Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 59

Sponsored Links

Page 5️⃣9️⃣

 

zeenat ta ce ” anty firdausi nide kibarmin junior dinkin nan wallahi kyau yakemin ” hararanta fanan tayi ta ce ” narigaki malama tun Yana ciki nace inaso ” sa hannu zeenat tayi tadauki junior akan cinyar fanan tadaurashi akan nata cinyar ta ce ” junior kace mata ni kakeso kaji” kamar wata me magana da babba , shide junior se dariya yake mata fanan ta ce ” Allah yashiryeki zeenat yanzu junior kikewa magana?” gyada kai tayi dariya anty firdausi tayi ganin drama zeenat da fanan akan junior , kallon fanan anty firdausi tayi ta ce” muje zamuyi magana ” tayi gaba fanan tabita abaya zama sukayi akan gadonta ta kalli fanan dakyau ta ce ” fatan de yanzu komai normal keda mijinki babu wata damuwa ko?” ta ce ” eh anty firdausi komai alhamdulillah ” hakan yayiwa anty firdausi dadi , ta bata shawarwari da koya mata wasu abubuwan bude wata karamar wardrobe tayi tafito mata da magunguna dakuma mayukan gyaran jiki, dasu turarurruka masu yawa ta saka mata su a yar jaka me kyau sannan ta fada mata yanda zatayi amfani dasu godiya fanan tayi mata suna cikin hira taga Kiran Mr azaad dagawa tayi , ya ce” dare yayi kuzo mutafi ” yana gama fadin haka yakatse kiran, fitowa sukayi tare ita da anty firdausi suka samesu a falo sundawo ga zeenat dake wasa da junior, mikawa anty firdausi junior tayi tana ” senazo karbanshi ya yini awajena ” daddyn junior ya ce ” to shikenan sekinzo” haka suka rakasu packing space daddy junior nayi musu godiya sosai domin ya matukar jin dadin ziyarar da suka kawo mishi , sukayi musu adduah Allah yakiyaye hanya, suna tafiya akan hanya daga can nesa zeenat ta hango me soya awara murya asanyaye ta ce ” ayyah ya azaad dan Allah katsaya agun me awaran can ” juyowa yayi yawatsa mata banza kallo ya ce ” wato harkin mata da abinda yafaru dake ko ? baki daddara bako ? kisakemin maganar wani abun akan titi kiga iKon Allah” yafada yana kara wurga mata harara shuru bata sake cewa komai ba jikinta yayi sanyi , amma harga Allah kwadayin awaran take , tunkafin zeenat tahango me tuyar awarar fanan ta ganta tana kokarin yi mishi magana se zeenat tarigata jin amsar dayabawa zeenat ne yasa tayi shuru takama bakinta amma ita yanzu hakama ji takeyi in bataci awara ba bazata iya bacci ba , haka suka wuce masu suyar awaran sunaji suna gani Mr azaad ya hanasu siya .

