Yarima Suhail 37
*PAGE* 3⃣7⃣
bayan ta gama shirin fitowa tayi kuyanginta biyu suka take mata baya zuwa turakar dada, da sallamarta tashiga parlourn lokacin sultana sadiya da wasu mata ukkune sai dada kawai a cikin parlourn.
daga dada sai matan kawai suka amsa mata ammah sultana sadiya inba hararaba babu abinda take wurga mata har zarah tazauna k’asa cike da girmamawa tagaishesu nan suka amsa mata,
d’aya daga cikin matanne tace sannu ‘yanmata kema kinzo kiga abun arzik’in ko?
sultana sadiya ce tayi karaf tace ko kuma tazo gulma ba, dada ce takalli sultana sadiya tace haba ‘yarnan ko baki ganetabane? matar yarima fa ce,
murmushi sultana sadiya tayi tace ammah dada bakiga cikinmu tazo tazaunaba ko nan akwai sa’anta?
dada rik’e baki tayi tace oh ni.
d’aya daga cikin matan ne tacema zarah matso kusa kiduba ashe surukace, murmushi zarah tayi sannan tamatso sama-sama taduba kayan tana jinjina kai dan k’arshen kud’i an kashesu a wajen anzuba kaya nagani nafad’a, kasa sakin jiki tayi ganin kallon da sultana sadiya takeyi mata dan haka tayi murmushi tace masha Allah, Allah yasa alkhairi,
gabad’ayansu suka amsa da Ameen sannan tayi musu sallama tamik’e tabar d’akin.
daga nan tawuce part d’in iyayen yarima, lokacin da tashiga parlourn ummi ce da rahma sai Aunty husna (yayar yarima) zaune suna tattaunawa, gaba d’ayansu suka amsa mata sallamar da tayi,
ummice cikin sakin fuska tace oyoyo daughter,
murmushi zarah tayi tare da zama k’asa cikin girmamawa tagaishe da ummi,nan ummi ta amsa mata, sannan tagaishe da matar da taga tana kallonta, Aunty husna amsa mata tayi fuska sake, rahma ce tamik’e tace ummi bari inshiga daga ciki induba d’unkunan da aka kawo min, zarah ahankali tace rahma ina wuni?
lafiya kawai tace sannan tawuce tashiga bedroom d’inta.
Aunty husna kallon ummi tayi tace ummi wannan fa ammah ban santaba ko?
murmushi ummi tayi tace zarah ce matar yarima itace wadda akayi bikkin baku k’asar,
sannan ummi tace zarah wannan itace yayar yarima itace husna.
d’ago kai zarah tayi tad’an kalleta sannan taduk’ar da kanta.
dariya Aunty husna tayi tace ji wani kicifi miye nawani satar kallona? toh ai kin ganni nadai fi mijinki kyau.
dariya ummi tayi tace kindai fi sa ammah yarimana yafiki.
zarah k’ara duk’ar da kanta tayi cike da jin kunya.
Aunty husna tace haba ummi bama za’a ta6a had’amuba wannan d’an naki da jin kansa yayi yawa ko aurennan fa sai a wajenku nakeji kuma ko da nayi masa magana jiya da muka dawo yace min dai zai kawota,
ummi murmushi tayi tace ai my son abun nasa sai shi.
husna da take kallon zarah tace zarah halan ku ma yana yi muku miskilancin?
girgiza kai kawai zarah tayi alamun a’a
dariya husna tayi sannan tace kina dai karesane, yanzu dai nice babbar yaya dan haka kisashi yakawoki gidana kimin wuni.
ahankali zarah tace toh Aunty husna.
mik’ewa husna tayi tace ummi bari inshiga wajen dada,
ummi tace toh shikenan sai kin fito,
kallon zarah tayi tace zarah kigaishe da kishiyar taki tunda ita batazo muka gaisaba ko da kema d’in da sunan wajen ummi kikazo.
