Ina Kwana, tafada ciki ciki, “lafiya gimbiya jiya ko a kirani? “Kai meya hana ka kirana? Kuma yanzu ma kalla sai karfe takwas kake kirana. Cikin shagwaba tareda narkewa take mai maganar, ” are you waiting for my call my diamond? Wow Ashe ni d’an gata ne a wurinki baby. Numfashi yaja tareda yin Ajiyar zuciya, yace ” get ready karfe shabiyu zanzo muje gidan malam muyi musu sallama. Shiru tayi kadan tana tunanin Ina zasuje? Bata tanbaya ba domin bincike ba aikin tabane don haka amsawa kawai tayi yace zai wuce office letter, kashe wayar yayi, tabi da kallo, when zata samu dama itada mijinta? Yaushe ne zasu kasance atare batareda ya matsa ko nan da can ba, me nayi miki momy meye laifina, talauci aibu ne?
tasani Indai mutum yace bayasaon ka toh kawai kasa idanu tunda Wanda ya halicceka yana sonka, Abinda momy takeyi bai taba damunta ba sai yanzu da take kaunar zama tareda shi gashi momy ta haramta mata komawa gidan shi, batasan inda zai kaita ba amma ita tasan ba inda yafi mutunci sama da dakin Auren ta, batada mafita ta tattara ta fauwalawa ubangiji.

Da sassafe momyn salifa tazo Wanda har lokacin takasa tashi tana kwance cikin Aman tana shara baccin ta, koda suka shigo haka Momy ke toshe hancin ta, ” kingani ko Hajiya har yanzu ace tana kwance cikin kazanta yaza’ayi khaleel ya zauna da ita yana ganin irin wainnan Abubuwan? Idan ta saba shaye shayen ta a waje tayi Aure an rufa mata asiri ta shigo tanayi wane namiji ne zai zauna da ita….. “Ya isa mandiya wato kina nufin ya’ta batada tarbiya? Bayan kin haifi Abinda yafi karfin ki bayajin maganar ki, ai shine Abun tir ba Salifa ba yakawo santaleliyar yarinya ya Ajiye ba biyan bukata me kikeso tayi inbatasha Abinda zai cire mata damuwa ba, don haka bani wuri in kintsa abata kina wani toshe hanci kamar kinga kashi. Takasa cewa komai kawai fita tayi domin tafita masifa
Tana ayyana dole ta nemi mafita don bazata Y’ar da da wannan iya shegen nasu ba, tana fita momyn salifa ta kulle kofar ta dawo tareda bata fas a kumatu, zabura tayi dauke da Ashar” kutumar ubancan wane shegen…… Tayi ido biyu da momyn ta, ” momy meye haka don Allah Ina bacci na mai dadi kizo ki tasheni da Mari meyakawo ki gidan suruki early morning please?
