Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 50

Sponsored Links

*PAGE* 5⃣0⃣

Sultana sadiya tana nan zaune tana sak’e-sak’e a ranta a k’allah ta ci kusan minti goma sha biyar a haka, zuwan da baiwarta tayine yasa tabata izini tashigo.

Baiwar shigowa tayi d’auke da wata kula a hannunta cikin sauri tazube k’asa tana kwasar gaisuwa wajen sultana sadiya.

Sultana yatsine fuska tayi sannan ta amsa ciki-ciki, baiwar k’ara duk’ar da kanta tayi sannan tace ranki yadad’e na cika umurninki.

Sultana kallon kular tayi sannan tace bud’e mugani,
Cikin sauri tabud’e mata, tana addu’a cikin ranta Allah yasa kar sultana tace baiyiba dan tana tsoron wulak’ancinta.

Ta6e baki sultana tayi tace tashi kitafi.

Cike da jin dad’i baiwar tace toh ranki yadad’e nabarki lafiya, tana fad’in haka tamik’e cikin sauri tafita tabar d’akin.

Mik’ewa sultana sadiya tayi taje tad’auko maganin tazuba tamotse sannan tayi murmushi tace yau dai dole kicisa zarah, k’ulle maganin tayi tamaida ma’ajinsa sannan tadawo tasaka alkyabbarta tasa wata kuyangarta tad’aukar mata kular suka fito suka nufi 6angaren su zarah.

Zarah lokacin kwance take saman 3 seater tana ta juyi saboda wata irin yunwa da takeji gashi ta kasa cin komai, wayarta tad’auko takira yarima har tatsinke baiyi picking ba.

Haushine yakamata ta aje awar tana ta jan tsaki kad’an kad’an, bayan minti biyu sai ga kiransa ya shigo.

Zuba ma wayar ido tayi har tatsinke batare da tayi picking ba.

Daga chan 6angaren yarima da yafito wanka mamakine yakamasa ganin batayi picking ba kuma tsakanin kiran da tayi mai zuwa lokacin baifi 2 minutes ba, har zai k’ara kiranta a karo nabiyu sai chan 6angare d’aya na zuciyansa yace ba ajinka bane kak’ara kiranta, tsaki yaja ya aje wayan yacigaba da shirinsa ammah kuma duk da haka a cikin ransa yana jin ba dad’i dannewa kawai yakeyi dan shi abun har mamaki yake bashi ganin yadda yake ma zarah ko sumayya bata samun haka.

 

Lokacin da sultana sadiya ta iso part d’in zarah har a lokacin zarah tana kwance, ganin sultana sadiya yasa gabatanta yayi wani irin mummunan fad’uwa cikin ranta tsarin ubangiji take nema, koda sultana sadiya yau ma kamar jiya fuskarta a sake take.

Zarah cikin sauri tamik’e tsaye, murmushi tayi tare da d’an rissinawa tace ummah sannu da zuwa.

Sultana sadiya ma maida mata martanin murmushin tayi saida tazauna sannan tace yauwa zarah.

A k’asa zarah tazauna cikin girmamawa tagaisheta.

Amsa mata sultana sadiya tayi tace ya k’arfin jikin naki?

Zarah duk’ar da kanta tayi tace Alhmdllh ummah.

Kuyangar da sukazo tare da sultana sadiya duk’awa tayi tagaishe da zarah.

Cikin sakin fuska zarah ta amsa mata, nan sultana ta amshi kular tace tafita tajirata a waje, ahankali tace anganma ranki yadad’e sannan tamik’e cikin sauri tafita tabar d’akin.

Sultana sadiya kallonta tamaida ga zarah da take wasa da yatsun hannunta tace yau ma dai ga kwad’on na kawo miki dan nasan masu ciki akwaisu da kwad’ayi bare ma irin wad’annan kwad’on ganyukan…tak’arashe maganar tana ‘yar dariya.

Murmushi zarah tayi tace toh ummah nagode sosai.

Sultana sadiya tace haba zarah ai bakomai ke da sumayya duk d’aya nad’aukeku.

Zarah ahankali tace hakane ummah Allah yasaka da alkhairi.