murmushi zarah tayi tace Allah Aunty husna bansan kinzoba da tun d’azun nazo, wucewa husna tayi zata fita tace bawani nan.
bayan ta fita ummi kallon zarah tayi tace zarah kinshiga wajen su dada?
zarah cike da jin kunya tace eh ummi naje naga lefe Allah yasa alkhairi,
Ameen, sannan tamik’e tace ina zuwa,
bayan kamar minti ukku sai ga ummi tadawo da wata leda saida tazauna sannan tamik’a ma zarah tace ga anko d’inki daman d’azun nake cema rahma zan aiketa takaimiki, zara kar6a tayi tace toh ummi nagode, nan zarah tabud’e hand bag d’inta tad’auko cheque d’in da yarima yabata tace ummi ga wannan ya bamu muyi hidimar bikki.
murmushin jin dad’i ummi tayi tace aikam dai kin gode ki aje wajenki.
ummi daman na ashoben ne,
ummi murmushi tayi tace no ki aje, ni nasaimiki ashoben yanzu sai kishirya kije kikai d’inki ko kuma inturo miki madam zainab tazo ta aunaki dan ta iya d’inki sosai, sannan idan kina buk’atar wani abu sai kisa akaiki kisiyo.
zarah tace toh ummi nagode sosai Allah yak’ara girma da d’aukaka, Allah yak’ara rufa asiri.
ummi ta ji dad’in addu’an sosai tace Ameen zarah,
nan zarah tayi mata sallama tatashi takoma turakarsu,
daidai da zata shiga sai ga yarima da shaheed zasu fita, kallonta yarima yayi da mamakinta taji yace har kin dawo?
itama kallonsa tayi tace eh tare da gaishe da shaheed, murmushi shaheed yayi yace lafiya lou amaryarmu, kinga najanyo miki ango zamuje rabon IV,
murmushi zarah tayi tare da kallon yarima da yatsareta da ido, sannan tamaida kallonta ga shaheed tace ai kai ne angon yanzu, Allah yasa alkhairi ,Allah yasa ayi damu.
cikin jin dad’i shaheed yace Ameen amarya, gaskiya naji dad’in addu’an nan saidai ince Allah yabarki da angon naki,
zarah kallon yarima tayi nan sukayi ma juna murmushi, sannan yarima yace toh sarkin surutu yanzu dai kazo mutafi ko infasa zuwa, dasauri shaheed yayi gaba tare da cewa amarya sai mundawo,
toh zarah tace sannan takalli yarima da yake tafiya tace sai kun dawo dear,
cak yarima yatsaya daga tafiyar da yake batare da yajuyoba saida yad’anyi murmushi sannan yace Allah yasa,
itama zarah murmushin tayi sannan tawuce tashige gida.
da ta isa part d’inta zama tayi saman cushin nan tabud’e ledar tana kallon anko d’in, less ne brown colour, sai material d’in dinner maroon sai head d’in da za’a had’a silver ne, bayan tagama dubawa mik’ewa tayi takai ta adana sannan takwanta saman 3 seater tana kallo.
bayan sallar magrib madam zainab tazo har gida ta auna zarah nan zarah tabada kaya kala biyar ad’inka mata nan madam zainab tayi mata alk’awalin nan da kwana ukku zata kawo mata d’inkinta.
A chan 6angaren su yarima bayan sun gama kai I.V d’in ahanyarsu takomawa gida shaheed ne yake driving d’insu juyowa yayi yakalli yarima da yake jingine da sit d’in da yake, murmushi shaheed yayi yace ranka yadad’e duk gajiyarce hakan?
kallonsa yarima yayi yai murmushi cikin tsokana yace kawai ina tunanin auren shaheed ne kamar a mafarki.
dariya shaheed yayi yace to ya aka iya tunda kaima ka aje har biyu.
uhm shaheed kenan kaima kasan indai ason rainane da yanzu ban aje mace ko d’ayaba dan aure baya cikin plan d’ina a wannan lokacin kaduba fa kagani duka shekaruna nawa?
