Cuta ta Dau Cuta Hausa NovelHausa Novels

Cuta ta Dau Cuta 15

Sponsored Links

*_Typing_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_ _

 

_Shafi na goma sha biyar_

 

_ADVERT_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA’ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI… AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO’INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE…_

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS… THEY ‘VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED

____________

…….Yini guda haka Khadijah ta yisa da zazzaɓi a wannan ranar. Idanunta sun mugun kumbura saboda kuka. Wani irin mamakin canjawar Dafeeq take a ƙanƙanin lokaci haka. Duk da zuciyarta nace mata asiri Hajiyar nan ta masa wani sashe yaƙi yarda da hakan. Gaba ɗaya sai hankalinta da tunaninta suka kasu, ta rasa gane wanne ne gaskiya. Halinsa ne haka? Ko asiri Hajiyar ta masa?. Waɗan nan tunani biyu sune suka hana zuciyarta sukuni gaba ɗaya a yinin har dare salla kawai ke tada ita, tsabar yunwar da takeji har jiri ke ɗibarta, a haka dai ta daddafa tai sallar isha’i ta sake komawa ta kwanta. Dan tun rikicin safen nan bata sake jin ɗuriyar Dafeeq da amaryarsa ba a gidan. Wani wahallen barci ne yay awon gaba da ita mai cike da mafarkin iyayenta…

2:23am ya sake duba agogon dake gefen gadon. Ƙaramin tsaki yaja tare da duban gefensa da Hajiya ke barcinta hankali kwance. Gaba ɗaya zuciyarsa a ƙuntace take, dan duk yanda yaso yau ma ya more taƙi yarda. Dataga ma zai takura mata sai ta jefeshi da bandir na 1k guda biyu wai ta saya. Duk da yaji zafin abinda tai masan haka ya ɗauki kuɗin yana binta da kallo. Itako ta ɗauke kanta tana wani faman cika da batsewa tai kwanciyarta tare da jan bargo. Dolo haka ya kwanta a gefenta ya haɗiye abinda ke masa kai-kawo. Sai dai duk yanda yaso barci ya ɗaukesa hakan ya gagara. Dan ya riga ya saba ba haka suke da Khadijah ba. In har ba tana period ba baya iya ɗaga mata ƙafa koda faɗa sukayi kuwa, kai koda ma tana period ɗin dole tai masa yanda zai samu nutsuwa. Amma sai gashi yanzu da matan har biyu bashi da wani ƙarfin iko a kansu. (Har Khadijah?) Wani gefe na zuciyarsa ya ayyana masa. “Kai ina, ita kam ai bata isa ba”. Ya faɗa a zahiri yana wani girgiza kansa da sake ɗaure fuska. Hajiya ya sake juyawa ya kalla, ganin barci take sosai ya sake jan ƙaramin tsaki, sai kuma ya lumshe nasa idanun yana fatan barcin ya ɗaukesa shima. Sai dai ina babu alamar hakan, sai ma wutar fitina dake sake ruruwa a jikinsa. Zaram ya miƙe ganin zai halaka, cikin sanɗa kamar wani ɓarawo ya sauka a gadon, da rarrafe ya isa ƙofa ya buɗe a hankali yana waigen Kainaat ya fita. Sai da yay ɗan jimm ya tabbatar babu wani motsi na alamun ta farka sannan ya miƙe ya sauka ƙasa, dan nasu ɗakunan na sama ne na Khadijah na ƙasa. Kai tsaye ɗakin ya nufa abinsa…

