Hausa NovelsYar Zaman Wanka Hausa Novel

Yar Zaman Wanka 13

Sponsored Links

Tsayawa baƙin suka yi cak jin furucin Inna Imran kuwa ji ya yi tamkar ƙasa ta tsage ya shige saboda tsabar kunyar da ya ji ta baibayeshi. Sadiya tamkar ta saki kuka dan takaici, ji ta yi dama ta ce Inna ta shige cikin ɗaki in baƙin sun tafi ta fito. Dakyar Sadiya ta ƙwaƙulo dariyar yaƙe ta ce.

“Bismillah ku zauna mana, sannunku da zuwa”

“Eh, eh, eh ku zazzauna mana” Cewar Imran shi ma cikin inda-inda.

Zauna wa suka yi jikin matar sanyi ƙalaw sai wani haɗe rai take tana hararar Inna tamkar dai ita ta yiwa ba’ar.

“Ku da kuke cewa su zauna daga matar har mijin babu na ɗauka, yanzu tsakani da Allah mutumin nan ya zauna a kujerarki Halima, sai dai a sayi sabuwa inda hali in kuma babu hali sai dai a jefar, dan babu kafintan da zai iya gyara kujerar nan, ko a duniya masu girman mutumin nan basu da yawa” Ta faɗa tana daga tsaye.

Sadiya kuwa sai sigina take yiwa Inna da ido tana ta nuna mata ta yi shiru kar fa ta kunyata su.

“Ke ƙyaleni ni fa ƴar gaskiya ce wallahi, in zaka faɗi faɗi gaskiya komai taka ja maka ka biya, babu munafurci, yo ina zan yi munafurci Malam da yake faɗa mana cewa munafuki yana ƙasan kafuri a cikin wuta, a ce kafuri wutarsa bata kai ta munafuki ba a zafi kin ga kuwa ai abin ba ƙarami bane, kuma wannan ƙifƙifta idon ma ki daina Sa’adiyya dan wallahi babu kyau, yafice da ƙyafuce, ke kuma da kike hararata wallahi ni ban san harara ba sai ido ya faɗi kuma me kike ci na baka na zuba indai ni ce ina dawo wa kan ki” Cewar Inna tana kallon baƙuwar.

Babu wanda ya yi magana, Imran kuwa yanzu lamarin tsohuwar nan ya fara bashi tsoro dan yana tsoron ya tanka ko ya mata wani abu ta masa ramuwar gayya ta fi ta gayya. Sojan kuwa kallon kan sa yake ta yi yana so ya tabbatar cewa wandonsa na sojoji ne a jikinsa ko kuwa dai tsohuwar bata lura da wandon ba ko dai ita bata cikin masu tsoron sojoji, dan tun da yake a duniya ba a taɓa ci masa fuska irin haka ba duk da tsohuwa ce yana ganin da girma amma ai ba hauka take ba daga shigowarsu za ta fara musu wulaƙanci har da saurin miƙewa tsaye shi duk tunaninsa ma sara masa za ta yi ko kuma girmamawa ce ta sa ta yi hakan amma sai ya ga saɓanin hakan.

“Abdallah ina wuninku” Sadiya da take son datse maganar ta faɗa ƴar dariyar yake.

“Lefiya lo, Sediya, ya kake ya ya kuma babies?” Shi ma sojan ya amsa cikin gurɓatacciyar hausar sa dan gabaɗaya zaman kudu ya daƙusar masa da hausar.

“Lefiya lo, to wallahi gwara ma ka ce lefe irin wanda ake yiwa amarya, yanzu fa aka kira ka da Abdallah haba ina dalili kana bahaushe ɗan bahaushe menene kuma lefiya, haka kawai kuna arar yaren inyamurai kuna ɓata mana yaren hausa” Cewar Inna tana komawa ta zauna. Babu wanda ya kulata amma Abdallah ji yake kamar ya shaƙe Inna dan da ace a hanya ne ta musu hakan sai ya mata hukunci. Ita matarsa ma ta kasa cewa komai wace irin tsohuwa ce wa wannan, ransu in ya yi dubu ya ɓaci da abin da Inna take, Imran kuwa kansa a sunkuye yake yana jin a ransa da a ce Inna daga ɓangarensa take a yau ɗin nan sai ta bar masa gidansa dan ba zai iya da wannan abin kunyar ba.

