Hausa NovelsMatar So Hausa Novel

Matar So 22

Sponsored Links

Page….22
Tashi yayi jikinshi yayi sanyi sosai ganin rashin dacewa dukar da yayi min yake, ɗakin Hajiyarshi ya nufa huda na ganinshi ta mike ta shige inda nake.
Shigowar Sulaiman da magunguna yasa shi ɗago kanshi mika mishi hannu yayi suka gaisa, sannan shima ya zauna fitowa Huda tayi cikin murmushi tace.
“Uncle Man ka kawo magungunar Aunty mom ɗine.”
“Eh gashi akwai, Neurogesic shi ana shafa shine a bugu kowani gurin dake ciwo sai wannan magungunar su na ciwon jikine, Wai ita Maryam ɗin mi yasameta ne haka.? Dan hajiya taki min bayani sai dai tace min na kawowa Maryam maganin ciwon jiki dana sha da na shafawa.”

Tura baki tayi tare da kauda kanta ga barin inda Uban yake tace.
“Daddyne ya mata dukar mutuwa gata can a ɗaki sai Amai take, cikinta da kirjinta kamar zasu fashe da ciwo, Nima Allah yasa wani yayi min irin dukar da kai mata kaji yanda abin yake.”

Tana gama faɗar haka ta juya ta shige ɗakin.

Ina cikin bargo sai rawan sanyi nake, ɓalla min maganin tayi ta bani sannan ta guda na shafawar ta mika min ta fita a hankali na kwaɓe rigar na shiga shafawa da farko akwai sanyi sai da ga baya zafin ya fara ratsani, kuka nake wiwi,  tare da cire rigar sabida zafin inda na shafa man.
Shigowa yayi ɗakin, ya tsaya a bakin kofa maganar da Sulaiman ya gaya mishine yayi matukar kashe masa jiki. Tsurawa kirjina ido yayi yaga yanda suka koma ga sabida sunsha dukarshi.

Takawa yayi har bakin gadon ya zauna, ɗago kai nayi muka haɗa idanun, jan bargon nayi na rufe jikina. Ina ja da baya.
Janye bargon yayi, tare da tsare ni da ido yayi, sannan ya kai bakinshi ya fara hura min iska, wanda yake ratsa raɗaɗin da nake ji, ajiyar zuciya na shiga saukewa dan nafara jin dama dama.
“Yunus zaka fitan min a ɗakina, kafin na saɓa maka kaje Yarinyar da ka zalinta tabarka da Allah, kuma ka sake musu yar mutane kafin kabar garin nan ko kuma na makaka kotun musulunci a maka shegen dukarda kayi mata. Get out,”
Inji Hajiyarshi.
Zugwai zugwai ya fice bai iya ce mata komi ba yana fita ta koma kaina cike da masifa tace.
“Sannu lusara ya gama jibgarki yazo zai lallaɓaki, har da barinshi ko Maryam ke wacce irin mutun ce da bazaki rama abinda aka miki.”

….. A hankali kuka na yake fitowa, kaina a kasa nace.
“Toh bansan yanda zan rama bane, kuma tsoronshi nake ji.”

Tsaki tayi cike da  masifa tace.
“Kwatar kankine sai nakoya miki, ko tsiwar ma baki iya ba, Amma Malama ta cutar dake ainun, wallahi wannan wani irin tarbiya ce haka da yaro bazai kwaci yancin shi ba. Toh zauna zan koyq miki yanda zaki rama.”

Tana gama faɗar haka tafita tabar ɗakin, ni kuwa na cigaba da kukana.
Ban kuma ganinta ba har barci yayi gaba dani, cikin barci naji kaman ana lasar nonuwana a hankali, ina buɗe ido sai akan Mai Nasara kurr nayi mishi a hankali naja da baya tare da juya mishi baya.

Haurowa yayi samar gadon ya shiga janye bargon bance mishi komi ba na barshi ya janye, nace.
“Kazo ganin illar da kai min ne? Ko kazo latsa kazama ce, banziyar wofi, Hhhhh Yunus kenan kana taɓani yanda kake so kuma bai hanaka faɗa min magana ba, dukda haka bai maka ba kasa belt ka zane ni dubi yanda ka maida min da nonuwana wai in tambayeka kasan darajar Aure kuwa? Kasan darajar Mace kuwa? Duk wanda yasan wannan darajojin bazai taɓa wulakanta mace ba, daga Yau kasake taɓa jikina Allah ya isa min, kaje kasan darajar mace kuma dan rashin kirki Har Mahaifiyarka tace karka kara zuwa inda nake ka ɗibe kafafunka kazo dalla fitar min a ɗaki, taɓa ni da akayi na kwanaki akaci bulus ban yafe ba, kuma Aurenka ko ta masifa ce banayi koda shine abinda zanyi na karshe  a rayuwata dalla fitar min a ɗaki wanda baida yakana kawai.”

