Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 53

Sponsored Links

Shuru kawai sarauniya fanan tayi tana sauraran jaaazana har ya gama fadin abinda ze fada ya narke ya shige cikin jikinta , bangarewa tayi idonta suka fifito sosai hasken su da sheki yakara fitowa kulle idonta tayi ta sake budewa ta ganta a tsakiyar falonsu ajiyar zuciya tayi tanufi bedroom din Mr azaad slowly ta bude kofar dan gudun kar ya tashi yahau tambayarta ina taje shigowa tayi tamaida kofar ta rufe , juyawa tayi zata je ta kwanta kawai taga Mr azaad a tsaye a gabanta idonshi akanta kallon tuhuma yake binta dashi kafin yace” wifey daga ina?” tace nadanje kitchen na sha ruwa ne” ta karishe maganar tana inda_inda ” karya be dace dake ba domin baki iyashi ba karki fara ! sannan naga ga can bottle water akan center table ko me sanyi kikaje sha?” cewar Mr azaad da haryanzu ya tsura mata mayun idonshi da yasa takasa nutsuwa duk ta birkice se sosa wuya takeyi bazata iya sanar dashi lokacin tafiyarta ya qarato ba dan batason ya shiga wani halin damuwa, canza maganar tayi da ” habiby kazo muje mu kwanta bacci nakeji” be sake dauko mata wata tambayar ba ganin bataso taki bashi amsa se kauce_kauce takeyi yasa yakoma kan bed yakwanta hawa gadon tayi itama ta shige jikinshi rungumota yayi kamar wani ze kwace mishi ita.

