Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 23

Sponsored Links

PAGE* 2⃣3⃣

Sumayya a ranar kasa bacci tayi kuka kawai takeyi musamman ma idan tatuno da yarima yana chan kwance da wata ba itaba, nan takeji tsanar zarah ta k’aru a ranta duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi motsi kad’an sai ta duba lokaci daga k’arshe zinat takira a waya

zinat da take bacci dakyar tajawo wayarta tana tsaki ganin sumayya ce yasa tad’aga cikin muryar bacci tace ya dai baby?

sumayya cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace dear ke bacci kike hankalinki kwance nikau nan nakasa

zinat cikin ranta tace kujimin mace sai ink’i bacci saikace ni akayi ma kishiya… chan kuma sai tace toh dear kema ke kika sa kanki rashin baccin miye na damuwa tunda dai kinsan dole yakasance da matarsa yau k’ilama ya mance da batunki.

sumayya cikin sheshek’ar kuka tace dolene indamu zinat kiduba fa kiga irin son da nakema yarima ammah yau ace shine tare da wata ba niba wlh natsani ko ma wacece,

zinat tace kikwantar da hankalinki ai wlh ba zamu kyaletaba nima ai dan bana k’asar ammah bari indawo sai munsan yadda mukayi muka fitar da ita daga gidan kinsani ai

sumayya cike da jin dad’i tace saisa nake sonki k’awata yanzu dai yaushe zakizo domin nima kaina ina kewarki

zinat ‘yar dariya tayi tace kar kidamu dear very soon zan zo miki domin nima kaina ina kewarki sosai yanzu dai kikwanta kisamu kiyi bacci

sumayya tace hmm dear bana tunanin zan iya bacci a daren nan ni kid’an turomin d’an abinda zai sani nishad’i

zinat tace toh dear muhad’e a online.

sumayya tace ohk, sannan suka kashe wayar a tare,

sumayya ta dad’e batayi bacciba tana kallon abinda zinat taturo mata har daga k’arshe dai bacci yayi awon gaba da ita.

 

Kiran sallar asubane yatashi yarima daga baccin da yakeyi kallon zarah yayi da take takure k’asa ta6e baki yayi yawuce yashige toilet, jin motsinsane yasa zarah tafarka daga baccin da takeyi dasauri tamik’e tare da gyara alkyabbarta tafito daga d’akin, da karambani tamaida kanta part d’inta lokacin masu tsaron part d’intane kawai a wajen, cike da girmamawa suka gaisheta ta amsa sannan suka bud’e mata tashiga.

zarah alwallah tad’auro tazo tagabatar da sallar asuba bayan ta gama hayewa tayi saman gadonta saboda wani irin bacci da takeji nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.

 

yarima ko da yafito daga toilet baiwani damuba ganin zarah bata d’akin yaficce yafita masallaci.

bayan ya dawo bai koma bacciba yad’auko laptop d’insa a parlour yazauna yacigaba da aikinsa.

wajen k’arfe 8 guard d’insa yashigo duk’awa yayi yagaishe da yarima, yarima batare da ya kallesaba ya amsa, cike da girmamawa guard d’in yace ranka yadad’e daman jakkadiyace tazo shine nace bari infara dubawa inga in kana parlour,

yarima yace me zanyi mata?

guard yace ranka yadad’e bari inje intambayeta.

yarima kallonsa yayi nad’an lokaci sannan yace kubarta tashigo.

Duk’awa guard yayi yak’ara kwasar gaisuwa sannan yamik’e yafita yabar d’akin.

bayan kamar minti biyu sai ga jakkadiya ta shigo da sallamarta, ciki-ciki ya amsa batare da ya kalletaba.

zubewa jakkadiya tayi tace ranka yadad’e Allah yaja da ran yarima mai jiran gado, Allah yabaka tsawon rai, Allah yad’aukaka mana kai, Allah ya kunyata mak’iyanka dafatan katashi lafiya.

me ke tafe da ke? cewar yarima.

jakkadiya kyarma tafara tace am daman.

yarima batare da ya kalletaba yace ina jinki.

k’ara duk’ar da kanta tayi tace ranka yadad’e kagafarceni daman dada ce ta aikoni tace inzo induba lafiyarku sannan ind’auko bedsheet awanke.

ta6e baki yarima yayi yacigaba da abinda yakeyi saida yayi kusan minti goma sannan yace zaki iya shiga kid’auka.

shiga jakkadiya tayi tad’auko tafito nan tak’ara duk’awa tace atashi lafiya yarima sannan taficce daga d’akin.