“Sajidaaaaaaaaaaaa” ya daka min tsawa wallahi sai da cikina ya kaɗa, amma na wani ɓata rai tace.
“Saura zare belt a zaneni, tunda na faɗa maka magana hotiho kawai lusar..”
A fusace ya ɗaga hannunshi sama kuma ya gaza saukewa, murmushi nayi nace.
“Try it mana! Wallahi ka gama dukana kenan, kuma ka kuskura kace zaka taɓa ni! Ka taɓs aurenka dan dama sai ka sake dan ni ba baiwarka bace, tunda na taso Umma bata taɓa dukana ba, balle Malam wanda muka gado hakuri a gurinshi, kafita bana son ganinka in kuwa kaki zan maka ihu k’orto.”

Haushi ne ya cika shi ya fisgo ni tare da haɗa bakinshi da nawa aikuwa na kama lips ɗinshi na ciza, ya maza ya ɗaga yana huci nace.
“Da kenan kaci banza kana taɓa ni zan nuna maka ni jinjirace mara mutunci get out Yunus dama ban taɓa jin sonka ba balle kuma sha’awarka an cuce ni an haɗa ni da tsohon hannu comman love bai iya ba sai dukar mace ai wannan jahilcin tun 1999 Ka daina kai da ka dawo dashi kaje gurin tumakan matanka subaka abinda kakw bi a jikin kazama.”

Tsaki naja mishi na shige ban ɗaki dagani sai Pant dama rigar na zameta, oho dai na canza always ɗin na fito da gayya, nake tafiya ina girgiza nonuwar da ya taɓa lafiyarsu, jarababbe idanunshi na kai na haye gadona na kwanta, nace.
“Kwlelen kare da hantar kura.”
Na gyara kwanciyata addu’a nayi na shafa.

Yau naga masifa sam kamar mara zuciya ina kwanciya shima ya cire rigarshi ya kwanta a bayana har da ɗaura hannunshi akan nonuwar,
“Kan Uban can, Ni zaka renawa hankali ka jibge ni akan nonona kazo ka nanuke min, kayi na kuɗinka ” na mike zubur.
Na ware murya nace.
“Wayyo Allah na, xai kashe ni Hajiya kizo, wayyo Umma na shiga uku na lalace,  karka sake dukana wayyo, Wayyo ku taimake ni Mama kizo na shiga uku na banu Huda.”
.  Gabaki ɗaya na birkita gadon da shikanshi na tukunkuye shi, ta yanda kowa yazo zai zarge shi.
Aikuwa dake dare yayi sai ga Mama da Huda, a guje sun danno ɗakin, ina ganinsu na fauce a jikinshi har ina hatsilawa, gashi babu kaya jikina zanin gadon Huda taja ta rufa min, sunawa Mai nasara wani irin kallo.

Gashi na cika musu kunne da kuka, Hajiyace ta shigo ɗakin cikin rawan jiki taxo ta rungume ni, nace.
“Hajiya dan girman Allah ki maidani gurin Ummana bata taɓa dukana ba, Amma daddy ya same ni kamar jaka, indai haka ake auren na yafe ban taɓa ganin Malam ya daki su Umma ba, amma yana shigowa ya rike min kunnena na shiga uku nafasa auren sai na fadawa Ummana.”

Shiru sukayi har shi gyara muryan Alhajinsu yasa su juya da baya, yace.
“Lafiya?”
“Hmm Alhaji na zata zan iya kashe wutar kiyayyar da Yunƴsa ya kunnawa zuciyar Maryama, ashe ba haka bane, ynz ma ya shigo zai kashe musu yar mutane Alhaji mugun dukar da Yunusa yayiwa Maryama, Ko Yarsa gata nan bai taɓa mata ba ya farfasa mata jiki ya ilata musu Y’a don Girman.Allah kasashi ya sake musu y’a tun a cikin mutunci kafin ya janyo mana abinda zamu gaza kare kanmu a idon duniya.”

