Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 64

Sponsored Links

PAGE* 6⃣4⃣

K’ok’arin bud’e d’akin yashiga yi, yana bud’ewa mutuwar tsaye yayi lokacin da ya hangosu tsakiyar gado lullu6e cikin blanket, gabansa ne yayi wani irin mummunan fad’uwa ganin abun yake kamar a mafarki murza idanunsa yayi yabud’e yagadai a zahirine nan yafara rafka salati.

Sumayya jin muryar abbanta yasa tadawo hayyacinta nan tarikice tafito daga cikin bargon, cikin sauri yajanye idanunsa daga kallonsu hawaye suna malala daga idanunsa.

Ganin abbanta yasa tasaki wata irin razanannar k’ara tare da rufe duka jikinta da bargon tana kuka cike da tashin hankali.

Zinat ma lek’o kanta tayi daga cikin bargon cike da tsoro da firgita.

Sultan abbas girgiza kansa yacigaba da yi cike da takaici yana salati muryarsa tana rawa yace sumayya kin cuceni kin zalunceni ni a matsayina na mahaifinki ba irin wannan tarbiyar nabakiba Allah yasani, wlh baki isa kisani jin kunya a gaban ubangijinaba.

Cikin sauri sultana sadiya tanufo d’akin dan ta d’auka dukansu yakeyi da tajiyo k’arar sumayya cewa take haba Alhaji dan Allah kayi ha….maganarce talak’afe a bakinta lokacin da ta hango su sumayya a wannan yanayin wata irin k’ara tasaki tare da zama dirshan a k’asa tana wani irin kuka, nuna sumayya tayi da yatsa tace sumayya abinda kikeyi kenan? abinda kika za6ar ma rayuwarki kenan? nashiga ukku ni sa’adiya mekikeso duniya tad’aukeni? K’ara sautin kukanta tayi tace wlh daman tunda naga wannan munafukar k’awartaki hankalina bai kwanta da itaba, kaicona ni sadiya wannan wace irin *K’ADDARA CE* tafad’amin.

Sumayya ko inba kukaba ba abinda take tsanar zinat ce da mummunar rayuwar da tayi takamata a karo nafarko da taji ta yi nadama akan abinda take aikatawa, girgiza kai tashiga yi tace wlh ba laifina bane kuyafe min abba, ummah kiyafemin wlh bazansakeba nadaina daga yau.

Kallon zinat tayi da take k’udundune tana zare ido gabad’aya jikinta rawa yake, cike da tsanarta sumayya tace Allah ya isa zinat kin 6ata min rayuwata wlh na tsaneki na tsaneki.

Sultana sadiya dak’yar tasamu tamik’e cikin kuka tanufi inda sumayya take tace wlh kasheki zanyi sumayya inhuta da wannan bak’in cikin naki.

Sultan Abbas ne yajanyota cikin d’aga murya tace ni kasakeni ina amfanin haihuwar d’iya irin sumayya? Kaduba kaga mugun abinda take aikatawa.

Sultan Abbas share hawayen fuskarsa yayi tare da kallon sumayya yace kinyi farin ciki kin saka iyayenki kuka kin kyauta ni bazan miki komai ba tunda ke babbace ba yarinyaba kinsan daidai ammah ni ban haifi d’iya irinkiba dan haka kije na sallama ma duniya ke, sannan dole memartaba yasan da maganar nan,,,,yana fad’in haka yaja sultana sadiya suka fita daga d’akin.

Sumayya cigaba tayi da kukan tana k’wala ma iyayenta kira ammah ahaka suka fita suka barta, juyowa tayi takalli zinat tace kin cuceni kin 6atamin rayuwa kin kashemin aure munafukar banza ‘yar iska wlh dole yau asirinki yatonu dan ba nawa bane kawai yatonu.

Zinat cikin kuka tace sumayya dame kikeso inji da abinda yasameni ko da wulak’ancinki? Ni yanzu bari intashi intafi

‘Daga hannu sumayya tayi tasharara mata mari tace babu gidan ubanda zakije dole ne kema kizauna duk abinda za’ayimin kema ayi miki.
Cikin kuka zinat tace wlh baki isaba wannan tsakaninkine da iyayenki ni babu ruwana.

