Auren Gado 17-18
1⃣7⃣&1⃣8⃣
……….. Sai Karfe goma sha daya suka shigo main house, mommy na zaune sai faman jiran su takeyi,ta gwada numbobin su ba Wanda yake shiga, tanata sababi Su zarah na tausar ta, da sallamar shi ya shigo cikin falon while khaleel na biyeda shi cikin shigar shadda bugaggiya Y’ar gaske fara dal, “ko kin ga y’an rainin hankalin ko sai yanzu zasu shigo gida kusan Karfe goma sha daya. “Ahmed ne ya matso gefen ta tareda zama yana gaida Aunties dinsu, tareda cewa sorry mommy muna tareda Abokai ne. “Which abokai? Kai inkanada Abokai shi Wannan miskilin nadasu ne? Kun bar ya’yan mutane sukadai suna jiranku kamar masu gadi.
Carab ya bude baki a karon farko yace “jiran me sukeyi mana? Bayan ba ayi budar kai ba, sai su jira nan da sati daya idan an yi budar kai sai muje wurin su ni bacci nakeji, Yaya good night. Yafada batareda ya jira Amsar suba ya wuce Abinshi, ido kawai Ahmed yabishi da shi, bakin mommy a sake tace “Allah ya hadani da yaron banza, kai kuma bazaka tashi ka wuce dakin Amaryar taka ba? “Mommy gaskiya ne ita baza ayi mata budar kan ba? ” ubanka kaji tashi ka wuce ko ranka ya baci yanzun nan, shima zanje in same shi. Mikewa yayi domin baijin dadi sosai dauriya yakeyi kuma Allah yagani bayason kowa yasan halin da yake ciki yanzu.
Yana kallon kofar dakin shi kamar yashiga yakeji yasan halin da take ciki, Amma ba hali mommy ta kasa ta tsare. “Za abiyoka da kazar Amarci nasa anyi muku gashi mai kyau. Ko amsawa baiyi ba ya fita, a zaune Amaryar tashi take tayi dai dai cikin wasu irin fitinannun nighties duk jikinta a bayyane gata ba wani shahararren kyau ba, sai faman tauna chewing gum takeyi tana kas kas kamar wata tsohuwar karuwa.
Tundaga falon ya hango ta kafa daya kan daya tana jijjiga, zai iya cewa yaune karo na biyu ganin shi da ita Wanda baima san ta Ina zai fara yimata magana ba, domin ko ganin farko bai wani mata kallon arziki ba, don haka ko yanzu yana shigowa ya dauke kanshi ya wuce ta gaban ta. “Kai, tace cikin zafi. “Kashi ka wuce? ace ankawoni tun Karfe takwas kowa ya watse ya barni baka shigo ba sai yanzu? kuma ka ganni kamar wata Kashi ka gani. “Oh sorry ya fada batareda ya kalle taba domin bai sha’awar hakan, murmurshi tayi tareda matsowa tana karkada jikin ta da shirin rungume shi, yayi saurin ja baya tareda cewa “please bacci nakeji sosai kuma kaina naciwo, am very tired please let me go. Ya wuce da sauri yabarta tana cizon yatsa, batasan da yanajin lafiya yau sai ya nemo Matar sonshi yaci Amarci kota halin Yaya, Amma bayajin dadi shikadai yasan me yakeji a jikin shi. Yana shiga dakin shi ya datse gam batareda ya jira wani Abu ba, idanun ta sun nuna mai zata iya mai fyade inyayi wasa ta karasa shi, saida ya kwabe ya zube kan gado domin yayi sallolin shi a waje, ya janyo wayar shi yafara neman ta, tana kan dadduma tana lazumi taji Karar wayar, tasan shine don haka cikin Sauri ta mike ta dauka, Ajiyar zuciya yasauke yace “Y’ar Aljannah.” Ina wuni, ta gaidashi cikeda tausayin kansu domin yama fita zama Abin tausayi, “ba lfy my wife, ko in zo ne? ” aa. “Why?” mommy na falo suna hira. Hmm! zaki tayani hira har safe? eh, Amma hakkin Amarya fa? “Don’t say that again sai kisa inji guiltiness akan ki” naki hakkin fa? ” ni na yafe. “Nikuma fa? Ni Ina bukatar hakkina Naziya, kinsan cewa ba Abu bane mai sauki namiji yayi ido biyu da Mace kamar ke ya kawar da ido ba, mommy ce ta tsaya min akan layi da tuni munfara lissafin wata biyu cikina. Rufe idanun ta tayi gam saboda kunya kamar yana ganin, “shy girl, nasan kin rufe ido.
