Yar Zaman Wanka 24
Yadda ya zuro a guje babu birki haka su ma suka daddage ƙarfinsu suke binsa da gudun, har da masu tattare zane gudun samun mushkila. Imran da gabaɗaya a gigice yake sai da ya zo falo ya ga Sadiya da miciji a hannu ya ja ya tsaya a ransa yana ganin jarumta irin ta Sadiya yana kuma jaddada soyayyar uwa da ɗa, ganin Hassan ɗin ne ya dawo dashi daga firgici da tsurewar da ya yi sai a sannna ya tuna cewar ashe ma Sadiya ta taho da yaron kawai tsoro ne ya sanya ya ga kamar micijin ne ya biyo shi. Wani yawu ya haɗiye tare da sauke wani numfashi. Matan nan ma ganin ya tsaya sai kowacce ta dakata a wajen dan sun manta da micijin a ɗaki amma ganin Imran na gudu su ma suka fara suna jejjefa idanu kallonsu kawai yake, daga wacce take jige jagaf da fitsari sai wacce ke da ƙunshi ƙafa ɗaya ba a ƙarasa ɗayar ba, sai wacce baƙin lalle ya gogu a fuskar ta koma kamar wacce ta shafa shuni. Wata harara ya musu tare da jan wani uban tsaki, ya wani maje yana harare-harare amma ya kasa shiga ɗakin, hango me ƙunshi a ƙofar kicin ɗin sai lokacin ya ga rashin azancinsa da bai tsaya ya waiwaya ba bare ya gane ba miciji bane.
Harara ya dakawa matan nan da suka biyo shi, dan sun ma kasa shiga falon shi ma cikin wayancewa sai ya juya ya nufi kicin ɗin me ƙunshin da gudu ta bar wajan ganinsa ya taho. Imra n kuwa na shiga kicin ɗin sai ya tsaya a tsakiyar kicin ɗin yana maida numfashi dan ba ya so a raina shi shi yasa bai tsaya maida numfashi a gabansu ba, su ma suna nan tsaye sun yi carko-carko. Dafa kan freezer ya yi tare da ɗora kansa a kanta, Idanu ya rufe ruf yana jin yadda zuciyarsa ke lugude kamar me tseren gudu, hannayensa duka biyu ya ɗora a kan freezer sai ya kwantar da kansa a kan freezer, idanunsa a rufe yana tunano yadda Sadiya ke ɗauke da miciji a hannunta, Inna da tun daɗewa take ta faman magana a kan a kawo mata ɗauki babu wanda ya jiyo ta, dan haka ta raya a ranta za ta shiga jijjiga freezer da ƙarfi dan a jiyo ta a zo a buɗe ta. Wata jijjiga da ta yiwa freezer da Imran ke riƙe da ita gam, hakan ya sanya ya saki wata tusa ta tsurewa ba tare sa ya shirya ba, jin freezer na girgizashi tamkar ana girgizar ƙasa hakan ya sanya ya ƙanƙameta da ƙarfinsa.
Dan gabaɗaya ma sai tunanin guduwa ya kwance masa.
“Allah wannan baƙar wahalar da nake shiga tun ranar da Sadiya ta haihu Allah ka sa kaffara ne” Ya faɗa lokacin da ya saki wani kuka me cin rai Inna kuwa bata daina jijjiga a cikin freezer ba yi take tun ƙarfi.
“Ai wallahi da in mutu a binne ni a tsugunne na gwammace in daddara firinjin nan in bayyana kamar wata ɗan daren goma sha huɗu” Ta faɗa tana lokacin da ta kai hannunt ta ƙwarzani jikin freezer ganin yadda farin ƙanƙarar nan me kamar dusa ta fara baibaiye jikin freezer.
“Oh Allah ni Azumi kamar wanda aka sanyani cikin buhun fulawa ji yadda farin ƙanƙanarar nan ya maida ni kamar furfura ta kar ni, ganin mukullin ya faɗo daga jiki, saboda bugawar da ake, cikin sanyin jiki da tsoro ya ɗau mukullin ya sanya jikin freezer ya buɗe a tsorace tare da ja baya kaɗan bakinsa sai kaiwa da komowa yake wajen addu’a amma baka jin me yake cewa shi kansa be sai me yake karantawa ba.
