Garin Dadi Hausa NovelHausa Novels

Garin Dadi 41

Sponsored Links

G*D

{41}

*Ina kuke manyan mata ƴan ƙwalisa ma’abota son gyara da kece raini, maza ku garzayo ku nemi maman Maryam domin samun lafiyayyu kuma haɗaɗɗun Lagos lace wanda zaku iya samun ɗinkakku da kuma sabbi a ledarsu, kaya iya zaɓinki, gefe ɗaya muna da GHT product, zaku samu,*

~MAI DA TSOHUWA YARINYA

~FEMALE CARE

~REODEO

~VIGOR MAX

~ LONGZIT

~B CLEAR

*DUK ZAKU SAMU WADANNAN KAYA CIKIN SAUKI DA RAHUSA MAZA KU NEMI MAMAN MARYAM AKAN WANNAN NO 07080222187, SIYAN NA GARI MAIDA KUƊI GIDA…..*

~~~Har talatainin dare idona biyu banyi bacci ba ina taya shi hira kamar yadda ya saba raba dare ba tare da yayi bacci ba,

“Baby…..”

“uhmmm….” na amsa cikin shagwaba,

“yi bacci…. Dare yayi”

“kaima kayi bacci”

“no, ni zan kula dake a lokacin da kike bacci”

“ni ban yarda ba…..”

“please mana baby….”

Tashi zaune nayi ina yin hamma dan tunda ya ambaci baccin naji yayi min dirar mikiya,

“what?” ya tambaye ni cikin kulawa,

“fitsari zanyi sannan zan sha ruwa….”

“Duk ke daya?” ya bukata cikin tsokana, kai na daga masa ina lumshe idanuwa alamar bacci,

“ok lets go…”

Daukata yayi har cikin bathroom nayi abinda zanyi na gama daga karshe na daura alwala shima yayi sannan muka fito, falo yaje ya dauko min ruwa yayinda nikuma nake kokarin kwanciya,

“ni mai sanyi nake so….”

“baby bakya jin magana ko? So kike mura ya kamaki keda babynmu?”

“babu abinda zai faru, ni bana son marar sanyi dan baya kashe min kishin ruwa”

“to babu mai sanyi sai dai in saka miki yayi sanyi”

“toh”

Juyawa yayi ya sake fita nikuma na kwanta tare da yin addu’a, ko minti biyu banyi ba bacci ya kwasheni dama yanzu haka nake bani da wahalar bacci kuma kowanne lokaci zuwa min yake yi bawai sai iya dare ba, cikin baccina wanda ya fara nisa naji shi yana tashina a hankali bawan Allah wanda ni harma na manta da batun ruwan duk da dagaske ruwan sanyin nake so,

“baby tashi ki sha ruwan gashi…..”

Kasa tashi nayi har sai da ya sake maimaitawa sannan na tashi dakyar ya bani nasha sannan na sake komawa na kwanta shi dai ban san lokacin da yayi bacci ba.

***

“mom….. Wallahi ba laifi na bane, nayi duk iyakacin kokarina wurin ganin naja ra’ayin samz ya kulani amma duk abin yaki yuyuwa…. Kwata kwata yaki saurarata, kamar ba namiji ba haka yake sam babu wata da yake gani a gabansa sai wannan matar tashi banda ita bai damu da kowacce mace ba ”

Fushin dake kan fuskarta ne ya sake karuwa cikin harzuka tace,

” Felicia kin bani kunya, i don’t want to hear stories, abinda kika iya kenan koda yaushe, namiji guda daya kin kasa karkato da hankalinsa zuwa gareki har ki mallakeshi…. Kefa da bakin ki kika faɗa min matarshi ƙaramar yarinya ce you are older than her, kin fita wayo da duk wata dabara ta rayuwa to amma ya kika tsaya kina wasa da damarki har kina ikirarin hakura? Kin manta burinmu ne da kudurinmu a kansu? Ke kadai ce hope dina acikin wannan tafiyar idan kika yi giving up ki tabbata da duk wani burinmu da tanadinmu ya rushe…… ” madam comfort ta fada cikin fushi wanda ya jima da bayyana akan fuskarta,

” mom ba wai nayi giving up bane, kawai dai na gaji ne, na gaji da wannan wahalar akan samz, wulakanta ni yake ako ina kuma a koda yaushe….. ”

” haka zaki cigaba da hakuri ki daure har zuwa lokacin da hakarmu zata cimma ruwa, ki sani duk abu mai daraja samunsa baya zuwa cikin sauki kuma dole sai an sha wuya, kar ki sare kuma karki karaya, ki sani burin ki zai cika zaki samu samz kuma zaki mallakeshi mutukar baki giving up ba haka kuma burinmu zai cika…….. ”

” hakane mommy, tabbas kin sake bani kwarin gwiwa, ada na zama discouraged saboda irin yanda naga kamar babu hanyar cikar burinmu amma yanzu wadannan words ɗin naki sunyi encouraging dina kuma sun sake yimin ƙaimi na jin burina zai iya cika cikin kowanne lokaci…. ”

” Haka nake son ji, keep your hope alive, kije kici gaba da kokari, ni mahaifiyarki ina baki tabbacin nasara tana tare dake ”

” Thank you mom ”

” you are welcome my dear”

Cikin bedroom ɗinta ta shiga ta zauna bakin gado ta soma kiran no samz sai dai amma tana ta ringing ba a dauka amma duk da haka bata hakura ba sake kira tayi bayan ta katse nan dinma ba a dauka ba atakaice dai sai da tayi masa miss calls guda biyar sannan ta hakura.
