Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 62

Sponsored Links

PAGE 6️⃣2️⃣

 

Abba cire hular kanshi yayi dan ji yakeyi komai zafi yake mai suna cikin tashin hankalin da Allah ne kaɗai ze kawo musu mafita dakuma sa musu hakuri azuciyoyinsu amma kuwa sunyi Babban rashi arayuwarsu basaji da akwai wata yarinya dazata iya maida musu gurbin fanan.

Yaseer ne ya ce ” doctor yanzu menene mafita ? Kuma tsawon wani lokaci zedauka kafin ya warke?” Doctor ya ce ” ya danganta daga yanayin treatment din da majinyacin yasamu ne , mutum ze iya warkewa daga wata uku zuwa wata shidda , amma shi Broca’s aphasia cikin biyu ne inhar yadade ajikin mutum be warke ba so , wannan majinyacin ze iya rasa ranshi , yanzu de inhar ana bukatar abashi kulawa na musamman sede kufitar dashi abroad acan ne suke da manyan psychologist cikin yardar Allah Mr azaad ze warke ” jinjina kai sukayi cikin gamsuwa da bayanin da doctor ya musu Abba ya ce” mun gode sosai doctor ” murmushi yayi ya ce” bakomai akwai doctor dazan hadaku dashi a India babban psychologist ne sunanshi doctor Shankhar ” Kiran number doctor Shankhar doctor yayi ya mishi bayanin komai sannan yabawa Abba number nashi , yaseer na rike da little twinkle se kallonta yakeyi wata doctor ce ta shigo tace ” yallabai kabani ita angama preparing NICU ( neonatal intensive care unit” din ” miƙa mata twinkle yayi yanajin wani irin abu na sukanshi aranshi, haka doctor tashiga da twinkle akasata acikin NICU.

Fawwaz areef dasu ummi na zaune da Mr azaad da kanshi ke kallon ƙasa yayi shuru yazubawa waje daya ido kamar me nazartan wani abu, shigowa Abba da yaseer sukayi tare da doctor din Abba yazauna kusa da Mr azaad ya ce ” son katashi mu tafi gida ko ” ” duk fa maganar da zakuyi bajinku yakeyi ba balle yamaido muku da amsa ” cewar doctor,duk zubawa Mr azaad ido sukayi cikin tausayawa ummi ta ce ” barin inje wajan mamansu ” tafada tana mikewa ɗan bazata iya cigaba da kallon halin da Mr azaad yake ciki ba , bin bayanta zeenat da anty amina sukayi izuwa dakin da aka kwantar da mama, tana zaune akan gadon ta farfaɗo baba,ya usman, hairah, auta, suhaima,hafiz duk suna dakin sunyi ta gumi babu wanda yake iya magana acikin su , shigowa sukayi ummi ta zauna kusa da mama , rike hannun mama ummi tayi ta ce ” mamansu hakuri zamuyi saboda me faruwa yarigada yafaru , babu abinda feena take bukata agurinmu sama da addu’a, duk da rabuwa babu dadi amma mu abin alfaharinmu ne yau a ce yarmu tazama jarumar datayi nasara akan azzalumai harkuma takawo ƙarshensu , kuma koda wannan tafiyar nata be rabamu ba to tabbas mutuwa zata rabamu hakuri da tawakƙali shine abinda yakamacemu , itakuma muyi mata addu’ar nasara in kuma munada rabo da sake ganin ta Allah yatabbatar da ikon sa” maganganun Ummu sun ratsa mama sosai ajiyar zuciya tayi kafin ta ce” ina Azaad ?” ummi ta ce” son yasamu matsalar kwakwalwa yanzu haka anfara shirye shiryen fita dashi India twinkle kuma ansata acikin kwalba ” wani hawayene me zafi yazubo a idon mama jin Mr azaad yasamu matsala a brain dinshi, jikarta kuma tana cikin kwalba.

 

Haka wa’yannan ahali biyun suka tashi daga happy family izuwa sad and broken family, haka gidaje biyun nan suka rasa duk wani walwalarsu da farin cikin su , cikin kwana biyu aka gama shirya tafiyar Mr azaad , Abba da Fawwaz se yaseer ne zasu tafi dashi mama ma an sallameta sun koma gida , kusan kullum ummi da zeenat suna zuwa gidan .
Suhaima kuma ta roki Fawwaz akan yabarta tadanyi kwana biyu agida tare da su mama , kuma ya amince da hakan.

Suna zaune a falo kowa yayi shuru ko wannensu da abinda yake saƙawa a zuciyarshi , Mr azaad na kwance akan kujera kanshi akan cinyar ummi , da gudu Hafiz yasauko downstairs Abba ya ce ” Hafiz lafiya kuwa” sa hannu yayi ya dauki remote kafin ya ce ” bakuga labaran yau ba? Ko ina maganar anty fanan akeyi ” ya karishe maganar yana kamo tashar BBC Hausa duk mayar da hankalinsu kan tv sukayi banda Mr azaad dabemasan meye sukeyi ba balle yasan me suke fada.

