Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 65

Sponsored Links

PAGE* 6⃣5⃣

Asubar fari sumayya tafarka koda daman ba wani baccin kirki bane tayi, alwallah taje tad’auro tazo tagabatar da raka’atanil fijir sannan tazauna tayi ta tasbihi da istigfari kafin atayar da sallah.

Bayan ta gama sallah alqur’ani tad’auko tashiga karanta abinda ta iya acikinsa har saida gari yai haske sannan tayi addu’a takoma takwanta ammah bacci yace d’aukarni inda kika barni, haka tayita juyi ga baccin tanaji ammah ba dama, saidai hawaye kawai da suke fita daga idanunta.

Related Articles

A ranar haka tawuni cikin d’akinta bata fitaba saboda kunyar iyayenta da takeji, ko breakfast batasamu tayiba koda tana jin yunwa dan rabonta da abinci tun jiya da rana.

 

A 6angaren memartaba ko tun dasafe yatura aje abinciko masa yarima duk inda ake tunani za’a gansa anje babushi har gidansa da yagina saida akaje ammah babu labarinsa har marece yayi ana nemansa sannan daga baya akazo aka shaida ma memartaba.

Memartaba baiji dad’iba cikin daren har so yayi yafita dakansa yak’ara bincikawa ammah su sultan ahmad suka bashi baki dak’yar sukasamu yahak’ura.

Sumayya ko sallah ce kawai take tashinta daga saman gadonta cikin d’an k’ank’anin lokaci duk tatsure tarame kamar ba itaba, chan wajen marece ummi tashigo ganin sumayya a wannan yanayin saida tatausaya mata nan tasa aka kawo mata abinci dak’yar tasamu tad’anci kad’an sannan tak’ara yi mata nasiha da wa’azi, sumayya kuka tayi sosai sannan tace ummi dan Allah kuyafemin wlh bazan k’araba, sharrin shed’anne nadaina, k’ara sautin kukanta tayi tace ummi ina jin tsoron had’uwana da ubangijina.

Ummi cike da jin tausayinta tashare mata hawayen fuskarta tace yauwa sumayya indai har kinyi tuba wadda bazaki koma abisa abinda kike aikatawa toh ubangiji zai yafe miki zai kar6i tubanki domin ubangijinmu mai tausayin bayinsane idan yaso yana yafe abinda yake tsakaninsa da bawansa komai yawan zunuban mutum Indai katuba toh zai yafe maka inyaso, hak’ine kawai baya yafewa dan wannan tsakanin mutum da wanda aka zaluntane, dan haka kicigaba da istigfari da yawan tasbihi tare da addu’a, sannan yanzu kitashi kije kinemi gafarar iyayenki dan suma suna da hak’i a gunki.

Rik’o hannun ummi tayi cikin dashashar muryarta da tasha kuka tace ummi kitaimaka min kirakani k’ila idan dakene zasu iya yafemin ammah idan naje nikad’ai korata zasuyi.

Shafa kanta ummi tayi tace kar kidamu sumayya bazasu korekiba insha Allahu, tashi muje ammah bazan shigaba kekad’ai zaki shiga.

Mik’ewa sumayya tayi dakyar take tafiya jiki babu k’wari sultana sadiya tana rik’e da ita sukanufi part d’in iyayenta.

Daga bakin k’ofa sultana taja tatsaya, nan sumayya tatura d’akin ahankali tashiga, sultan abbas zaune yake a parlournsa yana kallo ammah idan mutum yalura zai gane ba kallon yakeba dan gabad’aya hankalinsa yayi wani wajen daban, daga nesa da shi kad’an sultana sadiya ce ta buga uban tagumi ta tsura ma waje guda ido.

Shugowar sumayya yasa gabad’ayansu suka juyo suka kalleta daga nesa dasu kad’an tatsugunna bata damu da mugun kallon da sultana sadiya take watsa mataba, duk’ar da kanta tayi nan hawaye suka cigaba da zuba.

Ummah ce cikin fushi tace ubanmi kikazo yi mana nan? Ko sai kinga kin kashemu sannan hankalinki zai kwanta?

Girgiza kai tashiga yi, muryarta tana rawa tace ummah Abbah dan Allah kuyafemin wlh nadaina.