‘Daga hannu sumayya tayi tak’ara d’auketa da mari cike da jin haushi zinat tace kam ni kika mara? Nan tad’aga hannu itama tarama sai dambe yakaure a tsakaninsu dukan juna suka shigayi.
Daga k’arshe safkowa akayi daga saman gadon aka cigaba da dambe, duk suka fashe ma juna baki, sumayya samu tayi tayada zinat k’asa tabi tadanne tacigaba da bugunta ta ko’ina, kuka kawai zinat take tanaso takwaci kanta.
Sumayya cikin kuka take cewa wlh baki isaba dole kizauna munafuka, yadda asirina yatonu toh dole kema naki yatonu..tana fad’in haka tatadata taje tajanyo doguwar rigarta tasaka.

Sultan Abbas koda yafito zama yayi saman kujera tare da dafe kansa takaici da bak’in ciki duk sun cikasa, sultana sadiya na a gefensa k’asa zaune tana ta rusa kuka itama cike da takaici da bak’in ciki, gabad’aya akarasa me lallashin wani

 

Wayarsa ce datafara ruri yajanyo ganin mahaifinsane yasa yayi picking muryarsa tana rawa yai sallama.

Jin yanayin muryarsa saida hankalin memartaba yatashi yace abbas ya najika haka ko bakada lafiya ne?

Ahankali yace a’a ranka yadad’e,
memartaba cewa yayi toh kazo yanzu akwai sak’on da nakeso inbaka zaka kaima governor,
Shuru Sultan Abbas yayi dan baima san abinda memartaba yake cewaba.

Daga chan 6angaren memartaba cewa yayi abbas ko bakada lafiya ne?

Girgiza kai yashigayi kamar yana a gaban memartaba sannan yace ranka yadad’e kagafarceni bansan ya zanyi da rayuwataba wannan wace irin masiface.

memartaba kwata-kwata bai fahimci inda yadosaba yace wai abbas me yake faruwa? sai a lokacin yajiyo sautin kukan sultana sadiya,,,cike da tashin hankali memartaba yace meyake samunku haka? Mutuwa akayi ko me?

Cikin karyayyar zuciya yace ranka yadad’e ko d’aya, kataimaka kazo kaga halin da muke ciki da idanunka.

Toh yanzu dai gamunan zuwa kasaurareni.
Toh kawai yace sannan yakashe wayar.

Sumayya fitowa tayi daga d’akin tana sand’a wuri tasamu daga chan nesa da iyayenta tazauna k’asa cikin kuka tace dan Allah kuyafemin abbah wlh na tuba bazan k’araba.

Wata uwar harara sultan abbas yawurga mata.
Sultana sadiya ko rarrafawa tayi ta isa inda sumayya take tarufeta da duka tace kin cuceni sumayya ban ta6a sanin wannan rayuwar kike aikatawaba wlh sai na kasheki kowa yahuta.

 

memartaba saida yakira sultan ahmad yace suhad’u gidan abbas sannan yamik’e yakalli dada da tuni ta shirya hankalinta a tashe tana jiransa sutafi, yace muje.

Koda suka fito kusan a tare suka shiga gidan da su sultan ahmad da ummi, suna shiga parlourn ganin sultan abbas sukayi ya dafe kai inda sultana sadiya take dukan sumayya tana kuka.

Dada da ummine sukayi saurin isa wajen suka rik’e sultana sadiya.
Dada tace sadiya menene haka kikeyi sai kin kasheta?
Cikin kuka sultana sadiya tace ranki yadad’e kubarni inkasheta kowa yahuta wlh sumayya batayiba ina ma ace ba jininabace.

Sultana bilkisu ce tayi saurin toshe mata baki tace haba sadiya menene haka kike cewa? Yakamata kidawo hayyacinki.

Gyad’a kai sultana sadiya tayi tace kune zakuga kamar banda hankali ammah ni nasan abinda nake kubarni kawai.

Memartaba da gabad’aya an d’aure masa kai waje yasamu yazauna sannan yace kowa yasamu waje yazauna ayi magana Cikin kwanciyar hankali.

Gabad’ayansu k’asa suka zauna, memartaba da dada ne kawai saman kujera, sumayya ko tana daga chan nesa da su tana kuka.