Yana buɗe freezer sai ya yi baya ya maƙe a bango, yadda ya tsaya kamar ka ce as ya zura a guje, jira yake kawai wani abu ya fito ya arce a na kare, dan ya yi alƙawarin idan ya doshi ƙofar gida sai dai idan ya je ƙofa ya ce kowa ya taho sarkin aljannu a frezer.
Inna ganin an buɗe dan ta ga alama murfin ya ɗan ɗaga da take ɗaga shi sama da kanta, hamdala ta yi a zuciyarta, ta fara kiciniyar miƙewa amma ina, ashe gabaɗaya zanin setin mazaunanta ya haɗu da ɗan sauran ruwan ƙasan freezer ya daskare har zanin. Hannu ta kai ta taɓo sai ji ta yi gabaɗaya ɗuwawunta yana danne da zani da ƙanƙarar.
Bata gama tsurewa ba sai da ta jita gabaɗaya a daskare har ta buɗe baki za ta yi magana sai ta fasa saboda ta san ita tana jiyo maganar mutane amma ita ta ga duk kwakwazon da take ba a jinta.Zunkuɗa kanta ta yi cikin sa’a kuwa sai ƙoƙon kanta ya buɗe murfin ya yi sama. Imran da ke rakuɓe a jikin bango dan tun lokacin da ya buɗe ya koma ya rakuɓe sai karkarwa yake kamar shi ne a freezer, ganin an buɗe ƙofar sai kawai ya saki kuka yana ta matse ƙafafunsa amma tsoro sai da y sa fitsarin da yake ta matsewa tun daga lokacin da freezer ta fara girgiza ya ƙwace masa ya zubo. Tsoro ne marar misali ya baibaiyeshi.
“Ku min rai dan Allah, in gidan ma kuke so mu bari a yau ɗin nan za mu bari a yanzu ma kuma ko tsinke ba za mu ɗauka ba, ku taimaka mana” Ya faɗa yana ta so ya zura a guje amma gani yake kamar ma rafkoshi za a yi a dawo dashi kicin ɗin.
Inna kuwa gyaran murya ta shiga yi dan muryar duk ta shaƙe. Ai gyaran muryar da ta yi sai ya bala’in ƙara sanya Imran cikin tashin hankali da mummunan tsoro, bai ankara ba sai jin bakinsa ya yi yana faɗin
“Ya kusamu ya mu rasa, ya kusamu ya mu rasa” Sai maimaitawa yake kamar wanda aka sa tilawar ƙur’ani, shi kansa bai san me yake faɗa ba. Ya gama jiƙewa da hawaye da fitsari ga majina duk shi kaɗai kawai sai ji ya yi ta cikin freezer an ce.
“Imirana, Imirana, Imirana” Jikinsa ne ya fara karkarwa be ma san ya aka yi ba kawai dai ya ga ya fara zagaye wani kofi da ke tskiyar kicin ɗin, sai zagawa yake kamar yadda ake ɗawafi yana cewa
“Ya ku samu, ya mu rasa” Dan yadda aka kira sunan nasa ya tsorata shi dan yanzu dai ya tabbatar sarkin aljannu ne dan ya ji an kira shi d sunansa da alama suna ganinsa suna kuma sane da motsinsa. Dan yadda muryar Inna ke shaƙe idan ta yi magana kamar an shaƙewa kuturu wuya haka sautin ke fita, gabaɗaya ma ya manta da wata Inna bare kuma ya gane ita ke kiransa Imirana.
“Imirana, yaka buɗe firinjin nan” Cewar Inna dan duk abin nan da ake murfin freezer ɗagawa yake kawai idan Inna ta buga kai a jiki.Imran kuwa ji ya yi tamkar ya zura a guje, amma ba hali.