Video ne da CCTV Camera yadauketa na duka asibitocin da taje ta taimaka musu da kuma short video lokacin da suka rungume juna itada Mr azaad ga kuma twinkle dake hannun Mr azaad, se playing din videos din akeyi again and again aƙasa a rubuta ‘the warrior ‘ wani journalist yafara kwararo bayanai ” wannan dakuke gani ita ce Jarumar da ta cece rayuka bila adadi, kwana biyu dasuka wuce wanda a wannan ranar ne muka tashi da tashin hankali mara misiltuwa , kamar yanda kuka gani a wannan dauka na CCTv camera ita ce ta cece jarirai da ake kokarin kashewa da kuma mata masu ciki da masu jego, dama ako ina Allah baya taba goyon bayan zalunci shisa yaturo mana da wannan baiwar Allah. Allah yashiga tsakanin mu da mugaye azzalumai yayi mana tsari dasu itakuma Allah yabiya mata bukatunta na alheri yabata Sa’a akan abinda tasa gaba, ya Allah ya kare ta aduk inda take , ƙasa Nijeriya dakuma ƙetare we’re very proud of her she’s our superstar warrior. Yanzu zakuji daga bakin wa’yanda suka kasance sheda na gani da ido, sune wa’yanda suke cikin asibiti abin yafaru ” magana wani magidanci yafara ” sunana Abubakar lawan . wato abinda yafaru shekaranjiya tabbas ni ganau ne ba jiyau ba domin nakai matata haihuwa ne wannan lamarin ya rufta damu a asibitin wannan baiwar Allah ita ta cece jaririnmu dakuma matata bazan taba mantawa da ita ba kuma , itadin matace ga azaad the billionaire sannan sirka ga ahalin mainasara, yanda ta taimaka mana Allah ya taimaka mata ya shige mata gaba aduk lamuranta ” haka sauran da aka gayyato suka dinga fadar irin aiyukan da fanan tayi da taimakonsu datayi, haka aka dinga hasko hotunan fanan ta ko Ina yazamana labarinta akeyi , ko ina aka waiga jama’a se addu’a sukeyiwa fanan manya da yara, kowa se bashi dama akeyi yana fadan ra’ayinsa dangane da fanan kowa alkharinta kawai suke magana .
Duk jikinsu yayi sanyi ganin irin yanda al’umma tun yanzu sunfara alfahari da fanan ko ina yabonta akeyi , guntun hawayen da yazubowa ummi ne tasa hannu ta share , Abba ya ce ” Allah mungode maka ” tashi yake kokarin yi idonshi yasauka akan video fanan da ake nunawa a tv asukwane yakarasa tashi yanufi tv da gudu yasa hannu yana shafa ” wifey kalleni , ki kalleni wifey kizo mu tafi gida kinji ” dasauri suka bi bayanshi zuwa wajan tv ganin yanason birkicewa lokaci daya, dukan tv yakeyi da iya karfinshi wai anashi tunanin yanason yafito da fanan din ne dake cikin tv ,dunkule hannunshi yayi ya bugawa tv wanda seda yayi sanadiyar wargajewarsa raga_raga rikoshi Abba da Fawwaz sukayi yanata sambatu yana kiran sunan fanan, su biyu suke rike dashi amma sun gagara mishi rikon da baze kubce ba ,fisgewa yayi yahaura upstairs da gudu yashiga part dinshi yarufe yasa key .

Yaseer ko magana ya kasayi yana zaune yayi tagumi abin duniya yadameshi ganin yanda babban amininsa da bayida kamarshi yana cikin wani hali, hawaye yataru a idonshi. Ummi kam izuwa yanzu bata iya controlling din hawayenta idonta sunyi ja sosai, daga ranar da fanan ta tafi izuwa yanzu kullum a cikin kuka suke da damuwa.

Haka abangaren su mama duk suna kallon labarai da suke yawo a gidajen rediyo da kuma social media, murmushin takaici kawai mama tayi aranta tanayiwa fanan addu’a.

Yau Flight dinsu Mr azaad yatashi zuwa kaishi India suka sauka a asibitin Narayana superspeciality hospital babban asibitine a India da babu kamarshi komai nasu na musamman ne , babban part aka bawa Mr azaad acikin asibitin aranar da sukazo a ranar doctor Shankhar yafara dubashi .
Bayan kwana uku Abba ya koma Nigeria, Fawwaz da yaseer ne zasu zauna tare dashi.

