Hausa NovelsNi da Patient Dina Hausa Novel

Ni da Patient Dina Book 1 Page 30

Sponsored Links

Page 3️⃣0️⃣

 

Gaba daya garin gombe da ketare ta amsa da wannan labaran kowa se tofa albarkacin bakinsa yakeyi wasu sun yarda wasu basu yarda ba. TikTok, YouTube, Facebook, Twitter, Instagram, Vidmate, duk wani kafafen sada zumunta ta amsa social media kowa se Allah wadai da halin azaad da fanan yakeyi ko ina kashiga labarin dazakaji yana tashi kenan.

Su abba suna gidansu fanan har karfe 2 na rana dukkansu abin duniya yadamesu har wata har rama sukayi har izuwa wannan lokacin fanan na kunshe adaki bakaramin tausayi tabasu ba ba ruwa ba abinci gaba daya tafita a hayyacinta tawani rame kamar wacce tayi jinyar wata daya fuskan nan yayi fayau kamar ba jini ajikinta tana zaune akan dadduma gashin nan buzu_buzu takafe waje daya da ido.

Yan uwan ummi a dubai sekira sukeyi suna kwantar musu da hankali haka masarautar gombe kakansu azaad yakira abba awaya yake tambayarsa ina azaad yace “yana gida sukuma suna gidansu yarinyar” kafin yakatse kiran.

 

Jingine yake ajikin makeken gadon dakinshi da alamun sallah ya idar yau yasamu yatashi daga baccin yabiya duka sallolin da akebinshi gaba daya yatashi daga azaad din dana sani yakoma wani daban duk wanda yakalli fuskarshi seya mugun razana da firgita dan yau ne ainihin true color dinshi yabayyana komawa yayi kamar boss, waya yadaga yasa akunne kafin yace ” spider inason kafin nan da 1hr kasamonin wayanda sukayi wannan hotunan ” yana gama magana kitt yakashe wayarsa mikewa yayi yabude wani locker dake dakin yafito da bindiga piston yasa abayan trouser dinshi fitowa yayi falon kasa fawwaz da areef se zeenat ne afalon suna zaune suna jimami sukaga fitowarshi ganinshi awannan suffar yasa babu wanda yayi kwakwaran motsi haryakai bakin kofar falo zefita wayarshi kirar iPhone 16 tafara ringing dakatawa yayi yaciro wayar yasa akunne spider ne yakirashi yaname sanar dashi ankama daya daga cikin mutanen dasuke dasa hannu, budan bakin Mr azaad yace” beat the hell out of him before na iso ” kittt yakashe yafita securities dinsa ne dukansu sukazo suna gaidashi ko kallonsu beyiba faisal ne jiki na rawa yayi saurin karban car keys din awajan driver yabude mishi murfin motar shiga azaad yayi yazauna tada motar faisal yayi gudu_gudu baba me gadi yabude musu gate suka fita duk yan aikin gidan susan abinda yake faruwa bakaramin tausayin me gidan nasu sukeyiba domin su ko aina zasu iyabada shaida akan Mr azaad baze taba aikata haka ba.

