Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 22

Sponsored Links

Kallonta kawai Sadiya take cike da mamaki

“Anya kuwa Inna bata fara shiriftun tsufa ba” Sadiya da ta yi niyyar faɗar maganar a zuciyarta bata san ta fito fili ba sai ji ta yi Inna ta ce.

“Bana son ƙaniyanci Halima, kar fa kaza ta tono wuƙar yankan ta fa, abin da kike min fa ya isheni tura ta kai bango aradu, ni ce nake shiriftun?”

“Allah Inna a raina na yi niyyar faɗa”

“Sai Allah ya toni asirinki ya fito min da ita fili na jita dama ai Allah ba azzalumin bawa bane”

“Yanzu dai ki yi haƙuri ki faɗa mini”

“Humm ke dai bari Halima ai yau na tsallake rijiya da baya, wallahi wani gida na je garin kallon gidan ƴan gayu wasu ɓarayi da suka zo satar wata mata muka yi arangama, aikuwa ji kike ƙiiii kamar sun samu tsohuwar motar da ta daɗe bata ga garejin gyaraba haka muka rinƙa nausawa daji kamar za mun doshi dajin sambisa, ke da na gaji dai na ga ana neman wuce gona da iri, ana neman a je a yi watanda da kaina, na yanke shawarar na fara yunƙurin ƙwatar kaina ta hanyar yin abin da ya dace” Cewar Inna tana gaftarar appale har tana lumshe idanu.

“Inna ba dai wani abin kika kwaɗa musu kika yi kisan kai kika gudo ba?” Cewar Sadiya a fili a zuciyarta kuma ta ce

“Na shiga uku kar dai tsohuwar nan ta sanyamu a uku a zo har gida a kame mu bamu ji ba bamu gani ba”

Ganin Inna tana ta dariya ko tsayawa bata yi sai Sadiya ta zuba mata ido kawai da mamaki.

“Wayyo Sa’adiyya ni na san abin da na yi yau wallahi ko ni na tuna abin da na yi sai na ji dariya da kunya sun kama ni, sai dai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, yadda na ringa shaƙe ƴaƴan mutane kamar Allah ne ya aikoni wallahi, daga na damƙi wannan sai na damƙi ta wancan” Cewar Inna a zuciyarta tana ta dariya tana hango yanda samarin suka yi ta zare ido daga zarar ta ƙwamuso al’aurar su.

Nan ta kwashe labari kaf ta faɗawa Sadiya, Sadiya kwa dariya har da riƙe ciki, tana ta mamakin Inna tabbas tsohuwar ta san kan mugunta amma kuma sanin muguntar tata ya mata rana tun da ta ƙwato kanta har da tsarabar kayan marmari. Imran da tun da zai shigo ya ji Inna ta kamo labari ya dakata ya laɓe sai da ya gama ji kaf sannan ya yi sallama ya shigo yana ta danne dariyarsa dan sosai yake hango idanun samarin da Inna ra yiwa wannan ɗanyan aikin da a ce wani zai samu labarin cewar ba aljana bace ya san idan suka haɗa hanya ba lallai su barta da rai ba dan ko shi yanzu ya hasaso irin yadda zai ji jiki da a ce shi aka yiwa haka.

Haka dai aka cigaba da ZAMAN WANKAN ana karawa tsakanin Inna da Imran, har ya zamana saura kwana biyu suna, ranar ta kasance ranar laraba inda suna ya kama za a yi shi ranar juma’a dan haka ranar ana ta yiwa me jego ƙunshi da wanda suka zo daga dangin mahaifiyar Sadiya da da wasu daga cikin ƙawayenta na kusa, sai Ashrof da ƴaƴan ƙanwar Mama, Jan lalle ne ake zana musu sai kuma fulawa da ake zana musu Inna da ke gefe a zauna tana ta kallon budurwar da ta duƙufa wajen zanen fulawa kamar dama can da shi aka halicceta yadda take zanawa, Inna da ta gaji da taɓe baki ta ce.

“Kai wannan yarinya da kudura kike da shegen son kuɗi yo in banda neman kuɗi ke ɗaya da ranki amma kin kama ƙafafu sai zane su kike kamar kin samu bayan ƙwarya, ke bakya ma tsoron aljannu su tasheki tsakiyar dare su ce ki zana musu a hannu da ƙafafunsu, baki ji ba an ce kwalliyar aljannu ce, a ce ki rasa sana’ar yi sai zanen aljannu ban da ɗorawa kai jafa’i” Cewar Inna tana kallon budurwar da tun da Inna ta fara rattabo maganganunta ta dakata ta zuba mata ido cikin mamakin kalamanta.