 

Acikin wata daya duk sun rame amma damuwar dasuke ciki yadan ragu dukda bawai yafita azuciyoyinsu bane kawai suna dannewa ne domin sunyi tawakƙali. Duk bayan sati daya se sunkaiwa little twinkle visit a asibiti suna kallonta acikin kwalba haka ma suna kaiwa Mr azaad visit duk sanda sukaje sesunyi kuka , acikin dakin dayake ko ina yayi bi bangon yazana hoton fuskan fanan da yana kallo shi kadai za’a ga yana magana, amma yanzu abun da sauki.

NASMINAYA.

Tafiya takeyi cikin izza da mulki hade da jarumta, tana sanye da doguwar riga yellow color kanta dauke da crown ( hular sarauta) din sarauta, rigar yanaja abaya kuƴangu suna rike mata da bayan rigar domin yana da tsayi sosai , jikinta tako ina tasha ado da zinari, fatar jikinta se yalki yakeyi da idanunta , gashin kanta yana abaje shima an mishi kwalliya da gold sosai tayi kyau , fuskanta babu ko da alamar murmushi. Tunda suka nufo hanyar fa da ake mata bushen sarewa duk inda ta wuce se an sunkuya an gaisheta sannan bazasu tashi ba seta wuce tukun zasu iya mikewa , tana shigowa fa da duk suka zube akan guiwowinsu suna ɗiɓan gaisuwa agun babban sarauniya, zama tayi akan kujeran mulkin da aka ƙawa tashi da lu’ulu’u ta ɗaura ƙafarta daya kan daya daga musu hannu tayi alamar ta karbi gaisuwar sannan suka koma suka zauna , manyan sarakunan aljanu ne takowa ni bangare sunzo ne domin yi mata barka da zuwa , agefenta kuwa akwai kujeran gimbiya afroza da na yarima ahil se kuma na manya masu muƙami a nasminaya irinsu galadima abdud Shakur da jakadiya da sauransu , tashi sukayi suna gabatar mata da kansu , haka ranar sukayi shagali sosai domin farin cikin dawuwar sarauniyarsu abin sonsu.

 

AFTER THREE MONTHS

Gangarowa zeenat tayi daga upstairs tadan rame ga cikinta da yafara fitowa tana ” ya areef wai kai da Hafiz baku gama bane nifa nashirya dan Allah kuzo mu tafi kunga su Abba sun riga da sun tafi ” tayi maganar tana saukowa daga staircase din , areef ya ce ” muje mungama muma” fitowa sukayi zuwa packing lot suka shiga motar areef yayi driving dinsu zuwa medical center. Ciki suka shiga ɗan karasawa inda su ummi suke , samunsu sukayi suna rike da baby a hannunsu se wasa sukeyi mata tasha hadaddun kayan baby Pink color , suna cikin farin ciki da sauri zeenat ta isa inda suke tsaye din ta ba ta fuska ta ce ” amma ai bahaka mukayi ba , Ni ce fa nace aduk sanda akazo daukan twinkle I will be the first person to carry her amma yanzu kun bata min Abinda nake matukar jira” du ka dariya sukayi jin maganar da zeenat tayi Abba ya ce ” to zee yanzu ma ai gata nan ” miƙa mata twinkle ummi tayi ta karbeta tana washe fuska se kallonta takeyi, fuskar fanan sakk take gani ana twinkle tsabar yanda kamanninsu yaɓaci sede fatar Mr azaad ne da ita , idonta arufe hannunta na cikin bakinta tana tsotsa hawayen da yazubo daga idon zeenat ne yasauka akan kumatun twinkle mutsu_mutsu tafarayi kamar zatayi kuka taname bude idonta kadan sannan ta rufe , zaro ido waje zeenat tayi lokacin dataga kalar idon twinkle da karfi ta ce ” laaah kuga ikon Allah idonta brown color ne irin na kaka me martaba ” zubawa twinkle ido sukayi suna jiran suga ta bude idon nata aikuwa tasake budesu , tabbas idonta iri daya dana me martaba shi ta gado a kwayar halittar ido kenan sannan natama yafi nashi nata brown ne sosai , haka suka koma gida cike da farin ciki bayan awa daya zuwa biyu su suhaima sukazo ganin baby amma banda mama da baba .
Baby girl gata nan yar lukuta da ita ga farin fata se karbanta sukeyi suna santin jaririyar sunayi mata photos suna turawa Fawwaz da yaseer da suke India su kansu sunyi farin ciki , adaren ranar me martaba da Fulani sukazo ganin jaririya aka tsayar da ranar suna nan da sati daya.

Tun bayan tafiyar fanan basu sake tsinkayar kansu acikin farin ciki ba se zuwan twinkle ita kadaima insuka gani ransu nayi musu sanyi domin suna kallon fanan atattare da ita, har yau daya kasance gobe suna baba da mama basu sa twinkle a ido ba sede a hoto ne suhaima da ya usman suke nuna musu ita , su umma rahina da amira da ya al ameen sunzo saboda suna da za’ayi.