Driving faisal yakeyi amma besan inazasuje ba gashi yana tsoron tambayar ogan nashi, ganin shuru baze kaisu ko inaba yasa murya nadan rawa yace ” sir inazamuje” ciki_ciki azaad yace ” my jungle” okay faisal yace dan yasan wajan nan ne azaad yakeda bosawan yaranshi sannan anan ne duk wanda yamishi laifi yakesa adauko shi yamishi mugun hukunci daga bisani yamikashi hannun yan sanda. dajine daya amsa sunanshi daji bazaka taba tunanin akwai bil adama aciki ba wani tankamemen gidane nahango daga nesa ga wasu Yan daba se buge buge sukeyi kamar wani abu suke hadawa ga wasu agefe se gasa rago sukeyi dukkansu duk wanda kika kalla kinsan ainihin cikekken dan dabane agun kirar jikinsu ma kadai zebaka labari , tunkafin motar takaraso sukayi cincirindo suna jira isowar boss dinsu motar na tsayawa wani daga cikinsu yabude mishi kofa wani yazo da lema yana rike mishi dashi dan kar rana yatabashi wani ne yazo kamar wani basamude yazo yatsaya agaban azaad kansa akasa yace ” boss can I help you with the shirt” gyada mishi kai yayi nan take yasa hannu yaballe mishi botiran riganshi yakoma gefe yatsaya cire rigan azaad yayi gaba daya nan take wannan kirar nasa yabayyana ga tattoo dake jikinshi tafiya yakeyi cike da izza yashiga ciki, sekwasan gaisuwa sukeyi wani bangare yanufa daga nesa babu abinda nakeji daya wuce ihu da kururuwa shiga wajan yayi wani matashine wanda akalla zekai shekara 27 zaune akan kujeran karfe anmishi daurin goro sunmishi mugun duka jikinshi se fitar da jini yakeyi ihu yakeyi kamar wanda ake zarewa rai juyawa azaad yayi yakalli spider nan take yakawo mishi kujera asetin matashin zama azaad yayi yasa hannu yadago fuskanshi agalabaice yake kallonshi dakyar ya iya furta “dan Allah ranka yadade kamin rai kayi hakuri” wani miskilin murmushi azaad yayi kafin yace” waya saka wannan aikin” shuru yayi bece komai ba alamar baze fada ba , dungule hannun azaad yayi nan take jijiyoyin hannunsa suka fito yakai mishi naushi afuska seda hakwaranshi guda shida suka zube hanci da baki suka fashe se jini suke zubarwa juyawa yayi ga spider yace ” ban wuka” dasauri spider yaciro wuka a kugunshi yabashi yana karba beyi wata_ wata ba ya caka mishi acinya razanenne ihu yasa seda gidan ya amsa,daga wukan yayi zesake caka masa yayi saurin fadin” kamin rai wayyo zan fada ! Zan fada maka wayanda suka sani ” shafa kanshi azaad yayi yace ” good boy maza fada inajinka” yana hakin wahala yace ” Alh Ibrahim tijjani ne yasani ! Nafada maka dan Allah kabarni intafi ” tunda ya ambaci sunan alh Ibrahim tijjani azaad yaketa girgiza kai dan yasan babu wanda zasu mishi haka sesu amma yafison ya tabbatar tukun nan, lallai alh Ibrahim yatabo ruwan dafa kansa amma yanzu yasan kafin gaskiya tafito seyadau lokaci yana cikin wannan tunanin wayarshi tayi ringing dubawa yayi yaga abba ne ke kiransa kamar baze daga ba can kuma yadaga yasa akunne yace ” hello” ajiyar zuciya abba yayi jin yadawo normal dan dama faisal ne yace mishi yafarka, cikeda bada umarni abba yace mishi ” duk abinda kakeyi kabari kazo gidansu fatima” tofa tunani yafarayi wacece kuma fatima kamar baze tambayi abba ba can Kuma murya ashake kamar wanda akawa dole yace ” wacece kuma fatima” rike baki abba yayi kamar wanda yake gabanshi daga karshe yanisa yace ” to nurse dinka yanzu base anjuma ba kazo gidansu” seyanzu yatuna da ita tare aka musu qazafi tausayinta yaji ganin ita macece sun bata mata suna gwarashi namijine amma itafa sun cuci rayuwarta tabbas bazetaba barinsu susha iska medadi ba sesunyi danasani aikata hakan mikewa yayi su spider suka bishi abaya.

