Nasarar Rayuwata 44
*Talented writers forum*
*44*
Bayan sallar Isha hajjo na falo tana kallon Wani movie inna ta shigo ta sameta ” yaushe zakuyi exams?” ” Sai next month zamu fara” ok idan Babu Wani abu serious Ina son ki shirya zamuje Adamawa next week ” cike da mamaki hajjo ta tashi Zaune tace ” why d urgency inna kodai Baba na ya dawo ne ?”
“A’a kawai Ina son mu fara zuwa ne kafin aje Neman aurenki a can ”
“Aure..aure Kuma inna ”
“Ehh aurenki da Aman din ko kin fasa ?” Cike da mamaki take kallon innar don Bata taba tunanin zata amince da wuri haka ba, shiru tayi sai Kuma tace ” da dai a bari mugama exams daga can sai mu wuce maid koh ” toh shikenan bari naga yadda abin zai kasance ” haka suka cigaba da kallon tare.
__________
*After 2 months*
Hajjo ta kammala exams lafiya sai 400 level kawai next semester sun gama 300 kenan sungama duk wani Shirin da zasuyi na zuwa yola da Maiduguri, maman Nana ta tafi garinsu itama ta Dade Bata je ba. Yaya Yusuf ya samo musu driver da masauki a cikin jimeta idan suka sauka Adamawa da flight zasu tafi sannan driver ya karasa dasu kojoli idan suka gama zasu samesa a Maiduguri, ranar da zasu tafi jirgin 11 na safe sukabi by 12 da few minutes suna yola international airport driver yazo ya daukesu Kai tsaye suka dau hanyar zuwa kojoli Wanda zasu ratsa cikin mayo da Jada local government kafin su iso kauyen. Karfe 3: 30 ya samesu cikin garin kojoli Wanda dakyar suka Gane gidan sai da suka hada da tambaya saboda sauyin da aka samu na gine gine , hajjo na kallon kauyen tana murmusawa tana tuna rayuwarta na baya da irin wahalar da suka Sha cikin wannan gari me albarka.
Sallama sukayi Diddi na zaune tana rike da carbi bisa dardumar sallah ta amsa musu sallamar tana kallonsu don gaba d’aya Bata ganesu ba , wata y’ar budurwa ta fito ta shimfida musu tabarma inna tana kallonta tace ” Habi angirma ” da sauri ta d’aga Kai ” wacece bangane ki ba baiwar Allah” “Aminatu ce matar Sule na da ” salati Diddi tayi nan kishiyarta ta fito sai Kuma ga sauran matan gidan sun fara taruwa ana ta salati Diddi ta kasa hakuri tace
” Dama kinkoma gun Yan uwanki suka boyeki shine akayi ta wahalar da sule Yana can Yana nemanku ” hajjo tayi saurin cewa
“Baba ya dawo wai, yaushe don Allah yanzu Yana Ina ” Yana can habuja kullum sai ya fita nemanku tun bayan tafiyar taku da watanni kadan ya dawo Yana nemanku ya samu labarin cewa Kun tafi habuja tare da kande daga haka yabi bayanku Allah baisa Kun Hadu ba, ya aika can Maiduguri sun nuna Basu da labarin ku ” haka dai sukayi ta hirar yaushe gamo inda suka nemi gafara kan abubuwan da suka aikata inna tace ta yafe musu hajjo ta karbi number wayar babanta ta kira switch off tayi saving kan zata cigaba da nemansa zataje har inda yake a Abujan. Abinci aka kawo musu da fura da nono suna ta mamakin Jin cewa inna tayi aure har ta haihu, suna ta hira sai wajen karfe 6 inna tace zasu tafi duk yadda sukayi akan su kwana taki tace driver na jiransu sai Wani lokacin zasu dawo, aka sauke musu buhun shinkafa da dankalin turawa da galon din Mai sai kudade da ta raba musu suna godiya tare da Jin kunyan abubuwan da suka aikata mata a can baya. Rayuwa kenan abunda yake baka tsoro wataran shi zai baka tausayi gashi yau inna takai matsayin da basuyi tunanin zata taka ba a rayuwa duk da cewa tun farko sunsan cewa Bata dace da Dan nasu ba dama ance matar mutum kabarinsa rabon hajjo yasa akayi auren gashi da rabon ya fito sun Rabu cikin mutunci.