 

wajen k’arfe goma zarah tafarka daga baccin da take daidai lokacin d’aya daga cikin kuyanginta tashigo dasauri taduk’a tagaishe da zarah cike da girmamawa, zarah amsawa tayi cikin sakin fuska, sannan kuyangar tatashi tashiga toilet d’in zarah tawankesa fes sannan tahad’a mata ruwan wanka, sannan tad’auko mata towel.

bayan ta fito duk’awa tayi gaban zarah tace ranki yadad’e ruwan wankanki ya had’u.

zarah murmushi tayi tare da kar6ar towel d’in tace nagode zaki iya tafiya.

kuyangar k’ara duk’ar da kanta tayi tace ranki yadad’e nice wadda zan dinga gyara miki d’aki mu biyune d’ayan tana parlour tana jiran fitowarki,

murmushi zarah tayi tace kubarsa kawai ni zan dinga gyarawa.

A tsorace kuyangar tace a’a ranki yadad’e kigafarceni aikinmune idan har akaga mun bari kinyi da kanki za’a iya korarmu.

zarah girgiza kai tayi tace baza’a koreku ba, mik’ewa tayi tare da wucewa tanufi toilet.

lokacin da zarah tafito angama gyara mata ko’ina k’amshi kawai yake tashi, ita kanta zarah yanayin gyaran da akayi ya burgeta,

gaban dressing mirror tazauna ta tsantsara kwalliyarta sannan taje tabud’e wardrobe saida ta tsorata ganin lodin kayan da suke ciki, Holland atamfa tasaka Red nd white colour, d’ankunnenta ma red colour tasaka, murza d’aurin kallabi tayi nan kyaunta yak’ara bayyana, k’ara kallon kanta tayi a mirror sannan tafeshe jikinta da turaruka masu sanyin k’amshi, plat shoes tasaka tatako ahankali tafito parlour, ganinta yasa duk kuyangi da bayin dasuke parlourn suka zube k’asa suna ranki yadad’e gimbiya, Allah yaja da ranki takawarki lafiya dafatan kin tashi lafiya?

zarah tana murmushi tataka cikin takunta taje saman cushin tazauna, saida sukaga ta zauna sannan suka d’ago kansu,

zarah har a lokacin fuskarta tana d’auke da murmushi tace wacece shugabarku?

d’aya daga cikinsu ce tace ranki yadad’e ganinan nice shugaba, sannan kowa anraba masa aikin da zaiyi.

jinjina kai zarah tayi tace dat’s gud, dafatan dai zaku bani had’in kai muzauna lafiya, indai kukayi haka toh zakuji dad’in zama da ni sosai.

gaba d’ayansu sukace Allah yaja da ran gimbiya insha Allahu zaki samemu masu amana.

murmushin jin dad’i zarah tayi tace nagode zaku iya tafiya, nan suka k’ara duk’awa sukace atashi lafiya,

gyad’a musu kai zarah tayi nan suka mik’e, biyu daga cikinsu ne sukatsaya sukace ranki yadad’e mune masu kula da abincinki ga breakfast d’inki chan a dining idan kin bamu izini sai muje muhad’a miki.

zarah mik’ewa tayi tanufi dining nan suka take mata baya, dasauri suka jawo mata kujera nan tazauna, ganin zasuyi serving d’inta yasa tadakatar da su dakanta tazuba tad’anci kad’an sannan tamik’e,

nan suka gyara wajen, zarah saman kushin takoma tazauna tare da d’aukar wayanta takira mama suka gaisa,

tana cikin waya yarima suhail yashigo cikin takunsa nak’asaita sanye da alk’yabba yasha kyau, zarah kashe wayar tayi dasauri tamik’e tsaye tare da d’an russunawa tace barka da safiya.

yarima kallo d’aya yayi mata yad’auke kai yace kije kishirya kizo muje mugaishe da su memartaba.

zarah ahankali tace toh sannan tawuce tashige bedroom.

gyalenta tad’auko white tayafa tafito lokacin yarima yana zaune saman cushin, kallonta yayi yace babu alkyabbane cikin kayanki?

zarah tace akwai.

shuru yarima yayi baik’ara cewa komai ba, ganin haka yasa zarah takoma bedroom, red d’in alkyabba tad’auko tasaka sannan tafito tasamu yarima a zaune,

kallonta yarima yayi har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, mik’ewa yayi yace muje.