“Kin ga Inna neman kuɗi halak ne, da a ce sata nake fa ai gwara na nemi halal ɗina, kuma da kika ce kwalliyar aljannu ce ni ban ma taɓa ji ba, kawai idan so kike a zana miki ki shiga layi idan layi ya zo kan ki in miki” Cewar budurwar dan dama da ganinta idonta a tsaitsaye yake kamar ma wata ƴar duniya-duniya.

“Allah kiyashe ni aikin da na sani, ni Azumi dan asara in zauna a zana min wannan abin me kama da jelar saniya, kakar dai wata me budurwar zuciya dan na faɗa miki gaskiya za ki nemi ki faɗa min magana to wallahi kar ki min rashin kunya kin ji na faɗa miki” Cewar Inna tana wani hayayyaƙowa yarinyar kamar ta kai mata duka.
Sadiya da ta shigo falon yanzu ta ga abin da ke faruwa dan dama kitso ake mata ta fita ta yi fitsari, ta dakatar da yarinyar tana baiwa Inna haƙuri dan a zauna lafiya duk da ta san Inna ce bata da gaskiya amma haka ta ɗan yiwa yarinyar signa a kan ta ja bakinta ta yi shiru.

“Faɗa mata dai ku da kuka san darajar mutane, me zan yi da wannan zanen fulawar ban da ma toshewar basira a zana maka ka je ka mutu da shi a kai ka kabari mala’iku su kankare maka da dutsin wuta, gwara in yi da lalle na asali tun na iyaye da kakanni, saboda gudun matsala ma da kayana na taho daga garinmu yana cikin jaka lalle me kamu idan ka ƙunsa ka ga ƙafafunka babu banbanci da ƙafar ba’indiyar da aka yiwa ƙunshi, , sai gobe zan ƙunsa kayana, na san aminiyata Tsahare ma shi za ta ƙunso in ta tashi ziwa suna.Bari ma dai na tashi na je na yi sallar azzahar dan na ga ku wannan abin ma kafin ya kama ku cire sai dai ku harhaɗa sallolin haka kawai ko tsoron Allah bakwa yi” Cewar Inna ta tashi.

Me ƙunshin ce ta raka bayan Inna da wata uwar harara tana murguɗa baki ba tare da kowa ya lura da hakan ba, ji take kamar ta yi ta dukan tsohuwar nan me shegen rangwangwan da shiga shari ba shanu. Ji take da a ce za ta samu dama babu dalilin da zai sa ta rama cin mutuncin da Inna ta yiwa sana’arta.

Kowa dai bai furta komai ba, dan gudun Sadiya da Ashrof kar su ji haushi, a haka aka cigaba da zana musu ƙunshi ja da baƙi.

Inna kuwa tana fita ta nufi bayi ta yi tsarkinta ta fito ta fara ɗaura alwala. Ƴan falo ana ta hira kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Hassan da Husaini kuwa Sadiya ta ajiyesu a bedroom saboda bacci suke kuma bata son hayaniya ta tashe su. Lokacin da Sadiya ta fita za ta jefar da gashin danya fita daga kanta da aka mata kitso, kawai ƴan falo sai ganin miciji suka yi ya fito zulululuu daga cikin ɗaki, gabaɗaya aka shiga gudun famfalaƙi kowa yana neman ceton rai haba wa Inna da ke zaune tana alwala lokacin tana wanke fuska sai ganin mutanen falo ta yi suna fitowa kamar ana korosu kowa yana kama gabansa, da mamaki ta dakata da alwalar da take tana so ta gano abin da ya sanya su wannan gudun. Sadiya da ta juyo daga wajen bola ta hango mutane kowa a ruɗe, Ashrof da ta yi wajen bayi ce kaɗai ta iya nuna mata hanyar falo da hannu alamar akwai wani abu tana nuna mata kwa ta yi wuff ta faɗa bayi ji kake gararaf ta banko ƙofa, ta jingina da ƙofar daga cikin bayin.

Inna ta kasa gane dalilin da ya sa ake tseran ta buɗe baki za ta fara sababin nata ba sai hango miciji ta yi ba ya fito daga falo, idanu ta zaro a kiɗime ta tashi daga kujerar da ta zauna take yin alwala, ji kake gwaraf ta bi ta kan butar alwala tana kama zaninta da ke neman faɗuwa, mamaki take duk sawayar da Hassan ke yi ma iyakarsa ya motsa jela ko kansa amma yau ya fito da kansa har tsakar gida, da alama farautar rai ya fito, aikuwa Inna ƙafa me na ci ban baki ba sai ta nufi hanyar kicin ko sauraren Sadiya da ke ta faman mata maganar ta kalli Hassan ya koma miciji ya fito bata yi ba ta faɗa cikin kicin har tana gware da bango sosai goshin ya bugu amma babu damar murzawa haka fa daure tana neman mafaka.

Tana shiga kicin ɗin ta hango ƙafar wata ta leƙo daga cikin lokar kicin ɗin da nan take niyyar shigewa, amma ganin kusan mutum biyar a ciki sun cunkusu wata ma a kan wata take sai Inna ta fara rarraba ido.