Yana zaune a bakin gado ya haɗa kanshi da hannayenshi, ya rasa abinyi.
“Ku fito.”
Inji Alhj.
Koda suka fita kayana aka barni nasaka, sai a lokacin ya mike yasa rigarshi gabana yazo ya rungumeni a hankali yace.
“Nagode maryam Sajida, Amma bazan sake ki ba ko da zan rasa komi nawa ne, zan fanshe shi dake koda kuwa da numfashina aka saka akan ki zan bada, amma ki sauya tunani rabuwarmu ba sauki.”

Shafa min cikina yayi zuwa cibiyana yana min tafiyar tsutsa, rike hannunshi nayi gam, ina sauke numfashi dakyar nace.
“Na,shirya rabuwa dakai ta kowani fuska.”

“Karki yi abinda zai ɓata miki suna da rayuwa kina kasa da sha takwas, kuma kina harin zawarci, bayan baki san daɗin auren ba.”
“Kai sanin daɗin aure ya dama, ina dai dai da nashirya rayuwata kamar kowa, kuma kaga duk namijan da zan aura sai aureni a ɓagas ne yana min kallon rogo ina masa kallon kitse, tunda namiji bai take ni ba don Allah free me Mr Mai nasara.”

Ina gama faɗar haka na fita ina murza idanuna da fake kwallar munafinci, da sauri na raɓe jikin Huda dama jikina da zafi take ta zabura tace.
“Aunty Mom kin sha magani kuwa.” cikin fida wani munafikin kwalla nace,” kunne ne yake min guɗa.”
“Innalillahi….Alhaji ka gani ko na shiga uku ni Hauwa’u kashe musu y’a zaiyi fa.” Inji Hajiya.
Kallon rashin Yarda Mama tayi min, irin anya Maryam, sunkuyar da kaina nayi jikina na rawa dan ba ɗabi’armu bane karya kuma ba’a ɗauramu akai ba.

Fitowa yayi a sanyayye, ya nemi guri ya zauna kanshi a sunkuye.
Kallona Alhaji yayi cikin lallashi yace.
“Maryama!!! Mi ya haɗaki da mijinki,”

Kallon Huda Mama tayi tace.
“Takwara bamu guri.”
Mikewa tayi jikinta a sanyayye ganin yanda ubanta ya koma lokaci ɗaya,

Gabaki ɗaya jikina ɗaukar rawa nayi ina kallon fitar huda, sunkuyar da kaina nayi, cikin kuka nace.
“Baba nice na fasa mashi laptop ɗinshi wanda yake abubuwan kasuwancinshi garin yin game, kuma ya hanani ɗauka da yazo ya tambaya nayi mishi rashin kunya Amma wallahi baxan kuma ba karku faɗawa Ummana, zatayi fushi dani.”

Na karshe maganar cikin kuka da yarfe hannuna, ina kuka wiwi.

Zaro ido yayi yana kallona, cike da mamaki, murmushi Mama kilishi tayi sannan tace.
“Alhaji ta tashi kawai taje, gurin Huda sukwana sai mu karasa maganar dashi.”

“Tashi kije.”
Ina mikewa tsabar tsoro kamar zan hantsila yayi maza ya mike zai tare ni, na faɗa jikin Mama by mistake na fama nonon kara nasaka tare da dafe gwiwarta na kifa kaina, ina sauke ajiyar zuciya kuka nake sonyi amma ganin yanda duk suka ɗaga hankalinsu ya sani mikewa ina murmushin dole nafita,

“Wallahi Yunus ka cuci kanka, dube yanda tayi karya dan ta kareka nayi Imani da Allah ba abinda tafaɗa bane ya faru mi tayi maka har kayi mata wannan dukar, fama kirjinta tayi fa, Gaskiya Alhaji kasashi yasake musu y’a dan girman Allah dan dole muje asibiti su duba kirjinta.” Hajiya ta karshe maganar tana share kwalla.
“Koni ma na yarda da maganarki dan babu sisinshi a auren mune muka mishi kuma matar tamuce dan haka mun fasa ya sauta kawai.” Inji Mama kilishi,

“Yunus Mi ya haɗaka da iyalinka kai mata irin wannan dukar, asanina kai mutum ne mai hakuri da biyayya da kuma bawa kowa hakkinshi. ” Inji Alhj,
Gyara zama yayi cikin sanyi murya yace.
“Wallahi sharrin zuciya ce, kuma yarinyar ta cika fitinane bansan mi zan mata bane, kuma gata bata da wni wayewa dan sauran Yan uwanta su Fareeda ai ba’a taɓa jina dasu ba, abinda na.lura shine akwai gidadanci a tare da ita, amma ayi hakuri zan makaranta kuma gaskiya Alhaji ayi mata magana ta daina wannan kukan banzan da rashin kunya.”