8:12pm dede suka shigo gida zeenat ce tafara fita a motar tashiga gida fita yayi harya fara tafiya yajuya ze riko hannunta yaga wayam batama fito ba tana cikin motar komawa yayi yabude mata murfin motar still bata fito ba kanta akasa tana wasa da yatsunta, sa hannu yayi yadago fuskanta zaro ido yayi ganin yanda fuskanta yayi jaga_jaga da hawaye , mamaki yafara meye aka mata take irin wannan kukan riko hannunta yayi ya ce ” baby meyafaru kike irin wannan kukar” kamar wacce take jira yayi magana takara volume din kukanta harda shesheka, tsugunawa yayi agabanta yana rike da hannun nata yazubawa sarautar Allah ido kuka takeyi bil hakki kamar wacce akawa mutuwa tambayarta yayi ko wani abun akamata tayi mishi shuru lallashinta yakeyi Amma kamar zugata yakeyi, haryama rasa me zece mata kawai yazuba mata idanunshi, seda tayi kukanta son ranta sannan tayi shuru da kanta har lokacin Mr azaad yana tsugune agabanta rike da hannunta, ganin tayi shuru ne yasa ya ce ” sorry wifey fadamin meye mekikeso ” ajiyar zuciya tasauke tagoge fuskanta da hijab murya ashagwabe ta ce ” bakai bane ba” nuna kanshi yayi da yatsa ya ce ” nikuma menayi miki?” turo baki tayi ta ce ” bakai bane ba kace bazaa siya awara ba bayan inason ci” sake hannunta yayi yadafe kanshi aranshi yana” ya salam yanzu dama akan wannan abun tatsaya tana kuka lallai mata rigimammune ” tsaban yanda yake cike da mamaki hade da al ajabi gagara cewa komai yayi se binta da kallo dayakeyi sake fashewa da kuka tayi ganin yazuba mata ido kuma shi bece mata komai ba , zaro wayarsa yayi ya kira layin faisal bugu biyu yadaga abangaren faisal yagaishe shi be ko amsa gaisuwar ba ya ce ” akwai wani abu ana siyarwa akan titi please kasiyowa wifey yanzu ” daurewa faisal kai yayi domin shi besan tankamemen abinda zaa siyoba tunda bawai yafada mishi sunan abun bane ya ce ” sir to meye sunan abinda zaa siyo din ?” shuru fanan tayi tana aika mishi da harara jin yatsaya yanawa faisal kwantancen abinda shikanshi be sani ba bekuma fadi sunan ba , yafi tsawon minti 10 yanawa faisal kwantancen amma be gane ba gashi Mr azaad ya manta sunan abun Kuma be tambayi fanan ba, iya cika fanan ta cika tazo har wuya takaici kamar ta tashi tabar mishi wajan shi besan abu ba Kuma baze tambaya afada mishi sunan ba gashi dare karayi yakeyi , sa hannunta tayi ta zare wayar akunnenshi tasa a handsfree, sallama tayi jin muryanta yasa faisal gaisheta, ” faisal awara ne zaka siyo , amma danye wanda baa soya ba dan Allah” tafada tana murgudawa Mr azaad baki murmushi yayi dan yasan acike take jira takeyi yace wani abun ta taso mishi da sabon rigima . faisal ya ce ” madam eh zaa samu dan kanwata ma tanayi na order yanzu haka bari in karbo miki ” yafada yana kunshe dariya wato mace de babu yanda bata juya namiji gashi oganshi lokaci daya matarshi tajuya mishi lissafi mutumin da maganar mint 2 ma bayi yakeyi ba amma yau dake tanason abu yatsaya yana bayani kusan na 10mint mata mutanen mu. godiya tayi mishi takatse kiran tana mika mishi wayarshi karba yayi yana kallon fuskanta da ta daureshi ita dole fushi takeyi bata kalli inda yake ba tadauki jakar da mama tabata dana wanda anty firdausi tabata tayi gaba ta barshi abaya , tafiya takeyi batako juyo takalleshi ba balle tasan yana binta abaya hannu daya yasa yadagata sama kamar wata yar tsana , mutsu_mutsu tafarayi na sede ya ajiyeta akasa ta tafi da kafarta be saurareta ba seda suka kusan isowa falo sannan yasauketa yarike hannunta suka shiga falon ba kowa aciki, kowa na part dinshi , part dinsu suka shiga zama fanan tayi akan kujeran falo tana ” washh nagaji ” tafada tana bude fashion bag din da mama tabasu ciro hadaddiyar liffaya tayi me matukar kyau multi color jikin liffayan yasha manyan stones bakaramin kyau yayiwa Mr azaad ba, har imagine kayan yakeyi ajikin fanan intasa ,shafa liffayan yayi ya ce ” wifey kayan nan zasuyi miki kyau sosai” har ranta taji dadi yanda ya yabi kayan dukda inde tayi kwalliya seya yabi kayan dakuma irin kyaun da tayi. maida kayan cikin gidanshi tayi ta ajiye agefe kallonta yayi ya ce ” wifey amma ai nima zaa ban tsumin in sha ko ?” Kallonshi takeyi bako kyaftawar ido mamaki ne yakusa sumar da ita aina yaji maganar tsumi kuma saboda tasan itade bata mishi ba sannan bawai bude