Nasarar Rayuwata 2
*Talented writers forum*
*NASARAR RAYUWATA*
*2* free page
*your comments are quite encouraging thanks alot fans, Mmn khairat ke ta daban ce n shatu Nah love u both*
Yarima Ayman yana bisa babban teburin cin abinci tare da sauran yan uwansa Wanda suke gida dama haka al’adar gidan nasu yake Aseem na satar kallonsa don gane halinda yake ciki da alama baya cikin kwanciyar hankali da alama akwai abunda ke damunsa, Gimbiya Safna kanwarsu ce itace autar gidan tafi shiri da Ayman tace ” my prince meke damunka it seems baka cikin walwala can you share it with me ” murmushi yayi dama can ba mai yawan surutu bane sak halayen Fulani ya gada komi nasa gentle ” am OK lil princess nagode da kulawarki gareni ” yana gama fada ya ajiye spoon ya tashi dogarin dake kula dashi ya sunkuyar da kai suka fara tafiya har ya shige part nasa, dogarawa ne sama da goma suke masa hidima yana shiga suka biyosa har bakin kofar falo wasu suka tsaya amintattun kuwa suka dora daga inda wannan suka tsaya har ya shiga bedroom akwai mai tsayawa dashi a bedroom tsaki yaja yace ” wanka zanyi please a bani guri ” ” angama ranka ya dade” yana fitowa kuyangi biyu mata suka kwankwasa suka shigo suka gabatar da gaisuwa bai amsa ba suka shige toilet, ruwan wanka suka hada masa har da furanni ciki da turarukan wanka masu shegen qamshi suka ajiye sabon towels sannan suka fito, suna fita ya kulle dakin yana jan tsaki shi ya tsani rayuwar gidan masarautar tasu komai a ce sai anmaka wannan wace irin rayuwace. Bayan ya fito daga wanka yana shiryawa aka kwankwasa kofa bai kulasu ba sai da ya gama yana xaune wani dogari ya daga murya yace” Allah taimaki yarima Fulani na son ganawa da yarima mai jiran gado, Allah yaja zamanin yarima ya tsareka da sharrin makiya ” murmushi yayi ya tashi don duk duniya babu abunda yake matukar qauna irin mahaifiyarsa, ya bude kofa suka zube suna gaisuwa yayi wucewarsa don ya gaji da amsar gaisuwan safe da yamma kamar ibada. Bayansa sukabi yana tafiya har xuwa kofar da zata sadashi da part din Fulani. tana falonta na biyu ya shigo da sallama ta amsa cikin sakin fuska hannu ta d’agawa kuyangin nata suka fice ya rage su biyu a falon ” barka da dare ummata abar alfahari na” “barka kadai yarima ubana yafi na kowa ” murmushi yayi yace ” Umma na sameki lafiya ” “lafiya alhmdllh dama sultan ne yace a shaida maka gobe zaka tafi Nigeria wajen Ammin Ku ” lumshe ido yayi yace ” ya ilahi yanxu kuma can zaku jefani ” ” haba Babana meyasa baka son karatu a rayuwarka , yanzu da yaci a ce ka kammala degree naka amma Sam Abu ya gagara why? ” turo baki yayi cikin shagwaba yace ” ni Umma nafison na zama Dan kasuwa a rayuwata bana son karatun boko ” ” Babana komai na Rayuwa da kake gani dole sai an nemi iliminsa, shi kansa kasuwanci dole yana bukatar ilimi donhaka nake so kayi alkawari idan ka tafi can zaka tsaya kayi karatu, dubi Aseem har yana final year amma kai ko kunya baka ji kaninka ya kusa gamawa kai kana yawo from one university to another yanxu shekarunka nawa amma baka gama first degree ba talkless of masters ” shiru yayi da ta gama yace ” sorry ummata idan na bata miki rai kiyi hakuri insha Allah wannan karon bazan baki kunya ba I promise ” “haka nake son ji daga gareka, Allah ya maka albarka ya tsaremin kai dama bana son zamanka kusa da gida ” hira sukayi mai ban shaawa ya sallameta ya tafi bangaren sultan, nasiha sultan ya dora akan ya maida hankali kan karatu ya tsaya ya nemi ilimin addini da na zamani duk da cewa ya haddaci litattafan addini da dama saboda a gida ake koya musu. Washe gari da safe motoci suka shirya ajere sukayi layi bodyguards ne zasu raka yarima airport private jet nasu na can yana jiransa yayi sallama da sultan da kuma Umma da Gimbiya