Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 18

Sponsored Links

Sun kusan zuwa inda motar take ai Inna da ta ga sun doshi mota sai hankalinta ya tashi dan duk tunaninta ƴan yankan kai ne za su tafi da ita su yanke kan nata.

“Wayyo Allah na, wayyo Malam wayyo Tasalla ku kawo min ɗauki gani a hannun ƴan yankan kai, Malam da Tasalla duk da na san kun min nisa amma dole in kira sunanku dan na san idan na kira Sunan Imirana sai dai su gundule min har ƙafafu dan wallahi baƙin halinsa ba zai sa ya taimaka min b mutumin da ya tsane ni, bari in ƙwaci kaina dan ba zan yarda a cire min kai ba in mutu in barwa Tasalla Malam ta zauna ita ɗaya” Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ja wani uban birki, aikuwa aka shiga turumurtu ita da su, har sai da na cikin motar ya ga Inna na neman ta gagaresu ya taso cikin hanzari rai a ɓace yana zuwa cikin ɓacin rai ya ce.

“Wai dalla malamai meye hakan sai kun sa asirinmu ya tonu yanzu ban da abin kunya har wannan tsohuwar ce kuka kasa kawo ta mota tana ta mayar da ku baya ” Ya faɗa yana hucin ɓacin rai a zuciye ya kama Inna wai shi nan mai ƙarfi aikuwa ta daddage ta cije a wuri ɗaya ta ƙi gaba ta ƙi baya ganin wankin hula na son kai su dare su uku amma sun kasa jan tsohuwa sai laya ya ce su mata cali-cali aikuwa cikin lokaci guda mutum biyu suka kamo ƙafar Inna sai gata an mata cali-cali biyu riƙe da ƙafar ɗayan kuma da saman kan har lokacin hannunsa a riƙe da bakin Inna, a haka suka saka ta a motar biyun suka saka ta a tsakiya, ɗayan ya shiga ya ja motar da uban gudu a sukwane suka bar layin. Tuƙi yake amma Inna sai uban bige -bige take a bayan motar ta hana samarin nan biyu sakat duk ta tara musu gajiya kamar wanda suka yi dambe. Sai da suka daddafeta da iya ƙarfinsu sai haki suke sannan ne suka ɗan samu salama amma kuma sun ƙulle mata idanu, da wani ƙyalle bakin kuma ɗayan ya rufe mata da hannunsa.

Hanyar bayan gari suka nufa duk ta tara musu gajiya, ba dan uban kuɗaɗe da Ogansu ya ce za a samu idan sun kamo tsuhuwar nan da na jaki za su lakaɗa mata su jefar da ita.

Tafiya suke amma Inna hankalinta a matuƙar yashe yake dan tana gani lokacin barinta duniya ya yi domin kuwa ta haɗu da waɗanda za su fille mata kai.

“Allah na tuba, ka yafe mini kura kuraina, ka sa ni a aljanna, ka haɗa fuskokinmu a gidan aljanna da malam, amma banda Tasalla ita ma a kaita aljannarta da ban amma ba wacce za mu zauna da ni da Malam ba ” Cewar Inna a zuciyarta hawaye zubo mata gashi babu damar ƙugawa dan an yiwa bakinta rub.

A haka dai ta shiga shirya abin da za ta musu duk da tana ganin mawuyaci ne ta kuɓuta amma za ta yi iya ƙoƙarinta wajen ganin ta musu wani abin ko da zai ita kasancewa bata rama ba. Dama dai ta san zai yi wahala a ce ka rama abin da wanda ke shirin rabaka da duniya zai maka. Ganin ta tuno abin da za ta musu sai ta fara tunanin aiwatarwa. Hannun damarta da ke gefen wanda ke damarta, kuma a wajen cinyarsa hannun nata yake duk da ya riƙe ra amma kuma wajen kafaɗarta ne ya kama ya maƙalƙale, dan haka tsintsiyar hannunta ba a riƙe take ba, dibara ta yi ta miƙa hannun wajen inda al’aurarsa take.

“Yau zan yiwa mazaƙutarka (Al’aura) Damƙar da tun da ka zo duniya ba a mata ba, kai ko wanda ya maka shayi lokacin kana yaro ai ba damƙarta ya yi amma yau za ka gwammace kiɗa da karatu” Cewar Inna tana lallaɓawa da hannun har sai da ta ji ta je saitin inda za ta samu abin da take so, amma ba wai tana ɗora hannun a wurin bane, tunda hannun baya kai ga ɗorawa a wurin ba dan haka babu wanda ma ya san ƴar tsohuwa akwai abin da ta shirya, kawai tun da sun ga sun samu lagonta na maƙureta a tsakaninsu sai basu kawo komai ba.