***
Cikin kwanakin biyu Felicia ta matsa masa da kira wadda ni kaina sai da na fahimci hakan dan bata tashi kiran sai da daddare ko da safe before ya fita office amma ban taba magana ba dan banma san waye mai kiran ba kawai dai naga baya dauka ko kuma sai dai inga yayi tsaki ya katse kiran nidai idone nawa sannan duk da damar da ya bani na wai zan iya daukar wayarshi a duk sa’ilin da naso ko nake doubting akan wani abu nake son in duba to ƙofa a bude take, duk da hakan ban taɓa garaje ko rawar kan ɗaukar masa waya ba sannan ko kiransa akayi ina kusa da wayar bana gigin dauka koda kuwa baya kusa,

Yanzun ma zaune muke a falo bayan na gama shan uban fruits din da na sakashi a gaba muka je muka siyo dan shi nake ta sha’awa tunda na tashi amma ban fada masa ba har ya fita office kuma lokacin da yake office dinma munyi waya har ya bukaci jin abinda nake bukata inyaso sai ya taho min dashi amma nace babu komai dan nima ina son fitar so nake mu fita tare shiyasa sai da na bari ya dawo bayan yayi wanka yaci abincin da yau dai na samu na girka masa wato white yam sai sos din alayyahu da albasa,

Lokacin da yaga abincin fada ya fara yimin cikin kwantar da murya ba wai cikin zafi ko tsawa ba a’a cikin sanyi da rarrashi,

“Haba baby….. Wa ya saki wannan aikin? Bakya son kamshin abinci amma shine zaki je ki wahalar min da kanki?”

“boo zan iya ne fa, kuma laifine dan na yiwa mijina girki?” na fada cikin shagwaba ina turo baki,

“ba laifi bane baby but…… Kinga situation dinki,in fact bana son duk wani abu wanda zai baki wahala…..”

“to ai wannan bai bani wahala ba sweet, na gaji da kallon ka kana cin abincin restaurant, duk restaurant din Abuja bana jin akwai wanda baka je Kaci abinci ba, sannan ai kayi kokari dan tunda nazo garin nan ban taba dafa maka abinci ba sai yau……”

“come here….. Did you vomited?”

Jikinsa na shige kamar yadda ya bukata sannan na girgiza kaina alamar a’a,

“thank you baby amma dan Allah daga wannan kar ki sake bana bukata, zan cigaba da zuwa restaurant ni ban dauki hakan a matsayin gazawarki ko careless ba…..”

“Nidai gaskiya ban yarda ba….” na ce dashi cikin shagwaba, kumatuna yaja ya fara cin abincin yana bani labarin wai abokinshi ahmad ya samo matar aure a Kano harma anje masa tambaya, fatan alkhairi nayi kafin nace,

“ka gama ka rakani in siyo fruits….”

Kallona yayi sannan ya bani amsa da “to me yasa baki kirani na taho miki dashi ba?”

“ina son in fita ne nima”

“kina son yawo dai, anyways nima ina son ki sha fruits din it’s good for your health” turo masa baki nayi dan na gane abinda yake nufi dama tun ba yanzu ba yana son insha fruits saboda yana samun abinda yake bukata sosai to sai gashi kuma yau na nema da kaina, nima na san yau sai abinda hali yayi kawai dan zan ci ƙaniyata a hannunsa.

Taren muka fita bayan ya kammala cin abincin muna tafe muna hirarmu kamar wani saurayi da budurwa wanda suka yi nutso cikin tsinkar furen soyayya, komai da komai ya hado min ya siyo tun daga kan lemo, ayaba, kankana, gwanda, abarba sai kuma tufa, haka ya lodo su ya zo ya yanyanka min da yake ina so sosai na sha sauran ya saka cin fridge, salla nayi bayan na huta sannan na tashi dan inje inyi shirin bacci, wayarshi ya bani akan in saka masa a charge domin shi wani aiki yake yi akan system dinshi,

Ina shiga bedroom ina saka chargen na ga kira ya shigo haka na juya naje na kai masa amma bai dauka ba ya katse wayar ya bani haka aka yi ta kira tun ina wanka ina ji shima kuma ina da yaƙinin ya jiyo, shiryawa nayi nabi lafiyar gado saboda yanzu abu kadan sai inji na gaji aiki ba aiki ba sai in ji gajiya ta taru min to haka kawai ma banyi aikin komai ba jina nake kasala tana damuna bare kuma ace nayi aiki komai ƙanƙantarsa. Na dan fara bacci sama sama naji shigowarsa kuma hakan yayi daidai da shigowar wani kiran cikin wayarsa, bude ido na nayi kafin na gyara kwanciyata,

“am soo sorry baby, phone dina ta tadaki ko”

‘No ” nace ina gyara kwanciya ta, wanka ya shiga kafin ya fito na sake komawa baccina, cikin baccin najishi cikin jikina yana shafa kaina, ni dai dadin bacci bai barni naji maganar da yake yi ba sakamakon kiransa da aka sake yi awaya……..

*Garin dadi littafin kudi ne ga mai bukatar cigaban labarin sai ya tura 500 ta 0774712835 Aisha Ibrahim Access Bank sai a tura evidence of payment ta wannan no 07044644433 ko a tura katin waya da shaidar biya wannan no 07044644433*

*_Ummi Shatu_*

Back to top button