Ameen, kibud’e kigani man,,,cewar sultana sadiya.

Zarah bata musaba tajanyo kular tabud’e saida tahad’iyi yawu saboda kwad’on ya burgeta kamar taitaci dan ganinsa yasa yunwar da takeji ta tashi, maidawa tayi tarufe takalli sultana sadiya da tatsareta da ido tace ummah ya yi min sosai kuma nagode Allah yasaka da alkhairi.

Murmushi sultana sadiya tayi tace kar kidamu zarah, kici kawai naga kamar yunwa kikeji.

Gaban zarah saida yafad’i jin sultana ta ce taci cikin ranta tace Allah yaimin tsari da abinda kuke shiryawa akaina, itama murmushin tayi tace ummah zanci sai zuwa anjima yanzu bana jin cin komai.

Fara’ar da take fuskar sultana sadiya raguwa tayi tace haba zarah yau fa dakaina nayi kwad’on kuma nayo tattaki nakawo miki ai bai dace kik’i ciba.

Zarah marairaicewa tayi tace ummah zan ci ai inason kwad’on kawai dai nafiso sai zuwa anjima.

Sultana sadiya cikin ranta tace wannan d’iyan akwai d’an banzan wayau anya batagane abinda nayimataba? murmushi sultana sadiya tayi tace hakane ammah ko kad’anne kid’anci kiji.

Zarah kallon sultana sadiya tayi, gyad’a mata kai sultana tayi alamun taci.

Zarah ido tazuba ma kwad’on tarasa yadda zatayi tana tsoron taci asamu matsala, d’ago kai tayi takalli sultana.

Sultana sadiya tasakar mata murmushi tace kici man.

Zarah har ta kai hannu zata d’iba sai ga yarima ya shigo da sallamarsa da mamaki yake kallon sultana sadiya itama ido tazuba masa tana kallonsu dan kwata-kwata bataji dad’in zuwansaba.

Zarah hamdala tayi tare da janye hannunta daga cikin kular.

Sultana sadiya murmushi tasakar mai tace ranka yadad’e ashe kana nan ai ban saniba da na aiko ankiraka mun gaisa.

Yarima batare da ya ce mata komai ba yasamu waje yazauna, kallon Zarah yayi da take zaune gaban kula sannan yamaida kallonsa ga sultana sadiya, ahankali kamar wanda baya son magana yace ummah barka da rana?

Sultana sadiya washe baki tayi tace yauwa yarima dafatan na sameku lafiya? Ai na ji labarine wajen dada ashe amaryarmu batada lafiya shine nazo ind’an dubata.

Jinjina kai kawai yarima yayi batare da yayi maganaba,

Haushine yakama sultana sadiya cikin ranta tace ka ji dai da abunka munafuki, chan sai tace ya jikin nata?

Murmushi yarima yayi yace Alhmdllh

Kallon zarah yayi da tatsaresa da ido har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa janye idonsa yayi yamaida ga kallon dramar da ake a TV d’inta.

Wajen shuru yayi ba wanda yak’ara magana, ammah gabad’aya yarima hankalinsa yana ga zarah dan ransa ya bashi dakyar inba wani abu sultana sadiya take son shiryawaba.

Sultana sadiya ko ta cika ta yi fam takaicinta shigowar da yarima yayi batare da tasamu zarah ta ci kokad’an bane, ji take kamar tarufe yarima da duka, ganin baida niyar basu waje yasa takalli zarah tasakar mata murmushi tace dota bari intashi intafi Allah yak’ara lafiya.

Itama zarah murmushin tayi sannan tace nagode ummah, sultana sadiya kallon yarima tayi tawurga ma k’eyarsa harara sannan tace ni na wuce.

Yarima batare da ya juyo ya kalletaba yace toh ummah mungode.

Wucewa sultana sadiya tayi zata fita cikin sauri zarah tamik’e tabi bayanta koda suka fito sultana sadiya kallon zarah tayi fuskarta d’auke da murmushi tace zarah kikoma kar kibar mijinki shi kad’ai.

