Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 24

Sponsored Links

PAGE* 2⃣4⃣

Yarima ganin zarah tana shirin wucewa part d’inta yasa yace suje part d’insa yanason ganinta, zarah bata musaba tabi bayansa dan bata iya musama yarima saboda girmansa da take gani.

ko da suka shiga saman cushin yarima yazauna, zarah har zata zauna k’asa yace tazauna saman cushin tunda suka zauna d’akin yad’au shuru.

yarima kiran sumayya yayi tana d’auka cike da jin haushi yace kinsan dai bana jira kuma baki isa inzauna ina jirankiba.

tsaki sumayya taja tace ai ganinan a hanya.

bayan minti biyu saiga sumayya tashigo fuskarta babu alamun fara’a ganin zarah yasa taja bakin k’ofa tatsaya, dasauri zarah tamik’e tad’an russuna tace Aunty barka,

wata uwar harara gimbiya sumayya tawurga mata tare da jan tsoki, tace Auntyn munafunci? kece kika auran min miji ko? lallai natayaki murna tak’arashe maganar tare da yin k’wafa

jikin zarah duk sai yayi sanyi.

yarima da yake dannar waya yana saurarensu batare da yakallesuba yace ma gimbiya sumayya ai saikizo kizauna kin wani yi ma mutane tsaye,

sumayya tana hararar zarah tatako cike da isa tazauna saman kujerar da yarima yake zaune, zarah ma jiki ba k’wari tazauna inda take tare da saddar da kanta k’asa.

yarima shuru yayi yana dannar wayarsa baice komaiba saida akayi kusan minti ukku,

sumayya ta k’ule kallonsa tayi tace haba yarima ya zakayi shuru kabarni a zaune.

banza yarima yayi da ita saida yagama abinda yake sannan yad’ago kai yakallesu d’aya bayan d’aya tare da gyaran murya kamar bayason yin magana yace toh Alhmdllh ba akan komai natarakuba sai dan infad’a muku dokokina domin duk wadda takeson zama da ni dole tabisu, kallon sumayya yayi da taci face yace ke sumayya kece babba dan haka kija girmanki banason fitina ko tashin hankali, sumayya cike da masifa tabud’e baki zatayi magana, yarima hannu yad’aga mata yace kar kikuskura, kin san wanene ni idan ina magana ba’a tsinkemin.

sannan yamaida kallonsa ga zarah da take wasa da yatsun hannunta yace ke kuma kece k’arama dan haka dole kibata girmanta sannan kizauna da ita lafiya kar kikuskura inji kinyi mata rashin kunya, zarah shuru tayi batace komai ba.

yarima yacigaba da cewa kar wanda yasaki yakawomin tashin hankali a gidana, sannan maganar kwana bayan sati guda zaku koma kowace kwana bibbiyu, jinjina kai yayi yace na fad’amuku kar inji kar ingani banason tashin hankali wlh duk wadda tanemi takawo min raini zan d’au k’wak’waran mataki a kanta, yana kaiwa nan yayi shuru na d’an lokaci sai chan yace idan akwai mai magana zata iya yi.

ba sumayya hatta ita kanta zarah taji haushin maganganunsa, sumayya ce tace yanzu dai wad’annan maganganun naka ban ganeba kafito fili kace da ni kake wannan shine adoki mutum sannan ahanasa kuka, ka gama yimin kishiya sannan ka…… hararar da yarima yawurga matane yasa tayi shuru, d’an guntun murmushi yayi yace ban miki alk’awalin bazan k’ara aureba kai koda ace a nan gaba naga wadda tayimin nakeso toh sai na aureta saidai duk wadda taji bata iya zama toh k’ofa a bud’e take dan haka kutashi kuban waje.

zarah ce tafara tashi dasauri tafita sannan sumayya.

zarah tana cikin tafiya taji muryar sumayya tace ke!
zarah batare da ta juyoba tatsaya nan sumayya tatako cike da isa tazo inda zarah take, kallonta sumayya tayi daga sama har k’asa sannan tace gimbiya zarah ko? l
dariya sumayya tayi tace gaskiya natayaki murna gaki d’iyar talakkawa ammah zaki had’a miji da gimbiya kamata, chan kuma sai gimbiya sumayya tad’aure fuska tace wlh baki isa inyi kishi da keba dan haka yazama dole kirabu da mijina, inkuma ba hakaba bakeba hatta talakkawan iyayenki sai sunsan kwad’ayi yakaisu ya baro, dan suma sai sun gane kurensu dan haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya.

tana gama fad’in haka tazagaye zarah tawuce tabarta nan tsaye.

zarah dai binta take da kallo cike da mamaki kasa cewa komai tayi tawuce tanufi part d’inta zuciyanta cike da k’unci

zarah ko da takoma part d’inta sama-sama tatsaya suka gaisa da kuyanginta sannan tashige bedroom d’inta, saman gado takwanta tana tunanin maganganun da sumayya ta yada mata, sai tatuno da yarima suhail, tsaki taja tace wlh darajar alk’awalin da nad’aukar ma malam bello da kuma darajar aure wlh da bazan yadda a wulak’antaniba.

hawayene suka fara zarra daga idanunta chan tafashe da kuka cike da tausayin kanta.