jakar da anty firdausi tabata tayi ba , cikin inda_inda ta ce ” habiby tsumi kuma?” dariya taso bashi amma yafuske ya ce ” yes up course tsumi kuma inzakisha kimin magana musha tare ” kunya kamar fanan ta nutse kasa tama rasa mezatace mishi , dariya kasa_kasa Mr azaad yakeyi dan tun dawuwarsu daga masallaci suna kokarin shiga falon gidan anty firdausi yaji duk hiran da sukeyi murmushi yayi aranshi ya ce ” Allah de ya biyaki maman junior” knocking sukaji Mr azaad yace ashigo Faisal ne yashigo hannunshi rike da food flask me girma ya gaishesu hade da ajiyewa akan table ya musu sallama ze tafi fanan ta ce ” ah ah katsaya agama soya awaran ” dadi sosai faisal yaji yana kara yabon matar oganshi nashi da irin kirkinta fita yayi zuwa main falo dan shigowarshi yabar zeenat da yaseer suna hira se fawwaz da areef sukuma suna kallon ball zama yayi ya jonasu shima. daukan kulan tayi zuwa kitchen taname jin dadin samun danyen awaran da akayi gyarashi tayi sosai ta soyashi sannan tayi sauce din hanta me dadin gaske, ta dafa kwai .
ba ita tagama ba se karfe tara saura kuloli madedeta ta dibo tasawa ummi nata tasawa abba nashi sannan se nata da Mr azaad, tasan su anty Amina suna tare dasu anty shayida tasa musu , se su fawwaz da areef da zeenat se kuma tasawa faisal dakuma hafiz nashi duk da haka awaran yarage nan ta sawa masu gadi da securities din gidan zuba kulolin tayi acikin basket taga basu shiga duka ba dauko wani basket din tayi tasa sauran kulan tafito rike da basket duka biyu a hannunta se nishi takeyi, tunda tafito daga kitchen Mr azaad yake kallonta yanayin ka zar _ ka zar dinta batada gandan aiki she’s not that lazy yana burgeshi amma bayason tadinga shan wahala. tunkafin takaraso yamike yakarbi basket daya ahannunta ajiyar zuciya tayi saboda daukan basket din datayi setaji duk ta gaji sosai kamar wacce tadau buhun cement ta ce ” thanks habiby dama downstairs zanyi amma mufara zuwa part din ummi ” bece komai ba yariko hannunta dan yaga kamar agajiye take sunje sunyi ziyara sannan tana dawuwa tashiga kitchen yanzu kuma zata kai musu . tausayi tabashi dan seyanzu yake ganin laifin kanshi dan da tun farko ya tsaya an siya awaran da yanzu awuce layin amma shi yaji tsoron hakan ne saboda abinda yataba faruwa da zeenat, part din ummi suka shiga nan ma ba kowa bedroom dinta sukayi sallama ta amsa hade da cewa ” ku shigo ” shigowa sukayi har a lokacin hannunsu na sarke dana juna murmushi ummi tayi ganin sune zama sukayi akan kujera fanan ta gaisheta hade da mata taaziya amsawa ummi tayi ta ce ” ya kika baro gidan naku fatan kowa lafiya? ”
” lafiya lau ummi ” fanan ta fada tana fito da food flask madedeci dake dauke da awara da sauce din hanta da dafaffen kwai ta ce ” ummi ga awara ” ta karishe maganar tana ajiyewa akan center table murmushi ummi tayi ” ahh lallai my feena sannu da kokari yanzu awannan daren kika tsaya yin awara kindebo gajiya sannu ko kidena wahala kinji ” ummi ta fada tana kallon fanan din da ta sunkuyar dakai kasa tana murmushi zatayi magana kenan Mr azaad yarigata da fadin ” ai yau ita da zeenat sekinga yanda suka dameni akan awaran nikuma naki saya akan titi gudun abinda yafaru yasake faruwa amma wannan feenan naki wallahi sekinga kukan datakeyi min akai ” yagama magana yana jan kumatun fanan dake muntsininshi , dariya sosai ummi tayi dantaga muntsin da fanan takeyiwa Mr azaad sake kallon fanan din tayi dakyau taga tayi fresh sosai tayi kiba tunani tafarayi kode fanan nada ciki saboda wasu sign din datagani amma bari zatayiwa Mr azaad magana yakaita asibiti agwada Allah yasa cikin ne dasunyi matukar murna , mikewa sukayi zasu tafi ummi ta ce ” nagode miki sosai daughter dama nadade banci awara ba Allah yamiki albarka” amsawa fanan tayi da ” ameen ameen ummina” suka tafi harsuka fita tana binsu da kallo taname godewa Allah daya nuna mata matar Mr azaad dan babu wanda yayi tunanin zeyi aure nan kusa kafin ya auri fanan ko andago maganar aneesa seya nemi hanyar da yasa se an kwantar da maganar finally gashi yanzu yayi aure kuma alhamdulillah suna farin ciki da matarshi bude kulan awaran ummi tayi kamshi yabugi hancinta faracin awaran tayi tana jinjina kai dan bata tabacin awara me dadin wannan ba haka tagama se Santi takeyi tana sawa fanan albarka.