“Ubanki dake kabari yakawoni Y’ar banza, wato bazaki daina daga kwalbar nan cikin gidan nan bako, nace ki hakura da duk wani iskanci har burin mu ya cika Amma kina wannan Rayuwar a gaban idanun shi yazai zauna dake? Zama tayi tareda kallon Aman, ta kwalawa maid dinta Kira, ” clean this mess ta wuce tabar momy, tashi tayi tabita tana bambami ” wato na zama karya inyita haushi ko? Kwabewa tayi tsirara agaban uwar Wanda ba wani Abu bane a wurinta tace ” tunda gani dutse ba namiji ba chilling ba kwalba bazan iyaba. ” kice dai ba y’an iskan kawayen ki y’an madigo, salifa tanbadewar ki tayi yawa wallahi ki rage kodan y’an cutukan nan. “Kinfa shiga rayuwa ta ne because of your greediness, meye bandashi you have money momy me zakiyi da kudi, inada big girls a kasashe masu kudi dake da burin mallakamin duk Abinda nakeso a fadin duniyar nan kin nace sai na Auri wannan mugun d’an wulakancin, Momy I don’t want to deceive myself , that guy hate me with passion yasan ni munsha haduwa a bangkok with my girlfriends, I can’t west my precious life here. “Oh baby na daura towel din tom kije kiyi wanka kifito muyi magana. ” nop Ina fitowa zanfita niba dutse bace inada appointment. “Ok ba kince kina sonshi ba? Shiru tayi kadan tana kallon momy, ” meye amfanin son? Abinda nakeso bazan samuba guduna ma yakeyi tun zuwa sau biyu nasa shi a ido na. “Jiya yashigo shi ya ganki a wannan halin uwar tafada min komai, kinga ga dama tasamu kin yi sake da lokacin da ya shigo kin samu kinja hankalin shi kin shafa wannan turaren da bazai kuma tsallake dakin ki ba Amma kinja mana asara. ” oh Momy nida nasa wannan turaren har dakin shi naje ba Abinda ya faru sai don yazo nan? ” kinga halin ki ko, wayace ki saka kifita waje wani yaji kamshin? Keda akace miki shikadai zai shaka Amma kinje kinyi min Asarar kusan million a banza batareda ribar ko dubu daya ba, mtsww kinada kayan haushi ni natafi kiyi duk tsiyar da kikaga zaki yi tunda bakida ganewa Abinda kikesha duk ya sa kwakwal war ki bata aiki.
Haka ta tafiyar ta batareda ta nemi Momy ba, Wanda tabar salifa da cizon yatsa, da ace jiya bata kwafsa ba da ta rage mugun zafin data dauka nashi koda ta hanyar yimai fyade ne domin tasan y’an da zatayi seducing dinshi dole ya biye mata kobaya so Indai ya kawo kanshi har wurinta, saidai Kash ta kwafsa. Haka ta sheka wanka cikin kana nan kaya kamar zataje club ta maka katon space tareda d’an wani yalolon gyale ta dauki key din motar ta tafice.