dariya shaheed yayi yace ai memartaba ya kyauta da yasa kayi aure tunda a k’arshe ji kayi mace d’aya bata isarka saida kak’ara da wata, ai kai gaba takaika.
tsaki yarima yaja yace kai dai kasani,
eh d’in ni nasani kuma harda kai cikin sanin nawa.
uhm da rabon inhana wani auren k’anwata.
wani irin burki shaheed yaja jikake k’iiitt ya tsaya, dasauri yajuyo yakalli yarima da shima yake kallonsa rik’o hannun yarima yayi yace dan Allah yayanmu kar kaimin haka wlh inason rahma kamar raina.
yarima fisge hannunsa yayi daga rik’on da shaheed yayi masa sannan yace indai kaimin biyayya toh, inkuma kacigaba da rainani sai insa afasa.
Allah yahuci zuciyar yaya yarima duk yadda kakeso haka za’ayi.
oya ja motar mutafi.
cikin sauri shaheed yaja motar yace angama ranka shidad’e,
dariya sukasa gaba d’ayansu sannan yarima yakoma yajingine kansa kamar bashine yagama yin dariya ba.
*WANSHE KARE*
yarima sawa yayi aka tara dukkan ma’aikatan gidan yabada kud’i da atamfofi aka raba ma mata, maza kuma yabada yadi da kud’i suma aka raba musu, nan sukaita murna suna shi masa albarka tare da yi masa addu’a.
lokacin da yarima yafito daga part d’insa zai fita gaba d’ayansu suka taru suka duk’a suna masa godia, murmushi kawai yarima yayi tare da d’aga musu hannu sannan yawuce.
Zarah tun da tatashi wani irin nishad’i takeji wanda ita kanta tarasa murnar me take.
kuyanginta da ma’aikatanta sukazo cikin murna suka nuna mata kyautan da yarima yayi musu tare da ce mata tak’ara yi musu godia wajen yarima, murmushin jin dad’i tayi dan har cikin ranta taji dad’in abinda yarima yayi.
yarima sawa yayi aka kawo ma rahma pics d’in design d’in gado da kujeru nan taza6a yace aje ayi mata room nd bedroom shine gudunmawarsa, ba rahma ba hatta su ummi sunji dad’i nan sukaita shimasa albarka.
6angaren shaheed ma yarima d’aukarsa yayi a mota yakaisa shagon d’inkinsa aka aunasa nan akace ma yarima zuwa jibi za’a kawo masa kayan, shidai shaheed mamakin yarima kawai yake dan baisan lokacin da yabada ayi masa d’inkuna ba, ko da yatambayi yarima shuru yayi bai tankasaba ganin haka yasa shaheed shima yaja bakinsa yayi shuru.
da dare zarah bayan tayi wanka saida tashafe jikinta da mayuka masu k’amshi da humra sannan tad’auki ‘yar night gown d’inta wadda iyakarta gwiwa tasaka mai hannun vest, sannan tafeshe jikinta da turaruka kallon agogo tayi taga goma saura dan haka tad’auki hijab d’inta har k’asa tasaka sannan tafito tanufi part d’in yarima,
tana shiga a parlour tacire hijab d’in talinke ta aje sannan tabaza gashinta yasafka a kafad’unta, bud’e bedroom d’in tayi tashiga,
yarima da yake zaune saman gadonsa yana dannar wayarsa jin anbud’e k’ofa yasa yamaida kallonsa ga k’ofar, tunda yakafeta da ido bai d’aukeba.
zarah cikin takunta mai jan aji tatako tanufo gadon fuskarta d’auke da murmushi tahau, har a lokacin idanuwan yarima suna a kanta,
hura masa ido zarah tayi nan yak’yafta cikin sauri yajanye fuskarsa daga kallonta.