Munafukar banza wlh ko kitashi kifita kiba mutane waje ko yanzu insa6a miki.

Shuru sumayya tayi kamar ba da ita takeba saida sultana sadiya ta kwatsa mata tsawa sannan tamik’e jiki babu k’wari kallon iyayen nata tayi d’aya bayan d’aya sannan tafita tana kuka.

Ummi da take tsaye ganin ta fito tana kuka yasa tace sumayya basu hak’uraba?

‘Daga mata kai sumayya tayi tace ummi kitaimaka muje tare k’ila insuka ganki zasu hak’ura.

Rik’o hannunta sultana bilkisu tayi tace kar kidamu yanzu dan suna cikin fushine kibari ak’ara koda kwana biyune sai kik’ara komawa yanzu muje kikwanta kihuta.

Girgiza kai sumayya tayi cikin muryar tausayi tace ummi dan Allah zanbiki part d’inki inzauna tunda wajenkune kawai nake samun sauk’i.

Murmushi ummi tayi tace shikenan sumayya muje ai da nan da chan duk d’ayane, cikin jin dad’i sumayya tayi ma ummi godia sannan sukaje part d’inta tahad’a kayanta suka tafi.

Room d’in da rahama tazauna nab taza6a aka shigar mata da kayanta, bayan ta yi sallah gado tahau takwanta nan tashiga rama baccin da ake binta.

Ummi bata barinta tana zama ita kad’ai janyota take sufito parlour suzauna takunna musu kallo, daga k’arshe malami tasamo mata yake zuwa yana koyar da ita littafan addini duk bayan sallar magrib.

Nan da nan sumayya tacanza takoma so silent dan magana ma bata dametaba bare fita babu inda take zuwa indai bata room d’inta toh tana tare da ummi, idanuwanta sun wani k’ank’ance saboda yawan kuka dan kuka kawai takeyi tasamu sauk’in zuciyanta ganin da take itace silar rugujewar duk wani farin cikin family d’insu, ga su yarima da take ganin ta zalunta, kullum addu’arta d’ayace Allah yabayyanasu ko tasamu tarok’i gafararsu.
su kansu ma’aikatan gidan saida suka dinga mamakin sauyin da sumayya tayi.

 

Memartaba ko badan komai yakyale sumayya ba sai dan ya fiso sai yarima ya dawo yayanke mata hukunci da kansa dan aganinsa hakan shine daidai.
a yanzu tare dashi da ‘ya’yansa ake fita neman yarima idan suka fita tun safe basu dawowa sai dare, wasa-wasa duk inda ake tunani za’a gansa anje ammah babushi babu dalilinsa saida akayi sati guda sannan yasa anayi masa safka tare da addu’a akan Allah yabayyanasa.

Gabad’aya memartaba ya fita hayyacinsa dan ko abincin kirki baida lokacin zama yaci, dada ita kanta batada buri sai nason ganin yarima.

Su ko iyayen gayya ba a magana dan danne zuciyarsu kawai suke ammah basuda buri da yawuce suga d’ansu, dan ita kanta ummi kusan kullum sai ta kira number d’in da yarima yakirata da ita but switch off take, tasha ta6oye a part d’inta taci kukanta, tana danne damuwartane saboda ‘ya’yanta da sumayya.

Dan rahama saida ummi tataka mata burki sannan tadaina zuwa gidan, shaheed kullum baida aiki sai lallashinta dan gabad’aya tarikice masa koda shima yana cikin damuwar rashin abokinsa.

ita ko husna daman ba gwanar zuwa bace koda ma tayo ma ummi waya tace zatazo toh hanata zuwa ummi take kan dole suke hak’ura.

 

Memartaba yau tunda yatashi da wani irin zazza6i yatashi hankalin kowa saida yatashi anso akira masa family doctor ammah yahana, chan zuwa anjima tun yana daurewa saigashi yakasa daga k’arshe saida zazza6in yakwantar da shi, wasa-wasa sai ciwon ciki, gabad’aya saida hankalin kowa yatashi dan ko abinci baya yadda yaci, dakyar aka samu ya amince akakira family doctor d’insu yadubasa.

Da family dr yazo yadubasa maganin zazza6i yabada sannan yace dole sai anje anyi masa scanning anga menene yake causing d’in ciwon cikin dan cikin har d’an kumburi yafara.