Abdallah kuwa tun da Inna dama ta ce zai lotsa kujera da ya zauna ma sai bai saki jikinsa ba ɗan ɗosanawa kawai ya yi dan shi bai taɓa zaton har ƙibarsa ta kai ya yiwa kujera illa lokaci guda ba.

Gaisawa dai suka shiga yi da tambayar bayan rabuwa, Abdallah yana jin daɗin ganin twins da ke kwance kan gadajensu sai addu’a yake a ransa Allah sa matarsa ta haifa masa dan tsohon ciki gare ta.

“Zo yaki nan ƴar yarinya” Cewar Inna tana miƙawa yarinyar da suka zo da ita hannu, da yake yarinyar bata jin hausa dan iyayen basa mata sai bata fahimci me Innar ta ce ba ta dai ga tana miƙo mata hannu, matar Abdallahn ita ta sanya hannu ta dafe yarinyar dan bata so ta je wurin Inna aikuwa Inna ta kalleta ta taɓe baki tare da sakin dariya, sai da ta yi dariya sosai sannan ta ce.

“Wai bakya so ta zo wurina, haba ke kuwa baiwar Allah ki ji da halin da kike ciki mana yadda kike da tsohon cikin nan amma bakya gani ji kike ɗaya kike da kowa shi yasa kika ɗauki wani uban jambaki kika lafta a leɓe to wallahi baki ganki ba yadda kika san akuya ta ci dusa, haka ya miki danɓarɓar babu kyan gani, hodar ma ta miki busu-busu ita da ban fuskarki da ban”

Ƙwallah ce kawai ta kawo a idon matar, dan tana ganin Inna ta gama da ita yadda ta tsaya ta ɓata lokaci a gaban mudubi tana kwalliya amma tsohuwar nan ta ce mata wai janbaki kamar akuya ta ci dusa, duk da dai tana jin ana cewa idan mace me ciki ta tsufa komai ma ta yi bata kyau saboda yadda wasu mata ciki ke maida su. Dama dakyar ma ta samu kayan da suka shigeta duk wanda ya sanya rigar bata shiga zanen ma sai ta ga ya ƙi ɗauruwa. Mijin ne ya yi saurin kallonta yana mata alamar da ta yi haƙuri dan ba ya so su nunawa Imran sun ji haushin abin da aka musu saboda kar ya ji babu daɗi haka ta haƙura ta zauna amma ranta in ya yi dubu ya ɓaci.

“Yanzu dan Allah Halima kalli kan yarinyar can, sun jamɓara mata gashin doki a kanta kamar tsohuwar ƴar bori babu kyan gani wai su nan cinyewa ce ni wallahi ban ga ba abin so a gashin doki” Cewar Inna hankali kwance dan ita gani take dai dai take yi kuma gaskiya take faɗa.

Shiru dai ba wanda ya sake tankawa, sai ƙaran TV kawai kake ji da aka kamo tashar namun daji, matarce kallon ya ɗan ɗauke mata hankali, wani miciji da aka nuno ta gani ta ce “Daddyn Amira ji wani misiji (mijici) ka san ina son misiji ” Ta faɗa hankalinta a kan TV kalla kawai ya yi bai ce komai ba dan gabaɗaya ransa a dagule yake.

Imran ne ya ce “Sadiya miƙo musu yaran mana, tun a waya Abdallah yake cewa yana son twins” Cewar Imran yana sakin dariyar yaƙe wacce bata kai ciki ba.

“Allah ya baku ƴan baiwa duka biyu mu ga ƙaryar inyamuranci” Cewar Inna tana hasaso yadda za su yi da zama da yara duka biyu masu baiwar sawaya zuwa micizai.