tallabo fuskarsa zarah tayi suka kalli juna nan tasakar masa murmushi, yarima zuba mata ido yayi sai chan yace ba dai haka kika tafoba,
shagwa6e fuska zarah tayi tace ya za’ayi intafo haka bayan nasan da mutane a gidan, gaban mijina kawai nazo haka.
yarima bakinta yake kallo tunda tafara maganar yanayinin yadda takeyi ne yaburgesa, fari zarah tayi masa da ido tare da cewa kallon fa?
janye idonsa yayi daga kallonta tare da ta6e baki sannan yacigaba da dannar wayarsa, zarah fisge wayar tayi daga hannunsa,
kallonta yayi yace ya haka? kibani akwai abinda nakeson yi.
bayanta tamaida hannuwanta tare da mak’e kafad’a tace nak’i,
murmushi yayi tare da kwanciya yalumshe idonsa, zarah zuba masa ido tayi tana murmushi sai chan takwanta itama saman k’irjinsa nan gashin kanta yarufe masa fuska.
fuskarsa d’auke da murmushi batare da ya bud’e idonsaba yajanye gashin, zarah d’agowa tayi tana k’are ma fuskarsa kallo nan k’irjinta yafara bugawa ahankali takai bakinta cikin nasa.
yarima kamar daman jira yake nan yacafke batare da ya bud’e idonsaba sukacigaba da kissing d’in junansu, kowa nuna k’arshen k’warewarsa yake nan duk suka fita hayyacinsu daga nan kid’i yacanza, dan yarima baibar zarah ba saida yabata wahala sosai shi kansa yasan ya wahalar da ita jurewa kawai tayi.
bayan komai ya lafa zarah jawo blanket tayi tarufe jikinta cikin d’an hasken da yake d’akin takai dubanta ga yarima da yake kwance idanuwansa a lumshe ammah fuskarsa d’auke da murmushi, saman jikinsa takoma takwanta tare da gyara musu rufin blanket,
ahankali taji yarima ya rungumeta tare da jan ajiyar zuciya,
k’ara gyara kwanciyarta tayi tanajin wani irin sanyi a ranta ahaka bacci yayi awon gaba dasu kowa da abinda yake sak’awa cikin ransa.
kiran sallar farkone yatashi yarima daga baccin da yake ahankali yajanye zarah daga jikinsa yazuba mata ido yana ganin yadda take baccinta a nutse ya dad’e yana kallonta sai kuma chan yajanye idonsa tare da mik’ewa yanufi toilet.
bayan ya fito saida yashirya sannan yaje yashiga tashinta, dakyar zarah tabud’e idanuwanta sannan tamaida talumshe, ahankali yarima yace kitashi lokacin sallah yayi.
juyar da fuskarta tayi gefe d’aya cike da jin kunya sannan tace umhum natashi.
jin haka yasa yarima yawuce yafita yatafi masallaci.
saida zarah taji fitarsa sannan tamik’e dak’yar tanufi toilet saida tagasa jikinta sannan tayi wankan tsarki tare da d’aura alwallah, bayan tafito rigarta da hijab tasaka nan tagabatar da sallar asuba.
bayan tagama a nan saman darduma tanad’e nan bacci yayi awon gaba da ita.
yarima ma koda yadawo daga masallaci bai shiga bedroom d’inba a parlour saman 3 seater yayi kwanciyarsa.
sai wajen k’arfe takwas yafarka nan yatashi yanufi bedroom, koda yashiga a saman darduma yaga zarah kwance tana bacci nan yawuce yashige toilet.
bayan ya fito a gurguje yashirya sannan yad’auki wayarsa da key d’in mota yafita saboda akwai patient d’in da zai ma operation nan da ‘yan mintuna.
zarah ko da tafarka kallon agogo tayi ganin har 10:30am yasa cikin sauri tamik’e ganin ba yarima saman gadon yasa tafito parlour nan ma wayam cikin ranta tace Allah yasa wanka yakw ba fita yayiba.
har tagyara bedroom d’in ammah bataji k’arar ruwaba dan haka taje taduba toilet bakowa nan tagane yarima baya nan bataji dad’iba dan tasan dak’yar idan yayi breakfast.