Suna fitowa daga bedroom din ummi suka shiga na anty amina suka same anty amina da anty zainab suna hira sama_sama akan kujera anty shayida kuma tana kishingide akan gado ta rufe idonta kamar bacci takeyi amma idonta biyu takoma abin tausayi dan tagama waya da mijinta da baya Nigeria yatafi Egypt kenan ta kwanta tana jin duk hiran dasukeyi , gaishesu fanan tayi hade da musu taaziya zama tayi kusa da anty shayida datake jinsu hannunta fanan tarike murya asanyaye ta ce ” anty shayida” bude idonta tayi akan fanan tayi mata murmushin yaqe ta ce ” naam feena ” gyara zama fanan tayi ta ce ” anty shayida dan Allah kidena sawa kanki damuwa haka karki kamu da wata cutar daban tabbas abin da ciwo amma kiyi hakuri kimika lamarinki ga Allah komai zewuce in sha Allah mommy kuma muta binta da adduah” siraran hawaye ne yake fita daga idon anty shayida tasa hannu ta goge sosai kalaman fanan ya kwantar mata da hankali ta ce ” nagode sosai feena samun yarinya me irin hankalinki awannan zamanin se antona! bawai nadamu da mutuwar mommy bane wallahi ah ah bandamu ba domin kuwa kowa ze mutu duk zamu koma ga ma haliccinmu amma ina tuna irin mugun tabon datamin wai ace mahaifiyata ce tamayar dani juya karfi da yaji , feena sau takwas fa inasamun ciki yanzu kila bazan taba samun wani cikin ba ” duk ta kashe musu jiki mugun tausayinta ne ya kamasu mommy ba karamin illa tayiwa rayuwar anty shayida ba, anty amina da anty zainab duk idonsu ya taru da hawaye sun kuma ji dadin zuwan fanan domin kuwa yanzu anty shayida ta amayar da abinda yake damunta tunda akasa mata drip tayi bacci ta tashi babu wanda takeyiwa magana sede ta girgiza kai tsoro sukaji kar tashiga depression amma zuwan fanan yasa tayi magana ta amayar da abinda yake zuciyarta, mikewa Mr azaad yayi yazauna akusa dasu shima yarike dayan hannun anty shayida ya ce ” meyasa zakice bazaki kara haihuwa ba ? baa cire rai daga rahamar Ubangiji kidena irin wannan maganar kinji komai yayi farko zeyi karshe ” ajiyar zuciya tasauke tana fadin ” nagode muku sosai kannena Allah yabarmu tare kuma in sha Allah zanyi amfani da abinda kuka fadamin ” duk murmushi nadauke akan fuskansu ganin ta sa ki ranta har ana hira da ita mikewa fanan tayi tadauki kulansu ta ce ” ga awara dazun nayi ” jinjina mata sukayi suna yar dariya anty amina ta ce ” ahh lallai feena sannunki da kokari da wannan daren yin awara kode munsamu karuwa ne ?” ta fada cike da zolaya kallon juna Mr azaad da fanan sukayi ya kashe mata ido daya itade kunya takeji se rufe ido takeyi tana buya ajikin anty shayida sosai anty shayida take dariyar fanan da take buya ajikinta dan anyi maganar ciki , bude kular anty amina tayi tana ” wow irin wannan liyafar haka godiya muke ” tunkafin takarasa abinda zata fada sukaga anty shayida ta toshe hancinta sannan daga baya ta tashi da gudu tafada toilet tana sheka amai kamar zata amayar da hanjin cikinta rufa mata baya sukayi banda Mr azaad daya fita a bedroom din yana kayittaciyar murmushi, taimaka mata sukayi ta gyara jikinta suka riketa suka fito aka zaunar da ita akan bed , muryanta kamar zatayi kuka ta ce ” dan Allah ku rufe awaran nan please” rufewa sukayi sunayi mata sannu duk basuyi tunanin wani abu ba duk gani sukeyi kamar zazzabin da takeyi ne hakan yasa anty amina kara kiran layin doctor safiya ta sanar da ita abinda yafaru abangaren doctor safiya ta ce ” Kinga dare yayi dana dawo amma yanzu kinsan me dazun nayi mantuwa adakinki kiduba zakiga handbag dina akwai PT aciki seku gwada fitsarinta ” tunda doctor safiya tafara jawabi jikin anty amina yake tsuma jira kawai takeyi tagama jin abinda take fada ta aiwatar cikin sauri tadubo handbag din aikuwa taci karo da PT dauka tayi taje kusa da anty shayida ta ce ” anty shayida tashi muje toilet mugwada yin abinda doctor tafada ” batare da musu ba anty shayida ta mike anty Zainab ta kamata suka kaita toilet suka barta tayi fitsarin acikin wata yar container tabawa anty amina suka barta a toilet din tayi pt din bayan wasu mintuna baro_baro jan layi guda biyu suka bayyana da karfin gaske anty amina tafurta ” alllahuuuuuuuu akhabarrrrrrr ” dasauri tafito rike da PT strip din ahannunta, jin yanda taja kabbarah ne yasa suka taso zasu shiga toilet din sukaci karo abakin kofar toilet din sa hannu anty zainab tayi ta karba tana kallo farin ciki ne mara misiltuwa yakamata tafara ” alhamdulillah! alhamdulillah! alhamdulillah! alhamdulillah ! Allah mungode maka daka nuna mana wannar rana me albarka tabbas wannan kalmar gaskiya ce da akace wani hanin ga Allah baiwa ne , Allah me yanda yaso , Allah mungode maka da sa muna cikin rayayyu dazamu sheda wannar rana me cike da albarka ” rungume juna anty amina da anty zainab sukayi suna murna haka fanan ta rungumi anty amina da anty zainab, tayi matukar jin dadi sosai dakuma taya anty shayida murna .