Tashi Sadiya ta yi ta ɗakko Husaini za ta baiwa mijin, ganin hakan Inna ta yi karaf ta ce

“Ki baiwa matar tasa mana shi sai a bashi Hassan ɗin kin ga sai su riƙe biyu a tare ko sa musu goshi” Cewar Inna tana ɗan washe baki dan ta hango diramar da za a yi saboda ganin Hassan yana miƙa ta san kwa daf yake da sawaya zuwa miciji, za ta ga ƙaryar soja. Sadiya da bata fahimci manufar Inna ba ta miƙawa matar Abdallah Husaini, ta dawo ta ɗauki Hassan da bata lura yana miƙa ba ta baiwa Abdallah shi. Sai yaba kyan yaran suke suna fatan su ma su haifi ƴan biyu.Ƴar tasu ce take ta dariya tana son a bata Hassan amma uban ya hanata yana mata magana Inna da ba sanin me suke cewa ta yi ba sai baki ta taɓe dan yarinyar bata jin hausa sai turanci.

“Za ka yi yaren nasara da kyau wallahi daga lokacin da ka ganka riƙe dumu-dumu da miciji.

“Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta yi dariya kawai tana ta kallonsu, ana jimawa sai kuwa Hasaan ya fara rikiɗa yana sawaya, babu wanda ya lura, sai da ya gama zama miciji sannan ne fa Abdallah ya zaro idanu ƴar tasa kuma sai ta matsa ta yi wurin inda Inna da Sadiya suke zaune, cikin jin tsoro, matar ma a sukwane ta tashi daga mazauninta tana zare ido ta yi wajen su Sadiya, Abdallah kuwa bakinsa ya kasa haɗa ko da kalma ɗaya ne sai zazzare ido yake ya kalli Hassan sai ya ɗago ya bi mutanen falon da kallo, jikinsa a take ya shiga mazari sai karkarwa yake . Imran kuwa tsaye ya miƙe yana so ya tallafawa baƙon nasa y karɓi Hassan ɗin dan ya ga alama ana jimawa Abdallah suman zaune zai yi saboda irin yadda fuskarsan ta bayyana tsoro muraran amma ya kasa ko da yunƙuri ne.

“Ashsha yau ake yinta wallahi a gidan nan, ga soja ga miciji ashe dai sojoji ma suna da tsoro” Inna ta faɗa tana dariya tana kallon Abdallah ba komai ke bata dariya ba irin yadda abokan biyu suke rarraba ido kamar mararsa gaskiya, shi kansa Imran kamar dai yau ya fara ganin Hassan ya zama miciji yadda yake ciccira ido kamar ka ce kulle ya ce cass dan dama a kusa da ƙofar fita daga falon yake a kan kujera amma ganin abin danke faruwa sai kawai ya miƙe tsaye. Sadiya kuwa gabaɗaya ma ta manta cewae ana taɓa Hassan ya dawo mutum gabaɗaya a ruɗe take irin yadda ta ga baƙin mata na yi kamar waɗanda aka sanya wa bakin bindiga a ƙoƙon kai.

Cikin jarumta da daddagewa Abdallah yake ƙoƙorin haɗa laɓɓan bakinsa domin ya karanto ko da addu’a ce amma tsabar tsoro da fargabar da yake ciki ya kasa ko da a magana ce, Kawai kallon ikon Allah yake wai shi ne ɗauke da ƙaton miciji haka miciji mai sanye da riga da wandon jarirai.Ganin micijin ya kafeshi da ido yana dillo harshensa mai haɗe da dafin da ke cikin bakinsa wanda idan ya sari mutane dafin ke kashe su. Dakyar sai ya iya fara magana, ya fara jero national anthem (Taken Nigeri’a) Wata dariya ce ta so ƙwacewa Imran ganin Abdallah ya daddage yana yiwa Nigeri’a kirari yana zayyano mata taken ta duk a tunaninsa addu’a yake karantowa. Inna kuwa sai dariya take abinta ta ce.

“Yau de maza sun faɗi yo soja kamar kai ga ƙiba tabarakallah kamar mai cin ƙatuwar tukunyar tuwo amma miciji ya razana ka”

dama ai karanbanin akuya yasa ta leƙa ɗakin kura, gaskiya Hassan kana birgeni yaro masomin babba ubanka ma baka bari ba da baiwarka, to yai kuma ga ubanka soja nan sai rattabo yaren nasara yake (Turanci) Har gwara ni ranar nan da na karanta alif an baki waw zal, a ce daga cikin baƙaƙen larabci suke amma shi ka ga” Ta faɗa tana dariyar. Abdallah kuwa sai gumi yake yana ta karanto taken Nigeri’a yake daga ya je ƙarshe sai ya dawo farko ya sake kamowa jikinsa sai maƙyarƙyata yake.