Karfe shadaya tagama shiryawa cikin wata doguwar riga Y’ar saudiya mai shegen kyau taji stones tana sheki, ta yana gyalen ta tafito kamar balarabiya, takwashe lokaci mai tsawo kafin ta gama shiryawa saboda kawai ta burgeshi,Wanda Aunty ta yaba, tace ” kaga madam khaleel gaskiya zaki rikitashi irin wannan ado haka, ga kirjin sun kunburo hips dinta d’an dai dai ya bayyana saboda shape din rigar duk da bawai takamata bane Amma tafito da perfect figure dinta,
Karfe shabiyu dai dai ya Kira wayar ta, lokacin tana shan wani hadi mai shegen dadi da Aunty tabata, na Zuma da kanun Fari da kuma mazarkwaila ga dadi ga aiki mata. Ganin kiranshi yasa ta Ajiye cup din tayi picking ” Ina waje let go. Ya datse kiran, mikewa tayi tace “Aunty yazo.
Wani turare ta dakko mata domin ita batasan Ina zasuje ba, ta ce ta shafa,

Tun daga nesa ya zuba mata ido ganin y’an da take tafiya cikin natsuwa, saida ya kalli ko Ina yaga ba idanun mutane yasamu natsuwar kare mata kallo, har ta iso bakin motar, batareda ya motsa ba, ita sam bata ganin shi ta rasa dalilin da yasa duk motocin shi kamar na matsafa saboda tinted glasses danna motar yayi tareda bude mata, dukawa tayi ta shiga, ya juyo da kyau ya zuba mata ido itama ta kalleshi cikin adon manyan kaya, yayi matukar haduwa harda hula wadda sai jefi jefi zaka ganshi da ita, idanun shi dauke da katon eye glass daya karamai haiba da kyau, batasan lokacin da ta shagala da kallon shiba, shima kare mata kallo yakeyi shikadai yasan me yakeji, baiki ya kwantar da kujerar motar nan yayi mata kaca kaca ba domin tasa mai zafi, numfashi ya fesar mai zafi, ” don’t dress like this inkin san ba agidan mu mukeba, I feel like striping you necked right now. Ya fada muryar shi a shake. Kunya taji ta dawo hayyacin ta tareda gaida shi, ya amsa “mubar nan kafin inyi miki tsirara anan gidan surukai.
Tayarda motar yayi tareda riko hannun ta gam da dayan hannun shi domin rage zafi y’an da yake murza hannun ma nasa taji wani iri a jikinta ga hannun shi laushi kamar na mace, domin baya wahala, waka ya saki na su p square na no one be like you yana bin wakar a natse cikin kwarewa tareda d’an juyowa yana kallon ta, turo baki tayi domin wannan glass din da yasa haushi yake bata yanzu duk da yayi mai kyau ita burinta taga kwayar idanun shi da yanda yake aika mata da kallon shi mai cikeda tasiri a zuciya da gangan jikinta. Yana ganin reaction dinta baice uffan ba har suka isa kofar gidan malam Wanda tundaga nesa ya faka ganin cin cirindon mutane ya zare glass din ” oh god zamu juya fa. Yafada yana matse rai, Wanda ita dai murna takeyi tazo gida zataga Inna, jin kalmar shi yasa tayi saurin juyawa, ” saboda me? ” can’t you see, maza cike yazan bari kifita cikin wannan adon su kalleki?
“Almajiran gidan mune sun sanni batun yauba meye a ciki please don Allah muje. Tafada cikin marai raice wa, ” excuse me, kikace sun sanki? Ba Wanda ya sanki sai Ibrahim khaleel, don haka if you want to go in call Shukrah ta kawo miki katon hijab if possible harda nikab am not a fool.
“Don Allah meye haka? ” kishin iyalina.
Yafada tareda gyara zama yana cewa ” call her or mu juya yanzu we have a plight to catch time is going.
Wayarta ta daga domin Allah yagani bataga samu taga rashi ba don haka ta Kira Shukrah tace don Allah takawo mata hijabi tana waje, karbar wayar yayi jin Shukrah na tanbaya wane irin hijabi kuma meke faruwa? ” Shukrah ki kawo mata please muna jira harda nikab please. Dariya Shukrah tayi tareda mikewa tana cewa “Aunty kinyi Aure. saida ta dakko mata kato cikin kayanta nagida sabo tareda nikab domin tanada su tafadawa inna tana zuwa Yaya khaleel nakiranta a waje.
Fitowa tayi tana kunshe dariya harta matso gaban motar ya zuge glass yace ” Shukrah tank you for saving her da bazataga Inna ba yau. Gaidashi Shukrah tayi tareda mika mai ya karba ya mika mata tana tura baki ta zura, gefen ta shukrah ta zagaya tace “Aunty kece da irin wannan shigar yanzu Yaya khaleel ya taimake ki da keda malam ma. ” Shukrah kyaleta saboda tasamun hawan jini yasa takeson fita a haka yanzu. Ya bude motar yafito tareda zagayo wa gefen su harta daura nikab din ya bude mata ta fito, yace “wow koke fa yanzu? Harara ta watsa mai cikin wasa yace “I will pay for that look letter. Yayi gaba yana murmushi, matsowa Shukrah tayi tareda cewa “Aunty wannan irin love, when how? Gaskiya kunfi matching da Yaya khaleel look at him, inama kinki Y’ar da, Dana shige ni. Tafada cikeda tsokana, ta kai mata Dan dukan wasa, har suka isa kofar gidan ta wuce Abunta ciki shikuwa yayi wurin da malam yake da manyan Almajiran shi,