Hira sukasha sosai yana yi yana bata hakuri tareda alkawura masu yawa.
Gefen Amarya ta cika ta batse momyn ta ta Kira tana kuka tafada mata angon yaki ko shigowa dakin ta, a daren Karfe biyu ta Kira mommy tana sababi, “nifa ba dutse nakai muku ba yarinya ce shakaf mai jini a jika don haka kari nji kar ingani, zancen wulakan ta min ya’. Tayi ta bata hakuri kafin ta gwada kiranshi yana busy, ta hakura ta barwa safiya, banzar kuwa kazarta ta yaga iya son ranta ta sha baccin ta nak, domin tasan dai dole yagama gudun shi yadawo mata domin a shirye take tsab.
Fauzy ma tasan halin kayan ta batasa akaba tasani tunda dai ta shigo, a juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe, Amma zama daram itada Khaleel tunda buri ya cika.
Gefen shi ma baccin shi yasha har safe batareda tunanin wata kaya fauzy ba,sai Asuba ya fito da shirin zuwa masallaci, ya samu mommy zaune itada bata tashi da wuri, tace Yauwa ku nake jira kuyi sallah kuzo kaida d’an uwan ka Ina jiran ku yanzu, fita yayi kawai Abun shi yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta k’oki.
A masallaci suka hadu, saida suka idar yace “her excellency is calling. “Who? “Your mom. “Oh ba MAMAN ka bace kai? Shiru yayi kawai, domin shikam baisan me zaiyi mommy ta canja ba, ciki suka shiga yana mai nasihohi masu ratsa jiki da taba zuciya, suna saka kafa tafara sababi “nikam yau zanyi maganin ku duka sai kunfada min inkunada wata uwar bayan ni, Ina muku gata yara kuna watsa min kasa a ido, toh yau dukan ku Ina bukatar ku dakin matayen ku banason jin rashin kunyar ka Ibrahim. Sannan kai tunjiya Ina kiranka kaida ubanwa kake waya? Da ka kwashe tsawon dare kana busy? “Mommy kiyi hakuri, nida Naziya ne. “Innalillahi, Wato tanan ka bullo Ahmed kuna hadewa ta waya, ita kuma munafuka kamar salaha, mayya ta lashe min kurwar yaro to wallahi zanyi maganin Abun, karyar buzu tsohon ta yakeyi, mu munsha tabara mun sha yaseen , ta rangada mata Kira, Wanda duk tanajin komai.
Da sauri ta fito da hijabin sallar ta tace “gani momy. “Ni ba uwar ki bace ta cikin bukka munafuka, ke kin kaini bango hakurina ya kare akan ki inba zuciyar kare kikeda ba kizo ki koma gidan ubanki, ace mace don rashin zuciya miji bai neman ki baidamu dakeba saboda kin rab’i Ac kin like kin manne kamar kaska, ke wa ya iya da bakin nacin talaka? zo don Allah kibarmin gida Ahmed dai yayi Aure aje aci gaba da cin tuwon dawa da gero.
Tafada tana nuna mata hanya.
Kuka takeyi tunda momy tafara magana Wanda Wanda duk sauran bakinta sun taso, fauzy ma data bugo sammako ciki taji komai, tana dariyar mugunta tareda komawa ta Kira Salifa tazo kar ayi bata, domin tasan da zaman Naziya kuma tasan komai akai don haka tasan zatayi farin ciki yau idan taga Abinda mommy tayi,
Dafe kirjin shi yayi yana mai wani irin zafi tuni numfashin shi yafara seizing batareda kowa ya luraba, domin kan Khaleel na kasa idanun shi kamar wuta saboda bakin cikin halin mommy, da kuma irin cin zarafin da takeyiwa Naziya.
