Hausa NovelsNasarar Rayuwata Hausa Novel

Nasarar Rayuwata 34

Sponsored Links

*Talented writers forum*

*34*

Inna ce zaune a falonta dake cikin Apo Amina court, yau satinta guda a cikin gidan ya tsaru iya tsaruwa tayi jugum tana tuna rayuwarta na baya da irin wahalar da tasha a hannun dangin baban Hajjo, idan Allah yasa hajjo ta rubuta WAEC zata dauketa suje Adamawa ta nuna mata dangin mahaifinta duk da cewa Basu kaunarta, gidan ya mata girma zaman kadaici ya dameta ya zama dole ta dauki maman Nana ta dawo kusa da ita tunda akwai dakuna enough. Door bell taji don haka ta tashi taje budewa dama a falon kasan take tana jiran dawowarsa , Bude kofar tayi ya shigo da sallama fuskarsa dauke da murmushi ” amarya Baki laifi” murmushi tayi ” barka da zuwa Yaya nah Kuma mijina ” Kuma duk duniya Babu Wanda yakaini sonki kanwata ” ya jawota ya rungumeta suna dariya ” ya zaman gida ya kadaici, sorry nabarki ke d’aya aikine ya min yawa a office ” gaskiya akwai kadaici Kam shiyasa nake son maman Nana su dawo kusa Dani” ya ware Ido yace ” tun yanzu, bamu fara cin amarcin ba zaki dauko mana wasu ” haba dai Yaya wane irin amarci Kuma ya rage ” yayi mata rada a kunne suka tuntsire da dariya ya d’agata cak! Yayi sama da ita Yana taka staircase a hankali tana kwance a jikinsa.

Related Articles

________

Aman ana zuba soyayya kamar bazasu rabu ba zee harda kukanta lokacin da zasu shiga camp dakyar ya raba jikinsa da nata Ayman ya juya gefe Yana ganin rashin kunyar zee a bainar jama’a take wannan abin kunyar, Failuzaa kuwa ta tsaya ta kura musu ido suna matukar birgeta Amma Sam Ayman baya Bata irin wannan kulawar. Haka Aman da Ayman suka shiga camp zee taja mota suka koma gidanta dama a can Failuzaa zata zauna for 2 weeks din kafin Ayman ya dawo su koma Lagos tare.
Hajjo kuwa anyi hutun first term Bata koma gida ba dama akwai students dayawa da zasu zauna suyi summer camp itama ta zauna saboda ita Ummeey taki komawa gida tare suka zauna har 3 weeks din ya kare akayi resuming second term.

Bayan sun fito daga camp ne akayi posting Ayman Lagos kamar yadda ya nema nan ya shirya ya dauki matarsa suka wuce, Aman Kuma a EFCC office ya samu ya fara zuwa service Yana makale da matarsa suna zuba soyayya, bayan wata biyar sai ga zee da cikin wata uku Aman ya rage fita ana rainon ciki . A wannan lokacin ne Ayman ya Bude sabon kamfanin sarrafa man gyada ana fitar dasu zuwa kasacen Africa, irinsu Ghana Mali Sudan Burkina Faso Gabon da sauransu. Kafin kace me kamfanin A&A vegetable oil ya samu karbuwa harkar ta fara bunkasawa cikin iKon Allah kudi suka fara shigowa ta inda Baiyi zato ba, bayan wata bakwai suka kammala service dinsu a lokacin ne zee ta haihu ta samu da namiji Aman kuwa ya samu aiki da EFCC head office dinsu dake jabi. Ayman kuwa yana gama service yayi applying masters a king fuad university jedda nan ya tattara ya tafi bayan ya samu masu kula masa da kamfaninsa dake Lagos inda yake son Bude reshe a birnin Jeddah.