 

wajen azuhur kuyangarta tashigo tahad’a mata ruwan wanka.

bayan zarah ta fito wanka tad’and’ara kwalliyarta gown d’in atamfa tasaka, bayan tayi Sallah tafito parlour, ganinta yasa kuyanginta suka zube suna kwasar gaisuwa, zarah bata ce komai ba saida taje saman cushin tazauna sannan tace banason irin wannan gaisuwar da kukeyimin kudaina duk’amin.

zabba’u shugaban kuyangince cike da girmamawa tace ranki yadad’e kigafarceni matsayinkine da k’imarki da cancantarki sukaja haka, murmushi zarah tayi tace nagode ammah kudaina, yanzu dai inason asani nishad’i wazai ban labari mai dad’i?

nan zabba’u takalli d’aya daga cikinsu tace daso aikinkine, wadda aka kira da daso nan tafara ba zarah labari suna dariya, cike da nishad’i suke hirarrakinsu.

chan wajen k’arfe ukku zarah tace yanzu lokacin cin abincinane, nan suka duk’a sukace toh ranki yadad’e atashi lafiya sannan suka mik’e suka fita.

masu kula da abincinta har sun tsaya nan zarah tace sutafi kawai.

zarah dakanta taje tayi serving d’in kanta taci abinci, bayan ta gama nan takira tace suzo sukwashe abincin suje suci.

bayan sallar la’asar zarah kallo takunna tana yi duk kad’aicin ‘yan gidansu ya dameta, saida aka kira magrib sannan taje tayi sallah dakanta tashiga kitchen tadafa ‘yar indomie, duk yadda kuyanginta sukaso tabari suyimata ammah tak”i tace musu zaman ne ya isheta saisa takeso tad’an motsa jikinta, kan dole suka hak’ura suka barta.

bayan sallar isha’i zarah ‘yan gidansu takira sukasha hira tare da tambayarsu yaushe zasuzo, Aysha tace saidai kin ganmu kawai abbah ne yahanani dan naso inzo yau yace a’a sai kinkwana biyu.

zarah cikin rashin jin dad’i tace toh Allah yasa ya amince kuzo kuyi min kwanah ni wlh kad’aici yana damuna.

dariya Aysha tayi tace haba yaya zarah wane kad’aici bayan gidan akwai mutane kuma ga kallo, ni wlh ji nake daman nice.

tsaki zarah taja tare da kashe wayanta tace Aysha kenan, shirin bacci tayi ta sallami kuyanginta tayi kwanciyarta.

 

*wanshe kare* bayan zarah ta yi sallar asuba bacci takoma sai wajen k’arfe goma tafarka, nan aka had’a mata ruwan wanka tayi tashirya cikin material coffee colour kayan sun kar6eta sosai, nan tafito suka gaisa da kuyanginta tayi breakfast, bayan ta gama breakfast kallo takunna tanayi kasancewarta mai son kallo, kuyanginta suna zaune k’asa, sallamar da taji anyine yasa tad’ago kai, Rahma ce tashigo cikin shigarta ta alfarma sanye da alkyabba, ganinta yasa kuyangi suka duk’e k’asa suna kwasar gaisuwa, zarah tunda taganta tasan jinin yarima ce saboda taga kamansu dasauri tamik’e tare da d’an rissinawa cike da girmamawa tace sannu da zuwa, kuyangi bayan ta amsa musu tashi sukayi suka fita daga d’akin, nan Rahma tatako taje tazauna saman d’aya daga cikin kujerun d’akin saida tazauna sannan zarah ma tazauna tare da gaisheta.