Zuba musu ido kawai anty shayida tayi dan ita gani takeyi kamar mafarki takeyi jin wai ita akace take dauke da ciki acikin mahaifarta , hawaye masu zafine suke sauka akan kuncinta adduah takeyi Allah de yasa ba mafarki takeyi ba domin tasha yin ire_iren wayan nan mafarkan amma nayau kam fatan ta daya inma mafarkin ne Allah yasa karta tashi ta tabbata ahaka .

Rike kafadunta anty Zainab tayi itama tana hawaye ta na fadin ” Allah ya amsa adduo’in mu shayida! Allah yadubeki da idon rahama bayan shekara goma sha takwas yau gashi kema kinadauke da da ajikinki kinkusa zama uwa alhamdulillah”

tabbas yanzu tasake tabbatarwa ba mafarki bane zahirine yasa ta rike hannun anty zainab da dan karfi kafin ta rungumeta sosai tana adduo’in acikin zuciyarta , raba jikinsu tayi , tayi sujjada taname godewa Allah daga hannunta sama tayi hawaye na kwarara a idonta ta ce ” tabbas baa cire rai da rahamar Ubangiji, nadade da dena tunanin nima zanga jinina wacce na haifa banyi tsammanin bayan wayan nan shekarun zan zama uwa ba se yau Allah nagode maka, ya Allah ka karemin abinda ke cikina daga sharrin masu sharri kasa yafito lafiya ” haka taci gaba da adduah suna amsa mata da Ameen lalubo wayarta tayi tana me dialing din number mijinta kusan missed call biyu tayi mishi be daga ba se daga baya yakirata hannunta na rawa tasa ta daga tana ” alhaji albishirinka ?” yanayin yanda yaji muryanta adashe gakuma yaji ta ambaci albishir ne yasa ya ce ” hajiyata meyake damunki naji muryarki haka ?” bata bashi amsar tambayar da ya mata ba tasake maimaita mishi ” albishirinka?” amsawa yayi da ” goro ” dan yaga inbawai amsar tambayar yabata ba tofa shima bazata bashi tashi amsar ba cike da zumudi ta ce ” Allah ya amsa kukanmu alhaji ni da kai nanda watanni tara masu zuwa inda rai da lafiya zamu zama iyaye ” alhaji auwal aiki yakeyi a laptop yana shigar da wayansu bayanai jin wannan maganar da anty shayida ta furta mishi yasa ya tsayar da komai yaname cire wayar akunnenshi yakalli wayar dakyau sannan yamaidashi kunnenshi murya a sarkaqe ya ce ” hajiyata banji me kikace ba ko Zaki iya maimaitamin ?” Duk murmushi sukayi na farin ciki sunajin abinda alhaji auwal yake fada saboda anty shayida tasa wayar a handsfree maimaita mishi tasakeyi kabbarah alh auwal yayi hade dayin sujjada yana mika godiyarshi ga Allah madaukakin sarki me kowa me komai meyin yanda yaso a lokacin da yaso . kasa magana ma yayi ji yayi yafi kowa murna awannan daren tunda ya karbi sako me matukar girma da daraja sosai sukayi waya dashi sannan yakashe .

daukan basket din duka biyu fanan tayi dan Mr azaad yatafi bedau dayan ba , taya anty shayida murna tayi sannan tayi musu seda safe ta tafi , har yanzu su fawwaz basu bar falon ba dan tun da ta tunkaro downstairs takeji muryansu suna musun ball hangota sukayi rike da basket har guda biyu tasowa areef yayi ya karbi dayar ya ajiye akan table zama tayi ta gaishesu suka amsa suma suka gaisheta kin amsawa tayi yaseer ne ya ce ” antynmu barka da dare ” kallon shi tayi batace komai ba dan tasan tsokana ne kawai can kuma ta ce ” ayyah ya yaseer dan Allah kudena banaso ” kwaikwayonta zeenat tayi tana ” ayyah antynmu kema kidena kin amsawa ” dariya sukayi harda ita fanan din tajefawa zeenat pillow tana ” kekuma zanyi maganinki ” fiitowa kowa kulan awaran shi tayi tabasu suka karba suna godiya Faisal kam ana bashi nashi ya ce ” tom nikam natafi seda safenku madam nagode” yatafi . Fawwaz ne yabude nasu kulan yaga awara ne ya ce ” yau akwai cin dadi irin wannan zazzafar liyafa haka antynmu” murmushi kawai tayi zeenat jin an ambaci sunan awara ne yasa tabude nata kulan ido biyu sukayi da awara ihu tayi ” yessssssss wallahi awara ne” toshe kunne sukayi saboda ihun zeenat datakeyi na farin cikin ganin awara dan tunda suka dawo ta sallamar ba samu zatayi ba harta cireshi arai , kallon fanan tayi ta ce ” gaskiya anty fanan kedin ta musamman ce wallahi Allah ya suburbuda miki albarka muah” takareshi tana yi mata blowing din kiss dariya kawai fanan tayi ta ce ” tom yanzu de gaki ga awara amma kafin ki faraci tashi ki rakani wajan abba inkai mishi nashi ” jikin zeenat har rawa yakeyi dan so takeyi sukaiwa abba sannan ta dawo tacinye nata takuma hada danasu ya fawwaz dan plan din data shirya kenan.

kallon areef fanan tayi ta ce ” nikam ya areef hafiz ya farka ne ?” ” Eh yatashi yayi sallah yasake komawa bacci bayan yaci abinci ” areef ya sanar mata ta ce ” tom ganashi nan inkun shiga ku bashi please”. ” to shikenan antynmu ” tun kafin subar falon ma fawwaz da areef, yaseer sun faracin nasu se santin girkin sukeyi .