Koda akaso memartaba ya amince aje k’iyawa yayi yace shi ba inda zaije ai Allah yana sane da halin da yake ciki sucigaba da yi masa addu’a kawai in da rabon yatashi toh zai tashi, shidai burinsa suje sucigaba da bincika masa yarima.

Nan fa hankalin kowa ya ida tashi aka shiga lallashinsa akan ya amince aje, ita kanta sumayya hankalinta ya tashi sosai dan wajen ummi takejin komai taso taje taganosa ammah ummi tace a’a kar tatafi saboda gudun kar wata matsalar takunno kai, su rahama ma kusan kullum yanzu sai sunzo dubasa ummi da taga suna niyar zama sudad’e sai tahad’e fuska kan dole suke tashi sukoma gidajen mazajensu.

Ita kanta sultana sadiya gabad’aya tayi sanyi sosai dan kowa saida yai mamakin sanyin da tayi, dakyar tasamu mijinta yasafko daga fushin da yake da ita shima saida taje tana ma dada kuka tana rok’onta sannan dada ta amince takirasa tarok’esa akan yai hak’uri sannan yahak’ura ammah ya ce kar wanda yasa baki akan sumayya,

 

_______________

Yarima firgit yayi yafarka daga baccin da yake nan yatashi zaune tare da dafe kansa yana furta innalillahi wa’innah ilaihiraji’un, mafarkin da yasabayi ne kusan kullum dan a yanzu mafarkin ya zame masa jiki, saidai na yau yafi firgitasa.
memartaba ne yake gani cikin wani irin yanayi yana kiransa yana cewa yadawo garesa, yau kuma har da umminsa da sauran danginsa yagani a ciki,,,,dafasa da akayine yasa yajuyo yakalli zarah, cike da tashin hankali tace meyake faruwane ko mafarki kayi?

Murmushi yasamu yak’ak’aro yayi mata, ganin idanuwanta sun cika da k’wallah yasa yajanyota jikinsa yarungume sun dad’e a haka sannan yace zarah kidaina damuwa mafarkine kawai nayi ba wani abuba.

Ajiyar zuciya tasafke tace toh ai ina lura da kai kusan kullum sai ka tashi a razane.

Kidaina damuwa dear kinsan sharrin mafarki nima daga yanzu ban k’ara damuwa addu’a kawai zan cigaba da yi incanza hannu.

‘Dago kai tayi takallesa cikin ido tace promise?
‘Daga mata kai yayi yana murmushi sannan yakwantar da ita tare da rufeta da blanket, rik’o hannunsa tayi, ganin haka yasa yakwanta a gefenta nan suka sakar ma juna murmushi, hannu yakai yana shafar cikinta ahankali yace oya sleep now.

Maida idanuwanta tayi tarufe, nan yazuba ma zara-zaran eye lashes d’inta ido, yanaji har bacci yad’auketa sannan yazare hannunsa yamik’e jiki babu k’wari yanufi toilet.

Mafarkin da yayi yashiga dawo masa nan yad’ibi ruwa yawatsa ma kansa tare da safke ajiyar zuciya, alwallah yad’auro sannan yafito yacigaba da yin nafila bashi yadainaba har saida aka kira sallar asuba yayi raka’atanin fijr sannan yaje yatashi zarah.

Saida yaga ta mik’e sannan yawuce masallaci.

Lokacin da yadawo gari ya d’anyi haske dan a chan Dr mu’az yabarosa shi yadawo gida.
Daga bayan zarah yaje yakwanta tare da rungumota ta baya ahaka yasamu bacci yai awon gaba da shi.

 

Chan cikin bacci juyin da zaiyi yaji ba zarah yalaluba bai jitaba dan haka yabud’e idanunsa, bin d’akin yayi da kallo ko’ina fes sai k’amshi ke tashi ammah babu zarah a ciki, murmushi yayi sannan yakai kallonsa ga agogon da take manne a jikin bango.

Zumbur yayi yamik’e ganin har 12pm tayi, mamakine yakamasa ganin irin baccin da yasha kuma zarah bata tashesaba cikin sauri yawuce yashiga bathroom.