Kallonsu Memartaba yayi d’aya bayan d’aya sannan yace kun d’aure mana kai dan gabad’ayanku kuka kukeyi ya kamata kufitar da mu bak’in duhunnan da kuka sakamu a ciki

Sultan abbas share hawayen fuskarsa yayi sannan yanuna sumayya yace ranka yadad’e kaduba kaga wai wannan d’iyar cikinace ammah kwata-kwata bata d’auko halinaba ina amfanin haihuwar d’iya irinta me bak’in hali.

Dada zuba masa ido tayi sannan tace kuyi mana bayani yadda zamu fahimceku mana.

Cike da takaici yashiga girgiza kai tare da runtse idanunsa sai chan yabud’e.

memartaba ne yace muna saurarenka.

Muryarsa tana rawa yace ranka yadad’e gatanan wai jininkace take neman mace ‘yar uwarta.

Gabad’ayansu cikin rashin fahimta suke kallonsa

Sumayya da take raku6e gefe k’ara sautin kukanta tayi

Dada ce tace kayi mana bayani yadda zamu fahimta.

Nan yakwashe yadda yashiga yaganta da k’awarta yafad’a musu.

Gabad’aya labarin ya girgizasu nan aka fara salallami.

Dada batasan lokacin da tazamo k’asaba daga saman kujerar da take zaune, kallon sumayya tayi tace Allah wadai wlh bakiji dad’in rayuwarkiba ashe hakanan nake ganinki kamar mutuniyar kirki nan ko ‘yar banzace,,,tak’arashe maganar tare da fashewa da kuka.

Memartaba idan ransa yayi dubu toh ya 6aci duk sanyin A-C d’in da take d’akin ammah zufa yake, yana kallon sumayya cike da mamaki, sannan yace sumayya abinda kika za6arma kanki kenan abinda ubangiji yaharamta, laifin da Allah ya kife mutunen annabi lud’u saboda shi, kina zuwa islamiyya kin karanta kuma kinsani saidai bakiyi amfani da saninkiba shin mancewa kikayi da fad’ar ubangiji da yace ya halitta mana mata dan musamu nutsuwa daga garesu, haka kuma yahalitta maza dan kuma mata kusamu nutsuwa daga garesu, shin hakan da kikeyi ke kina ganin shine daidai agareki? Rayuwar da ko dabbobi basu irinta, wlh baki gani dabba tana neman jinsinta, Ko kinsan makomarki idan kika koma ma mahaliccinci?

Girgiza kai sumayya tashiga yi cikin kuka har muryarta ta fara dishewa tace kuyafemin wlh na daina zinat itace ta6ata min rayuwa da ace ban amince ma zinat ba a matsayin k’awata da hakan bata kasance da ni ba.

Murmushi memartaba yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace tashi kizo min da k’awartaki

Mik’ewa tayi jiki ba k’wari tanufi bedroom d’inta, tana shiga tatarar da zinat ta had’a komai nata, cike da tsanarta sumayya tace munafuka alguguma babu inda zakije kizo memartaba yana nemanki.

Cike da tsoro zinat tadafe k’irji tace eyeh na’am.
Harara sumayya tawurga mata tace dallah kizo mutafi ko yanzu asa afiddoki.

Ai zinat cikin sauri tawuce tabi bayan sumayya, suna fitowa parlour nan ta ida tsurewa tsaye tayi tana binsu da kallo cike da tsorata.

Sultan ahmad ne yadaka mata tsawa yace bazaki zaunaba?
Cikin sauri tazube k’asa jikinta yana kakkarwa.

Memartaba kallonsu yayi d’aya bayan d’aya yajinjina kai yace toh wanene mijin wacece matar?

Kuka kawai suke aka rasa me amsawa a cikinsu.
Dada ce cikin 6acin rai tace dan ubanku ba tambayarku akeba ko sai ansa dogarawa sun tambayeku?

Sumayya rage sautin kukanta tayi cike da nadama tace wlh duk abinda na aikata zinat ce silah, ita ce silar mutuwar aurena, ita tahanani inyi ma mijina biyayya.

Gabad’ayansu salati suka saka, dada tace kar dai kice min yarima baida laifi acikin sakin da yayi miki.