Karfe Tara da rabi driver yayi parking cikin harabar gidan Yaya Yusuf Dake unguwar Bekaji cikin jimeta , Babu kowa sai maigadi cikin gidan dama sunyi takeaway a hanya nan kowa yayi wanka suka ci abinci kowa ya wuce dakinsa dama maigadi ya share ya gyara musu inda zasu sauka, 3 bedroom flat ne da falo 2 hajjo ta haye gado suna waya da masoyin nata tana bashi labarin dawowar mahaifinta ya tayata murna bayan sungama ta kira Ummeey suka Sha hira tana cewa tun yanzu ta fara kewarta har zuwa 11 ta ajiye wayar ta kwanta bacci saboda sammako zasuyi zuwa Maiduguri.
____________
*Borno state Nigeria*
Yaya Yusuf ya tara Yan uwan inna a falon yakumbo suna ta hira cike da Jin dadi da annashuwa hajiya Balqis tace ” Yaya don Allah ka fada mana menene wannan surprise din, tun daga Abuja fa ka tasoni ka kawoni garin nan Amma ka kasa fada mana menene shi” dariya yayi ” haba Gimbiya saurin me kike saura kiris ai ” ya Duba wrist watch nasa lokacin karfe 1 saura , Yana magana wayarsa tayi ringing ya dauka ya fice . Yakumbo tace ” kema da rashin aikin Yi yanzu don wannan maganar har yakai a ce kin tashi kinzo , Kai Amma yaran yanzu Baku daukan aure da muhimmanci a zamaninmu mace Bata yawan tafiye tafiye haka kurum Kuma idan zakiyi tafiya sai tare da mijinki, idan aka ganki ke kadai zaa kamaki a maidake d’akin ki zaa ce gudowa kikayi ” gaba d’aya falon aka kwashe da dariya ta cigaba da Basu tarihin aurensu na zamanin baya suna ta dariya Yaya Yusuf yayi sallama dauke da Sadeeq a kafada inna tana bayansa tare da hajjo, kan inna na kallon kasa hawayene cike da idanunta yau itace take taka mahaifarta nan Wani kuka ya kubce mata hajjo tayi sallama ta shigo, zumbur anty Balqis ta tashi tsaye yakumbo tace” me nake gani haka Yusuf Ina ka samo d’a me kama da Kai ” murmushi yayi yace” ga abunda na kawo muku yakumbo Bude ido ki gani Aminatu ce Aminar ki ” salati tsohuwar take anty Balqis kuwa tuni ta kankame y’ar tilon kanwar tata suka fashe da kuka, hajjo dai ta zama y’ar kallo inna ta karasa ta fada jikin yakumbo suka rungumi juna ya Yusuf yace ” wannan d’ana ne da Aminatu ta haifamin , Alhamdulillah ko yau na mutu burina ya gama cika a duniya, yakumbo ga Aminatu nan Kuma matata halak malak ” gaba d’aya kallonsa suke cike da mamaki ya Kalli Hajjo yace ” zauna abinki dota ” nan suka Maida hankali wajen hajjo ga kamanninta da inna sak sai Kuma hasken mahaifinta anty Balqis ta jawota kusa da ita tana mata sannu da zuwa, kafin kace me labari ya karade gidan sarautar cewa ga Aminatu ta dawo nan kuwa falon yakumbo ya cika makil da dangi ana zuwa ganin inna , ita kuwa sai aikin kuka take yau wannan duk danginta ne haka zagaye da ita hajjo tana mamakin irin gatan da inna take dashi nan kuwa Mai martaba ya nemi ganinta Yaya Yusuf yace ” taso muje nida kaina zan masa bayani ”
Anty Balqis ta rike hannun hajjo tace” zo muje ki gaisa da kakanki y’ata ” yakumbo tace” ko ruwa a bari susha man bakusan inda suka fito ba, Kai mutanen yanzu Babu lissafi Amma mutum ya iso ko ruwa Bai samu ba a damesa da hayaniya, daga ganin wannan farar y’ar tata akwai gajiya da alamun yunwa a tare da ita da dai a bari su huta suci Wani abu kan aje gaisuwar amma ni a waye da zan Yanke wannan danyen hukuncin, toh kuje yanzu dai nasan dole uban ya yafe mata tunda ba kashe Dan Wani tayi ” tana ta zuba surutu suka fice aka barta da zance ita kadai.