zarah bayansa tabi suka fito a jere nan guards d’insa da kuyanginta suka take musu baya yanayin yadda suke tafiyar kawai zaka kallah sai sun burgeka ko da ad’ankwai ‘yar tazara a tsakaninsu anutse suke tafiya har suka isa fada itadai zarah duk fargaba da tsoro duk sun cikata kanta sadde yake k’asa har suka shiga fada da take cike mak’il da jama’a nan mutane suka fara gaishesu, yarima ne kawai yake amsawa ahaka suka isa gaban memartaba,

lallausan carpet ne aka shimfid’a musu nan dogarawa sukayi musu zobe har saida suka zauna bisa sannan suka janye manyan rigunansu gaba d’ayansu suka duk’a suka gaishe da su yarima, yarima gyad’amusu kai yayi nan suka mik’e sannan yamaida kallonsa ga memartaba da yake kallonsu yana murmushi.

Zarah ce tafara gaishesa sannan yarima suhail, gyad’a musu kai sarki yayi alamun amsawa, nan fadawa suka d’auka sarki ya amsa gaisuwarku yarima da gimbiya ku ma angaisheku, Allah yaja da ranku,

memartaba kallon zarah yayi yace Alhmdllh ina tayaki murnar shigowa wannan masarauta tamu muna fatan Allah yasa alkhairi a cikin aurennan naku.

nan fada tad’auka da Ameen.

wata ‘yar jakka sarki yasa aka mik’o masa yaba zarah yace ga kyautata gareki.

zarah hannu biyu tasa takar6a tare da duk’ar da kai tace nagode ranka yadad’e Allah yak’ara girma da d’aukaka, nan kuyanga takar6a

nan fadawa suka d’auka sarki ya amsa godiarki gimbiya angaisheku.

memartaba kallon yarima yayi yace Allah yatayaka safke wannan nauyin da yahau kanka fatana Allah yasa ka kwatanta adalci atsakaninsu.

yarima kansa na sadde k’asa yace Ameen ranka yadad’e.

memartaba murmushi yayi yace zaku iya tafiya.

godia sukayi, dasauri dogarawa sukazo suka baje rigunansu suna ranka yadad’e atashi lafiya, takawarka lafiya jarumin jarumai saida suka tabbatar da sun mik’e sannan su kuma suka duk’e k’asa nan zarah da yarima suka fito sukabar fadar, kan zarah ya d’aure sosai ahaka suka shiga cikin gida turakar dada.

duk inda suka gifta duk’awa ake ana gaishesu, yarima d’aga musu hannu kawai yake itakuma zarah saidai tabisu da ido,

masu tsaron k’ofar dada ganinsu yasa sukayi saurin bud’e k’ofa tare da duk’awa sukace ranku yadad’e Allah yaja da ran yarima me jiran gado.

yarima bai tankasuba yana gaba zarah na biye da shi ahaka suka shiga nan kuyangin dada suka zube suka Kwashi gaisuwa sannan cikin sauri suka tashi sukabar d’akin.

yarima takawa yayi yaje saman cushin yazauna, zarah ko k’asa tazauna cike da ladabi tagaishe da dada.

dada nan ta amsa mata, fuskar yarima d’auke da murmushi yace ‘yar tsohuwa ina kwana?

dada tace au yau kuma da tsokana kazo? toh bazan amsaba, yarima yace ayya yi hak’uri, murmushi dada tayi tace dafatan kun tashi lafiya?

yarima yace lafiya lou, dada kallon zarah tayi da har lokacin bata d’ago kai ba tace amarya ya bak’unta? zarah murmushi tayi tace Alhmdllh.

dada kallonta tamaida ga yarima tace akwai matsala fa
yarima yace tame fa?

dada gyara zamanta tayi tace babu wata sheda da kuka nuna mana, mutane suna nan sun kasa kunne suna saurare ammah shuru wai meyake faruwa ne naga bedsheet d’in babu komai a jikinsa, ta k’arashe maganarta tare da kallon zarah.

murmushi yarima yayi yace ranki yadad’e saboda Allah komai ace sai mutane sun shaida, wannan ai tonon asirine.

dada tace a’a yarima wannan kasan shine zai d’aga darajar mace a idon kowa dake masarautarnan sannan kuma gada mukayi tun kaka da kakanni, rashin ganin jini zai iya sa ad’auka mace tazubar da mutuncinta a waje.

zarah da take saurarensu saida gabanta yafad’i dan ta fahimci akan abinda dada take magana.

yarima cike da rashin damuwa yace haba dada inbanda abinki yanzu ai anbar wannan.