Zubewar da yayi Tim yasa khaleel ya zabura yayi kanshi, Wanda yabawa sauran damar ganin Abunda ke faruwa, har mommy tuni tayi dif kamar ruwa ya cinyeta,
“Yaya” khaleel yafada cikin tashin hankali, ya tarai rayoshi, saidai tuni jini yafara bin hanci da bakin shi, wani irin zubewa Naziya tayi jikin ta na rawa kukan da take ya tsaya ba Abinda take kallo sai jinin dake fita a fuskar Ahmed, cikin tsananin jarumta da mazantaka khaleel ya cirashi da gudu yayi waje yana mai kwalawa driver Kira yakawo mai key, yasaka shi cikin motar tareda rungume shi cikin tashin hankali driver yaja suka fita a guje domin gari yayi haske,
Mommy daskarewa tayi tana jin numfashin ta kamar zaifita saboda tashin hankali, Ba Abinda takeso duniya sama da ya’yan ta da kuma dukiyar ta, batasaon rasa kodaya a cikin biyun nan, don haka ganin yanayin Ahmed yasa tajita kamar ana zarar ranta. Saida zarah ta jijjigata ta dawo dai dai, “zarah muje wurin dana ingan shi, kar yarona ya mutu muje inga halin da yake ciki.
Ita ta dakko mata key da hijabi suka fito, su fauzy na tsaye turus basuda niyyar motsi, sanin halin khaleel yasa suka Kira driver yafada musu inda suke, Naziya kuwa kuka takeyi kamar zata mutu, idan ta kalli jinin dake kwance inda aka dagashi, hijabin jikinta ta zare cikin rudu ta goge kasan tiles din tsab tana kuka, Aunty Raliya ta Kira tana kuka tafara fada mata, ta lallashe ta tareda cewa “kiyimai Addu’a Allah yabashi lafiya ba kuka ba, banason shirme. Toh Aunty. Ta datse kiran tana mai dauro Alwala ta koma kan dadduma hannayen ta a Asama domin neman sauki wurin mai duka.
Gefen mommy koda suka isa Asibiti daidai da zuwan kawu modu domin Khaleel ya kirashi, hawaye yake sharewa tareda sintiri, kawun na zuwa yace ” Meya same shi khaleel? ” d’an uwana Kawu yana Aman jini hanci da baki suna ciki har yanzu basuce komai ba, ya mugun fita hayyacin shi, matsowa Mommy tayi jikinta na rawa “Ibrahim me yasamu d’ana?. Dago idanun shi yayi ya kalle ta cikin kallon kece sanadi mommy. “Look at it mommy kinga irin ta ko, d’an uwana na cikin Wannan halin because of you, mommy don dai ke uwata ce Amma in wani ne bazan taba yafe mai ba, now just pray d’an uwana ya tashi lafiya I promise dole abashi farin cikin shi that’s enough! hakurin shi yayi yawa. “Ibrahim ‘ kawu ya daka mai tsawa, “me yasa kake fadawa mahaifiyar ka magana haka, me yafaru? Matsawa yayi cikin karyewar zuciya, ya fada jikin kawun ya saki kuka mai zafi Wanda ba Wanda zaice jarumin namijin ne ke irin Wannan kukan.
Bubbuga bayan shi kawu yayi ” ya isa insha Allahu zai tashi lafiya, Kayi shiru haka. Fitowar likita ne yasa ya yi saurin share hawayen yace “lafiya doctor yaya na fa? “Please kaine Khaleel?. “Yes”. Come your brother is calling you.
Bin likita yayi da Sauri kawu ya bishi shima, mommy zata shiga likita yace su tsaya waje mutane zasuyi yawa a emergency.
Jinin ya tsaya kadan sai Wanda ke bin hancin shi kadan kadan, yana isa yaja gefen rigar shi ya goge mai, “yaya please ka cire damuwa zaka tare da Matar ka I promise you kaji. Wani irin numfashi yaja mai wuya tareda fitarda murmurshin dole.
Yace “kawu”, tareda mika hannu yace ga Amanar d’an uwana, kawu don Allah ka kula dashi ka tsaya mai akan komai, inason yayi farin ciki, kawu don Allah make him happy kar ya shiga damuwa idan bana nan, Khaleel take care of Naziya, where is she? Please call her, ka kawo min ita Ina so in roketa gafara please go and bring her. Ja da baya yayi tareda girgiza kai, ” no no no stop that yaya nothing is going to happen to you, bari inkawo ta please yaya kadaina magana haka ciwo ai ba shine mutuwa ba, I don’t like this, stop it. Am sorry Khaleel. Yafada yana mai kallo mai cikeda sakonni, fita yayi da sauri yana yi kamar zai tashi sama, riko hannun kawu ya kuma yi, “kawu don Allah kar Kabari Naziya ta fita agidana ko bani, kawu kabawa Khaleel ita ya Aura nasan zai bata kulawa saboda soyayyar da yake min please kawu”. Mugun sanyi jikin kawun yayi domin Abun ya tsorata shi, a’a Ahmed kadaina irin Wannan maganar, haka d’an uwana yatafi yabarmin Amanar ku, bangama saukewa ba zaka bani wata, Insha Allahu zaka tashi kaji, likita kuyi aikin ku mana,. Yafada cikin tsawa, “Alhaji muna bakin kokarin mu Amma zuciyar shi tariga tagama kunbura shiyasa yake Aman jini, tunfarko yasan yanada ciwon zuciyar yabari tunani yashige shi Wanda yafi karfin zuciyar.