Securities kowa nakan aikinshi su fanan sunzo dede inda suke suka gaishesu mika musu nasu kulan tayi ta ce ” bansaniba ko kunacin awara gashi ” sa hannu sukayi suka karba suna ” munaci madam mungode sosai ” wucesu sukayi suka nufi part din abba .yana zaune afalo yashiga duniyar tunani bemasan da shigowarsu ba sakeyin sallama sukayi se anan ne yajisu ya kallesu da fara’a ya ce ” fatima yau kinkawo min ziyara kenan ?” Kan fanan akasa ta ce ” abban barka da dare! ya Karin hakurinmu Allah yajikanta da rahama” nuna musu wajan zama yayi suka zauna , amsawa yayi da ” ameen ameen Fatima ,naji azaad yace gobe zaku tafi ko ? ” ” Eh abba haka yace ” jinjina kai abba ya ce ” masha Allah , Allah yakaiku lafiya ” ita da zeenat suka amsa da ” ameen” ajiye mishi kular awara tayi ta ce ” Abba ga awara ” sa hannu yayi yadauki kular awaran yabude cikin barkwanci ya ce ” gaskiya Allah yataimakeni da yasa banyi bacci yanzu ba da yanzu awaras ta wuceni ” sosai fanan da zeenat suke dariya dan Abba yabasu dariya shima darawa yayi ya ce ” to nagode sosai kuwa Allah yayi albarka” ta amsa da ameen, zeenat ce ta marairaice ta ce ” abbana nakaina dan Allah in tayaka ci?” hararan wasa yamata ya ce ” iyeeeh yau naga abin al ajabi wato baƙin kine yasan dadi nawa besani ba, to aikuwa ko budewa ma bazanyi ba sekin tafi ” yayi maganar yaname rufe kular , dariya fanan takeyi na drama abba da zeenat itade ji tayi babu wacce takaita saa saboda Allah yahaɗata da sirkan nai nagari masu kuma sonta kamar yarsu kowa na gidan yana matukar kaunar fanan dakuma girmamata, kullum addu’ar ta shine Allah ya bata iKon kawo farin ciki akan fuskokinsu wannan al kawarine da ta daukawa kanta bazata taba barin wannin su da bakin ciki ba inde har akwai yanda zatayi na ganin farin cikinsu yanda take kaunar familyn ta haka take kaunar su . sallama sukawa Abba suka koma part din ummi shigowa falon sukayi suka samu su fawwaz sun gama cinye nasu awaran yaseer yana ganin shigowarsu ya ce ” alhamdulillah my girl gwara da Allah yadawo daku yanzu wallahi Allah ne kawai yasa kinada rabon cin wannan daddadar awaran , saboda dakyar na iya kwace kular ahannun su fawwaz wai tunda bakya nan zasuci rabin naki ” yafada yana hararan su fawwaz dasuke kunshe dariya hade fuska zeenat tayi ta ce” Allah ya fawwaz da ya areef da kuncinye min awarata yau da se anyi yakin basasa ” dariya fawwaz da areef sukayi Sannan suka tafa sake fusata zeenat sukayi yasa tadauki kular takoma kusa da yaseer tazauna tanaci .

fanan de seda safe tayi musu domin kuwa tasan yanzu haka Mr azaad yanacan yana jiranta harta haura upstairs setayi wani tunani ganin yanda suketa hiransu kamar basu ji labarin anty shayida nada ciki ba hakan yasa tajuyo cikin yar daga murya ta ce ” albishirinku ?” dukkansu suka bata amsa da ” goro ” gyara tsayuwa tayi ta ce ” Kuma dole sekun bani goron albirshir dina! Anty shayida tanada ciki takusa haihuwa kusata a adduah Allah yasauketa lafiya ” kabbarah sukayi cike da farin ciki suka godewa Allah yanzu darabon zasuga jinin anty shayida zeenat kam harda rawa girgiza kai fanan tayi tabarsu abinta tashige nasu part din tana murmushi itama , haka sukata nishadinsu part din ummi zeenat tafada domin sanar da ita wannan labarin , har ummi tafara bacci zeenat ta tasheta tafada mata jitayi baccin ya yaye babu abinda take furtawa se kalmar alhamdulillah tashiga bedroom din anty amina nan tasamesu rungume anty shayida ummi tayi dukkansu suna farin ciki sosai ummi tadinga mata adduah sannan tabar dakin tashiga nata takira abba ta sanar shima yayi matukar murna sosai haka suka kwanta kowa na cike da farin ciki.

Samunshi tayi adaki yana kwance abinshi yayi shirin bacci cire kayan jikinta tayi tadaura towel tashiga bathroom tayi wanka tafito ta shirya jikinta sannan taje kitchen tazuba musu nasu awaran a plate tashigo hannunta dauke da plate da ruwa zama tayi ta ce ” habiby kazo muci awara ” yana daga kwance ya ce” wifey kici kawai ni bazan iya ci ba ” yanda yayi maganar tasan kota matsa mishi ma bacin zeyi ba yasa taci abunta harta koshi tasha ruwa ta maida komai kitchen ta gyara musu zama .

Dawuwa tayi tahau gadon tashige jikinshi ta kwanta matseta yayi ajikinshi ya ce ” se yanzu kenan ?” ” uhmm yeap kasanme anty shayida takusa zama mother” ta sanar mishi tana sakin murmushi bata amsa yayi da sexy voice dinshi ya ce ” nasani Allah yasauketa lafiya! Saura ke nakusayin ajiya anan wajan ” yafada yana shafa shamulallen cikinta murmushi kawai tayi manna mata kiss a goshi yayi, ya kashe light din dakin yabar bedside lamp yaja musu bargo , duk shuru sukayi kuma basuyi baccin ba dago fuskanta dake kirjinshi yayi yakalli cute face dinta ya ce ” gobe 8:30am flight dinmu ze tashi ” kamar me rada ta ce” Allah yakaimu habiby ” ya ce ” ameen ” adduah yayi musu sannan kowa yayi niyar bacci suna manne da junansu.