dada tace injiwa? abinda muka gada tun kaka da kakanni? kai ni banyarda da kaiba anya kakwanta da yarinyarnan? inkuma ka kwanta da ita toh ya akayi babu wani alama da yanuna budurwace?

murmushi yarima yayi tare da kallon zarah da duk tabi tatsure cikin ranta mamakin maganganun dada take tace gidan sarauta akwai tonon asiri,
ahankali yarima yace dada period takene saisa hakan takasance, zarah dasauri tad’ago kai takalli yarima da yake dannar wayarsa saikace bashine yayi maganar ba, yarima ya fad’i hakane gudun kar su ummi suji labari dan yasan sai dada ta fad’a musu kuma sai sun fahimci wani abu.

dada ce tace ayyah Allah sarki ‘yar nan ai bamu saniba, kinsan haka abun yake, kinsan daren farko munaso muga alamar da zata nuna mana mace cikakkar budurwace dan hakan ne yake d’aga daraja da k’imarta.

zarah cike da kunya tak’ara sadda kanta k’asa, dada tace kikwantar da hankalinki zanyi ma kowa bayani yadda zasu fahimta.

yarima ne yace haba dada wannan ai tonon asirine.
.
dada tace gidanku, kaima ai kasan dokokinmu na wannan masarautar, yanzu dai yaushe ne zakiyi tsarki?

zarah kallon yarima tayi da shima yazuba mata ido, muryar dada taji tace ina saurarenki.

zarah batasan lokacin da tayi su6ul da baka tace jibi ba.

murmushi dada tayi tace Allah yakaimu, nan dada tamik’o mata alkyabba maikyau da turare tace ga tukuici na,

kar6a zarah tayi tare da godia ammah har lokacin jikinta rawa yakeyi.

nan yarima yayi ma dada sallama suka mik’e suka fito, daganan suka nufi part d’in sultana sadiya,

lokacin da suka shiga tana tsakiyan kuyanginta, da sallama suka shiga nan kuyanginta suka gaishesu sannan sukabar d’akin, ganinsu yasa gimbiya sadiya tad’aure fuska tare da wurgamasu harara, yarima baidamu da yanayin kallon da take musuba yaje saman kujera yazauna, inda zarah kuma tazauna k’asa tare da gaisheta, .

sultana sadiya shuru tayi bata amsaba, yarima suhail ne yace ranki yadad’e ana gaisheki fa, yamutsa fuska sultana tayi tace oh banjiba amarya kin tashi lafiya?

zarah k’ara duk’ar da kanta tayi tace lafiya lou, yarima suhail yace ranki yadad’e barka da safiya dafatan kin tashi lafiya.

lafiya, cewar sultana.

murmushi yarima yayi tare da kallon zarah yace wannan itace ummah sadiya mahaifiyar matata sumayya,

gyad’a kai kawai zarah tayi, ummah tace hmm mu ai muna nan muna jira muji anyi gud’a ammah har yanzu shuru babu abinda mukaji hakan yana nufin ba budurwa bace kenan kayayo mana cikin masarauta.

murmushi yarima yayi yace ranki yadad’e ai gud’a bashine ba kar kimance sumayya ma ba’ayi gud’aba lokacin da na aureta,

cike da 6acin rai sultana sadiya tace kar fa kayi min rashin kunya,
yarima cikin kwantar da murya yace haba ummah ni na isa inyi miki rashin kunya? kawai dai tuna miki nayi saboda laifi tudune katake naka kahango na wani.

zarah abun ya d’aure mata kai ganin yadda yarima yakeyi ma surukarsa,

sultana sadiya har ta bud’e baki zatayi magana sai ga sultan Abbas ya fito daga d’aki fuskarsa d’auke da fara’a yace a’a wai amarene?

murmushi kawai suhail yayi tare da d’an zamowa daga kujerar da yake yace abbah ina kwana?

sultan Abbas zama yayi yace lafiya lou yarima dafatan kuna lafiya?

murmushi suhail yayi yace lafiya lou Abbah, zarah k’ara sadda kanta tayi cike da ladabi tagaishesa.

cikin sakin fuska sultan abbas ya amsa mata tare da cewa amaryarmu ya kike ya bak’unta?
zarah tace Alhmdllh Abbah.

sultan Abbas yace masha Allah, dafatan zakiyi hak’urin zama da mu kinsan yanayin gidan sarauta sai andinga hak’urin zama da juna fatanmu kizauna da kowa lafiya, ko da yanayin ya nuna bazakiyi fitinaba.