Washe gari 5:20am

Tashinta yayi daga bacci ” baby time for prayer” tashi tayi tazauna tana mika da salati bin kirjinta yayi da kallo, kallon setin da yake kallo tayi taga yazubawa kirjinta ido kashe mata ido yayi kafin yafita zuwa masallaci . Sallah itama tayi yau alhamdulillah ta tashi tana iya takawa ba laifi kuma baya mata zafi tana zaune akan sallayar tana azkar shuru_shuru Mr azaad be dawo daga masallaci ba har 7 tashi tayi ta share bedroom dinshi tagyara kan bed, tayi mopping ta wanke toilet komawa falo tayi tagyara ko ina hade da bedroom dinta ta kunna turaren wuta ko ina yayi fess yana kamshi kitchen tashiga nan ma ta gyara ko ina sannan tafara tunanin me yakamata ta musu na breakfast. Cikin store tashiga ta dauko doya madedeci tasa ruwa acikin bowl tadauki wuka ta fareshi tsaff ta yankashi acikin bowl dake dauke da ruwa , kunna gas tayi ta daura ruwa acikin tukunya yafara zafi tasa doyan da gishiri ta rufe , bayan doyan yadafu tasashi a basket yadan sha iska eggs ta dibo guda shida ta fasa acikin separate kwano tasa magi,albasa
se ginger kadan saboda karni kwai ta kadashi yakadú,daura frypan tayi akan gas din tasa oil tasa albasa sannan tafara sa doyan acikin kwai tana soyawa harta gama daga ido ma kadai mutum ya kalla yasan zeyi dadi ba dan kadan ba, cabinet taje ta bude tadauko dinner set food flask masu kyau dukda sabbine seda tasake wankesu tagogesu da dry towel tazuye soyeyen doya da kwan aciki tarufe ta ajiye agefe. Fridge din ingredients (kayan miya) ta bude takwaso abubuwan bukata saboda miyar kwai takesonyi kamar su attarugu,albasa,Karas, green pepper , green beans ta gyarasu, tayi blanding attarugu . fasa eggs din datasan zeyi mata miyan tayi tayanka albasa acikin kwan ta ajiye agefe , ruwan zafi ta dibo tafasheshe a heater tasaka karas din da green beans da baking powder kadan rufe bowl din tayi ta barshi few minutes, budewa tayi ta tsameshi, sake wankewa tayi sannan shidinma ta ajiye agefe ,
Daura tukunya tayi akan gas tasa butter ta narka shi tasa albasa yasoyu sama sama . attarugun datayi blanding dinshi tasa aciki da curry, thyme, tasa ruwan zafi kadan aciki tajuyashi tarufe da marfi , can tabude tasa kwanta data fasa acikin tukunyan tarage wutan tasake rufe tukunyan tabarshi nawasu mintuna tasa mishi karas da green beans tajuya ahankali tabarshi ruwan yatsotse ta tabbatar da yayi ta kashe gas din tajuye miyar kwan acikin food flask ta kaisu dinning ta jera tadawo tadafa tea dayaji kayan kamshi shima takaishi dinning, wanke duk wani abinda tayi amfani dashi tayi tanufi bedroom dinta tacire kayan jikinta tadaura towel tashiga bathroom tashiga jacuzzi dake dauke da zuwan zafi ta gasa jikinta sosai sannan tayi wanka tafito tana tsane jikin da dogon gashinta da tsayinshi yakai kugunta zama tayi agaban mirror tadauki hand dryer ta busar da gashin ta shafa mayukan gashi ta tajeshi tayi packing da ribbon fari, lotion tashafa tayi light make up ta fesa turare kaya tadauko Pakistan riga da wandonshi fari da pink hade da gyalenshi ,wandon pencil ne rigar kuma yanada tsayi yakawo mata har guiwa gefe da gefenshi a tsage yanada dogon pencil hand yasha stones, yafa gyalen tayi akanta da bashida wani girma sosai tasa farin plate shoe, tayi kyau sosai kasancewarta chocolate color,se color kayan suka karbeta white and pink sake feshe jikinta tayi da body spray tafito falo ta tsaya tana jiranshi ta bawa kofar falon baya, shigowa yayi shakar kamshin dayaji yake tashi apart din hade dana jikinta yayi ahankali ya hada jikinshi da nata ya rungumeta ta baya ya saukar da kanshi awuyanta yana shakar kamshin turarenta hannunshi duka biyu ya daura akan kugunta seda suka kai almost 5mint ahaka , rike kafadunta yayi ya juyo da ita suna facing juna , manna mata light kiss yayi a libs yace ” morning kiss ! Kinyi kyau baby kullum Kara kyau kikeyi ” sa hannunta tayi tazagayo dashi awuyanshi tana shafawa kadan kadan tace ” morning habiby ” be amsa ba kawai yamata murmushi tsayar da ita yayi yana binta da kallo from toe to head, godewa Allah yayi daya bashi mata me hankali dakuma sonshi tsakani da Allah, me tsafta kamarshi dukda akwai masu aiki a gidan amma ita take komai da kanta ta iya kula da jikinta.
( to mata gareku , kurike tsafta! kurike tsafta maza sunason mace me tsafta da tattalin kanta ,karki kasance ballagaza da bata damu da jikinta ba bare tayi tunanin gyara muhalli . Babu na mijin da bayason mace me tsafta Koda shi yakasance kazami bayida tsafta amma ke inkina da tsafta zakiga shikanshi ze rage , zekuma jidadi duk sanda yadawo gida yasamu ko Ina tsaff dakuma ke kanki kinyi wanka da kwalliya kin feshe jikinki da turare kina tashin kamshi , tsafta na daya daga cikin abinda yake kara soyayyarki azuciyar miji dan bakowa bane zeyi toleranting kazanta ba , mata da yawa aurensu ya mutu ta dalilin rashin tsafta .
To adage adinga tsafta dan faranta ran oga ,bama dan oga ba kema kanki inkina tsafta sekinfi jindadin jikinki da rayuwarki,a shigo gidanki ma aganshi tsaf ai da dadi bazakiji kunya ba . ) rike hannunshi tayi ta langwabar da kai hade da turo dan karamin bakinta me red libs tace ” habiby aina ka tsaya haka inata jiranka baka dawo da wuri ba” tsurawa dan karamin red libs dinta ido yayi dake fitar da kalma daddaya kamar bata iya magana ba tsaban shagwaba, ji yayi kamar yakama libs din yata tsotsa , tallafo habarta yayi yasa idonshi cikin nata yace ” am sorry baby ! na tsaya a falon ummi ne ” sake turo bakin tayi takoma kamar wata teddy tace ” to yanzu muje kayi wanka sekazo muyi breakfast nafara jin yunwa ” ta fada tana kai hannunshi kan cikinta ,shafa shamulallen cikinta yayi dayake plate kamar batacin abinci kai hannunshi yayi kan maranta yadan shafa yace ” baby yanzu baya miki zafi sosai ko” ganin yana kokarin zarcer da hannunshi kasa ne yasa tayi saurin rikewa kam tace ” muje kayi wanka” dariya taso tabashi ganin lokaci daya tadan tsorata jan hannunta yayi zuwa bedroom dinshi yana ” yau ke zakimin wankan ” zaro ido waje tayi tafara zazzaresu gasu dama masha Allah manya_manya dasu tace ” nide ah ah”.