saida tagyara masa ko’ina fes sannan tafita tabar d’akin takoma part d’inta
yarima sai wajen 4pm yadawo gida
bayan yayi wanka kwanciya yayi saman gadonsa dan yahuta saboda a gajiye yake yau.
gimbiya sumayya ce tashigo fuskarta d’auke da murmushi tace ashe kadawo? yarima baice mata komaiba nan taje tahau gadon takwanta gefe tare da tsaresa da surutu shi dai yarima idanuwansa a lumshe suke bai tanka mataba domin surutun da take duk ya ishesa, ganin haka yasa gimbiya sumayya tad’anyi murmushi tace sweetheart na isheka da surutune? yarima batare da ya bud’e idonsaba yace wani abu kike buk’ata?
haushi yakama gimbiya sumayya ganin kusan tambayar da yarima yake mata kenan idan yaga tana shige masa ko da kusan hakane ammah bakowane lokaci bane sai tana buk’atar wani abuba.
ahankali tace haba yarima meyasa kake min haka yanzu banda ikon zuwa wajenka sai idan ina buk’atar wani abu?
yarima banza yayi mata baice komai ba, bud’e k’ofar da akayine yasa duk suka maida hankalinsu ga k’ofar,
zarah tsaye tayi tana kallonsu cike da mamaki kishine k’arara yabayyana a fuskarta ganin sumayya wajen yarima alhali kuma duty d’intane, yarima cikin rashin damuwa yamaida idanuwansa yalumshe,
inda sumayya itakuma take ta wurga ma zarah harara kamar idanuwan zasu fito. chan sai tace malama lafiya zakizo kiyi ma mutane tsaye kina kallonsu?
Zarah abun ya bata haushi ganin sumayya tana nema taraina mata wayau wannan shine adoki mutum sannan ahanasa kuka, d’aure fuska zarah tayi tace malama ba wajenki nazoba wajen mijina nazo dan haka babu ruwanki, zarah takawa tayi ta isa wajen gadon tahau d’ayan gefen yarima takwanta tare da d’aura fuskarta saman k’irjinsa tace dear ashe kadawo, bacci zakayi?
yarima shuru yayi bai tanka taba ganin haka yasa takai hannu tafara shafar fuskarsa cikin wani irin siga.
haushine yakama sumayya ganin yarinya k’arama tana neman taraina mata hankali dan haka itama komawa tayi takwanta tana shafar gashin da yake kwance saman k’irjinsa, nan ita da zarah suka dinga wurga ma junansu harara,
cike da jin haushi zarah takai bakinta ga na yarima tafara kissing d’insa, sumayya cikin 6acin rai tace kam ke ni zaki nuna ma tashanci?
ahankali zarah tazare bakinta daga cikin na yarima tayi murmushi tace Auntyna kin mance yau duty na ne?
yarima duk yana jinsu yayi shuru yakyalesu.
harara sumayya tawurga mata tare da cewa uban dutynki ke har kin isa daga kin samu antaimaka an aureki shine zaki zo kinuna min kema daidai kike da ni.
yarima bud’e idonsa yayi tare da tashi zaune fuskarsa a d’aure yace bakuda hankali zakuzo min d’aki ku duka biyun kukwanta min?
sumayya cike da nuna ita ta isa tace ai itace tashigo dan neman rigima
zarah tace ammah ai yau duty nane tayi min shishigi
yarima fuskarsa babu walwala yace kutashi kufitar min daga d’aki.
sumayya cike da isa tace ammah ai…..wani mugun kallo da yawurga mata yasa tayi shuru.
ganin haka yasa zarah tasafka daga saman gadon tana kumbure-kumbure nan itama sumayya tasafka.
yarima hanya yanuna musu da hannunsa fuskarsa ba alamun wasa ganin haka yasa gaba d’ayansu suka fita daga d’akin kowa yana hararar d’an uwansa.