Bayan ya fito tsaye yake gaban dressing mirror yana shiryawa baisan lokacin da zarah tashigoba saidai ji yayi anrungumesa ta baya, murmushi yayi tare da kallonta ta cikin mirror, itama murmushin tasakar masa sannan tace ashe ka tashi dear? Dafatan antashi lafiya my heartbeat, jawota yarima yayi tadawo gabansa saida yaja kumatunta sannan yace shine kika tashi baki tasheniba?

Ash dazafi fa,,,tafad’a tare da turo d’an k’aramin bakinta da yasha jambaki, sannan tace toh ai gani nayi jiya bakayi baccin kirkiba tunda katashi baka komaba.

Cije le6enta yayi sannan yace injiwa yace ban koma bacciba?

Fari tayi masa da ido tace ina fa kallonta lokacin da kake sallah duk farkawar da zanyi sai naganka kana sallah.

Hancinta yaja yace toh naji sarkin sa ido yanzu dai jeki kid’auko min kaya insa intafi kinga nayi late.

Kwantar da kanta tayi a k’irjinsa tare da marairaicewa tace please kahak’ura da zuwa yau tunda baku clinic kaga sai kazauna gida kahuta.

K’ara rungumeta yayi a jikinsa tare da tura fuskarsa cikin gashin kanta da yazame mata d’ankwali, jin baiyi maganaba yasa zarah tace please kar kaje.

Janyeta yayi daga jikinsa yace toh in nazauna me zakiyi min, Inma ba ciwon kai ba da zaki sanyani.

Zarah turo baki tayi tace au nimace nakesanya ka ciwon kai? Toh shikenan kayi tafiyarka inda ba a sanyaka ciwon kai,,,tana fad’in haka tajuya taficce daga d’akin.

Murmushi yarima yayi yace ina ruwan zarah sarkin rigima, nan yawuce yabud’e wardrobe yad’auko kayansa yasaka sannan yafito parlour yatarar da zarah zaune ta had’a rai.

Murmushi yayi yazo gefenta yazauna tare da rik’o hannunta yace baby fushi kuma?

Fizge hannunta tayi tace ni kakyaleni kaje kawai chan inda ba’a sanyaka ciwon kai, daman nasani ni ba ajin aurenka bace kawai dai nayi babban kuskure da na amince ma zuciyata tafara sonka.

Yarima ido yazuba mata cike da mamaki har saida takai aya sannan yace nifa zarah dawasa nakeyi miki babu inda zanje yau ina nan gida tare da mummyn baby.

Mik’ewa zarah tayi tana turo baki tawuce zata bar wajen nan yajanyota saman cinyarsa yace please fushin ya isa haka tunda na fad’amiki babu inda zanje.
Uhm ni da nake sanya maka ciwon kai.
Oh zarah ni fa wasa nake miki yakamata kiyarda dani.

Murmushi zarah tasakar masa tare da tallabo fuskarsa da hannu biyu sannan tace idan ban yarda da kai ba habibinah toh dawa zan yarda?

Shima maida mata martanin murmushin yayi yace nima tunanin da nake kenan baby, yanzu dai jeki ki kawo min breakfast inyi dan yunwa nakeji inyaso daga baya naji da rigimar taki.

Kissing d’in bakinsa tayi tace angama ranka yadad’e yadda kakeso haka za’ayi sannan tamik’e tana tafiya dakyar tafita taje parlour tad’ebo musu breakfast sannan tadawo nan suka zauna sukayi breakfast.

Bayan sun gama bajewa sukayi saman carpet yarima yad’aura kansa saman cinyarta, turo baki zarah tayi tace ni kad’agani inba so kuke kai da babynka kukaryaniba.

‘Dago kai yayi yakalleta yace shikenan tunda haka kikace bari ma kawai intashi intafiyata.

Cikin sauri zarah tagirgiza kai tace a’a kayi kwanciyarka ni da wasa nakeyi.

Dariya yarima yayi yace dad’ina da matarnan tawa matsoraciya ce toh me kikeji ma tsoro a ciki?

Zarah d’aure fuska tayi tace ai dole inji tsoro saboda ‘yan matan garin nan kamar mayu nasan kullum idanunsu suna a kan mijina saisa duk fitar da zakayi hankalina a tashe yake har sai ka dawo,,,tak’arashe maganar kamar zatayi kuka.