Tana shiga ta kwalawa Inna Kira cikeda doki da kewa, tana zaune tana kulle kullen ta tace “Aa Amare da rana?
Zama tayi suka gaisa Shukrah ta kawo mata zobon Inna mai sanyi tasha tana lumshe idanun ta “I miss this. Inna fuskar ta dauke da walwala da farin ciki, tace “Y’ar nan kina can kinyi shar dake ni Ina nan kullum tunanin ki tunda nasan bakiso wannan Auren ba Naziya, da Alama wannan Khaleel yana kulamin dake tunda har kinsaki jiki kinyi fes, kai Alhamdulillahi. Murmushi kawai tayi tareda dukar da kai saboda kunya, haka suka shigo tareda malam ya gaida Inna cikin girma mawa kafin malam yace “sunzo yimana sallama ne zasuje can kasar waje. Saurin kallon shi tayi Wanda idanun shi na kanta kur ko kunya baiji aganshi, ya kashe mata ido daya, wato tafiya zasuyi shiyasa yake neman hoto,
Wanda duk batasan shirin shi ba,
Sunkai karfe hudu a unguwar barinta ciki yayi shikuma ya fita waje wurin malam saida ya kirata ta mike batareda ta gaji ba tayi missing Inna, Shukrah ta rakata bayan tasha nasihohi wurin Inna da malam, yabawa malam kudi sosai yace akarawa Almajirai Abinci, domin yasan in shi zaibawa bazai karba ba, Shukrah ma yabata yace tasiya kayan kwalliya, wayar hannun Naziya ya karba ya mika mata bayan ya cire layin yace ” kiyi manage kafin inkawo miki sabuwa. Tayi tsalle tana godiya domin ta mugun lora wayar tunda taganta, murmushi Naziya tayi tareda karajin shi cikin zuciyar ta yanda yake sakin jiki da yan uwanta All that ego da take tunanin yanada yau bata gani,
Haka suka tafi fuskar ta kamar gonar Auduga tana Kara daura damara,
Gidan kawu sukaje Wanda ta yaba da karamcin su, sun karbeta hannu biyu, hardai uwar gidan da taji dama haka Momy takeyi da ita. Sunyi mata shatara ta Arziki kafin yace tafito sutafi, kamar karta tafi ga y’an matan da dama sun d’an saba tun lokacin Ahmed.
Karfe biyar da rabi suka isa ainihin kofar gidan su Wanda bai shiga ciki ba yace ta jirashi ya dakko kaya, ido tabishi da shi, har ya shiga katon gate din, bai wani dauki lokaciba ya fito dauke da akwati madai daiciya, ya saka a bayan motar, “nakira Aunty nafada mata sai mundawo jirgin mu yakusa tashi.
Yafada yana tayarda motar, tareda kiran manager dinsu yace su hadu Aminu kano Airport yanzu,

Abun kamar wasa taganta a filin jirgin Wanda all her life bata taba mafarkin zuwa ba, yau gata wai jirgi zata hau zuwa wata kasa, ta zubawa sarautar Allah ido, suna isa manager na isowa, yace “naso muyi wanka before going Amma har anfara announcing, hanata fitowa yayi ya bashi envelope ya kaiwa momy gobe da key din motar if he needs him zai kirashi. Saida yaji ana Kara Announcing yace ta fito baida yanda zaiyi,
Fitowa tayi still da katon hijab dinta saidai ta cire nikab din yanzu domin tagaji, suka gaisa da shi sama sama kafin ya sallameshi ya rike hannun ta suka wuce.
Wai yau ita naziya ce zaune a cikin jirgi first class seat tunda jirgin na y’an kasuwa ne, yana zaune a gefen ta ba wasu mutane sosai a wurin ya daura mata belt tareda d’an saka hannu ya rungume ta domin supporting dinta don yasan karon ta nafarko kenan, Wanda tayi matukar kokari wajen natsa kanta da dauriya karta nuna kauyancin ta,
Sai gasu a sararin samaniya, jirginsu ya daga, taso tayi sallama da Aunty Raliya Amma yabawa Shukrah wayarta, sai muyi musu fatan sauka lafiya…….. 🖊

 

Me kuke ganin zaifaru da rayuwar momy masoya, ga khaleel ya tsallake ta batareda tasani ba ya dauki Y’ar da bataso ya bar kasar, ga momy nan dauke da sabon shirin kashe Auren shi tareda nemo mai wata Matar, muje zuwa dai ankusa isa, inda nakeson kaiku da Yar dar Allah.

 

Back to top button