Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 64

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*64*

Matar ta kallesu tace ” Ina kwananku ” lafiya suka amsa Ummeey ta tashi tace ” Ina hall ku sameni a ciki ” ta juya ta tafi hajjo da naima suka Kalli juna , matar ta nemi waje ta zauna ta Kalli Hajjo tace ” wallahi Ina carrying course din ne bana fahimtar komai don Allah ko zamu zauna tare ku dan taimaka min ” hajjo ta girgiza kai tace
“Allah Sarki CO Babu dadi wallahi, Allah ya bamu sa’a” ameen ai ke Aisha kin gode Baki da ko d’aya ” Naima ta fada tana kallon Hajjo, sauke numfashi tayi tace ” Allah yasa dai mugama lafiya ”
“Ameen Kinga ni course din ne ya rikeni nayi spilling out” ” haba dai toh Allah yasa Hakan shine Mafi alheri ” ” Ameen nagode sunana ummu Abeeha ”
“Ok sunana Aisha wannan Kuma Naima”
“Ok Allah sarki bani number ki ” nan Hajjo ta kira mata ta dauka tai flashing ya shiga sukayi saving, hajjo tace” mu shiga ciki is almost time”

Related Articles

tashi sukayi a jere suka shiga hall din can baya suka hango Ummeey tana kwance Saman desk tana ganinsu tare da wannan matar ta Kara tamke fuska, dalibai na ta shigowa aka raba question paper suka fara hajjo na kusa da umme Abeeha ta taimaka mata sosai har suka gama aka kawo Wani ummu Abeeha ta musu sallama ta tafi tana godiya, paper 3 suka rubuta kowanne 30 minutes ne sannan suka fito sai Kuma gobe.
Suna fita daga hall Ummeey ta Kalli Hajjo tace ” wallahi ki raba kanki da ummu Abeeha naga sai Wani zakewa kike ke a dole mai son jama’a toh wallahi raba kanki da wannan mata ba sarar ki bace ”
“Dama kinsanta kenan shine kike ta Shan kunu ” Naima ta fada tana kallon Ummeey, hada rai tayi tace ” ehh..nasan ta wallahi shedaniya ce , ke wayema baisan ummu Abeeha ba me maganin mata ga tara Yan iskan mata a gida gidanta kamar dandalin mata sai gulma da munafunci nidai na rabaki besty Babu ruwanki da ita ”
“Toh yanzu ni nace Miki zanje gidanta ne besty ”
Naima tai caraf tace ” toh ke a Ina kika Santa naga dai ke ba matar aure bace bare a ce kina zuwa Siyan magani ”
” Kawar anty zee ce da Amma taso taci amanar anty zee suka rabu ke Kuma besty yau ta hangoki da Lambo shine zata Wani like Miki kibi a hankali ” ” nagode besty ni zan wuce sai gobe ana jirana ” tabe Baki Ummeey tayi” ohh besty dama haka aure yake wato yanzu Baki da lokacin mu ko y’ar hirar nan Baki zama ayi kamar da hmm Allah ka aurar damu Naima ”
Murmushi naima tayi tace” Ameen Amma dai ki mata uzuri saboda driver na jiranta ”
” Ni lokacin da muke zama muyi hirar bana ajiye driver ya jirani ne kedai bakison gaskiya ne ” girgiza kai hajjo tayi” kedai kwanan nan kin canza besty da dai bahaka kike ba”
“Kema kin canza bare ni ”
“Nidai ayi hakuri sai gobe ”
Hajjo ta juya ta fara tafiya Ummeey ta kwashe da dariya tana cewa ” wayyo Allah aure dan ni’ima aure dan zako ” murmushi hajjo tayi tana girgiza kai ta d’aga musu hannu ta wuce mota Fauzan na ganinta ya fito Yana Bude mata tana masa sannu da Jira, idanun kawayen nata na wajen suna kallon komai Naima tace ” gaskiya Aisha ta samu duniya wallahi na mata murna Allah ya bamu namu mazajen ”
“Hmm..tashi mutafi malama ” Ummeey ta fada tana gyara bag nata daga haka suka wuce motar gidan su Ummeey tare suke zuwa suke komawa.