A hankali ya taka ya ƙarasa wajen hannunsa na karkarwa ya kama murfin freezer yana sakin wani kuka me cin rai marar sauti, haka ya buɗe freezer cikin cika umarninsu amma sai ya rufe idanunsa gam dan gani yake idan suka yi ido huɗu ganinsu zai sa ya haukace.
“Oh ni Azumi matar Malam sai yanzu kuka kawo min ɗauki” Imran da ke riƙe da murfin freezer ido a rufe hawaye na kwaranyowa sai karkarwa jikinsa ke yi ya tsinkayi muryar Inna daga cikin freezer da sauri ya buɗe idon aikuwa idanunsa ya sauka a kan Inna da ke cikin freezer ita ba a zaune ba ita ba a tsugunne ba, ga wani ɗankwalinta ya yi gefe ɗaya ya mata wani zungurgur kamar hular ibro.Ta yi wani yamutsatsa kamar an tsamo ɓera daga ruwa, Gabaɗaya sai Imran ya manta halin da yake ciki na damuwa, a take ya saki wata dariya dan har ya hango dalilin shigar Inna freezer.
“Hassan” Ya faɗa a zuciyarsa, wato dai saboda miciji ta shiga freezer ya baiwa kansa amsa.
“Ko wa ya kulleta kuma?” Ya faɗa a ransa.
“Tabbas a kwai ayar tambaya da…
“Imirana tsamoni dan Allah”Cewar Inna murya a shaƙe.
“Me kika ce ” Ya faɗa dariya na fitowa daga bakinsa irin dariyar ƙetar nan, Wani haushi ne ya turnuƙe Inna dan ita babu yadda za a yi ta fito dan ɗuwawunta daskare yake a jikin zani”
“Ni yau na ga abin mamaki ɓatan nono a ƙirjin budurwa” Cewar Inna cikin shaƙewar murya
Lura da Imran ya yi cewar Inna a daskare take sai ya miƙa hannu zai fiddota, aikuwa ya finciko ta da ƙeta.
“Wayyo mafitar kashina, wayyo Allah na haba Imirana ƙanƙara fa na yi” Cewar Inna cikin shaƙeƙƙiyar murya.
Dariya Imran ya ƙyalƙyale da ita, dan daga yadda ya finciko hannun Inna ya jita a manne da freezer, amma a haka yake ƙoƙarin fiddota amma ta ƙi ɓanɓaruwa.
“Haba Imirana ka kashe firinjin mana mazaunan nan nawa su ɗan saka mana, amma kake janyoni baka ji yadda muka yi tif da taya ni da firinjin ba kamar an manne tangaran da sufagilu” Cewar Inna cikin fuskar tausayi, haka dai ya kashe soket ɗin sai da ta ɗan saka ya taimaka mata ta fito, amma dariya na cinsa, haka ta fara takwa dakyar saboda yadda jikinta duk ya yi tsami ga karkarwa da atishawa da take yi a kai- a kai. Haka ta dudduƙo ta fito daga kicin ɗin tana dudduƙawa, tana ta kwashewa yarinyar nan me ƙunshi albarka, a haka ta fito ta kwa yi ido huɗu da sauran matan nan tsaye cirko-cirko har Ashrof lokacin ita ma ta fito sai maida yanda aka yi suke. Ganin Inna a yanayin da take sai kowa ya zura mata ido. Banda yarinyar da aka riƙewa mamanta, ta daddage sai masifa take a kan an riƙe mata nono a loka har sai da ta yi fitsarin wuya.Ita kuma ɗayar sai bata haƙuri take ta ce ba da niyya ta yi ba amma sai masifa take. Inna na ƙarasowa ta kalli yarinyar a shelaƙe ta ce
“Ni ina dalili kin damu mutane tun ina cikin firinji nake jin kina an damƙe miki nono, wai a nan ina nonon yake? Ba dan fuskarki ba ma babu yadda za a yi a banbance gabanki da bayanki, abu kamar an sawa muciya zani ba gaba ba baya, amma a haka kike cewa an damƙi nono, yo an damƙi nono ko dai an damƙi fata da fatar ma kika ce da daɗi, dan ban ga nono a nan ba wannan ƙirji naki kamar ƙirjin babe”