suhail sannan ya fito aka bude masa wata wagon zai shiga kenan yaji an rungumesa ta baya an kankameshi da sauri ya juya Gimbiya Sabreena ce ya’r sarkin kush, hada rai yayi yace ” ke meye haka, baki da hankaline ko jahilci ke damunki” tayi murmushi ta sakeshi tace” haba Yarima yanzu zaka tafi babu sallama, meyasa baka damu dani bane, Yarima kasan irin tsananin son da nake maka meyasa zakayi nisa dani, zan iya yin komai a kanka Ayman saboda Ina mutuwar sonka kuma Ina fatan zamanto uwar y’ay’anka I love you Allah ya tsare sai na kawo maka ziyara ” tsaki yaja ya shige mota tana d’aga masa hannu aka tada motocin suka fita daga gate na farko na masarautar Fulani dake bakin window dake saman bene ta sauke wata kyayyawar ajiyar zuciya tana masa fatan alheri a rayuwa.
**********************
*Adamawa state Nigeria*
Kande na bayan motar Sharon tare da Inna da hajjo a garin mayo-belwa suna jiran mota ta cika saura mutum d’aya kwandasta na cewa ” Taraba jalingo, taraba jalingo a nan saura mutum d’aya ” suna nan wata mata ta biya kudi driver yaja suka dau hanya, bayan wasu awanni suka sauka a cikin tashar jahar Taraba nan kande ta biya musu kudin Abuja suka shiga mota bata cika ba suna xaune, Inna tace ” ohh… Duniya ban taba tunanin zuwa Taraba a rayuwata ba saboda bani da kowa ta nan bangaren daga borno sai yobe sai kuma na taba zuwa kano sau daya kafin nayi aure” kande tace ” dama komai sai da dalili, yanxu muna xuwa kika samu aiki kinga shikenan baki da matsalar rayuwa, daga nan sai ki biyani kudin mota koh” hakan zaayi insha Allah kande bazan manta da halaccin da kika mana ba, zamu biya kudin da yardar Allah ” Hajjo dai na raba ido tana kallon mutanen da suke sabgoginsu cikin tashar. Sun share minti 40 kafin mota ta cika suka fara tafiya lokacin karfe 10 na safe driver na ta surutu akan rana tayi basu taso dA wuri ba, tafiya suke kowa na hira da na kusa dashi tafiya tayi tafiya sun wuce katsina Alu wukari da zaki biam suka iso Benue kenan sai ga motoci na juyowa driver ya tambaya aka ce hanya babu kyau mutanen makurdi na fada driver yayi dariya yace ” ahaf wannan su ya shafa mu Ina ruwanmu tsab zamu wuce ” wani passenger yace” driver da dai kabi yan uwanka mun koma” ah haba babu komai kawai karya ce ansaba mana haka ” nan dAi mota ta kaure Ana muhawara wasu suce a wuce kawai driver yana cewa yanxu idan suka koma Ina zasu bi haka dai ya cigaba da tuki har suka fita dAga garin lafiya yana cewa ba nA gaya muku karyace kurum, suna cikin tafiya sukazo wani qauye an tare hanya matasa na rike dA gora Ana haya haya a titi ga motoci a gefen hanya Ana fasa mUsu gilasai mutane na guduwa, salati suka farayi driver yaso yayi taurin kai nAn fa matasan suka taru akansa yayi parking passengers kowa na ta kansa kan kace me wasu sun yanka daji abin dai babu kyaun gani sai dai Allah ya kawo mana sauki, Inna na rike da Hajjo suka shiga daji kowa na ta kansa sunyi gudu mai nisa sannan ta duba babu kande cikin matan dake wajen, ta gama duk waige waigenta babu alamar kande haka suka cigaba da bin sauran mutanen hajjo na haki Inna na jan hannunta sunyi tafiyar awa guda kafin suka b’ullo titi babu komai a titin shiru kawai. Sun kalli gabas da yamma daga ganin yanayin rana ansan la’asar ta kusa idan ma batayi ba haka suke jAn kafa sunkai mutum 7 kowanne daga cikinsu ya gaji wasu suna tsinewa driver, suna tafiya har suka kai wani gari a nan suka sha ruwa wani direban tsohon bus ya tbayesu inda sUka nufa sukace Abuja yace su kawo dubu 3500 zai kaisu, aka daidaita ance kowa ya bada 3000 zai taimaka musu saboda abunda ya samesu Inna ta kwance bakin zaninta dama ta siyar dA katifa da wasu kayan dakinta tana da kudi a hannu batason nunawa kande ne saboda tasan halinta na son kudi.