Ganin abin da Inna ke yi Imran ya yi ta maza ya ƙarasa gaban Abdallah ya ce.

“Miƙo shi ka huta wannan gumi kamar ka yi tsere Abdallah” Ya faɗa yana tsaye a gaban Abdallah, shi ma Imran ya faɗa ne dan kar Abdallah ya ga bai kyauta masa ba amma har ga Allah ba zai iya ɗaukan miciji ba.

“Haba Imran ta yaya zan iya ɗaga shi ma baka ganin misiji ne (miciji) To wallahi ko kunama ba zan iya ɗagawa ba bare misiji dan Allah ka ɗauke kar in mutu saboda tsoro.

“Daddyn Amira ka bashi micijin mana ya za ka bar miciji a kan ka sai ya cutar da kai” Matarsa da ke rakuɓe jikin bango tun lokacin da ta ajiye wa Sadiya Husaini a kan cinyarta.

“Ƴar jakar uba kai, wa ya faɗa miki barno gabas take, to wallahi mu nan da kike gani abin kunya gaba muka bashi ba baya ba, ashe rainin wayo ne abin naki ɗazu kika ce misiji amma yanzu gashi nan kin ce miciji ashe da hausarku a bakinku kuke rainawa mutane hankali” Cewar Inna tana dariya.

Babu wanda ya mata magana, Imran ne ya ce.

“Abdallah ya kake national anthem ne wai, duk zaman kudun ne ya sa ka manta da addu’a, Allah fa cewa ya yi Allahzina iza asabathum musibatun ƙalu innalillahi wa inna ialaihir raji’un, amma kuma kai sai kake karanta taken Nigeri’a ko Nigeri’ar ce za ta kawo maka ɗauki.

” Abdallah dai bai ce komai ba dan ba ma ya fahimtar abin da Imran ke faɗa.

“Mummy let’s go home, im afraid” Cewar Amira tana neman sakin kuka.

“Ke rufewa mutane baki kina ƴar hausawa kina magana da bakin nasara, uban leshi ma( let’s) Goron uban wa (go) “Cewar Inna tana zarewa yarinyar ido, da sauri ta matsa jikin Mummynta suka maƙure a jikin bangon tare suna rarraba ido.

Miƙewa Inna ta yi cikin sanɗa, sai da ta je kusa da Imran da ya bata baya, ta shammacesa ta kama ƙasan rigarsa aikuwa yana ƙoƙarin fisge rigar amma sai da Inna ta dangwarashi ga Abdallah

. Aikuwa ya fara zazzare ido cikin tsoro ya kalli idon Inna da ta ɗaure fuska ya maida kallonsa kan Hassan sannan ya kalli Abdallah da zuwa lokacin bakinsa ne kawai ke motsi ba ma a jin abin da yake cewa.

“Yo kai Imirana haka ake, ai baƙonka annabinka, amma ka ƙyaleshi a cikin ɗimuwa, kuma da kake cewa ya kasa addu’a yana taken Nigeri’a har ƙwara wata wainar da ta wake kai fa sumewa ka yi da ka ga Hassan a kan ka, kai da kake ubansa bare kuma shi da yake abokinka”

Imran ma dai ya kasa magana dan ganinsa dab da Hassan sai ya ji ya nemi nutsuwarsa ya rasa.

Yiiii, wayyo, a kirawo tawagar sojoji su zo da bindigo su haɗo har da igwa (Motar harbi ta sojoji) Su kawo mini ɗauki” Abdallah yake sumbatu cikin tsoron yana sakin kuka.

“Wallahi babu mai harbe Hassan kawai ku yi addu’a ya dawo halittarsa ta mutane” Cewar Inna da ke tsaye a kan su Abdallah, cikinta har murɗewa yake kan dariya.

