Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 17

Sponsored Links

Page 1️⃣7️⃣

 

 

5:20am suka farka daga bacci sallah sukayi bayan sun gama azkar ne FANAN ta tashi ta haye gado taci gaba da bacci saboda bacci takeji sosai suhaima ce tafito tayi aikin gidan gaba Daya tamusu breakfast harsun fara karyawa mama tace “suhaima Ina fanan din take ” Takoma bacci cewar suhaima Jin hakan yasa Basu Kara magana ba sukaci gaba da karyawa , har karfe 11 tagota bata tashi ba time din su baba duk sun fita yarage daga mama SE suhaima da fanan Dake bacci. Tashi tayi daga bacci tana salati da Mika zuro kafanta kasa tayi gashin kanta duk ya babbaje toilet tanufa bayan 7mint tafito daure da towel gaban mirror tazo ta shafa man gashi tasa cum ta tajeshi ta hadasu guri Daya ta daure Mai Tashafa ajikinta sannan tadauko kaya wando ne falazo me manyan fulawa SE riga body hook ja tasa hula Baki bakaramin kyau tayi ba wayarta tadauka takunna ganin time din tayi “wai gaskiya yau nayi bacci sosai” falo tafito tasamu mama da suhaima gaishe da mama tayi kafin tazauna sallaman Amira sukaji tashigo gidan afalo tasamesu tagaida mama, besty ykk suhaima ya gajiya zama tayi suna hira dasu tana rike da yar karamar bakar jaka ahannunta kallon mama tayi tace ” mama dama nazo in tambayeki ne FANAN zata rakani gidan anty fati hajiya ce ta aikeni ” mama har cikin zuciyarta bataso FANAN tafita Amma kawai tace “to shikenan Amma karku Dade kunji ” to sukace suhaima ganin zasu tafi subartane yasa tace nima zani bari in dauko hijab dina” sallama sukawa mama suka fito su uku suna tafiya suna hira Amira ce tace ” bakusan meyafaru jiya ba hajiya ta aikeni cafene nayarda kudin duka dakyar na iya dawowa gida Dan banma San yazanyi ba” suhaima tace”wai garin Yaya haka katuwa Dake kika zubar da kudi ” lallai kam to ai tsautsayi bata yanda bata kamawa Kuma Allah yayi ba rabo bane ” cewar FANAN “ato fada mata de sukaci gaba da tafiya suna hira , wata corner suka sha aikuwa turus suka tsaya sakamakon abinda suka gani karnuka ne guda 3 suna kwance abinsu , tsoro ne yarufe su “wayyo Allah kare yazamuyi mu wuce nan Dan Allah gashi hanyar dayane “amira tagama magana tana rike hannun FANAN Da karfi FANAN cire takalmanta tayi tarike ahannun tafara fadin ” karkuja abinda zesa karnukan nan subimu muwuce kawai karma ma mu nuna mungansu kundeji Ina” takarasa maganarta tana kallonsu to shikenan tafiya sukeyi sanda sanda kamar wasu marasa gaskiya harsun kusa wucesu suhaima ta dantabo Amira, ke Amira kindauka karene aikuwa ihu tafasa tasa gudu karnukan na ganin haka suka fara haushi kan kace me sun bisu gudu sukeyi kamar kafarsu ze fita fanan kam da take rike da takalmanta ko juyawa batayi ba balle ta kallesu gaba Dayansu rabuwa sukayi kowa hanyanta daban tabi Ashe karnukan ma sundade da Dena binsu Basu sani ba Amira ce tajuya taga basa binta tsayawa tayi tana Maida numfashi hango bishiya tayi taje tazauna agun tana tunanin inasu FANAN sukayi, ke suhaima dataga gudun baze kaita ba kawai tafada wani gida suna ganin tashigo da gudu Suma sukashige daku nansu a tamanin can wata tace baiwar Allah meyake faruwa ne awajan cikin Maida numfashi tace “wlh karnuka ne suka bimu “sake Baki sukayi suna kallonta yanzu akan kare kike irin wannan gudun lallai kam sannunki fitowa tsakar gida sukayi Daya daga cikin matan gidan taleka waje tace” sunkoma bakowa awajen sallama tamusu tafito tana ta leke_leke tafiya tafarayi yanzu yazanyi innemo su Amira gashi nabar wayata agida yanke shawara tayi gwara in koma gida seyafi min takama hanyar gida , gudu takeyi kamar Wanda Zaki yake bi harta hau kan titi bata sani dukda titin shuru ba motoci, tafiya yakeyi a motor kamar walkiya tagilma wul‍♀️ ta gabanshi taci gaba da gudunta birki yataka Yana mamakin wacece haka take wannan uban gudun duk yanda akayi wasu ne suka biyota, bin bayanta yayi da mota harya iso kusa da ita da sauri yafito gashi taki tsayawa taku uku mekyau yayi yariko hijabinta yajawota baya aikuwa kamar wacce take Jira Takoma bayansa ta kankameshi tana fadin ” kataimakeni zasu kamani ” sa hannu yayi yajawota yadawo da ita gabanshi zaro ido yayi ganin itace ” ke Meye kikeyi akan titi kamar wata mahaukaciya kalan motar yabigeki ko ” Jin daddadar muryanshi ne yasa tadago ido cikin muryan tsoro tace ” Mr azaad wlh karnukane suka bimu zasu cije mu Dan Allah kataimakeni ” zuba mata ido kawai yayi tsaban takaici yarasama bakin magana yarinyar nan da kanwarshi ce irin dukan dazemata seta koma hankalinta yanzu dama duk uban gudun nan datakeyi WA karene ba abinda yakeyi Banda jefa mata harara gashi a ido de kamar wata me hankali Jan hannunta yayi yaje yabude motar yajefata ciki kafin yashigo yaja be tsaya Ako inaba SE akofar gidansu. Ahankali yace “saukamin a motar tunkafin in karkaryaki ” dasauri tasauko tana nagode Mr azaad kaceci rayuwata tana magana tana haki shiga gida tayi abunta , shide lamarin yarinyar nan mamaki yake bashi daga gani an sakalta tane tsaki yaja kafin yaja motar shi yayi gaba.

Tundaga tsakar gida takejin muryan Amira da suhaima suna bawa mama labarin abinda yafaru shigowa falon tayi tana galla musu harara ” kufa kwata kwata bakwajin magana seda nace mutafi ahankali Amma seda kukasa suka bimu” zama tayi taci gaba da Maida numfashi”nikam garin Yaya muka rabune kowa yadawo daban daban ” inji suhaima aikuwa dariya suka fashe dashi ba qaqqautawa seyanzu ma suke tuna irin gudun dasukayi dariya sukeyi kamar cikinsu zeyi ciwo hhhhhhhhh mama kanta abin yabata dariya dama tunda tagansu Daya bayan Daya jikinta yabata wani Abu Ashe karnuka ne suka fafuresu Kai ” to yanzu yabatun aikan hajiyar taku kunkai dinne?? mama ce take tambayarsu ” Ina mukaga takai aika ” nikam ai yau senayi jinyar kafata gaskiya FANAN tagama magana tana mamatsa kafanta

 

Gaskiya yau dog sunyi aiki

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

Story Written by (MRS ISHAM )

 

Da sunan Allah me rahama mejinkai Ina fatan kamar yanda nafara rubuta wannan littafin lfy yabani iKon gamawa lfy ameen

 

 

 

Wannan littafin sadaukarwa ne gareku fans Dina allah yabar zumunci

 

 

 

____________________________________________

 

Back to top button