Cikin barci taji ana taɓata, firgigit ta farka sai dai bata da wani kuzari a jikinta. Sosai ta ware idanunta na mamakin ganin Dafeeq. Zatai magana ya wani rungumeta yana girgiza mata kai alamar kartace komai. Ƙasa cewar tai kuwa, ta cigaba da binsa da kallo kawai. Hakan ya bashi damar sake shige mata jiki alamar dai akwai abinda yake buƙata. Cikin rawar murya da sanyin jiki ta ce, “ALLAH bazan iya ba yunwa nake ji”.
Shiru yay yana kallonta, sai kuma yaja ƙaramin tsaki yana miƙewa ya fita a ɗakin. Jitai kamar ta kurma ihu ta ce ya dawo amma tasan halinsa bazai saurareta ba. Tana nan kwance hawaye har sun fara ziraro mata sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da kwalin yogurt. Ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi, kafin ma ya ƙaraso ta miƙe zaune. Kusa da ita ya zauna yana wani ciccin magani shi adole har yanzu haushinta yake ji. Da taimakonsa tasha madarar, ganin ta ɗan samu ƙarfi duk da jikinta akwai zazzaɓi sosai babu tausayi ya shiga neman hanyar cimmata. Sunyi nisa sosai a yanayin da suke ciki babu zato babu tsammani kawai sukaga haske ya karaɗe ɗakin.
Matuƙar firgita Khadijah tai tare da fashewa da kukan baƙin ciki ganin Hajiya Kainaat tsaye a kansu babu kunya babu tsoron ALLAH idonta ƙyar a kansu. Ga Dafeeq baida alamar ɗagata balle nuna firgici da wannan cin zarafi na matar nan. Batama san wani ƙarfi yazo mata ba ta hankaɗesa taja bedsheet ta cikukuye jikinta tana kuka.
Wani irin ihu Kainaat tai musu kamar zata kashesu. “Dafeeq ni zaka cima mutunci ka zubar min da kimata. Tsabar kai tataccen ɗan iska ne kwana na zaka ɗakko ka kawoma wannan kidahuman matar taka ɗan cin amana!! A ɗaura aurenmu jiya matsayin amarya kazo kana ɓarar min da mutunci a wajen wannan jakar da bata san ciwon kanta ba…..”
Wani kalan yunƙurowar ɓacin rai Khadijah dake kuka tayi, sai dai da sauri Kainaat ta dakatar da ita a zafafe. “Ke kuma karki sakamin baki dan banzo kanki ba tukunna, hasalima baki isheni kallo ba kiji ma da matsalar gabanki wawuya kawai wadda ta rako mata duniya. Ya gama jibgarki ɗazun nan amma da yake ke karya ce har ki amince yazo yay yanda yaso dake yanzu da dare. Koda yake banyi mamaki ba, dan kekam na kula bakin iyaye ke ɗawainiya ma dai da ke. Tunda har kika iya haukan kishi da jure zama da wanda ko sha’awar haɗa jini baida buƙatar yi da ke, wanda ke ɓarar miki da ciki domin buƙatar kansa ai kekam sai a shafa miki lafiya. Wlhy kikai wasa wataran janki zai a tsakar anguwa a titi ya yardama bola ƙaramar daƙiƙiy……”
“Kainaat!!!”.
Dafeeq ya faɗa a tsawace illahirin jikinsa na ɓari. Da alama maganganun ta sun masifar shigarsa. Wani kallon banza ta masa ta sheƙe da dariya. “Karka sake min tsawa Dafeeq, danni ba irin wannan bace, a daren nan sai kabar gidan nan kai da ita wlhy. Ƙarya nayi bakai ke zubar mata da cikin ba? Ai gaka gata ka rantse ba kai bane. Ni kuma a safiyar gobe saina kawo likitan da ke baka ƙwayar da kake zuba mata ta sha, bakai kace ɗan iska bane, a kwana ɗaya har kake tunanin nuna min halin maza! To baka isaba kuwa dan a tafin hannuna kake. Ka rabota da iyayenta da yake itama daƙiƙiyace ta yarda ta bika kazo nan kana cutar da ita har kake tunanin babu wanda yasan kanayi. To barima kiji ba zubar da cikin ba kawai har abinda zai hanaki sake ɗaukar ciki ya saka miki, shirinsa ya gama morarki ya watsar yaje ya sake auro dai-dai da shi lokacin ke kin tashi aiki mahaifar ta gama lalacewa, kuma in baki sani ba ki sani a yau ke ya maida wawuya da bata san darajar iyayenta ba shiko yana zuwa duba nashi duk ƙarshen wata, wannan kwana biyun na ƙarshen wata da yake miki ƙaryar Company ya riƙesu su masa aikin gyaran wajen da za’a saka kaya ƙarya yake ganin iyayensa yake zuwa yi. Wannan kaɗanne daga jaridar yarinya idan kina son sabon labari ki ƙara shiga gonata. Kai kuma zaka zo ka saman ne, zan tabbatar maka akwai banbanci tsakanin Kainaat Usman da wannan ballagazar matar taka da bata san ciwon kanta ba ƴar rakiyar mata duniya”….

