Hausa NovelsYarima Suhail Hausa Novel

Yarima Suhail 41

Sponsored Links

*PAGE* 4⃣1⃣

Wajen k’arfe biyu da taimakon wata kuyangarta zarah tasamu tayi wanka tai sallah ko da tayi lunch maganin tak’ara shafa ma k’afar sannan takwanta saman 3 seater nan bacci yayi awon gaba da ita.

Wajen k’arfe ukku yarima yadawo daga wajen aikinsa, bayan yayi wanka ya shirya yai lunch sannan yafito yanufi part d’in zarah dan yak’ara dubata, ko da yashiga ganinta yayi tana bacci ahankali yataka yaje wajen kujerar da take kwance a kanta, daga gefen k’afarta yatsaya nan yakai hannu yad’an tatta6a k’afar gani yayi kumburin ya sa6e kad’an yarage nan yad’auki maganin yak’ara shafa mata sannan yafita yabar d’akin.

Zarah ko da tafarka k’amshin turaren yarima ne da taji yashaida mata yazo d’akin murmushi tayi sannan tatashi tana bin bango tasamu har taje toilet tad’auro alwallar sallar la’asar, bayan ta fito shimfid’a darduma tayi daga zaune tayi sallah bayan ta gama ahankali tamik’e tana d’an k’engesawa har taje parlour tazauna.

 

Wajen 8 yarima yashiga part d’inta lokacin tana zaune saman gadonta cikin shirin baccinta tana tufke gashin kanta, ido tazuba mai har yazo gefenta yazauna, kallonta yayi sannan yad’auke kai ahankali yace ya k’afar ina fata dai tayi sauk’i?
Zarah marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace da dai sauk’i, yarima ido yazuba mata sai chan yad’auko k’afar yad’aura jikinsa yana dubawa batare da ya kalletaba yace ammah ai kumburin ya sa6e kuma zaki iya d’an takawa, jin shuru batayi maganaba yasa yad’ago kai yaga ta tsaresa da manyan idanuwanta, janye k’afar yayi daga jikinsa sannan yace kinsha magani?
Gyad’a mai kai tayi alamun eh,
Yarima mik’ewa yayi yace akwai abinda kike buk’ata ne?
Zarah k’wallah ce tacika mata ido tayi shuru,
Yarima har zai shareta yatafi sai kuma yaji baya iyawa, komawa yayi yazauna tare da rik’o hannunta yace ya akayi ne?
Zarah jikinsa tafad’a tare da rungumesa tana jin wani irin sonsa a cikin zuciyanta.
Lumshe idonsa yayi tare da kai hannu yana shafa gashin kanta, nan ta ida lafewa a jikinsa,
ahankali yajanyeta idanuwanta suna a rufe yakwantar da ita ya d’an jima yana kallon fuskarta chan kuma ko me yatuno cikin sauri yamik’e har ya juya zai tafi kawai sai ji yayi ta ruk’o masa hannu.

 

Cikin sauri yajuyo yakalleta wani irin tattausan murmushi zarah tasakar mai wanda yakusan zautasa sannan tasaki hannunsa tace sai dasafe.
Yarima kasa magana yayi dak’yar yaja k’afafunsa yafita yabar d’akin cike da kasala,

ahaka yakoma part d’insa yakwanta cike da kewarta dan duk jikinsa ya mutu jiyake kamar yakoma d’akinta yakwanta ko bakomai zai rungumeta yad’anji sauk’in abinda yakeji tare da ita ammah yasan jin kansa bazai barsa yayi hakanba, chan kuma sai yatashi zaune tare da dafe kansa yace me yake faruwa da nine? kar dai ace… dasauri yamik’e tsaye yafara zagaye d’akin yace hakan bazai ta6a kasancewa ba, ni dai nasan tausayinta nakeji, inba hakaba ya za’ayi inso yarinyar chan, me takeda shi da kamata *yarima suhail* zaiso? Nasan dai abu d’aya yasa nake zaune da ita saboda za6in iyayena ce ammah babu soyayyarta a tare da ni.
Nan sarautar tamotsa masa cikin rashin damuwa yakoma yakwantar tare da kashe gloves d’in d’akin, zarah ce kawai yake gani a duk juyin da zai yi saidai yaja tsaki ahaka yasamu bacci yad’aukesa.

 

A chan 6angaren zarah ma bayan yarima ya fita daga d’akin jawo pillow tayi tarungume a jikinta tare da lumshe idonta tana jinta cikin wani irin yanayi, chan kuma sai ga k’wallah tana fita daga idonta ahankali tafurta Allah kasa ma wannan bawan sona koda da k’wayar zarrane tausayin kantane yakamata dan ita kanta tasan yadda takeson yarima suhail batayi ma malam bello rabin sonba, tana acikin yanayin baccin yad’auketa.

 

Da asuba taji sauk’in k’afan sosai dan dakanta taje tayo alwallah batare da antaimaka mataba dan jitayi ta daina yi matazafi,
Bayan tayi sallah komawa tayi takwanta dan jiya ta dad’e bacci bai d’auketaba.