Almost an hour ne yakawosu gidan shigowa yayi compound din gidan qin shiga yayi dukda yanajin muryoyinsu ganin tsayuwar yayi yawa yasa faisal yin sallama fitowa ya Usman yayi yagansu mikawa azaad hannu yayi sukayi musabaha da yamikawa faisal Bismillah yamusu akan sushigo , shiga sukayi zama yayi akujera mezaman mutum daya kasa_kasa yabude baki yagaidasu amsawa duk sukayi suna jajanta abinda yafaru shide kala bece musu ba amma sunbashi tausayi sabodashi ne rayuwar yarsu yake kokarin tarwatsewa . Idonshi akasa yafara bin mutanen dakin daya bayan daya yana kallonsu ganin beganta afalon bane yayi tunanin ko tana daki.
____kallonsa Abba yayi yace ” azaad fatima tunjiya data samu labarin abinda yafaru takulle kanta adaki haryanzu bata bude ba tunda tashiga baakarajin motsinta ba dan Allah kozakayi naka kokarin kozata bude kofar!?”Abba yagama mgn yana nuna mishi kofar dakin, Duk tsareshi da ido sukayi suna sonjin mezece, harkusan 10mint bece komai ba harsun cire rai akan zebasu amsa,mikewa yayi yaje bakin kofar yatsaya yamarasa mezece cikin sexy voice yace ” Fatima kibude zamuyi magana” shuru sukaji can kamar 2mint yasake cewa ” Fatima kibude zamuyi magana ” kamar amafarki takejin muryansa yana mata gizo_gizo akunne kara kasa kunne tayi kozata sakeji can tasakejin yayi magana dasauri ta dago kanta tana kallon jikin kofar dakyar ta iya mikewa kamar zata fadi tangal_tangal tayi kamar zata fadi tasamu tatsaya dukda dishi_dishi take kallon komai nadakin tsaban yanda tagalabaita tun dogon rigan jiyane ajikinta haryanzu gaba daya baa ganin fuskanta saboda yanda gashin nata yabazu sannu ahankali take taka kafarta hartakai bakin kofan without touching the door shi dakanshi yabude kansa , jin Karar kofa ne yasashi dagowa su baba duk tasowa sukayi suka tsaya agefen azaad suna kallonta takawa yayi kusa da ita yasa hannu yatattare gashinta yamaidasu baya, seda yaji dam akirjinshi bashi kadaiba hartasu Abba gaba dayansu sun firgita daganin yanayin fanan gaba daya lokaci daya tazafge kamar wacce tayi jinya fuskan nan yakumbura idonta yakara girma gaba daya tafita a hayyacinta, mama kwalla fal a idonta tace ” innalillahi wainna ilaijiraji unnn ji yanda sukasa yata tashiga wani hali wallahi Allah seya saka mata ” matsowa tayi daff da azaad dayake tsaye agabanta kallon jikin idon juna sukeyi babu ko kyaftawa hannunta tasa tacakumi kwalar rigarshi cikin muryan daya galabaita tace ” Mr azaad inason kafadamin mena musu meye natsare musu meye hadina dasu dazasumin haka” cikin kara zare ido tacigaba da fadin” kasan mesu kace akaina cewa sukayi wai ni karuwa ce mazinaciya nasha zubar da ciki, wai ni dadironka ce kana kwaciya dani meye na aikata aduniya dana cancanci wannan qazafin meye na aikata musu da zafi haka” takarasa maganar da karfi tana jijjigashi, bakaramin dauriya sukayi ba mazan kamar su zubar da kwalla sukeji ummi kam gaba daya tausayin fanan yakamata tarasa ma yazatayi mama se share hawaye takeyi , ba abinda kakeji afalon se sheshekan kukansu Amira, suhaima da auta.
__ sa hannunshi yayi duka biyu yatallafo kumatunta cikin husky voice yace ” kifadi duk wani abinda ke ranki domin bakiyi magana da kowa ba kiyi kuka son ranki zakifi jin raguwar radadin dake kunshe azuciyarki ” kallonshi takeyi ido cikin ido kamar me neman wani abu gyada mata kai yayi kafin yakara maimaita” kina bukatar kuka ! Kiyi kuka ” nan take hawaye yafara gangarowa daga idonta kamar wanda aka kunna famfo rike hannunshi tayi kam kafin tasaki wani irin marayan kukan dake cinta tun jiya amma takasayi durkusawa kasa tayi tana kuka bana wasa ba,babu wanda yayi kokarin hanata dan dama abinda take bukata kenan tayi wannan kukan komai zataji yazo mata dasauki kukanta tasha ma ishe kafin ummi tazo tadagata tarungumeta suka zauna akan kujera sambatu tafarayi acikin kukan wanda baama jin metake fada tsaban yanda kukan yayi yawa, kusan 1hr tana kukan kafin tasamu relief tayi shuru tana bin kowa da ido abincin da suhaima tadafane takawo mata da ruwa Abba ne dakanshi yace ” Fatima kice abinci kinji” gyada mishi kai kawai tayi kafin tasa hannu tadauki spoon din tafaraci jallof din macaroni ne da kifin ruwa kadan kadan takeci dukda bakinta ba apatite haka taci abincin tura abincin gefe tayi ta kwantar da kanta akafadar ummi , dukansu tattaunawa sukeyi tayanda zaasamo mafitan wanke sunan azaad da fanan doctor ammar ne yace” inada shawara ” duka kallonshi sukayi suna jiran suji mezece ” meze hana azaad din da fanan sufito suwa yan jaridar bayani kancewa sharri aka musu ” girgiza kai yaseer yayi yace ” wannan bazeyi aiki ba waye kake ganin ze yarda da wannan maganar dakayi ko