Zarah duk’ar da kanta tayi cike da jin kunya tace toh ummah mungode sosai Allah yabada lada,

Sultana sadiya tace Ameen.

har zarah ta juya zata tafi sai jin sultana sadiya tayi ta kira sunanta, tsayawa zarah tayi tare da juyowa.
Murmushi sultana tasakar mata sannan tace dan Allah kitabbata kinci kwad’on nan ko kin d’an samu k’arfin jikinki dan daga ganin yanayinki yunwa kikeji, na san zai taimaka miki sosai idan kikaci kinga badad’i ace kina zama da yunwa.

Zarah murmushi itama tayi sannan tace toh ummah insha Allahu zan ci.

Cike da nuna kulawa sultana tace kin tabbata?

Zarah d’agamata kai tayi alamun eh.

Murmushin jin dad’i sultana sadiya tayi tace yauwa Allah yaimuku albarka.

Zarah tace Ameen ummah, nan suka k’ara bankwana sannan zarah tajuyo tadawo part d’inta, yarima har a lokacin yana zaune inda tabarsa, ahankali tace sannu da zuwa?

Yarima batare da ya kalletaba ya amsa

Wucewa tayi tad’auki kwad’on sai a lokacin yarima yajuyo yakalleta yace ina kika sami wannan abun?

Zarah kallon kular kwad’on tayi sannan tace ummah ce takawomin.

Ta6e baki yarima yayi sannan yace kinci?
Girgiza mai kai kawai tayi alamun a’a.

Janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace ban amince kiciba.

Zarah fuskarta d’auke da mamaki tace saboda mi?

Yarima juyowa yayi yawurga mata harara sannan yace saboda hakan nayi ra’ayi.

Shuru zarah tayi batace komai ba, cikin zuciyanta tace daman ai ba ci zanyiba, chan kuma tace anya yarima baisan wani abuba game da matarnan?

Muryar yarima taji ya ce meyasa da nakira wayanki bakiyi picking ba?

Zarah cikin zucinta tace kujini da mutum saikace ba ni nakirasa bai d’aukaba, kallonsa tayi taga idonsa yana a kan tv, ahankali tace bana kusa da wayanne.

mik’ewa yarima yayi yana kallonta yace akwai abinda kike buk’atane?

Zarah kallonsa tayi tace inason cin faten tsaki.

Toh ai zaki iya sa ma’aikatanki suyi miki ko?

Zarah gyad’amai kai tayi alamun eh.

Wucewa yarima yayi zaifita cak yaja yatsaya batare da ya juyoba yace wannan abun kije kizubar a shara sannan ko nan gaba ban amince a aiko miki wani abu kiciba, duk abinda kike buk’ata kisa ma’aikatanki suyi miki indai bakya iya yi dakanki.

Zarah cike da mamakin maganarsa tace Toh.

Wucewa yarima yayi yai tafiyarsa yabar zarah nan tsaye rik’e da kula.

Bayan ya fita Wucewa tayi tashek’a ma zogalen ruwa saida tawankesa tass sannan tak’ulle a leda takira wata kuyangarta tace taje tazubar a bola ammah kar tabari kowa yaganta.

Kuyangar duk’awa tayi tace Toh ranki yadad’e sannan tamik’e tafita.

Zarah komawa tayi tazauna tare da dafe kanta tana mamakin yarima tace anya baisan wani abuba game da halin su sultana? Chan kuma tatuna da maganar jakadiya da tafad’a mata cewa yarima ko iyayensa bai cika bari suna sanin ta cikinsaba saboda yana da zurfin ciki sosai, jinjina kai tayi sannan tamik’e taje tahad’o coffee dan ji tayi fatenma duk ya fita ranta.

Ahankali tasamu tasha coffeeen ba laifi sannan tajanyo remote tacanza channel tacigaba da kallonta, ahaka har aka kira magri tamik’e taje tad’auro alwallah.