‘Daga kai tayi tace eh baida laifi wlh duk abinda nafad’a muku k’aryane, yarima yana k’ok’arin kyautatamin wannan ce take hure min kunne.

Gabad’ayansu saida maganar Sumayya tarikitasu sultana sadiya cikin kuka tace wlh sumayya banda abinda zance miki saidai ince kije da halinki duniya zata koya miki darasi.

Dada ko mik’ewa tayi tanufi wajen sumayya tahauta da duka tana fad’in sumayya kin cuceni kin rabani da jikana kin had’ani da shi kinsa nad’aura masa karan tsana, bazan barkiba dole kema yau kibar gidannan.

Sultana bilkisuce tazo tajanye sumayya da takasa tashi, cikin muryar kuka tace narok’eki dada kiyi hak’uri kibarta, dada girgiza kai tashiga yi tace ya akeso inyi ina zanga jikana?

Rik’o hannunta sultana bilkisu tayi taje tazaunar da ita tace kiyi hak’uri dada duk inda yarima yakasance yana cikin k’oshin lafiya.

Memartaba da yake binsu da kallo sai a lokacin yayi magana yace kaicona ina ma ace naba yaronnan dama yafad’i ta bakinsa, tabbas 6acin rai baiyiba kamar yadda zartas da hukunci cikin fushi baiyiba.

Sumayya kin zubarmin da k’ima da daraja a cikin masarautata kin rugazamin duk wani farin cikina na rayuwa, kin rabani da jikana da nafi so a rayuwata.

Sumayya tsagaitawa tayi daga kukan da take tace kuyafemin wlh *nayi nadama*

Jinjina kai Memartaba yayi yace sumayya kenan dole ku amsa hukuncin abinda kuka aikata kamar yadda nake zartas ma da sauran al’ummah dan haka zansa ayi muku bulala tamanin tamanin

Murmushi sumayya tayi tace indai har haka zaisa insamu sauk’in abinda na aikata toh na amince.

Sultan Ahmad ne yace ranka yadad’e yakamata a sassauta musu.

Girgiza kai Memartaba yayi yace wannan shine adalci nan yajanyo wayarsa yakira wani amintaccen dogarinsa sahalu,
ko da yazo nan memartaba yace ashiga da su sumayya ciki ai masu bulala tamanin tamanin, kasa tashi dogarin yayi dan jin maganar yayi kamar ba daidai yajiyoba, saida memartaba yace umurni nabaka kuma amana dan haka banda ragi,
cike da girmamawa yace toh ranka yadad’e.

Nan aka shiga da su sumayya cikin d’akinta dan gudun kar wasu sugani, sumayya tafara kwanciya dan ita bata tsorata da bulalar da akace za’ayi mataba ita dai burinta ubangijinta da iyayenta suyafe mata, bulalar farko wata irin k’ara tasaki koda akan adalci yayi musu ba kamar wadda za’ayi ma namijiba su ya d’an safsafta musu saboda matane, bai kyaletaba saida yayi mata tamanin tun tana iya motsi har takasa daga k’arshe sumewa tayi ahaka aka gama tana a sume, sannan yadawo kan zinat itama tana ihu da hargagi ahaka aka gama aka barta kwance bata iya motsin kirki.

Memartaba gudun kar suji k’ara yasa aka kunna tv tare da cika volume ammah duk da haka sunaji sama-sama, ummi, dada, sultana sadiya kuka kawai suke ahankali cike da takaicin abinda sumayya ta aikata

Bayan dogarin ya fito nan yatabbatar ma da memartaba ya yi kamar yadda ya umurcesa nan memartaba yasallamesa yatafi.

Sawa yayi aka rage volume sannan yakallesu cike da damuwa yace yanzu ya duniya zata d’aukeni? Da wane suna za’a kirani? Innalillahi wa’innah ilaihiraji’un wannan wace irin *k’addara ce* yanzu duk mutuncina da darajata sun zube a idanun mutane

Sultan abbas cike da damuwa yace ranka yadad’e ni kaina narasa ya akayi ina zaune da sumayya ammah bansan abinda take aikatawa ba, kokuma ni k’arani kan waccan uwar banzar da akodayaushe take tare da ita ammah batason laifinta sannan ace batasan duk wani motion d’in d’iyartaba toh wannan wace irin soyayyace takeyimata, wannan ba so bane haukane tunda baki iya tarbiyar da d’iyar cikinki dan haka daga ke har ita kutafi kuban waje bana buk’atarku a cikin rayuwata.