Rahma da take k’arema d’akin kallo amsawa tayi ciki-ciki, zarah fuskarta d’auke da fara’a tamik’e tace bari inkawo miki ruwa,

sumayya yamutsa fuska tayi tace no kibarsa kawai am ohk, daman nazone mugaisa ina fatan kinji labarina wajen mijin naki, nice k’anwarsa.

murmushi zarah tayi tace eh ummi ta fad’amin jiya tace bakyanan ne saisa bamu had’uba, Rahma mik’ewa tayi tsaye tace zan wuce Allah yabada zaman lafiya, zarah ma mik’ewa tayi tare da rissinawa tace mungode Allah yakiyaye, Gimbiya Rahma batace komai ba tawuce tafita.

zarah komawa tayi tazauna tare da dafe kanta cikin ranta tace wannan indai halin yarima ne takwaso daga gani zatayi wulak’anci _(Ni kuma nace haba zarah gani d’aya kawai ammah har kin fassarata)_

 

bayan sallar azuhur wanka tashiga tayi.

zarah bayan ta fito daga wanka kwalliya tazauna tayi sosai sannan tashirya cikin boyel less d’inta blue nd orange colour d’inkin riga da skirt ne kayan sun kar6eta sosai sannan tad’aura alkyabba orange colour daga saman kayan tayi kyau sosai saida tafeshe jikinta da performs sannan tafito parlour lokacin kuyanginta na zaune k’asa suna jiran fitowarta ganinta yasa gaba d’ayansu suka rissina sukace barka da fitowa sarauniya tsarki ya tabbata ga ubangiji da yahalicci wannan kyakkyawar kuma mata ga sarki mai jiran gado angaisheki gimbiya.

gimbiya zarah takowa tayi tana murmushi kamar ba zatayi maganaba ammah ganin basuda niyar d’agowa yasa tace nafad’a muku banason hakan da kukemin ammah kunk’i dainawa ko?

kuyanga d’aya batare da ta d’ago kaiba tace ranki yadad’e kigafarcemu ke shugabace agaremu kuma mai mutunci dan haka girmamawa yazama dole muyi maki,
murmushi zarah tayi a karo nabiyu sannan tace wasu sutaso surakani 6angaren gimbiya sadiya.

kuyangi hud’u suka mik’e nan zarah tashiga gaba suna biye da ita a baya, tako take irin na masu ji da kansu,

duk inda tazo wucewa sai anduk’a angaisheta itakuma tana tsayawa tana amsa musu fuska a sake sannan tacigaba da tafiyarta ahaka har tazo 6angaren gimbiya sumayya.

bayin gimbiya sumayya biyu da suke tsaye k’ofar d’akinta ganin gimbiya zarah yasa suka duk’a suka gaisheta nan ta amsa musu fuska a sake dasauri suka tashi suka bud’e mata d’aki tashiga.

gimbiya sumayya da take zaune saman kujera inda bayinta da kuyangi suke zagaye da ita tana ta dannar wayarta.

gimbiya zarah ce tashigo da sallamarta fuskarta d’auke da fara’a kuyanginta suna biye da ita, ganinta yasa gimbiya sumayya tahad’e fuska,

nan ma’aikatan sumayya suka zube suna kwasar gaisuwa, tsawa sumayya tabuga musu dasauri duk suka mik’e tsaye, gimbiya zarah bata damuba tad’an rissina tace barka da rana.

wata irin harara gimbiya sumayya tawurga mata cikin tsawa tace meyakawoki d’akina?

zarah murmushi tayi tace nazo ingaishekine

gimbiya sumayya tace ashema kinzo kigaisheni to kirik’e gaisuwarki bana so ke ga kicifaffa watakau kinzo kimin iyayi
toh bari kiji kibar ganin kin auri yarima yadda kika shigomin gida dole kifita kibarsa sannan daga yanzu kar kik’ara shugo min d’aki duk ranar da kika k’ara gigin shigowa sai nanuna miki matsayinki a gidannan ke bakomai bace face talaka makwad’aita.

damamaki zarah takebin gimbiya sumayya da kallon yadda tadage tana ta zuba mata ruwan rashin mutunci.

sumayyw k’walama bayinta da suke tsaye bakin k’ofan d’akinta kira tayi dasauri suka gurfana gabanta kamar zasuyi mata sujjada dan tsoro sukace gamu mun amsa kiranki ya shugabarmu,

sultana sumayya a wulak’ance tace meyasa kuka bari wannan d’iyar talakawan tashigo min d’aki?

shuru sukayi suka fara ‘yan kame kame

gimbiya sumayya kishingid’awa tayi a saman kujerar tare da cewa kufitarmin da ita na baku kinti biyu idanko ba hakaba a bakin aikinku.