 

Bayan sallar isha’i saida tayi karatun alk’ur’ani sannan tamik’e taje tashiga wanka,
bayan ta fito shafe jikinta tayi da lotions masu k’amshi, powder da lipstick kawai tashafa sannan tad’auko night gown d’inta iya cinya tasaka, gyara gashin kanta tayi tafeshe jikinta da perfumes alkyabbarta tad’auko tad’aura saman kayan jikinta saida takashe gloves d’d’in d’akin sannan tafita tasallami kuyanginta tawuce tanufi part d’in yarima.

Ko da tashiga parlournsa bakowa dan haka tawuce tanufi bedroom d’insa ahankali tabud’e k’ofar kwance tahangosa tsakan makeken gadonsa ya yi pillow da hannuwansa kansa yana kallon ceiling kamar mai tunani.

Maida k’ofan tayi tarufe saida tacire alkyabbarta sannan tataka tanufi wajen bed d’insa, tsaye tayi tana kallonsa har a lokacin bai juyo yakalletaba da alama ya yi nisa cikin tunanin da yake, ahankali tahau gadon takwantasaman jikinsa tare da d’aura kanta saman faffad’an k’irjinsa, yarima sai a lokacin yakallota.

Zarah murmushi tasakar mai tare da shafa d’an siririn sajen da yake a fuskarsa, da mamakinta sai gani tayi shima ya sakar mata tsadadden murmushinsa ahankali ya d’aura hannunsa a bayanta ya rungumeta zarah ido tazuba mai inda yarima shikuma yazuba ma k’irjinta ido, sai daga baya yamaido kallonsa a fuskarta yana kallon cikin idonta sai kuma chan yamaida idanuwansa yalumshe,

Zarah murmushi tayi sannan tazame jikinta daga nashi tamik’e dan takashe masu gloves, da mamakinta sai ji tayi yarima ya rik’o mata hannu, cikin sauri tajuyo takallesa shima d’in ita yake kallo daga sama har k’asa, sun dad’e a haka sai daga baya yajanyota tafad’o jikinsa yarungume ahankali kamar mai rad’a yace kinci abinci yau?

Zarah turo baki tayi kamar zatayi kuka tace na sha dai coffee,
hannunsa yakai yajenye mata riga yana shafar cikinta yace coffee ai ba abinci bane,

Zarah d’ago kai tayi takallesa cikin shagwa6a tace toh ai kaima shi kakesha da dare.

Yarima ido yazuba mata har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.

Zarah maida kanta tayi takwantar a kafad’ansa sannan cikin wata irin siga tace please dear inason zuwa gida gobe?

Yarima shuru yayi nad’an lokaci sannan yace me akeyi gidan?

Zarah murmushi tayi sannan tace gobe za’ayi baikon Aysha.

Da mamakinta sai gani tayi ya yi murmushi sannan yace toh Allah yakaimu kishirya sai insa akaiki,

Cike da jin dad’i zarah tad’ago takai mai wani hot kiss a baki cikin wani irin salo wanda yakusan rikita yarima, sannan cikin wata narkakkiyar muryarta tace nagode dear, yarima wani iri yaji danma ya dake bai nuna mataba, kashe mai ido d’aya tayi tace ka gama min komai dear,

Yarima hannu yakai yashafi wuyanta ahankali yace bakomai, daga nan yagangaro da hannunsa yazame mata d’an siririn hannun rigarta wanda yasa fiye da rabin k’irjinta yafito waje, zarah ido tazuba mai ganin yadda yakafeta da manyan idanunsa, hura mai ido tayi ahankali, lumshe idonsa yayi sannan yakai bakinsa a wuyanta yafara kissing d’inta cikin wani irin salo da yarikita zarah daga nan yagangaro zuwa k’irjinta gaba d’aya yasalu6e mata rigar da take jikinta, inda hannuwansa suka kasa tsayawa waje d’aya a jikinta, zarah ma ba’a barta a bayaba biye mashi tayi suka cigaba da faranta ma juna.

 

Bayan sun samu nutsu zarah a k’irjin yarima tashige tana mai kukan shagwa6a, yarima jin kukan nata yake har ransa duk yadda yaso yashare kasawa yayi ahankali yace zarah wai me kike ma kuka haka?