Sadiya da tun da aka fara abin ta zabga uban tagumi hakan ya mantar da ita cewa tana taɓa Hassan ya dawo mutum, sai yanzu da Inna ta faɗa ta tuno da sauri ta tashi ta je wurin Abdallah ta taɓa Hassan aikuwa cikin sauri sai gashi ya dawo mutum tare da sakin kuka, ɗaukansa ta yi, Abdallaj da matarsa da Amira suka bi Sadiya da kallo cikin mamakin ganin tana taɓa yaron ya koma mutum.

Imran gefe ya rarrafa jikin ɗaya kujerar da matad Abdallah ta tashi ya je yana daga kan gwiwoyinsa ya kwantar da kansa a kan kujerar ya rufe idanunsa tare da sakin wata ajiyar zuciya.

Sadiya saka Hassan ta yi a nono, kafin su ankara matar Abdallah ta ja ƴarta sai ganinsu suka yi a bakin ƙofa. Shi ma Abdallah da jikinsa ya mutu murus tsabar kaɗuwar da ya yi, yunƙurin tashi ya yi, bayan wandonsa har da danshi-danshin lema wataƙila ya fara sakin fitsari ne tsabar tsoro.

“To fa yau ake yinta, lallai akwai maza, akwai mata maza, akwai muna maza kuma alamar ƙarfi dai tana ga mai ƙiba, yau dai mun tabbatar duk girman ɗan tsako ƙwai ya fishi, soja kake ko sojojo, wallahi yau dai sai matarka ta maka ruwan zafi za ka ji dama-dama saboda mutuwar da jikinka ya yi, in kunne ya ji jiki ya tsira” Cewar Inna tana kallon Abdallah da ya tashi dakyar ga nauyin jikinsa ga nauyin tsorata.

“Imran za mu wuce” Cewar Abdallah cikin sanyin murya, ya faɗa yana kallon Imra n da ya ɗora kansa a kan kujera yana sauke numfashi da ɗaɗɗaya idanunsa a rufe.

“Uhm, to,to, har za ku tafi?”

“Ya har za mu tafi baka gani abin da ya faru ne ko kai makaho ne” Abdallah ya faɗa yana ɓata rai, ga haushin Inna da yake mugun ji sai dai ya yi alƙawarin sai ya ɗau fansar wulaƙancin da ta masa yau. Haka ya juya yana shirin fita daga ɗakin Sadiya ta ce .

“To muna godiya ƙwarai, mumyn Amira ku gaida gida”

“Gida ya ji” Cewar Mummyn Amirar amma Abdallah da ido kawai ya bita bai ce komai ba. Imran ma miƙewa ya yi zai musu rakiya, yana kallon Inna da ta kafe su da ido shi da abokinsa tana sakin wani murmushin jin daɗi da alama wasan da ya gudana ya mata daɗi.

“To Sojojo ka gaida gida sai kuma ranar suna, kar kuma in kuma jin ko da wasa ka kira kanka Soja marmari daga nesa, in kunne ya ji jiki ya tsira, kai kuma Imirana ka dawo yanzu ka riƙe mata Hassan ta yi wankan yamma” Cewar Inna har lokacin bata tsagaita da dariya ba.

Fita suka yi suna tafiya kamar mararsa lafiya, dakyar Abdallah ya iya buɗe ƙofar motarsa ya shiga, matar ma da kanta ta buɗe suka shiga da ƴar saɓanin kullum da shi ke buɗe musu su shiga ya rufe.

“To Abdallah nagode Allah bar zumunci, ranar friday ne sunan” Cewar Imran da ke riƙe da marfin ƙofar. Shiru Abdallah ya yi bai ce komai ba.

“Sojojo, Sojojo, kai Sojojo” Cewar Inna da ta fito daga cikin gidan riƙe da ledar viva.

“Imirana tsayar da su sun yi mantuwa” Cewar Inna tana ƙarasowa.

“Ga kayanku kun manta”

“Ki mayar na babies ne da muka kawo”

“To,to,to, Allah amfana madallah, Allah sa a daɗe ana yi sai kun zo suna” Ta faɗa tana juyawa ta koma cikin gida.

 

 

Masu son a tallata musu hajarsu 09030283375
[24/03, 5:13 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa’iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

Back to top button