*2:30* ta gama girkin ta shirya komai yadda ya dace cikin manyan kuloli ta zuba saboda Bata sani ba ko Yana tare da baqi zobo me shegen dad’i ta hada ta Zuma cikin sababbin containers Wanda Fauzan ya kawo , ta hada kunun aya me dabino da kwakwa da milk sai qamshin flavor ke tashi ta gama ta adanasu a falonta. Part din Failuzaa ta shiga dauke da abincin ta sameta a falo nan suka baje bisa kafet kowacce ta zuba cikin plate suna ci suna y’ar hira, sallamar Fauzan ta sinkayo kamar a kofar falonta yake nan ta tashi tace tana zuwa , ta Mika masa komai ya dauka ya Kai mota ya sake dawowa ya kwaso sauran abubuwan sannan ya tafi.
Failuzaa tana kallonta bayan ta shigo “kamar muryar uncle Fauzan koh”. “ehh abinci yazo dauka ”
“Abinci Kuma…toh sabon salo abinci a office ” murmushi hajjo tayi” shiya bukaci Hakan ”
“Ohh..kinsan Baiyi breakfast ba ya fita inaga yunwa ce dayake yau girkin ki ne , yanzu kwana biyu din zakiyi kenan koh”
“Wannan sai yadda kika fada uwargida ran gida ”
dariya tayi harda shewa tace” Kai wannan amaryar tawa akwai fasa Kai wallahi kina burgeni yadda kike da ladabi dama baka ya kamata kowace amarya ta girmama uwargidan ta wallahi ” hajjo dai tana kallon iKon Allah wajen Failuzaa wato Bata iya boye komai sai ta nuna.
” Wai don Allah ya kikayi daren amarcin ku don nasan Qalbee ba daga nan bah ” murmushi hajjo tayi ” hmm lallai kuwa ”
” Ke ki daina Jin kunya nifa a matsayin y’ar uwa na daukeki don naga kina da saukin Kai ga ladabi donhaka karki boyemin komai ki fadamin ”
“Nagode da kika daukeni matsayin y’ar uwa ”
“Amma ya fada Miki baya son maganin mata koh,hmm ai idan yasan kina amfani dashi zai mugun bata Miki Rai kingani yanzu bana Shan komai wallahi Kuma yace Hakan yafi so , ance magani na cire test din mace ” hajjo ta gyara zama tace” da gaske..Allah yasoni dama bansha ba ”
“Haba kina nufin Baki Sha komai ba?
“Ehh mana an kawomin Amma ban fara amfani dasu ba ” ” yawwa Hakan yafi miki wallahi natural taste naki yafi burge namiji , ga Kuma cancer da magungunan ke haifarwa ”
“Hakane Allah ya karemu” “Ameen fah , Kuma kinsan shi Qalbee yafison ki barshi yayi komai da Kansa kedai ki baje kawai ”
“Kai mum meenal”
“Allah na gaya miki idan kina masa Wani abu sai Kiga ya hada rai, kinsan ni mun Dade nagane duk abubuwan da yake so shiyasa nake fada Miki yadda zaki faranta masa”
“Hakane gaskiya nagode sosai ” murmushi tayi” ai ba komai duk yiwa kaine farin cikin mijinmu ai namune duka ”
“Hakane nagode ”
“Kai Amma kin iya kunun aya dama kin fara yin na siyarwa da zakiyi ciniki sosai ” ” Allah koh ”
“Serious Kinga makota zasu na Siya ”
“Toh shikenan zan gwada ”
“Ko ni nan zan shiga na fada musu kinayi kinsan ni na Saba dasu sosai yanzu ne bana shiga kwana biyu da kullum Ina can ” “ok ayya bari naje na dan kwanta ”
tashi tayi don ta gaji da surutun, tana komawa part nata ta haye gado ta kwanta bacci takeson Yi yaki zuwa. Wayarta ya fara ringing ummu Abeeha ke kira murmushi tayi ta danna answer
“Anty Aysha ya kike ya test din”
“Alhamdulillah kinkoma lafiya” “lafiya kalau dama tambaya zan Miki ” hajjo ta gyara zama tace ” ok Ina jinki ”
“Nace wannan yarinyar Ummeey Armani Kun Dade tare ne ?”
“Ehh kawatace sosai tun a secondary school”
“Toh wallahi kiyi hankali da ita Basu da mutunci shu’umar yarinya ce nasan kaf Yan gidansu gaba da baya Basu da tarbiya dan gwara gwara ita Ummeey akan sauran yayunta donhaka kiyi taka tsantsan da ita, zasu shige jikinka sai sungama sanin sirrinka kaf su juya su fara yaki da Kai kibi a hankali bance ki rabu da ita ba Amma ki kwantar da hankalinki ki karance ta da kyau ” shiru hajjo tayi
“Kina keina anty Aysha ”
“Inaji ummu Abeeha ”
“Yawwa don ni nafiki saninsu bakiga tana ganina ta tashi tabar wajen ba, yayarta aminiyata ce Sosai amma yanzu mun rabu saboda sun so suci amanata Niko naci uwarsu mukayi baram baram muka rabu , kedai sai mun Hadu wataran zan Baki labari amma ki Maida hankali sosai ”
“Toh nagode sosai Allah yabar zumunci ”
“Ameen ba komai wallahi naji kin kwantamin a rai shiyasa nace bari na kira na fada Miki gaskiya ”
“Ayya thank you so much ”
“You welcome ”
ta kashe wayar hajjo ta sauke numfashi tace ” Kai jama’a ni Aishatu da wanne Jan yadda , toh Amma Ummeey dai Bata taba nunamin Wani mugun hali ba sai kwanan biyu din nan ne bana gane mata ,but Anya zata iya cutar dani ? maganganun sun tsaya mata a rai waya ta dauka ta kira inna ta zayyana mata komai inna tayi shiru Sannan tace ” toh..bamusan me Hakan ke nufi ba dama mutum yafi dare duhu amma Ummeey ai Kun dade tare idan ba dai yanzu auren da kikayi ne zatayi bakin cki dashi ba amma Ina ganin Bata da matsala kedai ki Maida hankali din ki lura da komai idan akwai Wani abu ki sanar dani Kuma ki rage fada mata sirrinki musamman sirrin gidan aurenki , idan akwai Wani abu ni zaki kira ki fadawa bance ki nemi wata kawa ba kina ji ai ”
“Insha Allah inna zan daina fada musu don ko yanzu naga kamar ta fara canza min ba kamar yadda muke da ba”
“Hmm kiyi a hankali ki rike adua Kuma karki wasa da azkar Allah ya kiyaye ” ” Ameen inna anjima zamu zo dama ”
“Me Kuma zaki zo Yi ?”
“Inna kedai Baki son ganina toh Wani surprise zan kawo Miki ”
“Allah ya kaimu Amma ni banson wannan yawace yawacen ki gama makarantar ki nutsu gidan mijinki ” murmushi hajjo tayi sukayi sallama taji hankalinta ya dan kwanta yanzu mutanen duniya tsoro suke Bata don idan har Ummeey zata iya mata Wani abu toh lallai Babu amana a wannan zamanin.