sunfito social media sunfada bazasu taba yarda ba” jinjina kai sukayi tabbas abinda yaseer yafada gaskiya ne babu wanda ze yarda baba ne yabude baki zeyi magana kira yashigo wayar Abba me martaba sarkin gombe ne yake kiransa dagawa Abba yayi kafin yace ” umarni zanbaka dakai da azaad din kuma abinda zanfada shine babban mafita daze wanke musu suna yanzu kaida suwaye a inda kake !?” Kallon yan falon Abba yayi kafin yace” nida iyayen Fatima ne da yan uwanta sekuma mu ” me martaba ne yace ” kacewa matan subamu waje zamuyi magana ” batare daya katse Kiran ba abba yace ” dan Allah inba damuwa kudan bamu mintuna kadan zamuyi magana, tashi sukayi ummi narikeda fanan dake binsu da ido mama ta mata Bismillah suka shiga dakinta sukuma su amira suka shiga dakin fanan , ganin suntafine yasa wayar akunne yace” me martaba nayi yanda kace ” gyara zama me martaba yayi yace asa wayar a handsfree aikuwa haka akayi .
_____gyaran murya yayi kafin yafara magana ” assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum ” amsawa sukayi yadora dacewa ” inason ku saurareni da kunnen basira nasan duk kunajina , naji abinda yafaru kwata kwata bemin dadi ba bani kadai ba hatta duk wani wanda yasan azaadu da wannan baiwar Allah yasan wannan qazafine! Anbata musu suna a idon duniya kowa kallon fasikai yake musu ! To nasamo mafita wanda nasan dukkanku tunanin ku bebaku Shiba babban abinda ze wanke sunan su a idon al’ummar duniya nan da hour 3 zuwa 4 shine su kasance ma aurata!
Nan ne zasu iya fitowa su karyata wannan lamarin da full confidence dinsu Kuma kowa ze yarda dukda zaayi mamakin yaushe babban shahararren Dan kasuwan nan yayi aure batare da sanin duniya ba, zasu iya cewa auran nasu bewuce sati dayaba anajiran dama tayi saukane seta tare wannan shine maganata!?” Kaff dinsu nutsuwa sukayi suna sauraranshi domin maganar shi shine mafita girgiza kai azaad yayi cike da rashin yarda da shawaran yace ” no bazeyuba taya wannan zezama solution bazan taba yarda da hakan ba never” kallonshi kawai Abba yakeyi yama rasa mezece mishi duk abinda Mr azaad yake fada akan kunnen me martaba cikin tsawa yace ” azaadu ni kake mayarwa magana ina fada kana fada ko ubanka be isa insa doka yaki biba balle kai” afusace azaad yace ” shi kace ai taya ze tsallake abinda kafada ai shi ka haifa bani ba sekayi wannan takaman dashi” wani irin tsawa Abba yadaga wa azaad ” mahaifin nawa kake maidawa magana saboda gaka ishashen mara kunya ko wannan taurin kan naka azaad kakiyayeni randa zanyi maganinta nazuwa, murmushin takaici me martaba yayi yace ” karka damu ai dama masu iya magana sunce kahaifi da baka haifi halinshi ba nikuma zan nunawa azaadu na Isa dakai din ina mahaifin yarinyar!?” Cike da girmamawa baba yace” inajinka me martaba” ” kaji abinda nafada bansan kai amatsayinka na mahaifinta ba meka yanke shin kabamu auranta !?” Gaba daya sun daure baba da jijiyoyin jikinshi gashi baze iyacewa me martaba ah ah ba dan dattijo ne me daddaku da Kamala da sanin yakamata mutum ne shi me adalci, inkuma be yarda ba yanaji yana gani sunan yarshi yabaci, awani bangaren kuma ganin reaction din Azaad yatabbatar mishi da bayason fanan shikuma bazeso abinda ze kuntata mata ba he’s out of word, tabashi Abba yayi jin bece komai ba jiki asanyaye yace “nabaku me martaba” hamdala sukayi duk da yayyun fanan su ya Usman wani bankwarakwai sukaji lamarin. Tambayar kwatancen gidan me martaba yayi aikuwa dasauri yaseer yaturamai da address azaad de zuba musu ido yayi ganin abinda suke shirin yi wai kamarshi zasuwa auran dole. Motocin masarautar gombe ne tadira akofar gidansu fanan dukda zuwan sirrine mota ukune kawai daga me martaba se matarshi ta biyu Fulani se amintattunshi waziri da galadima se bafade guda daya kiran Abba yayi yasanar mishi dasun iso fitowa abba da baba sukayi suka musu iso farine sol suna matukar kama da abba shigowa falon sukayi suka zauna cikin darajawa da mutuntawa suka gaisa baba ne yace ” Al ameen jeka kiramin mamanku ” mikewa ya al ameen yayi yakira mama yasanar da ita sunyi baki tafito suka gaisa sannan takawo musu abin sha dasu snacks da fruit mikewa Fulani tayi tabi bayanta suka shiga dakin mama suma suna tattaunawa kan batun duk da basusan abinda ke faruwa afalo ba.
_______ kallon ba faden waziri yayi fita yayi yabude motar yadauko sweets da goro aka kawo falon, dan jimantawa baba yace wani hanzari ba gudu ba yakamata kafin ayi wannan auren kusan asalinmu sannan kusan wacece fanan kar ayi aure kuma wata matsala tabiyo baya, hamdala duka sukayi tabbas maganar shi gaskiya ne bakaramin jindadi sukayi ba domin dama kowa burinsa yaji menene taqamemen fanan.