Ba Hajiya da Mama ba hatta Alhaji sake baki yayi yana kallon Mai nasara cikin takaici da bakin ciki, murmusawa Alhaji yayi cikin dattako yace.
“Toh ba damuwa mun ji korafinka shi knn ko akwai wani damuwar bayan haka.”

Girgiza kanshi yayi alamun babu, gyara zama Alhaji yayi cike da mamaki da dariyar wautar Yunus, “Toh Yunus ko xaka iya bani takardan Maryama, ina son nanda karshen shekara na bawa Sulaiman Aurenta dan bazamuyi wasa da rasata cikin zuri’armu ba duk macen da tasan rufawa namiji asiri ba matar da za’aki bane, Idan mukayi dubi da kirsar Annabi Ibrahim (A.S)da matar Annabi Isma’il(A.S) lokacin da Annabi Ibrahim yayi zuwarshi na farko bayan barin Hajra da ɗanta sai yasami Annabi isma’il yayi aure, sai ya sami matar yace.
“Baiwar Allah ya halin maigidan nan yake.”

Nan tashiga aibanta Annabi Isma’il, ai yayi kaza bayi kaza ba, tana gamawa, yayi mata godiya da zai tafi yace mata.
“Idan mai gidan ya dawo kice ya sauya kofar gidan nan bai dace da gidan ba.”

Bayan mai gidan ya dawo wato Annabi Isma’il ta faɗa mishi wani tsoho mai kama kaza mai kala kaza ga abinda yace, aikuwa Annabi Isma’l yace mahaifina ne kuma yana min ishara da na rabu dake.”

Next zuwanshi yasamu Annabi isma’il yayi wani auren daga zuwanshi matar ta tarɓeshi ta shiga mishi alkhairi da kyautata mishi haɗi da faɗar alkhairin Mijinta ta ɓoye sharrinsa ta nunawa kowa mijinta na kyautata mata sama da komi…..

Ban kawo maka wannan maganar dan ka zauna dole da Maryam ba dan nima nafi son ka saketa nabawa sulaimanu, ita shi zai iya zama da ita komin muni halinta, dan nasan shi ɗin mai biyayya ne da muradin Iyayenshi. Sati biyu jal na baka kawo min takardanta kaje ka zauna da wayayyun matan, sannan kuma kar na kuma ganin kafarka a cikin gidana indai ba da takardan saki ba, tashi ka tafi Allah ya bamu alkhairi.”
Tashi yayi ya fita jikinshi a sanyayye, dan bai wani ji ba daɗi ba.

……..Ni kuwa zafi jikina yayi sosai amma na boyewa huda har tayi barci amma ni na gaggara barci.

…….Shiru Alhaji yayi kafin yace.
“Miskili yana sonta bai san yanda zai janyo hankalinta bane amma bari muga gudun ruwanshi.”

Mikewa sukayi kowa ya nufi inda zai kwana amma nikam barci yaki idanuna.
Har aka kira sallar asuba a lokacin jikin yayi zafi fiye da jiya, dan nonon sun kumbura sabida famasu da nayi ga zogi azaba, tun ina kuka har na daina na lumshe idanuna koda Huda ta tashi taɓa goshina tayi tajishi da zafi ta fita ta kira Mama, suna zuwa aka fito dani, shirya jikina sai da huda ta taimaka min, aka fadawa Alhaji,, asali bansan miye duka ba a rayuwata ba, kuma dukar da yayi min a kirjina ya haifar min da ciwo ga jikina da yayi mugun tsami.

Dakyar muka fito zuwa gurin motar Alhaji, dai dai shigowarshi daga masalaci kenan, tsura min ido yayi tare da lasar bushashiyar laɓɓashi, ɗago kaina nayi idanunmu ya sarkafe da juna, kwalla ce ta zubo daga idanuna na kauda kaina, shiga motar mukayi na kishingiɗa ina sauke ajiyar zuciya.

