Adandi Hausa NovelHausa Novels

Adandi 9

Sponsored Links

*9*

 

Ajiyar numfashi yayi tausayin ta na qara mamaye duk wani sajran guri dayayi saura a zuciyarsa yace “kiyi hqr My Samha yanzu yaushe zaki dawo makaranta semester ta fara nisa fah” lumshe idonta tayi ta kwanta sosai tace “ko yanzu kace zan taho My Abdul naji sauqi sosai kwana takwas kenan da aka sallamoni daga asibiti dama tsoron nazo naji lbrn dazai katsemin numfashi game dakai shine ya hanani dawowa amma yanzu tunda ka dawo nima very soon zan dawo insha Allahu”

 

Murmushin jin dadi taji yayi yace “is ok My Samha Ina kewarki wlh” dariya tayi me sauti tace “da gaske My Abdul kayi kewata oh gud! naji dadi sosai ka jirani nanda qarfe biyu zan shigo Idan na shigo zan kiraka kai nskeso ka fara ganina a Kano”suna murmushi sukayi sallama sukaajiye wayoyin ta miqe ta fara hada kayanta a trolly daidai lkcn Dad ya shigo yaga tana hada kaya yace “aa ya haka Ina zaki Pretty?”tanaci gaba da hada kayanta tace “Dad My Abdul ya dawo skull yanzu ya kirani yake fadamin wayoyinsa ne suka zube kuma ya rasa number ta tafiya zanyi dama lectures sunyi nisa”

 

Murmushi yayi ya zaro wayarsa yayi Mata transfer ta dubu dari biyar yace “ga wannan kiyi amfani dashi kafin wata ya qare maza taso na saukeki a airport” miqewa tayi ta sanya hijjab dinta ta sanya safa ta daura niqaf dinta sannan ta dauki handbag dinta ta fito a parlour ta tarar da Mamy babu wani sakin fuska sukayi sallama saboda ita Allah ya sani batason mu’amalar yartata da Abdallah gani takeyi wataran zaa wayi gari kwata² ta daina bin umarninsu saina Abdullah.

 

Dad yana sauketa a airport ta cire wayarta ta tura masa saqon tunatarwa vkan cewa tana hanya daya da hamsin jirginsu ya sauka a birnin dabo tana saukowa ta hangeshi tsaye jikin motarsa qirar HYUNDAI baqa takowa tayi a nutse shima nufota yayi duk da idanunta cikin glass yake kuma cikin hijjab take amma hakan bai hanasa ganin ramarta ba.
Trolly din ya karba a hanunta cikin sakin fuska yace “your are welcome My Samha” bude but din yayi ya sanya trolly din a ciki ya juya ya bude mata ta shiga shima ya shiga zuba mata ido yayi ya langwabar dakai gefe yace “My Samha kin rame sosai meyasa?” Murmushin yaqe tayi tace “nasha wahala sosai kuma ciwona yana da alaqa da rashinka hutunnan kwata² banji dadinsa ba” murmushinsa yayi na isa yace “meyasa?”ajiyar zuciya ta kumayi tace “saboda rashinka na kira wayarka yafi so million bata shiga”dariya yakeyi sosai duk damuwa da nauyin da yakeji a zuciyarsa sai yaji ya gushe suna tafe sunata hirarsu yana fada mata irin damuwar daya shiga saboda rashinta.

 

Saida ya kawota gdanta yayi horn megadin ya bude musu get suka shiga bude parlourn tayi da yake kaca² da qura ajiye trolly din yayi ya matsa kusa da ita yana kallonta ya zare niqaf din fuskarta ya sanya hanunsa ya tallafo fuskarta ya dora bakinsa saman nata yayi mata kiss me zafi da ya sanya dukkansu sukaji wani zummm a jikinsu yayi saurin sakin fuskarta yace “kyauta ce daga yaya zuwa ga qanwarsa” yana fadin haka ya fara dube tsintsiya ya dauko ya nade hanun rigarsa tayi saurin riqesa tace “akwai masu aiki zasuzo suyi” zamar da hanunta yayi daga nasa ya fara sharewa “don Allah ka bari yanzu Rahmah zata dawo daga skull zasu gyara komai” dagowa yayi yana sharce gumi yace “zanyima qanwata komai batare dana gaji ba inayin komai bisa aminci” zuwa tayi ta karbi tsintsiyar ta fara sharar kafin ta gama ya dauko mopper yanayi mata mopping tare da karkade mata duk wata qura saman TV stand ya hangi shisher tare da wasu kwalaben syrup.

 

Tsayawa yayi cikin tashin hankali ya kirata da wata razananniyar murya gabanta ne ya fadi ta juyo da sauri ganinsa dauke da da kwalaben ta nufesa da sauri ya daka Mata wata uwar tsawa yace “ubanme kikeyi da wadannan magungunan meye hadinki dasu?” Cikin mugun razana ta fara ja baya yana binta cikin fitar hayyaci ya damqi wuyanta yace “bazaki taba daina halinki ba bazaki taba canzawa ba Samha nayi miki iyakar abinda zanyi miki saboda haka ki fita dags rayuwata kowa yayi tasa…” Da sauri ta rufe masa baki da hanunta idanunta sunyo waje tace “wlh Azeem rabona da shisher ko cording nafi wata biyar My Abdul kada ka raba ruhina da naka saboda kai da soyayyarka na hqr da abubuwa da yawa na rabu da mutane da yawa My Abdul ka yarda dani duk tantirancina na baya bana qarya pls ka aminta dani nayi maka rantsuwa bazan iya rabuwa dakai ba inasonka Abdul inasonka don Allah ka amince dani zan iya sadaukar da duk wani farin cikina dominka……”