TUSHEN LABARI

 

 

Alh umar haifaffen dan gombe ne Kuma dan kasuwane yanada rufin asiri dede gwargwado babu abinda yafi karfinsu shida matarsa rukkaya sunada yara biyu maza, babban dansu shine Muhammad se nabiyu kabiru tunda rukkaya tahaifi kabiru batasake haihuwa ba har suka kammala secondary school dinsu nan ne rukkaya tafara laulayin ciki ana haka suka samu addimission a university jari alh Umar yabasu Suma su tsaya da kafafunsu alhamdulillah sun bude shagunan su a kasuwa na trader suna karatu suna kasuwanci nan ne rukkaya tahaifi ya mace aka samata suna firdausi suna matukar sonta tana ganin gata sosai, har Allah yasa suka kammala karatunsu Muhammad dama shi business yake karanta kabiru Kuma engineering, a time din ne iyayensu suka sasu agaba akan maganar aure Muhammad akwai yar makociyarsu yadade yanasonta amma betaba nuna mata ba da aka matsa musu akan batun aurene yafadawa baba aikuwa sunyi farin ciki domin kuwa sumayya yarinyace kyakyawa me tarbiya da nutsuwa yar shekara 16 haka kabiru ma yafito da budurwansa rahina, acikin watanni kuwa akayi komai da komai aka daura musu aure bayan aure da wata uku kabiru yasamu aikin engineer a bauchi state suntayashi murna sosai haka yadauki matarshi dake da karamin ciki dukkansu basu saniba suka tafi. Laulayin ciki sosai sumayya tafara kamar bazatayi rai ba dan cikin yawahalar da ita sosai bayan wata tara suka haihu arana daya itada rahina suka haifi yara maza dawuwa gida sukayi dan ayi suna atare suna akayi yaron muhammad akasa mishi usman takwaran kakansu marigayi mahaifin alh Umar shikuma dan wajan kabiru yaci sunan alh umar anamai inkiya da Al ameen. Haka suka dinga samun kulawa na musamman agun dangi musamman alh Umar da rukkaya dan bakaramin son jikokin nasu sukeyi ba ana arba’in kabiru yazo yadauki matarsa suka koma bauchi .
Wata rana alh umar da matarsa suka shirya domin zuwa suga inda kabiru yake zaune dan basu taba zuwa ba sun isa bauchi lafiya ,satin su daya suka juyo domin dawowa gombe har tasha kabiru yakaisu sukayi bankwana ahanyarsu ta dawowa suka hadu da hatsari allah yamusu rasuwa firdausi ce kadai tatsira da rai sun matukar girgiza da rasuwan domin mutuwar iyaye babban ciwone haka aka musu Jana’iza aka kaisu gidansu na gaskiya daukan firdausi Muhammad yayi tadawo gidan shi.

Bayan shekara hudu kasuwancin muhammad yana tafiya dede Kuma har lokacin summaya bata kara samun ciki ba itakuma rahina family planning sukayi , daga firdausi har usman suna zuwa makaranta a lokacin firdausi nada shekara 9 usman kuma 4 ahaka suke rayuwarsu duk sanda engineer kabiru yasamu hutu agun aiki suna zuwa hutu da matarsa da al ameen ana haka ciki yabayyana ajikin rahina nanma sunyi farin ciki sosai.
___ sumayya kam shuru_shuru amma se shegen kwadayi dacin kayan kwalam duk babu wanda yakawo ciki gareta saboda har period tanayi wata rana ta tashi da wani irin mugun ciwon ciki nan take sukayi asibiti da ita aka bata gado gwajine farko suka gane tana da ciki harna tsawon wata biyar ajikinta amma ciki plat babu alamunsa wannan lamarin yabawa dangi mamaki tana samun sauki suka koma gida da ita sukaci gaba da kulawa da ita, tundaga wannan ranar suka fara fuskantan wani bakon yanayi akoda yaushe cikin sumayya wani irin daddadar kamshin turarene wanda bazaataba cewa ga kalarta ba akasuwa kokuma awani waje ba kullum gidansu kamshi ne kawai yake tashi Abu na biyu Kuma shine koyaushe sumayya jikinta agajiye takejinshi kamar wacce tayi wani aiki abubuwa de iri_iri.