Yana son magana Amma Mama kilishi ta tsare gida, haka muka fita muka barshi a gurin, wani asibitin kuɗi aka kaini take, aka shiga bani taimakon gaggawa, daga allurai da drip.
……… Muna fita shima ya haɗa shirginshi sai kaduna……
*****
“Kaii Abban Chuchu baka gajiya ne da abu ɗaya nifa cikina ya fara ciwo.” Inji Rahimah da take kwance a jikin Ahmad bayan ya gama murzeta son ranshi, a gidanshi dake Cikin gidan iyayenshi a garin katsina
Dariya yayi sosai sannan yace.
“Yarinya zakiyi bayani ma raguwa kawai amma kina kokarin taimaka min gurin samin nutsuwa, nagode Rahimahta.”

K’amk’ame shi tayi tana murmushi, rungumeta yasake yana shafa abinda yake bala’in so a jikinta ganin haka ta gyara kwanciyar yq cigaba da yin hidimarshi dasu.
****
A garin maiduguri cikin Rahilah ya fito sabida bata da jiki, zama tayi a gaban Mamie tana cin abincin da aka mata da safe Mamie sai murmushi take cike da jin daɗi tace.
“Rahilah, ina Aman banganshi bane.”
Murmushi tayi kanta a sunkuye tace.
“Mamie ai yana sama, aiki yake a can yasa baki ganshi ba.”

“Kema yunwar cikinki ya koroki da bazan ganku ba sai rana.” Inji Mamie, dariya Rahilah tayi, kawai.

Dukkansu suna cikin farin ciki da jin daɗi.

………
Ya isa garin kaduna karfe bakwai da rabi ya tattara al’amarina ya watsa gefe, ya shiga hidimar gabanshi.

……..Sai da na kwashi kwana biyar asibiti, aka sallameni, nan huda ta shiga haɗa kayanta zata koma, kamar nace zan bita amma nayi shiru, dakyar muka rabu ita kuka ni kuka, haka na dawo kamar kurma.
Bana zama a cikin mutane sai a ɗaki, dakyar nasami wayata na kuna kullum ina online, muna hira dasu Rahilah amma ban faɗa musu abinda ya faru ba dan nabarshi a sirrin gidana.

**** Sati ɗaya babu shi babu dalilinshi, har aka shiga sati nabiyu aka cinye kwanakin, da yamma Hajiya takirashi cike da masifa tace.
“Kaiii Yunus kafita idanuna ka turo min sakin yar mutane wato ga dattawan banza ko nabaka nan da kwana ɗaya kazo min da takardanta ko nina zo maka.” kashe kiran tayi abinta.

…….Yana zaune a office takirashil, lumshe idanunshi yayi cike da tashin hankali yake jinta, idanun nan kamar jan gauta, Aman ne yace.
“Mr Marafa lafiya?”
Tashi yayi ya zauna dakyar ya iya faɗa musu halin da yake ciki, shiru sukayi Ahmad yace.
“Ka daketa kuma, sabida tana Period taɓata maka ɗaki, Mai nasara, lallai da kaine da Hafsa da ka harbeta.”
Nan ya faɗa musu abinda tayi mishi na rufe mishi datayi zaro ido sukayi, murmushi yayi yace.
“Kuma naki saketa, ina kallonta da abinda tayi ni kuma naxe mi? Gaskiya baka kyauta ba, gwara kasake musu yar mutane gari da yawa mayye baya cin kanshi, zata sami wanda zai riketa tsakani da Allah, wai ma kai miye matsalarka da itane kaga yanda Yan uwanta suke kokarin kyautatawa Rayuwarmu.”

“Rabu da ɗan iska, don Allah ka saketa zan nimawa wani cousin broda na aurenta kuma kaga shi ba anan yake da zama ba ɗan kwallon Real Madrine kuma karamin yaro dan 29 ne bakai da kake niman 42 ba, zai iya janta nisan zango har sau uku ko hudu.”

“Zanci abu kazan kazanka shege ɗan iska, matar tawa kake faɗa min wani namiji zaiyi sex da ita har sau hudu a dare billahilazi sai naci Uban tsinane.”
Inji mai nasara, take yashiga fasa duk wani abu na cikin office ɗin, ya fita zuwa gidanshi, yana zuwa yasami gidan a rufe nan ya tambayi maigadi ina matan gidan, shiru mai gadin yayi kafin yace.
“Ai sun koma gra nazata kasani ne, yau sukayi parking.”