 

INDIA
NARAYANA SUPERSPECIALITY HOSPITAL

 

Yau tunda suka tashi doctor yazo ɗan ganin ya yanayin condition din Mr azaad yake saboda yanzu ne yacika wata uku da sati biyu inhar de be samu lafiya a wannan lokacin ba to fa sede afara mishi shirye shiryen treatment din wata shida, yaseer da Fawwaz suna zaune akan kujera suna ganin yanda doctor din yake kokarin yin conversation da Mr azaad amma yakiyin magana ,yau haka suka tashi dashi ko irin dan sambatun da yake yi ma beyi ba yana zaune yabasu baya yana kallon waje daya, doctor Shankhar ya ce ” Mr azaad don’t you want to speak to me today?” Ko kallon inda yake Mr azaad beyiba doctor Shankhar yasake cewa ” alright is okay, but do you know that you’re a father now ?” kamar daga sama batare da sun taba tsammanin hakan ba kokuma tunanin haka ze faru ba , sukaji Mr azaad yabawa doctor Shankhar amsa da” Yes i know ” shikanshi doctor Shankhar seda yaji kamar kunnen shine ya mishi gizo yasashi sake cewa ” okay do you know you’re a father right?” murya adaƙile kamar wanda ake takurawa cikin rashin sonyin magana ya ce” Yes i know and please don’t disturb me ” atare Fawwaz da yaseer suka ɗaga hannu sama suna godewa Allah matsanancin farin ciki suka shiga wanda baƙi baze iya faɗa ba zama sukayi kusa da Mr azaad fuskokinsu dana doctor duk na dauke da murmushi, congratulations doctor yayi musu sannan ya ce nanda One week za’a sallameshi , kafin doctor Shankhar ya rufe baki Mr azaad ya ce ko kwana ɗaya baze ƙara a asibitin ba , yanayin yanda yake magana kaɗai ma mutum yaji yasan ya canza sosai domin inyana magana ko ɗago kai ba yayi balle ya kalli me mishi magana miskilanci yaƙaru fiye da na da . Sallama doctor yayi musu yafita, yaseer ya ce ” dude nayi farin ciki sosai da Allah yabaka lafiya” banza yayi dashi kamar be jishi ba se bayan minti goma ya ce ” ina twinkle?” Fawwaz ya ce ” an karbota a asibiti,gobe za’ayi sunanta” tundaga nan besake ce musu komai ba ya mike yashiga toilet bin bayanshi sukayi da kallo , ganin a ƙashi ɗari na halinshi nada yanzu ƙashi 90% yadawo, saboda dama shigowar fanan rayuwarsa ne yasa yarage amma yanzu sundawo fiye dana da dinma , suna magana yafito daure da towel a kugunshi kallonsu yayi be ce musu komai ba dan maganar ma wahala yake bashi , fahimtar abinda yake nufi da sukayi ne yasa Fawwaz mikewa yabude wardrobe a bangaren da kayanshi yaje ya fito mishi da jallabiya fa ra , karba yayi ya koma toilet din yasaka yafito fuskan nan adaure kamar wanda besan menene kalmar dariya ba arayuwarsa.
Sude se aikin binshi da sukeyi da ido , Dan sunsan ko sunyi mishi magana ma ba kulasu zeyi ba hakan yasa suka zuba mishi ido kawai, kira ne yashigo wayar yaseer number Abba ne dagawa yayi suka gaisa sannan ya tambaye shi Mr azaad , girgiza mishi kai Mr azaad yayi alamar kar ya ce musu komai. Kamar yanda ya buƙata haka yaseer yayi yace mishi yana nan lafiya haka suka gama magana sannan ya katse kiran.

” Fawwaz kayi mana booking flight ayau din nan zamu koma Nigeria”. ” okay ” Fawwaz ya amsa sannan yayi musu booking flight s online karfe 6:00mp jirginsu ze tashi.
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story & written by ✍️
MRS ISHAM
( Yar lelen Jarumai)

 

* JARUMAI WRITERS ASSOCIATION *

⚜️J. A. W️

 

THE END .

*Wato Hausawa sunyi gaskiya dasukace komai yayi farko zeyi karshe haka zalika laifin daɗi karewa,ya Allah ka yafemin kura kuran da nayi acikin wannan littafin duk wanda na batawa rai yayimin afuwa ya yafemin dan ɗan Adam ajizine . Masu min addu’a da fatan alkhari ina godiya bazan taba mantawa daku ba, masu karfafamin guiwa Kuma ina godiya bazan taba mantawa daku ba domin kun ban babban gudunmawa nagode sosai Allah yabar zumunci*

 

 

Back to top button