 

Dafe kuncinta tayi saboda saukar yatsunsa da taji daidai lkcn da Rams ta ya nunata da yatsansa yana huci yace “ashe ke mahaukaciya ce bansani ba ashe kidin bakida tunani Samha yanzu ni zaki yaudara da wadannan yan iskan kalaman naki na yan iska irinki dama dalilin da yasa kika shigo rayuwata kenan no wonder Ni dama nasan angulu bata jewar banza saboda haka na dade da shiryawa wannan ranar shawara daya zan baki tun lkc bai qure miki ba ki nemi ajinki dan iska irinki daidai da ke amma ni babu abinda zanyi dake na tsani halinki Samha na tsani karuwa fasiqa irinki wadda iliminta ya kasa amfanarta da komai sai lalacewa ni yanzu nayi soyayya dake nace nayi dawa nace da iyayena me kinaso nace musu ADANDI muka hadu dake kome? Shashashar banza da batasan kantaba kawai”

 

 

Yana kaiwa nan ya juya ya fice cikin tsananin damuwa da tashin hankali bin bayansa tayi da gudu tana kiran sunansa amma ko kallonta baiyi ba ya shige motarsa ya figeta da gudu ya fice daga gdan zubewa tayi a gurin ta dora hanunta aka ta rushe da wani irin kuka me tsuma zuciya tana furta “shikenan na rasashi Innanillahi wa innah ilaihir raji’un Allah Kaine ka jarabceni da son bawan nan naka Allah kasan komai kayimin maganin matsalata Allah kada ka bari na rasa rayuwata ta dalilinsa na shiga ukuna ni Samhanatu”

 

Daqyar Rams ta rarrasheta ta koma ciki ta fada kujera taci gaba da kukanta, cikin tausayawa Rams ta shafa inda yatsunsa suka kwanta radau a fuskarta tace “kiyi hqr Samha shi hqr me tadda rabone kuma guda gdan mokoki da’awa take inaji a jikina Abdullah zai soki Samha” kifa kanta tayi a cinyarta tsci gaba da kukanta me ban tausayi daqyar ta iya tashi ta shige dakinta ta shiga bathroom ta dauro alwala ta shimfida sallaya tayi sallar azahar tayi nafila tare da roqon Allah ya sassauta mata abinda takeji game da Abdullah ya yanke mata wahalarta ya zaba mata abinda yafi alkhairi sannan ta kwanta.

 

Kalma mafi muni a rayuwarta a kirata da karuwa ita Abdul ya kirata da ita to waye a duniya zai gasqata imaninta ya yarda ita ba karuwa bace waye zai yarda abinda tayi a baya ma qaddararta ce kuma ta tuba tuba me tsafta tayi alqawarin bazata sake ba har abada haka ta yini a kwance ko ruwa ta kasa sha cikin dare numfashinta ya sarqe saboda dama tanada Asma ga wani azabbaben ciwon kai daya hanata sukuni ga damuwa kuma dama ita kanta bana daukar damuwa ba sai farkawa tayi ta ganta a asibiti kwana biyu kenan.
Tunda ta farka take zubar da hawayen nadama tayi dana sanin wannan baqar rayuwa da tayi a baya wadda ta zame mata barazana ga cikar muradinta, Rahmah ce ta take fada mata take fada mata ta kira Abdul ta sanar dashi halin da take ciki yace babu ruwansa shine Mansoor da Ja’afar suka zo suka taimaka Mata suka kawota asibiti.
Wasu hawaye masu zafi suka zubo mata daidai lkcn da Mansoor ya turo qofar ya shigo ya zauna a kujerar dake jikin gadon yace.

 

“Sannu Samha ya jikin?” Bata iya tsayawa bashi amsa ba saima cewa da tayi “Mansoor don Allah Ina My Abdul Ina fatan yana cikin aminci” ba Mansoor ba hatta Ja’afar da Rahmah saida suka zubar da hawayen tausayinta ganin yanda suke kallonta ne yasata miqewa zaune cikin kuka tace “karku zargeni kuma don Allah wlh bansan sanda soyayyar sa ta fasa qirjina ta shiga ba kada kuma ku fahimceni baibai Mansoor so baqone da baya neman shawara lkcn shiga zuciya da ace so yana shawara kamar yanda Abdul yake iqirari da nima tun farko bazan bashi damar shiga zuciyata ba saboda na sani yafi qarfina ba ajina bane yanada qualities din dabai dace da karbar Samha tantiriya mara kunya a matsayin masoyiya ba amma duk da tantirancina wlh azeem ban taba aikata abu biyu ba lesbian da zina bana sonsu na tsanesu ku fada masa wlh niba karuwa bace saboda banida wata hujja ta kare kaina a gurin Abdul amma Allah shaidane na daina shaye² tun wata biyar da suka wucce kuma Ina addu’ar Allah ya qara nisantani dashi har abada”…….

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍*
[2/11, 2:59 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍: *_AD_*

 

*_Dont read this book if you are not married. Mature content contained in it. Reader discretion is advised. You read at your own risk._*

Back to top button