 

Wani irin gagarumin fadane yabarke tsakanin jinsin fararen aljanu dakuma mugayen kungiyoyin asiri, har cikin masarautar nasminaya suka shiga suka cimmusu da yaki bakaramin dauki badadi akayi ba awannan daren inda aka kashe rayuka bila adadi, yakine da akayisa akan hular sarauta dake kan sarki abdud daar shine sarkin dake mulkan duka wani farin aljani sarkine da yafita lamba daya domin kuwa adaline yanason jamaar sa haka Suma suke kaunar sarkinsu fiyeda rayuwarsu zasu iyayin komai akansa da matarshi sarauniya ajeebah da yayansu guda uku maza biyu mace daya da yarima Aadhil se yarima Aahil se yar karamarsu gimbiya Afroza, farmakansu da kungiyar SATANIC dakuma kungiyar BAPHOMET shuuman kungiyoyine masu kashe rayukan al’umma domin su samu biyan bukatarsu matsafane sosai Kuma tushensu daga turai ne sundade suna son kwace kambun sarautar sarki abdud daar domin insuka sameshi bakaramin karfin iko da tsafi zasu samu ba so suke su mulki duniya da mugun nufinsu. Duk farautar sarki abdud daar dasukeyi yana sane dasu bedaga hankalinshi ba domin ya yarda da Allah shine merayawa Kuma me kashewa jakadiya abashiyya taso sarki abdud daar yadau mataki amma yakijin ta. Acikin yakin da akayine aka kashe matar sarki abdud daar ajeebah dakuma danshi yarima Aadhil wasu suka mutu wasu suka raunata dakyar sarki abdud daar yasamu yadinga buya awasu sassan duniya ganin duk inda yayi sesun cinmarne yasa kawai yafado duniyar bil adama neman inda ze boye kambun sarautar yakeyi amma yarasa harya fara tunanin barin jinsin bil adama fara firewa yayi ahankali domin gaba daya sunji mishi rauni ,dakatawa yayi lokaci daya sanadiyar jin kamshin turaren sauban dayayi mamakine karara yabayyana akan fuskanshi dama aduniyar bil adama ma ana samun yaya yan baiwa masu sauban ajikinsu tabbas nan ne yakamata yaje ya boye kambunshi domin yanada yakini kambun zetsira daga wayan can azzaluman bin direction din dayake jiyo kamshi yadingayi harya iso dakin mama dake kwance suna bacci hankali kwance duk dayasan abinda ze aikata zunubine amma babu yanda ya iya dolenshi yayi hakan inkuma ba haka suka samu kambun sarautar da akawa lakabi da ( JAAAZANA) tabbas zasuyi zalunci yanke shawara yayi yashiga cikin mama ganin ya macece yasashi tunanin anya zata iya tsira daga sharrinsu kuwa tunawa dayayi itadin yar baiwace zata iya tunkararsu tayakesu hartaci galaba akansu domin takasance me karfi biyu daga jaaazana yayi sama yayi wasu sambatu nan take yanarke yakoma kamar ruwa jijiyoyin jinin jikinta yabi yadinga zuba mata su harseda suka gauraya da jininta tsaff sauran daya rage kuma yasa mata acikin cikin mama tayanda shine zezama ruwan shanta yana gamawa yafito daga cikin, dolenshi yamusu bayani domin kuwa yarsu yanzu tarigada tazama shugabarsu dole duk daren dadewa zata tafi tabarsu dan karamin guguwa yatayar saboda yasamu sutashi aikuwa da sauri baba da mama suka tashi wato(sumayya da Muhammad) ganin farin balarabe atsaye akansu yana sanye da fararen kaya sukwal kayan anmai ado da lu’u_lu’u jikinshi se zubar da jini yakeyi adan tsorace suka mike tsaye suna adduah dan sunsan de wannan ba mutum bane suna tsayawa kuwa sarki abdud daar yazube akan guiwowinshi ya sunkuyar dakai alamar girmamawa wa shugabarsu datake cikin ciki cikeda mamaki baba yace ” bawan Allah daga ina meyakawo wajanmu Allah yasa bada mugun nufi kazo mana ba ” mikewa sarki abdud daar yayi yafara basu labarin shi wanene shi daga karshe yabasu labarin abinda yasa yazo wajansu dakuma ajiyar dayayi ajikin yarsu datake ciki dakuma mugayen kungiyoyin dasuke son kasheshi dakuma yaqarsu da yar cikinsu zatayi yahada dabasu hakuri sannan yamusu waazi da kaddararta ne tazo ahaka , inbanda innalillahi wainna ilaijiraji unnn babu abinda suke nanatawa kuka mama tafashe dashi cikin kuka tace ” baka kyauta mana ba baka kyautawa rayuwarmu ba yar jaririyar dabataji ba bata gani ba wacce batama zo duniya ba zakasa rayuwarta atasgaro meyasa bakaje wajan wasu ba kazo gunmu wallahi kacuceni kuma allah seya sakamin nida nake mahaifiyarta kake kokarin rabani da yata zakasamin ita acikin rigamarku ” ta karashe maganar tana kuka me tsuma zuciya riketa baba yayi yana rarrashinta, sosai sarki abdud daar yaji tausayinsu amma bashida zabi jaaazana yarsu ta zaba dole itace zata mulki masarautar nasminaya daga kai yayi yakalli sama nan take jakadiya abashiyya tabayyana itama jikinta duk rauni da manya_manyan masu mukamai a nasminaya kusan su 10 suka bayyana suna kallon mama suka zube akan guiwowinsu cikin girmamawa bayani sarki abdud daar yamusu yace ga” amanata kuma sarauniyarku tagaba ku kula da ita kubata dukkan kariya da rayukanku karku yarda kubar wani abu yasameta koda kuwa kuzaku rasa naku rayuwar” juyawa yayi ga abdud Shakur babban nahannun damanshi yace ” kaida jakadiya abashiyya amanarta na hannunku ku kareta daga sharrinsu tanzarzar karda kusake waninku yayi gigin fada mata ko ita wacece harse lokacin karfin iko zefara bayyana ajikinta itada kanta zata gano ko ita wacece kuma tabar duniyar bil adama takoma masarauta domin baku kariya ” yagama jawabinsa yaname juyawa gasu baba ” yace iname nemar afuwarku daku yafemin dan banasan inmutu da hakkinku akaina dan Allah kuyafemin yarku tana cikin kariya babu abinda zesameta sekun tabka wani babban kuskure dazesa sufara farmakanta! Nan ne itakuma zata fara taka matakin rabuwa daku” cikin tsoro baba yace” menene wannan kuskuren dazamu kiyaye ” domin su gaba daya sun gama tsorata dasu ” budan bakin sarki abdud daar yace ” ko wani irin hali zaa shiga karku yarda sarauniya takai dare awaje inkuma hakan yafaru to sukuma zasu fara farmakanta da dukkan karfinsu ” jiki asanyaye baba yace zamu kiyaye in sha Allah kallon fuskanta mama sukayi wacce har alokacin kuka takeyi jakadiya abashiyya tace ” sumayya kuyi hakuri ku gafarta mana dole zamu kasance daku har tsawon sanda sarauniya zata koma gunmu zamuta bata kariya da rayuwarmu ” watsa mata harara kawai mama takeyi itakuwa abashiyya se murmushi takeyi mata ganin lokaci nakurewane yasa sarki abdud daar yace” bakuce kunyafemin ba dan nasan mutuwa zanyi ba lallai musake haduwa ba” hada baki sukayi wajen cewa munyafe maka duniya da lahira murmushi gaba dayansu sukayi, lokaci daya dukansu suka bace batt komawa masarautar sukayi suka samu anmusu taasa sosai shahada sukayi sukaci gaba da yaki cikin rashin saa tanzarzar yayi nasaran kashe sarki abdud daar har lahira, zagaye masarautar sukayi kaff basu samu jaaazana ba hakan yasa afusace sukabar nasminaya.
Bakaramin takaici sukayi ba da mutuwar sarki da matarsa da danshi ba sunji badadi sosai babu abinda yake kona musu rai kaman isukaga kujeran mulkinsa babu kowa akai tunsuna boye musu gaskiya har suka gaji jakadiya abashiyya da abdud Shakur ne suka fito suka musu bayanin kan cewa sarauniyarsu na nan zuwa garesu nan bada jimawa ba sunyi farin ciki dajin wannan maganar haka suka dibi dakaru fiye da dubu zuwa ga gidansu sarauniya domin bata kariya.