“Karka kawo min hauka nawa zanbiya ayi mai aiki, inba zaku iya ba infita dashi waje. Mommy ce ta shigo tana kuka tareda matsowa kusa da gadon da yake” Ahmed meke damun ka? Me yafaru dakai? Don Allah katashi.
Rikota kawai yayi dakyar ma yanzu yake fitarda numfashi, “ki ya fe min mommy na. Ya fada daya bayan daya yana riko hannun ta gam Wanda tanajin rikon cikin jijiyoyin ta rikone mai matukar karfi irin na fitar rai, koda takalle shi kafin tace wani Abu sai dai ganin jinin tayi yana Kara fitowa tareda kafewar idanun shi sama, kafin ya saki Hannun ta. Suman zaune tayi na wucin gadi kafin likita da kawu su gama magana su juyo, zarah ma tashigo, wani irin tsinkewa jinin ta yayi domin ba tantama Ahmed dai rai yayi halin shi,
“Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun. Kullu nafsin za’ikatul maut. Kowane rai tabbas ne zai daddani zafin mutuwa don haka sai muyi fatan cikawa da imani, Ahmed dai yatafi yabar Wannan duniya mai cikeda rudani.
“Aunty Ahmed yatafi” Zarah tafada tana dora hannun ta saman kai, kawu wani irin zuface ta karyo mai tuni ya ciro hular kanshi yana fifita, “ya Allah” Kawai ya iya fada saboda sarkewar kalmomin bakin shi, saida zarah ta jijjiga mommy, kafin ta fasa kuka”wayyo Allah na ni balkisu Ahmed tafiya Kayi kabarni, why Ahmed why?
Rufeshi likita yasa Akayi da farin zanin gadon, yace Alhaji sai hakuri Ahmed lokaci yayi. Dakyar kawu ya iya saita natsuwar shi yana goge gumi kamar ya hadiyi kunama, ya ciro wayar shi a Aljihu ya yakira Khaleel, ” kana Ina? “Yanzu na shiga gida kawu zan dakko Matar yaya. “Stay there muna zuwa. “Why yaya yac…. “Just do as I said, yafada cikin fada kafin ya katse kiran.
Shi ya hada komai yayi clearing aka basu Ambulance Abunka da kudi cikin minti kadan suka tafi da gawar su,
Mommy kamar ta haukace ji take kamar a mafarki wai Ahmed dinta ne ya mutu. Aunty zarah ido yayi Hulu Hulu.
Naziya tun fitar su take kan dadduma, zuciyar ta bugawa takeyi da karfi takasa ko motsawa, su kuwa Amare suna hakimce kowacce taci Ado kamar masu gasar gwal. Sun hakimce a falon,
A harabar kuwa Khaleel ya kasa gaba ya kasa baya saboda tashin hankali, ga umarnin kawu, yana daskare jikin motar yaji kukan Ambulance, wani irin kallo yake wa motocin su mommy, ganin yanda Aunty zarah ta riko mommy sannan kawu shima ya fito kai ba hula, ya maida idanun shi akan Ambulance yana kallon nurses din suna bude motar, ganin sunfito da mutum rufe da farin kyalle ya zube kasa war was, domin baya bukatar Karin bayani akai. Masu aikin ne suka ruga wajen shi domin jin faduwar tashi Tim.
Mommy ta tafi luuu itama tana shirin zubewa, shima ya mutu ko zarah? In ya mutu shima ni tawa ai takare kenan. Tafara sambatu, zarah ta riketa tana jijigata a’a Aunty bai mutuba, kai ku shiga dashi ciki, kawu dai nata gawa yasa aka shige dashi ciki, hakama Khaleel anyi ciki dashi,
Wanda tuni hankalin kowa ya kawo kan abinda yake faruwa banda Naziya, domin Amarya Salifa ita kanta jikin ta yayi mugun sanyi, wane irin Abu ne haka Auren ta jiya miji ya mutu yau,
Kukan da mommy ta fasa yasa Naziya fitowa jiki na tsuma da carbi, ganin mutum kwance akasa ga kawun su zaune agaba ya dafe kai yasa tafito jikin ta a mace tana sand’a kamar barauniya.