Sake hannunshi tayi yashiga toilet din, fitowa yayi daure da towel akugunshi karami kuma ahannunshi yana goge kanshi dake digar ruwa, karban towel din tayi ta goge mishi jiki zama yayi akan kujera ta shafa mishi lotion se kallonta yakeyi especially her cute face satan kallonshi tayi taga ita yake kallo. tana gama shafa mishi man tabarshi awajen tashiga dressing room dinshi tana tafiya ahankali tadauko mishi kaya kana na marasa nauyi takawo mishi tana tsaye agefenshi yasaka riga murmushin mugunta yayi kafin ya kunce towel din dake kugunshi ya fadi kasa, kara tasa tarufe idonta tazuya baya batayi tunanin ze iya hakan agabanta ba zuciyarta se bugawa yakeyi da karfi ita kadai tasan me tagani , Mr azaad kuwa se dariyar mugunta yakeyi harda dan rike ciki dan abinda yayi tsammanin haka kuwa yafaru tsoron fanan yayi yawa saka kaya yayi kafin ya rungumeta ajikinshi yanaci gaba da dariyar , kukan shagwaba tasa mishi tana dukan kirjinshi da duka hannunta rike hannayen yayi yana dariya yace ” Meye abin tsoro baby ?” murguda mishi dan karamin bakinta tayi tace ” nide munyi fada tam ” rike kunnenshi yayi yace ” afuwan wifey ” make kafada tayi, daukarta yayi cak be zarce ko ina ba se a dinning table yazaunar da ita akan kujera shima yazauna, bude warmers din tayi nan take kamshin abincin yadaki hancinshi seda yarufe ido sannan yabude ya kalli abincin dake cikin kulolin seda ya hadiye yawo, burinshi kawai yakai abincin bakinshi , serving dinsu doya da kwan tayi a one plate sannan ta zuba musu lafiyayyar miyan kwan tarufe warmers din, hada musu tea tayi sannan ta ajiye mishi plate agabanshi tace ” inde kanason inci sede kayi feeding dina” girgiza kai yayi yace ” abu me sauki ” dagata yayi yadaura akan cinyarshi yafara feeding dinta harta koshi sannan shima yaci dadin abincin ne yake ratsashi har kwakwalwarshi bayan girkin umminshi yadade beci abinci me dadi irin wannan ba haka suka gama breakfast dinsu yanata santin girkin ,tazo zata kwace kayan ya hanata dan bayaso tadinga shan wahala shida kanshi yakai komai kitchen din sannan yatayata wanke abinda suka bata…..

Bari muleka kungiyar BAPHOMET.

suna can duniyar su shugabansu daya kansance katon bakin aljani mara imani me mugun halitta mara kyaun gani rabinshi mutum rabinshi dabba kuma wata halitta daban ga katon qaho akanshi, yana zaune akan kujeran mulkinsa suna tattaunawa da wasu mugayen halittu marasa kyaun fasali inda sukema kadai duk bil adaman daya shiga inde yaje tofa fitowa se wani iKon Allah, wata bakar mujiyace daga zama tafado kasa kamar wanda aka wurgo tana fadowa gabansu takoma rabinta mutum rabinta mujiya tsirara ba kaya ajikinta duk jikinta gashi gashi ga qaho agaban goshinta, afusace shugaban nasu da murya me amo mara dadinji yace ” keeeeeeeee! Abinda yafi miki sauki shine ki sanar dani abinda naturaki kinemo min domin shi kadaine ze taimaka mana wajan mallakar sarauniyar nasminaya” muryanta kamar yanda kukan mujiya yake fita haka yake tace ” yakai shugabana SHUBUMBUM na samoshi ! shidin cikekken dan baiwane dayazo duniya besan shiwaye bane kuma babu wanda yasan da hakan se wata halitta kwali daya dake tare dashi wato tsuntsun arnass , shidin yakasance dan babban gida acikin bil adama shidin babban dan kasuwane da akeji dashi” murmushi kawai shubumbum yakeyi jin bayanan da aka kawo mishi duba madubin tsafi yayi ko ze ganshi domin yanzu shi kadaine ze iya sasu suyi nasara akan kungiyar satanic kuma harsuci galaba akan sarauniyar nasminaya, wasu surkullenshi yayi a hannu sannan ya watsawa madubin tsafin, hoton kafanshine yafara bayyana nan take kuma madubin tsafin yatarwatse kaca_kaca yana fitar da hayaki, seda suka ja baya suna jinjina karfin baiwan da yake tare dashi……

Tom duka duka anan nakawo karshen rubutun yau se mun hade tomorrow in sha Allah.

via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&rehttps://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8

‍⚕️‍⚕️ NIDA PATIENT DINA

 

Story & written by ✍️
MRS ISHAM
Wannan labarin qageggen labarine ban yarda wata ko wani yajuyamin labari ta kowani tsiga ba , bana bukatar ajuyamin labari ko ayi wani Abu batare da izinina ba

 

JARUMAI WRITERS ASSOCIATION

( J. W. A )

Back to top button