Jan motarshi yayi yana huci sai yaci mutuncinsu, Yana isa gidan ya sami falon kaca kace, Sameer ya hargitsa kuma yana kai a tsaye uban na shigowa ya kalleshi shekeke, ya cigaba da ɓarnan shi.

Ranshine ya kara ɓaci sakamakon hango kitchen ɗina abuɗe anyi kaca kaca da komi na ciki kamar an basu ajiyar,

Ajiye jakarshi yayi ya haura sama, dukkansu suna ɗakinsu sai Balkisu da take kishingiɗe. Rike k’ugu yayi cikin azalazaliyar ɓacin rai yace.
“Wani shegene ya baku izinin dawo gidan nan ba tare da sani ba, kuma wata Yar iskace ta shiga kitchen ɗin Maryam Sajida.”

Shiru tayi cike da mamaki yaushe mai nasara ya zama haka,ta lura tun dawowarsh sallah a zaria yake niman abokin mutuwa ya rasa, sai tayi shiru tana kallonshi.

“Nice nan na shiga kitchen ɗinta, kuma akan yarinyar da aka cusa maka kake wannan zage zagen sai kace wani sonta kakeyi yarinyar da nasami labari ka mata dukar kaw….”

“Ya isa wucce kije ki m gyara inda kika bata kafin naniki dukar mutuwa.” Ya faɗa mata azafaffe.
Kallon reni Fareeda tayi mishi kafin ta taɓe baki tace.
“Bazan gyara ba.”

Sam baisan mi yasa tunda aka ce mishi ya rabu ds Maryam yake jin haushin kowa ba, fincikar hannunta yayi suka sauko kasa ya wurgata kicin ɗin yace..
“Minti goma ki gyara kafin na shiga jikinki.”

Dariya tayi tare da cewa
“Hehehehw yeenanaye, Kana taɓani zan baka mamaki,har ka isa kace zaka taɓa ni kai namijine da zai nuna ikonshi a gidan nan toh bari na fada maka wallahi idan ka duke wancar jakar ka kwana lafiya ni bazak…”
“Tabbas bazan taɓa ki ba, amma kije gidanku sai nazo”

“Karya knn wallahi sai dai kai kafita min a gida dan nice mai ɗa namiji, a gidan banza lusari kawai.”

Runtsa idanunshi yayi, nutum ɗaya ce takira shi da lusari yayi hakuri bayan ita bayq jin zaiwa wani hakuri a kirashi lusari ba.

Buɗe idanunshi yayi wanda suka ciko da kwalla yace.
“Kije na sake ki saki ɗaya…………….”

“Wayyo Allah na, ni kasaka” Yunus ya faɗa da karfi ” get out.”
Take kowa ya kama kanshi, kitchen ɗin ya shiga yana kallon yanda aka hautsina komi, take jikinshi yayi matukar sanyi, sana ya koma ya buɗe ɗakina yasami Mufida sai hautsina ɗakin take,

Harɗe hannunshi yayi a kirji, yace.
“Kin mata ajiya ne.”

Juyawa tayi a tsorace, tace.
“Babu.” a shagwaɓe, zuwa yayi ya kamo kununta ya murɗa sai da tasaki fitsari aikuwa ya falla mata mari, ihu take tare da kuka yace.
“Ki ɗauko mopp ki goge mata ɗakinta kuma ki maida kayan if not.”

Fita yayi daga ɗakin, yana jin cin kaniyar kows duk wanda ya kawo mishi wargi.

A daren ya shirya zuwa zaria bai faɗawa kowa ba.

****
Ina kwance bayan sallar isha ina bin kira’a sheik Abdul rahman sudais. Idanuna a lumshe dake hajiya da Mama sun fita ɗazun gaida wata yarsu da aka kwantar a asibiti.

Ban ji sallamarshi ba sai ganin mutum nayi a kaina mikewa nayi salati.
Zama yayi akasar kafet ya zuba min ido, tsuke fuskana yayi cike da tsiwa nace.
“Mi haka zaka shigo kan mutane babu sallama, ayi magana ka rufe mutane da duka.” na karshe maganar tare da murguɗa bakina.

Murmushi yayi sannan ya mike yazo inda nake zaune yace.
“Su mutane har nawane a gurin da ban gansu ba.”