Sultana sadiya k’ara fashewa tayi da sabon kuka tace nashiga ukku idan karabu da ni ina kakeso inje inji dad’i bayan banida kowa bayanku dan Allah kayi hak’uri kayafe min wlh bansan sumayya tana wannan mummunar halayyarba.

 

Cikin d’aga murya sultan ahmad yace kai miye haka kakeyi idan rai ya 6aci ai baidace zuciya ta6aciba yakamata kadawo hayyacinka ita kuma sadiya miye nata laifin aciki? Itada ba ita tayimakaba shine zaka had’a da ita?

Girgiza kai sultan abbas yashigayi yace kubarni nikad’ai nasan abinda nakeji su dukansu banason ganinsu.

Memartaba jinjina kai yayi yace babu inda zasuje, sannan yakalli sultana bilkisu yace jeki kigano min su sumayya.

Mik’ewa sultana bilkisu tayi cikin sauri tanufi part d’in sumayya tana shiga yanayin yadda taga sumayya saida tatsorata dan batada banbanci da matatta, zinat ko numfashi take fitarwa sama-sama tana jan jiki daga kwancen.

Cikin sauri ta isa inda sumayya take tashiga jijjigata ganin bata motsi yasa tamik’e taje tad’ebo ruwa tamakaka mata, wani dogon numfashi sumayya taja ahankali tashiga motsa hannunta nan hawaye suka shiga malala daga idanunta, ahankali tabud’esu tasafke akan ummi da itama take hawayen, muryar sumayya ciki-ciki tace ummi kice min mafarki nake ba gaske bane, wlh ummi nayi nadama nadaina kuyafemin.

Ummi rungumo sumayya tayi a jikinta tace shikenan sumayya yanzu dai bari ingasa miki jikinki kinga duk ciwone.

Murmushin k’arfin hali sumayya tayi tace ummi ciwon da nakeji a zuciyata yafi radad’in bulalarnan dan Allah kitayani ba su abbah hak’uri.

Ummi sharemata hawayen fuskarta tayi tace kar kidamu yanzu dai muje kifara gasa jikinki,,,,haka ummi taje tahad’a mata ruwan d’umi ita tataimaka mata tagasa jikinta tayi wanka sannan tashiryata takwantar da ita saman gadonta saboda jikinta yad’au zafi sosai.

Juyowar da ummi zatayi nan taga zinat tana d’aukar kayanta tana bin bango dakyar take tafiya har tafita daga d’akin.

Ai tana fitowa parlour tacikaro da su memartaba rikicewa tayi tasaki jakkarta tare da duk’awa tace dan Allah kuyafemin wlh natuba bazan k’araba.

Murmushin k’arfin hali memartaba yayi yace dole ki amsa hukunci tunda kece silar lalacewar sumayya, kuma kece silar rugujewar duk wani farin ciki na masarautar nan dan haka yanzu zansa akaiki gidan yari kid’an kwana biyu.

Zinat sake fashewa tayi da sabon kuka tace dan Allah kuyi hak’uri wlh ba zan sake dawowaba.

Memartaba wayarsa yad’auko yai kira, cikin mintuna kad’an saiga wani k’aton barde yashigo nan memartaba yace atafi da zinat gidan yari duk wani aiki me wahala asata kar a sassauta mata .

Cike da girmamawa yace angama ranka yadad’e, nan yatusa zinat gaba tana kuka tana rok’onsu ammah ahaka aka fita da ita babu wanda yasaurareta.

Sultana bilkisu fitowa tayi tashaida musu halin da sumayya take ciki ammah kowa shareta yayi yace baruwansa, dada ma cewa tayi tamutu mana ina ruwan wani, sultan ahmad ne kawai yatausaya mata nan yakira family doctor d’insu.

Memartaba da takaici ya isheshi mik’ewa yayi batare da yayi ma kowa maganaba yawuce yaficce nan dada tabi bayansa.