gimbiya sumayya tace ke wlh idan kina min shishigi sai na miki dukan da bazaki iya tashiba saboda tare da yarima kikazo kika sameni.
inma banda abun talaka da yasamu waje sai yanuna yafi mai gida zak’ewa.
murmushi zarah tayi tace kar kidamu miji dai kike tak’ama da shi toh nima ina tak’ama da hakan sannan kuma arzik’i na Allah ne shi yakeba wanda yaso yahana wanda yaso dan haka yakamata kisan haka, nabarki lafiya gimbiya sumayya tana gama fad’in hakan taficce tabar sumayya tsaye domin ta kashe mata baki bata d’auka zarah zata iya magana hakaba.
sannan daga baya itama taficce tana sak’e-sak’e cikin ranta.
yarima suna fita yakoma yakwanta tare da dafe kansa yana mamakin irin halin wad’annan mata nasa da kwata-kwata basu jituwa indai za’a had’u sau goma toh sai anyi fad’a sau goma koda ya san laifin duk na sumayya ne.
Zarah tana komawa d’akinta batabi takan kuyangintaba tashige bedroom tafad’a saman gado nan tafara wani irin kuka haushin sumayyane yacikata da tsananin kishin *yarima suhail* tabbas ayanzu tasan tana ma yarima wani irin so da baya misultuwa, tabbas ta yarda da maganar malam bello da yace zata so mijinta saidai idan bai amsa sunan namijiba.
A ranar haka tasha kukanta batada walwala ko kad’an kuyangi da bayinta duk sunyi mamakin ganinta acikin wannan yanayi.
sumayya ma ko da tashiga d’akinta korar kowa tayi tafad’a saman gadonta tajanyo wayarta takira ummanta
ummah bugu biyu tad’auka tun kan tayi magana sumayya cikin fushi tace ummah nagaji nagaji wlh natsani inbud’e idona inga yarinyar chan cikin gidan nan.
ummah cike da damuwa tace me yake faruwane?
sumayya tace ummah wlh so take tashiga tsakanina da mijina sai wani shishige ma yarima takeyi yau ma muna tare tazo tatak’uleni rigima ak’arshe yarima yakoramu gaba d’ayanmu wlh ummah zan iya kashe yarinyar nan akan yarima.
ummah itama cikin 6acin rai tace wlh ba’ayi yarinyar da zatazo tahanaki sak’ewa a gidan mijinkiba dole ma ne ind’auki mataki ammah kidaina maganar kisa kibari abi komai a sannu.
sumayya tace ummah wlh yarinyar nan batada kunya
sultana sadiya tace koma dai menene kema harda laifinki sumayya kawai dai ina goyon bayankine.
sumayya d’if takashe wayarta cike da jin haushin ummah tunda itama tace tana da laifi.
wayar zinat takira har saida takusan tsinkewa sannan zinat tad’aga tun kan tayi magana sumayya tace ke wai sai kinga dama zaki d’aga waya
zinat daga chan 6angaren tace kiyi hak’uri dear yanzu dai meke faruwa naji muryarki kamar kina cikin fushi.
sumayya tace hmm zinat bansan ya zanyiba wlh yarinyar chan ce tatisoni gaba.
zinat tace ban fahimtaba meyake faruwa?
sumayya kwashe abunda yafaru tsakaninsu tayi tas Tafad’a ma zinat.
zinat dariya tashiga yi har sumayya tafara k’ulewa…
_Comments_
*nd*
_Share_
_Sis Nerja’art✍_
_*YARIMA SUHAIL*_
_*Written By~Sis Nerja’art*_
_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_
https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/
*INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE HEART TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS CURDLES GIGGLES AND MARRIEGE THINK
*JUST GIVE US FOLLOW….*✔
_Wannan page d’in mallakinkune *Zahra nd pinky novel* nabakushi a kyauta, sak’on gaisuwa gareka *S Dan muri* nagode sosai da soyayyarku agareni_