Kukan dasu Aunty zarah dasu Salifa keyi yasa ta gano duk Abinda yake faruwa. Dabas ta baje akasa kamar kurma, kafin kace me, tuni ji da ganin ta sun dauke.
Koda ta farko, taga dakin ta makil da mutane harda su gwaggon nin ta dasu Aunty Raliya da kuma matan kawu.
Zabura tayi tana kallon jikewar da jikin ta yayi da ruwan da aka rika kelaya mata,
Ganin ta zaburo Aunty Raliya ta riketa, “Naziya bi a hankali ruwa ne a hannun ki. Kallon hannun tayi, tareda kallon mutanen tace mafarki nakeyi ba mutuwa yayi ba ko? Aunty bai mutuba ko? Ku fadamin Ina yake?
Dafata kanwar malam tayi tace “ki yawaita Inna lillahi Wa Inna Ilaihir Raji’una Naziya. Tafiya takuma yi luuu. Suka kwantar da ita, kowa na share kwalla,
Khaleel kuwa saida akayi da gaske ya farfado, lokacin angama hada gawar Ahmed, zabura yayi kawai, ko digon hawaye yakasa fitowa a idanun shi.
Kannen shi ne yaran kawu maza suka rikeshi “yaya Khaleel bi a hankali karka fadi. “Let me go. Yafada cikin fada. Kafin ya fisge ruwan yafice cikin Sauri lokacin za adauki gawar zuwa makwanci, harda malam yazo gidan yau.
Cikin sauri yace “kawu kubari inyi mai Addu’a, fuskar shi ba ko Alamar hawaye domin ance kuka wuri yake samu watarana zuciyar shi ta cushe ta inda bako digon hawaye dake shirin zubowa.
Kowa yasan na zuci yakeyi Wanda ke cin zuciya, don haka malam yace “Ibrahima, ka saki zuciya Kayi kuka bakyau hadiye Abu yana illata mutum cikin sauri.
“Malam muje akai yayana makwancin shi. Yafada yanasa hannu ya daga makarar gefe daya domin yasan idan shine yayan shi zaiyi mai har wankan karshe, Amma tunda bai samu yimai ba shine zai sakashi cikin Kabari tareda samai kasa da binshi da Addu’oi.
Yabawa kowa mamaki yanda ya sakawa kanshi jarumta, har zuwa makabarta, inda da hannayen shi yasakashi cikin Kabari, tareda yimai kallon karshe, Wanda anan zuciyar shi ta karye ya fara fitoda hawaye, shikenan yayan shi yatafi, gatan shi Wanda saboda shi yadawo Nija, da ana dawo da hannun ago go baya da ya canja tsarin rayuwar Dan uwan shi , da ya hanashi shiga bakin ciki, Amma me komai mukaddari ne baida Wannan damar komai, yanda Allah yatsara haka zai kasance.
Lallabo shi akayi dakyar zuwa gida malam da sauran y’an uwan su, harma da mutane gari Wanda kowa mutuwar Ahmed din ta girgiza shi, Wanda sai ka mutu ake sanin halayen ka, wasu nacewa dazufa sun gaisa a masallaci, Wanda ita rayuwa haka take yanzu kana nan Anjima baka sai wani kuma, rai bakon duniya, Allah yasa mucika dakyau da imani………. 🖊
“Kai jama’a bantaba k’isa ba a littafina irin Wannan don haka nikaina na koka na girgiza Wanda nasan watarana saidai labarina nima zantafi, ya Allah Kayi mana kyakkywan karshe kasa mucika dakyau da imani don darajar ma aiki, S. A. WðŸ™
*Matar Soja*
10/20/21, 7:33 AM – Fiddausi Yunus: 🌻🌻AUREN GADO🌻🌻
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA,
BARIKI AUREN SOJA,
MUK’ADDARI,
WANAKE AURE,
ZANYI BIYAYYA, Y’AY’AN GATA, And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y’an 🇳🇪 Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,
*my fans masu maganar Ahmed yabar k’wanshi, ai mommy zataji dadi gwara tayi nadama ta har Abada tasan Allah yabata yaro mai yi mata biyayya har bayan idon ta, kuma shine zai zamar mata tabo har karshen Rayuwar ta don haka muje zuwa dama bahaushe yace in kana mugunta bakayi wa kanka ba to baka cika mugu ba*
Last 🆓 page