Ganin haka yasa sultan abbas ma cike da 6acin rai yatashi yawuce part d’insa, sultana sadiya ma tashi tayi tabi bayansa dan gabad’aya hankalinta atashe yake addu’a take cikin ranta akan Allah yasa kar aurenta yamutu.

Sultan ahmad da sultana bilkisu ne suka cigaba da zama har doctor yazo yaduba sumayya yabata drugs tasha, nan sultan ahmad yatafi yabar sultana bilkisu wajen sumayya tana cigaba da kula da ita tare da kwantar mata da hankali har dare sannan tafara shirin komawa turakarsu, sumayya ba dan tasoba haka tahak’ura tabar ummi tatafi.

bayan ummi ta tafi nan tadasa wani sabon kukan cike da nadamar abinda ta aikata, ji take ina ma tabud’e ido taga duk a cikin mafarkine komai yafaru saidai inaa *k’addara ta riga fata* haka tayita juyi tana kuka har wajen k’arfe d’ayan dare nan tatashi dakyar jiki ba k’wari taje tad’auro alwallah akaro na farko a rayuwarta da tafara tunanin yin nafila, nan taita sallah tana neman yafiyar ubangiji har wajen k’arfe ukkun dare, tana zaune a saman darduma tana lazumi ahaka bacci yai awon gaba da ita.

Sultana sadiya koda tabi sultan abbas part d’insa tana ganin ya zauna bakin gado nan tazo tatsugunna gabansa cike da nadama, cikin kukan tace Dan Allah kayafemin wlh zan canza rayuwata, duk abinda na aikata wlh akan kuskure da *SON ZUCIYA* na aikatasa, tabbas a yanzu nasan ba gata bane nanuna ma sumayya, dan Allah kataimaka kayafemin ba dan halinaba ko nasamu d’an sauk’i acikin raina.

Murmushi sultan abbas yayi wanda yafi kuka ciwo sannan yace sadiya kin aikata babban kuskure wanda tabonsa ba zai ta6a gogewaba a raina, na aureki ina gani kamar zaki taimaka min wajen ganin mungina rayuwarmu da ta ‘ya’yanmu cikin tsafta, ashe bahaka bane ni kad’ai nake haukana ke kin riga kin tsara taki rayuwar, toh me yayi saura a yanzu? Me zakice min?

Cikin kuka tashiga girgiza kai tace kayi hak’uri wlh tsautsayine insha Allah yanzu zan gyara.

A wulak’ance yakalleta yace kar ma kigyara dan ba matsalata bane dan haka kitashi kifita kiban waje tun kan ranki ya6aci.

Cikin sauri sultana sadiya tamik’e tare da cewa Allah yahuci zuciyanka sannan taficce tabar d’akin tana waiwayensa.

Memartaba koda yakoma turakarsu cike da tashin hankali tare da nadamar abinda yayi ma yarima suhail maganganun da yayine akansa yadinga dawo masa a k’wak’walwa, jiyake ina ma ace ya tsaya yai bincike kafin yakori jikansa dayafi k’auna a rayuwarsa Memartaba harda ‘yar k’wallarsa, dada ita kanta koda tana cikin tashin hankali ammah haka tadanne tashiga lallashin mijin nata dan soyayi yaje yafara neman yarima a lokacin, dakyar tasamu taja ra’ayinsa yafasa zuwa dan darene,

A 6angaren ummi ma koda takoma part d’insu kuka taci sosai har sultan ahmad yashigo yatarar da ita, cike da tausayinta yazauna gefenta d’ago kai tayi takallesa cikin kuka tace kagani ko suhail d’ina baida laifi dan Allah kasa baki memartaba ya amince sudawo gida.

Rungumota yayi jikinsa cikin lallashi yace sultana kikwantar da hankalinki suhail zai dawo agaremu tunda baida laifi a ciki, na tabbata memartaba zai sa anemo masa shi dan shi kansa yana cikin damuwar rashin suhail.
Kicigaba da addu’a kinji ko?
‘Daga masa kai tayi alamun eh, nan yacigaba da kwantar mata da hankali daga k’arshe suka kwanta.

 

Gabad’aya family d’in babu wanda yasamu yayi baccin kirki dan kowa hankalinsa atashe yake.

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_[5/3, 9:53 PM] Sis Naj Atu:

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

Back to top button