Laɓɓanta na baki ta shiga buɗawa a hankali yadda wanda ya riƙe bakin ba zai ankara ba dan ganin da suka yi ta saki jiki ta daina haure -haure da ƙoƙarin ƙwatar kanta sai ya sassauta riƙon bakin dama dan kar ta yi ihu ta tona musu asiri ya rufe bakin bare kuma yanzu da suka bar cikin gari suka doshi jeji inda ko ta yi ihun babu mai ji bare a ceceta ko a kawo mata ɗauki, sai da ta gama aunasu su duka biyun ta daddage ƙarfinta na bara ta damƙe gaban ɗayan(Mafitsararsa) Ɗayan kuma ta gantsara masa cizo, a tare suka saki wani uban ƙara mai firgitarwa, wanda hakan ya sanya direban ya taka wani uban birki dan ganin me ke faruwa suka saki ihu mai ƙarfi haka a tare bayan sun san suna cikin yanayin da suke buƙatar sirri duk da a jeji suke amma ya dace su kiyaye abin da zai zama tonuwar asirinsu, yana jan birkin ya waiwayo, har lokacin Inna tana riƙe da mazaƙutar ɗayan ɗayan kuma tafin hannunsa yana tsakanin haƙoranta ta musu mugun damƙa. Kowanne sai jijjiga yake kakar ya hau doki yana sukuwa saboda tsabar azaba dan wanda Inna ta damƙi mafitsararsa har balls ɗin ta haɗe ta damƙe. Ihu suke da iya ƙarfinsu suna neman ɗauki, gashi kuma saboda tsabar azaba sun kasa tunanin ɗaukan mataki ko yunƙurin ƙwatar kansu, dan burinsu kawai ta sakr su. Direban kashe motar ya yi ya juyo yana ɗura musu zagi, ashar yake surfa musu saboda bai san me ke faruwa ba, kuma bai lura ba dan wanda ya riƙewa Inna baki har lokacin hannun na a yadsa yake kamar ya riƙe mata bakin, direban kuma bai san an samu juyin mulki ba yanzu Inna ce riƙe da hannun me riƙon bakin a gefe ɗaya kuma ta damƙe mazaƙuta abinta.

Wata tafkekiyar dorina ya ɗakko ya buɗe motar yana riƙe da dorinar dan ya sha alwashin sai su duka jikinsu ya faɗa musu dan babu dalilin da zai sa su nemi jiƙa musu aiki, gabaɗaya sun jigata dan dama mafitsara makasar mutum ce haƙori ma dafi ne da shi, kuma shi wanda ta cija ɗin shi ma daga baua ta haɗa da mafitsararsa abu biyu ya haɗe masa goma da ashirin, a haka ya buɗe ƙofar cikin zafin nama, ya fito ai yana shirin buɗe ƙofar bayan Inna ta yi sauri ta bi ta tsakanin kujerun gaba ta koma gaban motar da yake gilas ɗin motar baƙi ne wuluk na ciki ba ya ganin na waje haka na waje ba ya ganin na ciki, tana komawa mazaunin direba sai gata fito ta ƙofar da direban ya bari a buɗe, duk abin da take bai lura ba. Su kuma wanda ta jigata masu, mafitsara da hannun ɗayan jin ta sake su sai suka yi laɓar a kujera kamar wasu mararsa lafiya dan gabaɗaya sun jigata basu da ƙarfi ko kaɗan, sun leƙo barzahu sun dawo. Inna na fitowa hakan ya yi dai dai da duɗewar da direban ya yiwa ƙofar bayan ƙwaƙwakwarsa na ƙoƙarin tambayarsa me ke faruwa sai idanunsa suka nuna masa tsohuwar ma bata cikin motar, gabaɗaya kwanyarsa ta tsaya da tunanin kar dai aljana ce suka ɗakko ta ɓace bai san ba Inna tana bayansa ɗan sunkuyawar da ya yi zai leƙa cikin motar hakan ya baiwa Inna damar damƙar tasa mazaƙutar, dan ta tsakanin ƙafafunsa daga bayan ta miƙa hannu ta kamo, dan da balls ɗin ma ta fara cin karo kafin hannun nata ya kai ga uwar garken, haka ta riƙe gam ya rinƙa zabga uban ihu da kururuwa.

Kina sha’aninki Inna

A yi hƙr yau kaɗan aka samu jiki da jini

MMN Afrah 09030283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

*Idan dan ki fitar min littafi za ki siya ki riƙe kuɗinki Hajiya ba na buƙata*

Back to top button