“Wannan tashin hankali da me ya yi kama ni Azumi, a ce kai kullum baka da kataɓus baka da kwanciyar hankali” Ta faɗa a ranta hankali tashe, hango yarinyar nan me ƙunshi Inna ta yi a bayan ƙofar kicin ɗin daga ciki sai raba ido take tana ƙifƙiftawa wata harara Inna ta doka mata tana juyawa ta fara waigen mafaka, ganin danƙareriyar freezer wacce suke ajiye kayayyaki, karamin frige ɗin kuma shi ne a falo da hanzari Inna ta buɗe freezer aikuwa ta yi sa’a babu komai a ciki ba ma a kunne take ba.

“Yawwa Allah ya bani mafakar ɓuya, haka kawai Halima ta haifa mana jaraba shi kuma wancan mijin nata me kai tun na haihuwa ya hana a kai yaron bakin ruwa su ɗau kayansu ya bar mana shi kullum mu hankali rabe a biyu” Cewar Inna tana kiciniyar shiga freezer, sai da ta shige ta miƙo hannu za ta rufe murfin sai ganin yarinyar nan me ƙunshi ta yi tana ƙoƙarin shiga ita ma da sauri Inna ta tashi tsaye daga ɗan ɗosana ɗuwawunta da ta yi a ciki ta tsugunna ta galla mata harara ta ce.

“Gidan uwaki za ki shiga, na ce gidan uwaki ne nan ɗin za ki shiga?” Cewar Inna tana yi tana dogon wuya dan kar micijin ya zo kicin ya farmata.

“Ki bari mana mu shiga tare baki ga na cikin lokar nan ba ma duk cunkusuwa suka yi wani kan wani, zama da ba na daɗi ba yaushe mutum zai ce baya son matsi”

“Ai wallahi ko haɗiyeki micijin nan zai yi sai dai ya haɗiye, ba ke taƙamarki fitsara ba to ma ji ma gani an rufe tsohuwa da ranta” Cewar Inna tana ture hannun yarinyar daga jikin freezer da shige tare da rufe murfin freezer.ƙwafa yarinyar ta yi ta duba mukullin freezer ta ga yana jiki, aikuwa ta kulle, ta ɗauki wayar freezer ta jona a socket ta kunna ta ce .

” Ma ga yadda za ki yi” Ta faɗa tana komawa mafakarta ta ɗazu bayan ƙofa ta raɓe tare da ɗaukan wani buhun shinkafa danya ƙare ta lulluɓa duk gudun kar miciji ya ganta.

A tsakar gida kwa Sadiya ta rasa yadda za ta yi, ta taɓa micijin ya fi sau a irga amma yaƙi komawa mutum kawai sai ta samu wuri ta durƙushe take rasgar kuka abinta da abin ya girmi tunaninta.

A kicin kuwa Inna da ke cikin freezer ta fara jin wani sanyi a ƙafafunta, dan babu takalmi a ƙafarta tun lokacin da ta kwaso fa gudu ta silleshi jin zai hanata wali wajen gudu. Jin wani sanyi yana ratsa ƙafafu da jikinta sai abin ya bata mamaki dan ta san dai da idonta ta ga wayar freezer ma bata jikin socket, amma kuma ya ɗauki sanyi sai hakan ya bata tsoro sosai, jim kaɗan kawai sai ji ta yi gabaɗaga freezer ta ɗauki mugun sanyi, a take ta fara karkarwa jin sanyi na ratsata ta ko ina.

“Habunallahu wa ni’imal wakil, kar dai shegiyar yarinyar nan ce ta rufeni a ciki” Cewar Inna lokacin da take ƙoƙarin buɗe freezer ta ji ta a rufe gam. Jin sanyin ya yi yawa ta fara share hawaye tana cewa.

“Malam ka ga Azuminka dai ko suna ba a yi ba amma ina karɓar uƙuba kala-kala daga wannan sai wannan sai ka ce wacce uwarta ta ce ki je kya gani, ko dai baka yarda da tahowata ba ZAMAN WANKAN nan ba har zuciyarka, a ce ina ganin ƙalubale kamar an min baki” Ta faɗa tana sa hannu ta bugi jikin freezer. Ƴan cikin loka da me ƙunshi da ke lulluɓe da buhu da bata gane daga inda ƙaran ya fito ba duk zatonsu miciji ne ya ƙaraso kicin ɗin, ƴan ckn lokar a take suka cure a wuri ɗaya kamar ƙarago, ta cikin buhu kuma ta tuƙunƙune gefen buhu ta cusa a bakinta gudun kar tsoro ya sa ƙara ya kuɓuce mata micijin ya ga maɓoyarta ya farmata.

Back to top button