*2:30am* suka shigo maraba don hanyar Akwanga yabi dasu yana xuwa ya saukesu a tasha babu mai kaya cikinsu sai wAsu mata masu handbag, driver ya tausaya musu yace mata su kwana cikin mota maza kuma su fita waje amma da asuba zai juya ya koma. A kusa da kasuwar Muhammadu Buhari international market yayi parking duk da cewa dare ya raba amma akwai mutane sosai a wajen, mai shayi na gefe haka Inna ta rike hannun hajjo suka jE aka xuba mUsu shayi da bread sai indomie suka ci sukayi hamdala sannan suka koma cikin motar Inna ta jingina da seat hajjo ta kwanta nan dA nan bacci yayi gaba dasu.
Da asuba direba ya tashesu yace zai tafi godiya suka masa a nan Inna taga matan kOwa na shimfida dankwalinta tayi sallama sai ta siyo musu pure water sukayi alwala sukayi sallah mutane sun fara watsewa wasu nA tare keke wasu machine wasu taxi nan Inna ta fara raba ido, wata mata zatahau machine Inna ta tareta ” don Allah baiwar Allah taimako nake bukata ” tabe baki tayi tace ” toh… taimako ta me fah? ” wllhi bani da inda zAni babu Wanda na sani a nan garin” dariya matar tayi har mai machine din suna dariya, matar ta kare musu kallo tace” da me kike tunani da kika taho, ni me zan mIki Allah dai ya bada sa’a tunda neman kUdi kuka fito ” ta haye babur ta xauna mai babur ya kallesu yace ” Abu d’aya zakiyi baiwar Allah ki tafi can unguwar makafi ki samu wata ta daukeki kuyi bara a baki makwanci ” Inna tace” Ina ne unguwar makafin? ” tsiit.. Ya tare babur yace” oga ka sAukesu Aso unguwar makafi please, kina xuwa kice a nuna miki Gidan shugaba zaa kaiki ” godiya tayi mai babur yace ta bada 200 ta biya sUka hau hajjo na tsakiya Inna a baya suka tafi. Yana tafiya suna rAba ido suna kallon manyan benaye ga manyan plazas ga filling stations ga dai abubuwa iri iri haka suka cigaba aka wuce dasu ta cikin kasuwar maraba sannan sUka kama hanyar Aso, suna xuwa ya saukesu yayi gaba Inna na rike da hannun Hajjo suna kallon tsarin unguwar kwatace duk inda ka duba ga nan kananun shaguna na kayan amfani da shagon dinki da sauransu ga wata yar kasuwa tana ci a gefe, wata karamar yarinya Inna ta tambaya yarinyar ta musu jagora xuwa gidan suna shiga suka iske maza da mata sunyi layi suna jiran shugaba ta fito.
*muje zUwa hurry and pay your 300 naira contact 07030077024 for details of payment thank you*