 

Washe gari

Sungama shirin tafiya yar karamar trolley fanan tadauka dakyar Mr azaad yabarta tadauka nan ma yana tsaye akanta tadauki abubuwan bukata hijabs ne se abayas da kuma jallabiya nayin sallah sekuma abubuwan da anty amina da anty firdausi suka bata daukan trolley din security yayi yakai boot suka fito suma kowa ya hallara afalo fanan na sanye da doguwar rigar abaya dark blue da mayafinshi se Mr azaad dake sanye da kana nan kaya jeans da riga sunyi kyau sosai .

Har kasa fanan ta gaida kowa hade da taaziya, suka amsa cike da so da kauna mikewa sukayi domin yi musu rakiya airport amma banda ummi,abba,anty shayida,anty amina,anty zainab, masu yi musu rakiya iyakacin yaseer, zeenat, fawwaz, areef se hafiz da yau yajishi klau alhamdulillah.

motoci goma ne ke fa ke a compound din gidan suna jiransu, shiga sukayi su ummi nayi musu adduo’in tsare hanya har suka bar gidan komawa cikin gidan sukayi kowa jikinshi asanyaye yau de sunsan zasuyi kewar fanan sosai .

daga ita se habibynta Mr azaad amotar se driver dake driving dinsu tana kwance ajikinshi Mr azaad shikuma yana shafa bayanta tana bashi labari taji ringing din wayarta cirota tayi a handbag dinta ganin my dad tayi yasa tayi murmushi dama sukadai ne basuyi waya da safen ba tayi waya da su baba da mama ya usman da auta Amira ma ta kirata duk sun musu Allah yakiyaye hanya, dagawa tayi da sallama abakinta ta gaisheshi amsawa uncle kabir yayi suka gaisa yamusu adduah shima sannan yamikawa umma rahina itama suka gaisa tamusu Allah yatsare haka suhaima da ya al ameen seda suka gaisa duka sannan sukayi sallama tana kokarin ajiye wayar kiran anty firdausi yashigo itama tayi musu adduah sannan tabawa daddyn junior bayan sun kammala ta kashe kiran.
dede kunnenta Mr azaad ya ce ” wow gaskiya wifey ke yar gatace kowa na sonki ” fari tayi da ido ta ce ” ehh mana shisa yanzu nafika fans ” murmushin gefen baki kawai yayi, yasa hannu ya matse libs dinta yamatso da fuskanshi daff da nata har suna shakar daddadar kamshin turaren jikinsu da ya hade yabada kamshi me dadi da tafiya da zuciya yace ” baby ai ke din ta dabance dole kifini” yagama maganar yana manna mata kiss a libs din sannan yasake ta gyara kwanciyarta tayi ajikinshi tana shakar kamshin jikinshi hade da lumshe ido, har aka iso airport basu sani ba seda sukaji tsayuwar motar , seda kowa yafito kafin yafito yabudewa fanan murfin motar tafito yarike hannunta suka fara tafiya seyanzu Mr azaad yalura da yan jaridun dasuke wajan tun fitowarsu akeyi musu videos da hotuna hankalin al’ummar airport din duk yadawo kansu ganin wannan shahararren dan kasuwan nan ne tare da matarshi bakaramin burge jamaa sukayi ba kowa se fatan alkhari suke musu wasu na burin Allah yabasu masoya irin Mr azaad, duk yanda sukaso suyi magana da Mr azaad bayuba ko kallon su beyiba jin anfara kiran sunaye yasa suka rungumi juna shida yaseer akunne yaseer ya ce ” dude karka yarda ku dawo baku samo mana baby ba ” dukan kirjin yaseer Mr azaad yayi Yana fadin” seka hanamu dawuwa ai dan iska ” dariya yaseer yayi yace”waneni ” haka sukayi bankwana dasu gaba daya suka fara hawa matattakalar jirgin suna daga musu hannu harsuka shige , direct Vip Mr azaad da fanan suka shiga sukadai ne awajan bakowa a vip zama fanan tayi Mr azaad yadaura mata belt , fara tafiya jirgi yayi yana kokarin tashi runtse ido fanan tayi sosai Mr azaad yariketa dan yaga yanda ta tsorata saboda wannan shine karonta na farko hawan jirgi shisa duk tabi ta rikice . duk ta galabaita harwani jin tashin zuciya takeyi kamar zatayi amai yana rungume da ita ajikinshi ahaka hartayi bacci.

 

19:00pm dede jirginsu yayi landing a Denver international airport , wato karfe 7 nadare kenan alokacin Nigeria duk dacewa akwai tazaran 7hours tsakanin Nigeria da USA . kallon fanan yayi da take bacci duk tayi laushi sau biyu tana amai ƙunce mata seat belt dinta yayi sannan yadauketa cak yafara taka staircase din jirgin hasken da airport din ke dashi tako ina yatashi fanan daga bacci tabude idonta tana karewa airport din kallo , kamar rana kowa se sabgar gabanshi yakeyi airport din kanshi abin kallo ne komai nawajan medaukan hankali.