Zarah cike da ladabi tace insha Allahu Abbah, mik’ewa sultan Abbas yayi yashiga bedroom bai dad’eba sai gashi yafito da wata leda nan yamik’a ma zarah yace ga kyautata,

zarah hannu biyu tasa takar6a tare da yin godia.

yarima suhail ne yamik’e yace abbah bari muwuce, sultan abbas yace to yarima mungode sosai a dai cigaba da hak’uri da juna.
yarima yace insha Allahu abbah mungode, nan zarah tak’ara yin godia sannan tataso suka fito.

ko da suka shiga turakar ummi duk inda suka gifta nan ma zubewa ake ana gaishesu, a parlour suka sameta kishingid’e ita kad’ai, ganinsu yasa tatashi zaune fuskarta d’auke da fara’a hannu tamik’a ma zarah tace zo nan kusa da ni d’iyata.

zarah cike da jin kunya tataka taje kusa da ummi tazauna, inda yarima yazauna saman cushin.

zarah cike da girmamawa tace ummi ina kwana? ummi tace lafiya lou daughter ya bak’unta?
zarah murmushi tayi tace Alhmdllh.
yarima ma cikin girmama yagaishe da ummi, itama ta amsa masa fuska a sake tace ya sumayya?

murmushi suhail yayi yace tana lafiya ummi, daddy fa yafita?
ummi mik’ewa tayi tace yana ciki bari inkirasa kugaisa nan tawuce tashiga bedroom d’insa bata dad’eba saigata sun fito tare da daddy,

bayan dady ya zauna nan suka gaishesa, daddy ya amsa musu daganan yad’anyi musu nasiha sannan yad’auko cheque yamik’a mata yace ga kyautata gareki.

zarah hannu biyu tasa takar6a tare da yin godia, daddy yace bakomai adaiyi hak’uri da zaman aure, sannan yatashi yafita.

ummi kallon yarima tayi tace inason magana da kai, saida tamik’e sannan tamaida kallonta ga zarah tace daughter yi hak’uri bari inzo,
zarah murmushi tayi tace toh ummi bakomai.

yarima tashi yayi yabi bayan ummi, bayan sun shiga bedroom ummi kallonsa tayi tace suhail menene haka kayi ban fahimcekaba daman nasan bakason auren nan yanzu saboda Allah kakyauta gashinan anata surutu akan baiwar Allahn nan?

yarima shuru yayi saida sultana bilkisu takai aya sannan yace ummi please kifad’amin menayi?

harararsa ummi tayi tace au kana nufin bakasan abinda kayiba kenan, yanzu saboda Allah an aura maka yarinya ammah babu abinda yashiga tsakaninku.

yarima sosa k’eyarsa yayi cikin jin kunya yace ummi am ba daman,

ummi tace daman me?
murmushi suhail yayi yace daman tana period ne.

dogon numfashi ummi taja tace toh ai shikenan na d’auka wulak’ancin nakane yamotsa nidai fatana karik’e min ita tsakani ga Allah kar kabani kunya.

murmushi suhail yayi yace ummi kenan saikace baki yarda da niba, kina tsoron inzalunceta ko?

murmushi itama ummi tayi tace ai nayarda da d’ana 100% Allah yayi maka albarka, murmushi yayi yace ameen ummina,

atare suka fito inda suka tarar da zarah inda suka barta, ummi murmushi tayi tace daughter munbarki kekad’ai ko?

itama zarah murmushin tayi tace bakomai ummi, wata leda ummi tamik’a mata tace ga wannan, sannan ummi tace rahama batanan da kun gaisa ammah insha Allahu idan tadawo zan turota kugaisa.

zarah tace toh ummi tare da yi mata godia, nan sukayi mata bankwana suka fito suka koma 6angarensu.

ahanyarsu ta komawa yarima suhail yakira sumayya

lokacin sumayya tana breakfast fuskarta babu walwala jin haushinta taje part d’in yarima ammah bata samesaba, dasauri wata baiwarta tamik’o mata wayar tace ranki yadad’e ana kiranki, kar6a gimbiya tayi a wulak’ance ganin mai kiranta yasa taja tsaki kamar bazata d’aukaba saida takusan tsinkewa sannan tad’auka babu ko sallama tace haba yarima yanzu saboda Allah ka…. yarima baijira tak’arashe maganarba yakatseya yace kisameni a part d’ina yanzu, bai jira jin abinda zataceba yakashe wayarsa.

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

Back to top button