Da yamma Ayman ya dawo ya sake wanka ya shirya cikin half jumpa black da ratsin fari ya saka simple sandal fari Yana zuba qamshi as usual bangaren Failuzaa ya fara zuwa Bata nan kofan a kulle wato ta koma yawon bin gidan makota da ya hanata, part nasa ya koma ya dauki kwalin sabuwar wayar da ya Siyawa hajjo ya nufi part nata da sallama tayi wanka cikin lace coffee n golden dinkin doguwar Riga ce da aka zuba stone akayi kwalliya da bakin leshin daga sama har kasa ta kada dauri tayi Kyau sosai, sannu da zuwa ta masa Yana ajiye kwalin wayar ya zauna
“Ya gida hearty ”
“Lafiya alhmdllh ya aiki”
“Alhamdulillah naci abinci thank you so much kamar kinsani kuwa nayi baqi kowa yaci Yana godiya ”
Murmushin Jin dadi tayi ya saka hannu cikin aljihu ya zare bandir din yan dubu sababbi yace ” ga wannan Wani abokina yace a kawo Miki tukuicin girki Yana sauri ya wuce Lagos idan ya sake zuwa zai shigo ku gaisa sunansa Mashkur ”
“Allah Sarki nagode Allah ya Bada Lada”
Wayar ya Mika mata”gashi ki cire sim naki bana son ganinki da wannan crack phone din ”
Ware Ido tayi iphone ce dalleliya new in town latest Wanda akayi releasing this year cike da murna ta karbi wayar ta ajiye nan ta rungumesa gam Yana murmushi a hankali ta furta” thank you so much ubangiji Allah ya Kara lafiya da arziki Allah ya tsareka da sharrin Makiya thank you thank you so much, ni bani da bakin godiya daga jiya zuwa yanzu bansan iya adadin nawa ka kashemin ba nagode sosai Allah ya biyaka da gidan aljanna” lumshe Ido yake Yana Jin dadin adu’o’in nata , Wani guntun hawayene ya fito mata tana rungume dashi tace ” ashe dama Kai kake sponsoring school dina ,yau da labarin nan ya sameni a gidan Wani ba gidanka ba da nayi bakin ciki saboda ka gama min komai na rayuwa amma Alhamdulillah da na kasance mata a gareka Allah ya biya Maka dukkanin bukatun ka , ka zamemin jigon rayuwta hakika kaine Nasarar rayuwata nagode sosai Allah ya barmu tare ”
Shiru yayi Yana sauraronta itama Shirun tayi tana Jin sonsa na shiga kowane Sako na zuciyarta tabbas Ayman ya cancanci soyayya agareta shine ya zame mata hasken rayuwa lokacin da take bukatar hakan lokacin da ta rasa mahaifinta shine ya maye gurbin mahaifi ya mata gata ya sanyata a makarantar da har yau tana alfahari da hakan,
“Is ok baby alhmdllh Allah ya amsa min aduata yau kin samamin matsayi cikin zuciyarki Ina fatan Hakan zai dore har abada” “insha Allah zaka sameni mai bin duk Wani umarni naka fatana shine Kaci gaba da Sona har abada kada ka karyamin zuciya please”
“Har abada kin wuce wulakanci awajena saboda soyayyar da nake Miki halitta ce tun ranar da na fara ganinki na fara sonki donhaka ki daina tantama akan hakan , if you are ready ki tashi mu tafi wajen innarmu matar da ta haifamin ke ta gama min komai a duniya ”
Murmushi tayi ta raba jikin nasu ta koma bedroom ta dauki hijab da jaka ta zuba wayoyin nata ciki da sabon da tsohon ta fito Yana gaba tana biye dashi a baya suka fita harabar gidan har yanzu Failuzaa Bata dawo ba, da Kansa ya Bude mata ta shiga ya zagaye ya shiga bangaren driver ya kunne motar maigadi ya wangale gate suka fice.

Back to top button