 

zarah murmushin takaici tayi tare da cewa bama sai kinsa an fitar da ni ba, ni zan fita da kaina saidai inaso kisan wani abu d’aya, talauci da dukiya duk na Allah ne dan haka na barki lafiya.

tana gama fad’in hakan tajuya tafito cike da 6acin rai duk Wanda yake wajen baiji dad’in abinda gimbiya tayima zarah ba saidai kowa yabar abun a ransa domin gudun 6acin ran gimbiya

 

suna fita daga d’akin kuyanginta suka zube k’asa sukace Allah yahuci zuciyar gimbiyanmu,

murmurshi zarah tayi sannan tawuce gaba suka tashi sukabi bayanta ahaka har suka shiga part d’inta bata kula kowaba tawuce tashige bedroom tare da maida k’ofar tarufe tacire alkyabtarta cike da takaici tafad’a saman gado tace wannan wace kalar rayuwace duk inda nayi babu sauk’i, takaicinta maganganun da Gimbiya sumayya tafad’a a kanta, hawayene suka cika mata ido tace Allah gani gareka.

 

wanshe kare zarah tara kuyanginta tayi taraba musu kud’i tace kowa yaje yasiya abinda yake buk’ata, sunji dad’i sosai nan suka duk’a sukayi mata godia sannan suka fita kowa yana murna

 

haule ce da zabba’u zaune bayan part d’in zarah suna cin abinci, haule takalli zabba’u tace gaskiya natayaku murna dan kunyi dacen uwargijiya ba kamar tamuba.

murmushi zabba’u tayi tace mukam ai saidai muce Alhmdllh dan wlh tana da kirki sosai batada girman kai.

haule tace hmm muko kinga tamu girman kai da wulak’anci gareta ke ni har tsoro nakeji inga na6ata mata rai dan sai kagane kurenka, duk abinda zakayi mata toh bazaka ta6a burgetaba, daman nima amaidoni wajen gimbiya zarah ko bakomai zan samu sauk’in wani abun, zabba’u har ta bud’e baki zatayi magana ganin rabi tanufo inda suke yasa tafasa.

 

 

bayan sallar magrib dada wani farin bedsheet d’in taba jakkadiya tace aje a shimfid’a part d’in yarima, jakkadiya kar6a tayi tare da rissinawa sannan tafito.

ko da taje part d’in yarima baya nan guards har sun hanata shiga saida tace dada ce ta aikota tagyara masa d’aki sannan suka barta.

ko da tashiga saida tak’ara gyara d’akin fess sannan tafito tanufi part d’in zarah, lokacin tana kishingid’e tana chart,

jakkadiya duk’awa tayi tagaishe da zarah cike da girmamawa, cikin sakin fuska zarah ta amsa mata, nan jakkadiya tak’ara saddar da kanta k’asa tace ranki yadad’e daman dada ce tace inzo intayaki kishirya sai inrakaki d’akin yarima.

zarah saida gabanta yafad’i jin an ambaci mutumin da kusan kwana biyu rabon da tasakasa a idanunta.

kuma ta fahimci abinda ake nufi, cikin ranta tace nashiga ukku.

muryar jakkadiya taji tace kigafarceni ranki yadad’e, idan kin ban izini sai inje inhad’a miki ruwan wanka.

zarah gyad’a mata kai kawai tayi nan jakkadiya tamik’e taje tahad’a ma zarah ruwan wanka.

zarah dakyar taje tayi wankan gabanta fad’uwa kawai yake duk tsoro da fargaba sun cikata,

bayan ta fito lotion mai k’amshi aka bata tashafa, sai humra da kulacca, powder kawai tashafa ma fuskarta sai lipstick, had’ad’ar night gown ce fara har k’asa aka bata tasaka, zarah ganin rigar shara-shara yasa tazaro ido tare da cewa a’a jakkadiya ba zan sa wannan ba canzamin wata.

murmushi jakkadiya tayi tace ranki yadad’e kar kidamu ai alk’yabba zaki d’aura a sama.
Zarah dai badan tasoba tahak’ura tabar rigar,

saida aka k’ara fesheta da performs sannan aka d’aura mata alk’yabba daga saman kayan nan tayi gwanin kyau.

duk’ar da kai jakkadiya tayi tace ranki yadad’e kinyi kyau, d’an guntun murmushi zarah tayi.
jakkadiya tace ranki yadad’e idan kin bamu izini zamu iya tafiya,

zarah gaba tawuce suna biye da ita a baya fuskarta kawai zaka kallah kagane tana cikin tashin hankali marar misaltuwa.

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_
?

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

 

_*Ina kuke team d’in zarah da kuma team d’in yarima suhail kuzo yau ranar takuce, lallai kunyi k’ok’ari sosai, saidai kash ni bana tare da ku, duk wanda yake tare da ni a team d’in Gimbiya sumayya toh yafito*_

 

Back to top button