Hannunshi naji yana turawa cikin zanina na tureshi tare da ɓata fuska nace.
“Bana son iskanci, nayi magana a zane ni da belt.”
Matsawa yayi sosai ya shiga kokarin haɗe jikinmu na kai mishi duka a kirji tare da tureshi, amma ko gizau saima kokarin sumbatar bakina yake naki tsayawa.

“Shika musu yar mutane” Inji Mama mikewa yayi yana sosa kai yace.
“Kun dawo lafiya.”

“Lau ina sakin yar mutane yake ” Ta mika mishi hannunta,

“Mama don Allah kuyi hakuri mana magana baya wuccewa ne yanzun na bata hakuri fa.”

“Dake mune sa’anka shine zaka rena mana hankali fitar min a falona.”

Gurin Umma ya nufa itama tayi mishi koran kare, Alhaji na dawowa ya haɗa mishi nashi zafin, kamar zaiyi hauka kuma yana binsu da suyi hakuri amma firr suka ki kulashi sai ma koranshi da sukayi,

Washi gari da ya shigo basu amsa gaisuwarshi ba sai mika mishi hannu alhaji yayi cikin tashin hankali yace.
“Alhaji kuyi hakuri bazan iya ba.”
“wallahi tunda ka iya faɗa mana nakasunta na rashin wayewarta sai ka saketa ko kuma na baka mamaki ka bani takardanta”

“Alhaji wallahi bazan iya ba, ka taimaka min kuyi hakuri.”

“Tashi kabar min gida kar na kara ganinka sai da sakinta ko kuma na baka mamaki mutumin banza, kawai.”

Hmmm kamar mahaukaci haka ya koma a cikin kwana biyu, Ahmad da Aman sun zo Alhaji yaki kulasu saima koran da yayi musu, ina ɗakin hajiya sanye da 3qtr, da riga mai dogon hannu amma kirjin a buɗe. Ya shigo dakesu hajiya suna falon Alhaji suna hira.
Kaina yayo kamar wani kura, ko tsorata banyi ba, niman taɓa ni zaiyi cikin tsiwa nace.
“Anga banza, ko? Toh baka isa ba koda wasa ka taɓa ni sai na maka ihu.”

“Wai mi kuke sonayi ne, na basu hakuri sunko abokaina sunzo sunki, Don Allah mi zanyi muku ne na gaji da izayarku ni kizo mutafi, gida.”

“Babu inda zani, koda zan tafi gidan iyayena zani.”

Shiru yayi, kafin nace wani abu ya saɓeni a kafaɗarshi, yayi waje dani.

A tsakar gida muka haɗu dasu Hajiya ina cewa.
“Sauke ni babu inda zan bika ai kasan da haka ka min shegen duka.”

“Sauketa!!… Kuma sai ka saketa yanzun ko nayi maka Allah ya is.”

A razane na sauko a kafaɗarshi na kare shi ina girgiza kai kwalla na zuba idanuna nace.
“Hajiya Ubangiji muna masa laifi ya yafe mana, balle kuma mu ya mu, yan adam.”

Zubewa nayi a gabansu tare da fashewa da kuka nace.
“Idan Iyayena suka ji haka wallahi Umma sai ta zare ni a cikin Yaranta horon yay….”

“Tashi ki bani guri, sake kine sai yayi fa. Kuma na baka nan da awa biyu ko kuma na maka Allah ya isar. Kema ɓace min da gani.”
. Da gudu na mike zuwa ɗakin da nake na rufe, shi kuma ya fita…

*****Washi gari da safe Mama tasani a gaba sai kaduna Gidan Mamie ta faɗa mata komi, sannan tayi min nasiha tare da nuna min dalilinsu na haɗa mishi zafin kai…..

[8/25, 3:00 PM] Real Mai Dambu:
*MATAR SO*

*MAI_DAMBU*
*Wattpad:Mai_Dambu.*
*HAZAKA WRITER’S ASSO*
(HWA)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai….

Sadaukarwa Ga Yan grp ɗin Matar So….
Dedicater To Hafsat Abubakar

_Wannan buk ɗin hakk’in masu shine idan kinsan baki saya ba karki karanta, mai fitarwa kuma ki duba girman Alkawarin da kika ɗauka na cewa bazaki fitar ba, tunda nace idan kinsan zaki saya ki fitar na Yafe ba sai kin saya ba_

Back to top button