 

Wajen k’arfe goma yarima yagama shirinsa saida yayi breakfast sannan yafito yanufi part d’in zarah, yana shiga lokacin zarah ta fito daga wanka tana zaune tana shafa kallo d’aya yayi mata yajanye kai,

Zarah saida gabanta yafad’i dan ya yi mata wani irin kyau, ahankali tagaishesa,
Amsa mata yayi batare da ya kalletaba sannan yace ya k’afar dafatan yanzu tayi sauk’i?
Zarah shuru tayi,
Ahankali yarima yatako yazo saman gadon yazauna,
Zarah kamar jira take nan tad’auko k’afar tad’aura a jikinsa,
Kallonta yayi nan tad’aga mai gira tare da yin fari da ido tace duba kagani,

Yarima zuba mata ido yayi yana kallonta dan gaba d’aya ta rikitasa,
Zarah turo baki tayi tace kaduba min, yarima baisan ma tana yiba dan gaba d’aya hankalinsa ya tafi wani wajen daban, ganin haka yasa zarah tata6osa,
Firgit yayi,
murmushi tayi tace ya dai tunanin me kake?
Yarima janye idonsa yayi, cikin borin kunya tare da duba agogon hannunsa yace ina tunanin wani theater ne da zanyi a hospital yanzu, janye k’afar zarah yayi daga jikinsa tare da mik’ewa,
Zarah binsa tayi da kallo sannan tace am baka dubamin k’afarba,
Juyowa yayi yakalleta yace naga ai alamun tayi sauk’i, yana fad’in haka yajuya yayi tafiyarsa.

Zarah murmushi tayi sannan tatashi tad’auko kayanta tasaka sannan takoma parlour tayi breakfast.

 

Bayan tagama kallo takunna tana yi cike da jin dad’in da ita kanta tarasa namenene.

 

 

Yarima baibaro hospital ba sai dare saboda ranar suna clinic ga kuma meeting sunyi,
Bayan ya dawo yayi shirin bacci yakwanta sai kuma yaji yanaso yaje yaga zarah dan rabonsa da ita tun safe,
Shigowar sumayya ne yasa yad’ago kai cikin sauri yakalleta ganin itace yasa yajanye idonsa daga kallonta,

Gefensa tazo takwanta tare da shafa sajen da yake a fuskarsa tace yarimana ya kake?
Batare da ya bud’e idonsaba yace klau, kefa?
Rungumesa tayi sannan tace nima haka dear,
Murmushi kawai yayi.

Sumayya d’ago kai tayi takallesa cike da so tace ina sonka sosai masoyina,
Murmushi Yarima yayi tare da bud’e ido yakalleta har ya bud’e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.
Sumayya zuba masa ido tayi ahankali tace toh kaima kace kana sona dan tunda mukayi aure baka ta6a furtamin hakaba a k’arshema sai kayi min rashin adalci.

Fuskar Yarima cike da mamaki yace sumayya rashin adalcin me nayi miki?
Maida kanta tayi takwantar a k’irjinsa sannan tace na auren da kak’ara man.
Murmushi yayi yace k’arin aure shine rashin adalci sumayya?
Ta6e baki tayi sannan tace ammah ai baidace kayi min kishiyaba kuma karasa wadda zaka aura sai ‘yar talakkawa,
Cikin d’aga murya Yarima yace ya isa haka sumayya!!
Sumayya cike da mamaki tad’ago kai takallesa har ta bud’e baki zatayi magana wata uwar harara da yawurga mata yasa takoma takwanta cike da tsanar zarah dan tasan duk saboda itane yacanza mata har yake yi mata tsawa, cikin zuciyanta tace dasannu zan kawo k’arshen wannan matsalar, ahaka tayita sak’e-sak’e cikin ranta har Yarima yayi bacci yabarta sai daga baya itama baccin yad’auketa.

 

A 6angaren zarah tun tanasa ran Yarima zaizo dubata ammah har dare baizoba nan takaici yacikata tace daman nasan bai damu daniba nan k’wallah tashuga zuba a idonta cike da tausayin kanta.

 

 

 

_Comments_
*nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_

_*YARIMA SUHAIL*_

 

_*Written By~Sis Nerja’art*_

 

_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_

https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔

_~Masha Allah my dear *Sadiya Sidi Sa’id* ina tayaki murnar kammala novel d’inki mai suna *MAHAIFIYA* hak’ik’a kin baje mana basirarki a cikinsa mun ilmantu, mun nishad’antu sannan kuma mun wa’azantu, gaskiya na jinjina miki sosai da namijin k’ok’arin da kikayi, Abinda kika fad’a daidai Allah yabaki ladan kurakuren da suke ciki Allah yayafe miki, nagode sosai da soyayyarki agareni inaso kisani ina ji da ke har cikin zuciyana saidai ince Allah yabarmu tare~_

_*I dedicated this page to you Admin of Admins*_

_On your birthday, today I wish u a year with loads of fun, excitement nd beautiful memories. Happy Birthday Admin of Admins *Hayatu Baba Zubairu (Yaya Hayat)*_

Back to top button