Da mamaki yazuba mata ido yana kallonta, ganin hawaye sun fara zuba daga idanunta yasa yatashi zaune tare da janyota jikinsa yace zarah yakamata kisan abinda mijinki zai iya da wanda ba zai iyaba, ni a yanzu ‘yan mata basu a gabana dan babu ma wacce ta isheni kallo.

Uhm ammah ai su kana gabansu idan su basa gabanka.

Janyeta yarima yayi daga jikinsa tare da jingine kansa a jikin kujera yamaida idanunsa yalumshe.

Ido zarah tazuba masa sannan tarik’o hannunsa ahankali tace kayi hak’uri.

Bud’e idanunsa yayi yakalleta yace zarah mekikayi min da kike ban hak’uri?

Cikin shagwa6a tace toh ai naga kamar fushi kake da ni.

Ta6e baki yayi yace no ko d’aya ni ba fushi nake da keba kawai rigimarkice naga tanaso tafi k’arfina.

Rik’o hannunsa tayi tare da marairaicewa tace toh nadaina kayi hak’uri.

Murmushi yarima yayi tare da duba agogon da take mak’ale a hannunsa sannan yace bakomai baby yanzu dai tashi muje kirakani wata ‘yar unguwa, cike da jin dad’i zarah tace dagaske dear.

Murmushi yayi tare da d’aga kai.
Fad’awa tayi jikinsa tarungumesa tace nagode sosai dear wlh daman ina ta so infita inga gari dan tunda mukazo babu inda naje.

Dariya yarima yayi tare da janyeta daga jikinsa yace baby kibi ahankali kar kiji ma babyna ciwo.

Itama dariyar tayi tace ni na isa inji masa ciwo ai da sai na amsa query wajen dadynsa tak’arashe maganar tare da mik’ewa taje bedroom tacanza kaya, Cikin atamfa tafito d’inki riga da skirt sannan tayafa veil tayi gwanin kyau.

Koda tafito ido yarima yazuba mata, matsowa tayi tahura masa ido kad’an, ajiyar zuciya yasafke sannan yace koma kisanyo hijab.

Turo baki tayi tace kaduba fa babban gyalene a jikina,
Mik’ewa yayi tare da d’aukan key d’in motarsa yace tunda baki shirya fitaba ni na wuce.

Cikin sauri tarik’o hannunsa ahankali tace dan Allah kayi hak’uri toh bari insanyo.

Kumatunta yaja yace muje hakan kar inja saboda turo bakin nan yata6o k’asa, duka zarah takai masa cikin wasa nan yagoce yana dariya yace kisameni a waje, yana fad’in haka yawuce yafita.

 

Zarah saida tabiya tashaida ma jamila zasu fita nan tayi mata adawo lafiya sannan tazo tatarar da yarima cikin motarsa zaune yana jiranta, tunda tafito yatsareta da ido har tabud’e motar tashigo sannan yajasu batare da yayi maganaba.

Gugu yakeyi sosai da motar zarah ko titi tazuba ma ido tana kallon tsarin garin cike da burgewa, gaban wani babban Boutique yayi parking daga sama zarah taga ansa symbol d’in baby’s paradise, muryar yarima taji yace bismillah madam.

Murmushin jin dad’i zarah tayi sannan tabud’e tafito, tare suka jera suka shiga ciki yanayin tsarin wajen ya burgeta sosai bin ko’ina da kallo take duk kayane masu kyau da tsada ahaka har suka haura saman step nan kuma taga kayan jarirai da na k’ananun yara, kallon yarima tayi tana shirin tambayarsa nan yasakarmata murmushi yace kiza6ar ma babynmu kaya.

Zaro ido zarah tayi tace babyn da baizo duniyaba bamusan ko namiji bane ko mace.

Murmushi yayi a karo nabiyu sannan yace kar kidamu baby duk wanda Allah yabamu munaso kuma in munsiya zamu iya ajewa ko saboda gaba.