Wata bakwai ciff_ciff mama tafara nakuda aikuwa adaren ranan jakadiya ce ta karbi haihuwar ganin fuskan sarauniyarsu dakuma bayanta nadauke da zanen tambarin masarautar su (tattoo dake bayan fanan) yasata shiga cikin farin ciki mara misaltuwa daduk masarautar nasminaya, duk data kasance bakwai ni amma tafi wani dan wata taranma girma dakuma kuzari jakadiya ce tabukaci da abawa sarauniya nata dakin daban saboda suji dadin kula da ita dukda basaso haka suka ware mata dakinta daban ranan suna yarinya taci suna Fatima suka mata lakabi da fanan, ahaka tadinga girma dawasu abubuwan mamaki atare da ita Kuma koda wasa basa yarda tayi nisa da gida dazesa takai mangrib kansu daya da suhaima yar gidan kabiru.
___ tunda takai shekara 10 kuma wayan nan abubuwan al’ajabin suka dena bibiyarta kawarta daya dal itace amira, fanan nada shekara she uku aduniya mama tasake haihuwar ya mace suka samata ilham (auta) time din kuma su usman suka gama makaranta , haka fanan da Amira suka girma harsuka gama secondary school dinsu tare akasamo musu addimission a garkuwa school of health lokacin suna aji hudu a islamiyya, dake 2yrs program ne suka gama dawuri sukayi graduate batare da bata lokaci ba baban Amira yasamo musu aiki a asibitin specialist suka fara aiki, akaxo akayi auren anty firdausi, babban abinda su baba suka fara lura dangane da fanan shine babu wani namijin dayataba tunkararta da sunan yana sonta abun yadaure musu kai Sosai amma haka sukayi shuru.