Wasu jibga_jingar motoci guda hudu sukazo daukar Mr azaad and Mrs azaad kuma dukkansu turawa ne sanye da bakaken suits , har suka sauko daga jirgin fanan bata sani ba hankalinta na kan airport dan ya burgeta sosai , cikin girmamawa turawan nan suke gaishesu beko kallesu ba daya daga cikinsu yabude musu murfin motar tsakiya Mr azaad yashiga dauke da fanan a hannunshi kwantar da ita yayi akan seat yadaura kanta akan cinyar shi shafa fuskanta yayi ya ce ” sannu ko wifey munkusa isa gida ” da muryanta da baya fita ta ce ” to habiby” tafiya sukeyi akan titi slowly kamar wayanda suka dauko sarki ko shugaban kasa har suka iso wani hadedden waje me matukar girman gaske wani katon sign bot kamar tv yana fitar da rubutu da colors kala_kala yana rubuta ‘ welcome to las Vegas ‘ babban birnin las Vegas kenan dake cikin kasar america .

Horn sukayi a tangamemen gida masu gadi suka bude aljannar duniyar gidan daya kasance daya daga cikin manyan gidaje a las Vegas komai na more rayuwa akwaishi awannan gidan akashe masa daula iya daula,gidan da ya yakasance mallakin Mr azaad, bude musu gate akayi suka shiga fanan kamar bakauyiya haka takoma domin gidansu Mr azaad na Nigeria bekai wannan kyau ba dukda cewa shima dankararriyar gida amma wannan ya hadu iya haduwa aikunsan banbancin gidajen turai dana gida Najeriya, tsayawa fada muku kyaun gidan ɓa ta ɓaki ne buɗe musu motar akayi yafito dauke da ita ahannunshi, turawa dake aiki a gidan se ɗiban gaisuwa sukeyi haka yashiga da ita cikin gidan kai tsaye wani ƙayitatciyar bedroom yashiga ya kwantar da ita akan makeken gado, luf tayi tana kallonshi daga mata gira yayi alamar tambaya girgiza kai tayi , dukunkune jikinta tayi waje daya saboda sanyi da takeji ganin haka yasa Mr azaad kashe ac sannan ya rufa mata bargo , kayan jikinshi ya cire yashiga toilet yayi wanka da alwala,yafito yasamu harta fara bacci batare da yasa kaya ba yana ɗaure da towel yahau kan makekiyar gadon , yaye bargon yayi yaɗagota yafara cire mata kayan jikinta , bacci ne a idonta duk abinda yakeyi tanajinshi amma takasa koda bude idonta ne haka yadauketa yashiga toilet da ita yamata wanka da ruwan zafi tayi alwala sannan yanaɗota a towel yakwantar da ita akan gadon sosai taji dadin jikinta.

Kitchen din dake cikin part din yashiga ya haɗa mata cornflakes yakawo mata hartayi nisa abacci babu yanda ya iya dole seya tasheta tasa wani abu acikinta baze barta ta kwanta haka ba zama yayi agefenta ya ce ” wifey kitashi kisha cornflakes seki koma baccin ” tana jinshi sama_sama hakan yasa ta make kafada tare da turo mishi dan karamin baƙinta , murmushi yayi yasa hannu yadagota zama tayi tana marairaicewa kamar wacce tasha maganin bacci dakyar ta iya cewa ” habiiiiibyyyyy kabarrrrni inyiiiiiii bacciiiii ” yanda take jan maganar nata seda yaji tsigan jikinshi yatashi musamman yanda takira shi se dayaji har cikin ranshi , fa ra bata yayi abaki harta shanye duka batama san tashanye ba kwanciya take kokarin yi yarikota ya ce ” ki bari muyi sallah seki kwanta” dressing room yashiga yadauko mata wandon da riga na bacci masu kauri se katon jacket din rigar sanyi domin ana sanyi sosai bude trolley dinta yayi yafito mata da hijab , shima jallabiya yasaka , sannan yadawo bedroom din, sa mata kayan yayi ya shimfida musu sallaya jansu yayi sukayi sallolin da ake binsu bayan sun idar tayi addu’a ta haye gado ta kwanta se bacci murmushi kawai Mr azaad yayi shima agajiyen yake hakan yasa yakashe wutar dakin yabar bedside lamp yaja musu bargo hade da musu addu’a bacci .

 

To sekuma gobe inme duka yakaimu da rai da lafiya .

 

Waiting for your comments and share fisabilillahi .
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story & written by ✍️
MRS ISHAM
( Yar lelen Jarumai)

 

 

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION

⚜️ J. W. A ️

 

Gargadi….
Ban amince wata ko wani yayi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowani siga ko a karanta minshi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a hadamun document ko amin edit idan kunne yaji jiki ya tsira koda Allah nabar mutum ze sakamin kuma yabimin hakkina.

Back to top button