Zarah k’ara tura kanta tayi cikin k’irjinsa sannan tace ni bacci nakeji

Yarima batare da yayi maganaba yashiga d’an bubbuga mata baya kad’an-kad’an, cikin sanyayyar muryarsa yace sorry my princess.

Zarah d’ago kai tayi kallesa tace princess?

Yarima shuru yayi dan shi kansa baisan kalmar ta fito daga bakinsaba, ganin ta tsaresa da ido yasa yace Zarah kikwanta kiyi bacci,

Komawa Zarah tayi takwanta tana murmushi dan har cikin ranta ta ji dad’in sunan da yakirata da shi, ahankali tace ina ma yasoni, maida idanuwanta tayi talumshe tana ji yana shafa mata baya ahaka bacci yad’auketa

 

Da asuba saida yai wanka yad’auro alwallah sannan yatasheta yawuce masallaci,
kayanta tamaida sannan tafito takoma part d’inta a chan tayi wanka tai sallah sannan tabi lafiyar gado takwanta.

 

 

wajen 9am zarah tafarka tayi wanka tashirya cikin tsadadden lace d’inta black colour mai ratsin red, ya yi mata kyau sosai, bayan tagama shirinta cikin jin dad’i tafito tanufi part d’in yarima, a dining tasamesa zaune cikin shirinsa yana breakfast, wajensa tanufa tajawo kujerar da take opposite d’in tasa tazauna, kallonsa tayi taga ya tsareta da idanunsa, murmushi tasakar mai tare da kashe mai ido d’aya sannan tace ina kwana?

Yarima janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace lafiya, ya jikinki?

Langwa6e kai zarah tayi tare da 6ata fuska kamar zatayi kuka tace da d’an sauk’i ammah jiya ka ban wahala sosai.

Harara Yarima yawurga mata yacigaba da breakfast d’insa,
Zarah k’unshe dariyarta tayi tare da d’an duk’ewa tace wash cikina,
Bata ankaraba sai ganin Yarima tayi ya mik’e cikin sauri ya nufo inda take, rik’ota yayi yace lafiya? Meyasami cikin?

‘Dago kai zarah tayi takallesa tasakar mai murmushi tace kar kadamu dear kawai d’an motsamin yayi.

Ajiyar zuciya yarima yasafke sannan yajuya zai bar wajen, zarah ruk’o hannunsa tayi, yarima tsaye yayi batare da ya juyoba.

marairaicewa tayi tace kanason babynmu ammah bakason Zarah ko?

Yarima runtse idonsa yayi yana jin tambayartata taimai nauyi sosai a kai shi kansa baisan amsar tambayartataba, ahankali yazare hannunsa daga cikin nata sannan yace idan kin gama shirin kije zan sa akaiki gidan.

Zarah shuru tayi batace komai ba saima binsa tayi da kallo har yafita yabar d’akin,,,Zarah safke ajiyar zuciya tayi cike da tausayin kanta sannan tamik’e tashiga tagyara mai bedroom bayan ta gama tagyara mai parlour sannan tafita takoma part d’inta.

Veil d’inta red tad’auko tayafa tarik’o handbag d’inta kuyanginta biyu suka take mata baya sannan tafito, a gaban gidan taga motocin Yarima ukku jere da guards d’insa hud’u suna jiranta,

ganinta yasa sukayi sauri suka bud’e mata dank’areriyar motar da take tsakiya, Zarah tana shiga aka maida aka rufe, motar baya kuyanginta suka shiga inda guards d’in Yarima suka shiga suma nan akaja motocin ajere suka fita daga masarautar.

Koda suka isa unguwarsu Zarah wani irin nishad’i Zarah takeji dan rabonta da gida ta kwana biyu, a k’ofan gidansu akayi parking d’in motocin cikin sauri guards sukazo suka bud’e mata k’ofan tafito.

 

 

_Comment_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_Sak’on gaisuwa da jinjina agareki mrs oga, *Hauwa A Usman* nagode sosai da kulawan da nake samu daga gareki mummyn zarah, inaso kisani ko da page ko babu ke tadabance a wajena saidai ince Allah yabarmu tare Allah yasa zumuncinmu yad’aure har jikokinmu I hrt u more dear❤_

 

Back to top button