Wannan shine takaitaccen tarihinmu cewar baba ba karamin girgiza sukayi ba dajin haka abin yabasu mamaki fiyeda yanda baa tunani gyaran murya me martaba yayi yace ” tabbas fanan baiwar Allah ce wacce batasan komai ba ta cancanci girmamawa da farantawa kafin tabar duniyarmu domin ni inada labarin nan domin kafin sarki abdud daar yabar duniya Abdud Shakur yasameni yafadamin abinda yafaru dukda bansan waye sarkin nasu ba amma na tausaya musu matuka gashi bamuda hanyar taimaka musu sede nasa akata musu adduo’i! Nasan abdud Shakur ne alokacin da natafi aikin hajji nida iyalaina muka hadu dashi muka fara abokantaka be boyemin komai ba yafadamin shi jinni ne hakan bedameni ba mukaci gaba da zumunci duk sanda yasamu lokaci yakan kawomin ziyara ,ranar wata jummaa ne cikin tsohon dare yazomin amafarki naganshi acikin mawuyacin hali nan ne yake sanar dani abinda suke fuskanta yakuma bayyanamin kancewa sunyi sabuwar sarauniya ashe fatima ce Allahu akhabar ” azaad de jinsu kawai yakeyi shidama tunda yaga fanan yagane bawai wani abu bane ajikinta itadince dakanta duk da bawai yayi believing da wayan nan abubuwan bane adduah yadingayi Allah yasa su shashantar da maganar auren. Haka suka cigaba da tattaunawarsu, Abba yace ” ai dah nakowane Allah Ubangiji yakareta dakuma al’umman musulman duniya daga sharrinsu” amsawa sukayi da Ameen fara raba goro akayi ganin da gaske sukene yasa azaad cewa ” Abba amma kasan dacewa akwai alkawarin aure tsakanina da aneesa ” Abba zeyi magana me martaba yarigashi da fadin” karka damu aikana da daman dazakayi hudu” dariyar shakiyanci yaseer yasa. Shuru yamusu yana sake_saken aranshi, haka aka daura auren azaad muhammad mainasara da Fatima muhammad Umar akan naira dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba nan take suka fara gaggaisawa da juna suna taya juna murna bakin ciki kamar zekashe azaad afusace yamike yafita a falon bin bayanshi doctor ammar da yaseer sukayi. Su ya Usman kuwa tunda sukaji wacece kanwarsu din gaba daya walwalarsu taragu barinma insuka tuna zata tafi tabarsu wata rana.

Bada umarni me martaba yayi akira mishi matan gidan kiransu ya al ameen yaje yayi suka fito danduk wainar da ake soyawa basu saniba zama sukayi suna gaida me martaba kallon fanan da har time din take kwance akan kafadar ummi yayi gyaran murya yayi yabude taro da sallama ” Fatima naji duk wani abinda yafaru daku iname baki hakuri da lefin danmu yashafeki amma kisani kaddara bata canzawa sede tadau lokaci ” haka de yamata nasiha me ratsa jiki ita da gaba daya jamaar dake falon daga karshe yace ” se abu nagaba yau aka daura miki aure keda azaad domin kutsira daga kazafin da akamuku ” dagowa fanan tayi dasauri tana kallon me martaba dan san gasgata maganar daya fada wani azaad din yake nufi …………….

Alhamdulillah nan nakawo karshen book 1 da izinin Allah .
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD

 

Back to top button