Murmushi tayi cike da gamsuwa da maganarsa tace hakane dear, nan tafara d’iban over roll saida tad’ibi kusan kala goma sannan tad’auki kayan baby gurl kala biyar na baby boy kala biyar.
kallon yarima tayi da yazuba mata ido tace nagama, janye idanunsa yayi batare da yayi maganaba nan yacigaba da d’iban kaya duk wanda yayi masa d’auka yake saida yahad’a kusan kala talatin, trolly guda yacika da kayan baby’s, zarah ko baki tasaki tana kallonsa har yagama sannan suka dawo k’asa itama yasata tad’ibi nata kayan sannan sukaje wajen payment yabiya su kud’insu nan aka kaimasa har cikin motarsa sannan suka shiga yatada suka tafi.

Yawo yayi da ita sosai yanuna mata wajaje dadama sunje pack da malls iri-iri, sayayya yayi mata sosai tun daga kayan tand’e-tand’e zuwa na amfani dan ko turaruka masu tsada yasiya mata, sai gab da magrib sannan suka dawo gida agajiye.

Bayan sallar isha’i kwance suke saman gadonsu zarah tana rungume a jikinsa shikuma yana dannar wayarsa, ahankali zarah tad’ago takallesa, yanayin yadda take kallonsa yasa yagane magana takesonyi dan haka ya aje wayar gefe sannan yace ina saurarenki dan wannan bakin naki nasan akwai magana a cikinsa.

Murmushi tayi tare da gyara kwanciyarta sannan tace tabbas hakane my heartbeat taimako da alfarma nakeso kayimin.

zubamata ido yayi batare da yayi maganaba, zarah janye idanunta tayi daga kallonsa sannan tace dan Allah kataimaka kakira min su mama mugaisa kuma kaga k’ashen watannan za’ayi bikkin Aysha.

Murmushi yarima yayi yace ai muna waya da su suna ma cewa ingaisheki bana fad’amikine saboda gudun rigimarki sannan maganar bikki kuma saidai kiyi hak’uri bazan iya barinki kijeba kuma na fad’ama su mama mun d’anyi tafiya, suma sunsan yanzu kinyi nauyi, dan haka kibari idan Allah ya safkeki lafiya sai muje kigansu.

Mamakine da bak’in ciki suka cika zarah tamarasa abinda zatace masa daga k’arshe zame jikinta tayi takwanta saman gadon tare da juya masa baya.

Shareta yarima yayi dan yasan inyace zai lallasheta a wannan lokacin rigima zatayi masa sosai, daga k’arshe mik’ewa yayi yakoma parlour yai kwanciyarsa saman kujera a nan yagama abinda zaiyi yai baccinsa.

Zarah ma saida tasha kukanta sannan bacci yai awon gaba da ita, cikin dare ko da tafarka talaluba taji babu yarima nan tatashi taduba bata gansaba dan haka tadawo parlour, ganinsa tayi kwance saman kujera yana ta baccinsa.

Zuwa tayi tazauna k’asa gefen kujerar nan tad’aura kanta saman kujerar ahaka tacigaba da baccinta.

Juyin da yarima zaiyi nan yaji abu ya takuresa, yana bud’e idanunsa da mamaki yake kallon zarah da take bacci a takure, dafe kansa yayi tare da furta oh zarah, sannan yamik’e yad’auketa yanufi bedroom da ita, yana kwantar da ita saman gado tana bud’e ido, daga gefenta yarima yakwanta yace kedai kinason wahalar da kanki menene nakwanciya a chan.
Kanta tad’aura saman k’irjinsa tace toh ai kaine kak’i kwanciya kusa da ni bayan ka sabamin ban iya bacci sai tare da kai, kuma fushi kake da ni,
Shafa kanta yayi yace ni ba fushi nake da keba zarah kawai na d’an baki wajene kihuta.
marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace toh kadaina guje min dan Allah kayi hak’uri na daina.
murmushi yarima yayi yace shikenan zarah nadaina yanzu dai kiyi bacci sai dasafe.
k’ara shigewa tayi jikinsa tare da cewa Allah yakaimu my heartbeat.
Tura kansa yayi cikin gashin kanta yana shak’ar k’amshinsa inda hannunsa yake shafar bayanta da shi ahaka bacci mai dad’i yai awon gaba da su.

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_
[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu: .

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….✔*

 

_~Happy Born day momcy sady wsh u many more years ahead nd Allah’s noor~_

 

_*My friendy Beebah M Shehu nd my lil sis Aysha Eesho kumatso kusa yau page d’in nakune sai yadda kukeso zakuyi da shi*_

 

Back to top button