**********
Ayman Bai bar kasar ba sai da ya tabbata ya gama biyawa Hajjo kudin jam’iyar Baze sannan ya damka komai a hannun Mrs Juliet akan cewa ta sanar dasu scholarship ta samu daga makaranta, Mrs Juliet ta cika da mamaki Amma batai magana ba ta amince da yadda ya tsara akan sai bayan sun rubuta WAEC zata sanar dasu har inna ,
Hajjo ta cika 17 years suna Shirin rubuta WAEC a SS2 alamun girma ya dada bayyana ga kyaun da ta Kara da Kuma wayewa da ya Kara shigarta ta zama wata big girl wacce duk fadin school nasu ana ji da ita sosai saboda iliminta ga Kuma farin jinin da Allah ya Bata, shakuwa tsakaninta da sultan Kuma sai abinda ya karu duk da cewa Bai furta mata Kalmar so ba amma Yana Bata kulawa shi a tunaninsa ba yanzu ne ya dace ya bayyana mata sirrin zuciyarsa ba. Saura sati biyu su fara WAEC donhaka sun dukufa suna karatu sosai saboda Ummeey ma tare zasu rubuta, suna zaune karkashin wata bishiya suna karatu Ummeey tace ” yanzu besty me next plan naki after candy, nidai da Ina da tsayayye da aure zanyi wallahi Kinga anty zee namu yadda take samun kulawa gun Ya Aman sai abin ya burgeki ” hajjo tace ” Aman dama hakane sunan mijin nata ” “ehh Baki taba sani ba yanzu gashi Fahad nasu har ya girma yayi wayo ” Allah sarki har na tuna first love dina Aman yakan kirani da besty ” “iyye shine Baki taba bani labarinsa ba ” murmushi hajjo tayi tace ” ko’ina yake yanzu sai Allah ” “toh ke ba gashi kinsamu Wani besty bah, ya sultan Kuma kinsan Yayan mijin anty zee ne fah ” au haba dai..ba taba sani bah ” Ina zaki sani tunda nace muje gidansu kikayi turning down ” uhm kinsan ban cika son shige shige bah ” ehh nice uwar shishigi tunda har dad naki yasan ni ” uncle Yusuf dai bakisan dad dina bah ” ohh besty wai har ynxu bakiyi accepting din mutumin nan ba a matsayin mijin inna, Kuma dai naga uncle naki ne na jini ” uhmm..” shiru sukayi can hajjo tace ” ya sultan zai dawo next week I think”
“Toh ke me naki tunda kince ba soyayya kuke ba ” “yanzu besty Baki yarda bane I told you we are just friends” ” I see…just friends da haka anty zee ta fara gashi yau suna da d’ansu” murmushi hajjo take suka cigaba da karatun har zuwa Wani lokaci. A kwana a tashi ba wuya gun Allah har ranar da zasu fara jaraba ya gabato suka fara rubutawa cikin kwanciyar hankali har suka kammala lafiya , dama sun rubuta jamb kowacce ta fito da sakamako Mai kyau . Gobe ne zasuyi sendforth party daga nan zasu wuce gida sun gama secondary da yardar ubangiji, da dare tana rike da wayar Ummeey tana jiran call din sultan ta kurawa wayar Ido Wani call ya shigo Mahfouz ne ke kira kamar bazata d’aga ba tayi picking ” hello Ina yini Yaya” hey beauty dama ke nake nema ya kike congratulations ” thank you Yaya ” ” how was the exams ” fine alhmdllh ” good wat next beauty nah aure ko School” murmushi Mai sauti tayi kafin tace ” school first” haba beauty ni Kuma Yaya kike so nayi ” meaning..? Meaning I wanna marry you n I mean it ” shiru tayi tana sauraronsa nan taji alamar Wani call ya shigo ta duba sultan ne ” hello beauty are you there ” yeah I can hear you ” shine kikayi shiru Ina ta magana” sorry Yaya ” ” sorry as in how am darm serious wallahi Ina kaunar ki dama Ina Baki space ne saboda da karatu but Alhamdulillah you graduated so if you don’t mind I want to introduce myself to your family ” but Yaya am still young Kuma.. “beauty nah.. please karki min haka i so much love you wallahi ” shiru tayi ta rasa me zata ce masa ” kinyi shiru again ” ya fada a shagwabe, lumshe Ido tayi tana Jin Wani irin yanayi ” beauty kina son ganina a school naku at this hour koh ” ta ware Ido tace ” no .. please don’t come ka bari zamuyi magana gobe ” ok korata kike koh , dama naji call ya shigo dazu maybe is someone you value d most Daz y u want me to end to call so that…” Yaya please bahaka bane ” numfashi yake saukewa a jere har tana Jin karar numfashin ” ya Mahfouz! ta kira sunan cikin Wani irin salo , ” am sorry Yaya nah kaji ” sauke numfashi yayi kafin ya kashe wayar, ta kira back yaki picking ta buga tagumi Wani call ya sake shigowa sultan ne . Wani murmushi ya subuce mata ” hello dost ” hi bae ya kike my big girl an girma an gama secondary sai university koh ” yeah..my dream , ya gida ya beb naka ” she is good, Baki tambayi yara ba sai beb ” ohh bakaji dad’i ba na tambayi rabin ranka ” are you jealous of her ” shii… jealous why, no please am not” dariya me sauti yayi kafin yace ” ki shirya gobe ni zan kaiki gida but kafin nan zamuje outing” hmm..babu ruwana wallahi haka kawaii zaka jawo min magana gun matarka ” why are you always mentioning her ” no please ka bar wannan zancen Babu shi ” ok toh shikenan yau nasan matsayi na ” ya kashe wayar ta Kalli wayar tace ” ah ahn wai yau lafiya kowa sai na Bata masa rai, iKon Allah toh kwaji dashi wallahi Babu inda zani mtsww..aikin banza ” ta tashi ta koma cikin d’aki inda mates nasu suke hira Ummeey ta tarasu tana Basu labari ta nemi waje ta kwanta.

Back to top button