Tofa
__________★

Komai nada mafari, wannan rana itace mafari tsakanin Anoosh da JJ. Dan kuwa washe gari ma dazai kaita makaranta haka ya sakata ta cire hijjab bayan ta shiga mota, zuciyarta bata son abin, amma kuma bata so ta ɓata masa rai saboda soyayyar da take ji tana masa. Tana masa wani irin mahaukacin so da take jin komi yace tayi dai-dai ne, duk da kuwa ita tasan ba dai-dai ɗin bane. Da zai ɗakkota ma hakance ta kasance. Wasa-wasa sai ta ɗan fara samun nutsuwa ganin har kusan sati biyu iyakarsa kawai yace ta cire hijjab ɗin ne idan zai kaita makaranta ko idan zasu dawo. Sai da suka cika sati na uku a haka ranar wata alhamis yake tambayarta miyyasa bata son saka ƙananun kaya ne?. Murmushi kawai tai batace da shi komai ba, kanta a ƙasa. Cike da makirci da yaudara irin ta azzalumai ya sake kwantar da murya. “My Anoosh ina bala’in son naga mace tasa ƙananun kaya, musamman ma ke da nasan zasu fi miki ƙyau fiye da kowacce mace a duniya, dan kinfi mata dubu bisa dubu ƙyau. Irinku fa nada wahalar samu Anoosh. Please ki koya sakawa kafin auren mu dan ina so sosai. Idan kuma kinfi son na dinga kallon matan titi dake sakawa to?”.
Da sauri ta girgiza masa kanta idanunta dake cikin glasses na cikowa da ƙwalla. Cikin alamar motsin lips ɗinta ta ce, “Ai Mommy bazata bari ba. Ko’a cikin gida na saka hijjab nake sakawa ko abaya”.
Murmushi ya saki cikin kannewa ya ce, “Ai hakan ba damuwa bane my Anoosh, idan kika sanya nima basai ki ɗora abaya ɗin ba kisa kuma hijjab. Kinga Mom bazata taɓa ta gane ba ai ko? Ko baki son farantama mijinki rai ne? Kinfi son yana kallon matan dake yawo a titi?”.
Kanta ta sake girgiza masa da sauri. Ya sakar mata murmushi yana riƙo hannunta a karo na farko. Duk da ya ga zaburar da tai da tsumar da jikinta keyi haka ya basar ya kai hannun bakinsa ya sumbata. Gaba ɗaya Anoosh ta gama daburcewa, sai dai ta kasa cemasa komai. Bayan ya sauketa har kuka tayi a aji cikin hijjab. Sam bata son abinda JJ ke mata amma ta kasa hanashi, ta kuma kasa faɗama wani. To wama zata faɗamawa? Ita ba ƙanwaba ba yaya ba, ba ƙawa ba. Sannan bazata iya tunkarar Mommy da wannan batunba ai, tasan zata iya halakata ma, kai ko Gwaggo bazata iya faɗawa ba.
_(Iyaye! Iyaye! Iyaye mu kula Please and please. Nasan wayonka ko dabaranka bashi zai kare maka yaranka ba. Amma mu daure, mu rage sabgogin gabanmu wajen jan ƴaƴanmu a jiki musamman ma ƴammata. Mu zama ƙawayen ƴaƴanmu ta yanda bazasu taɓa yarda da wata Aminiya ba a waje sai mu, balle har suji shakka ko tsoron tunkararmu da matsalolinsu. Jan yaranmu jikinmu kansa muyi saurin fahimtar sabon yanayi da suka tsinta kansu a ciki. Dan irin yaran nan da samari kan yaudara zakaga a farkon fara koya musu abubuwa ko sakasu yin wani abu suna cikin tsoron da idan uwa mai lurace zata iya fahimta. Sannan mu daina bama samarin ƴaƴanmu amanar yaranmu hundred percent, hakan kuskure ne wlhy, dan kawai muna son yarinyarmu ta samu mijin aure, ko kuma kada ya kuɓuce sai mu ɗauki dukkan yarda mu basa. Abinda fa muka kasa fahimta mafi yawan irinsu JJ da fuskar mutanen ƙwarai suke zuwa ga ƴaƴayenmu bada ainahin fuskarsu ta azzalumai ba. Sannan a matsayinki na uwa ya kamata ki zama maisa ido wajen fahimtar raunin ƴaƴanki akan abu, ko kuma ƙarfin sha’awarta tun daga sanda ta fara balaga, kija abinki a jiki da samun hanyoyin kare mutuncinta inba hakaba wlhy kina nan hankalinki akan neman kuɗin da zaki saya mata kayan kwalliya dana kayan ɗaki wani sakarai zai miki sakkiyar da ba ruwa. Yaranmu na yanzu sunada wayo, dan kafin sukai ko’ina sun san minene ma ake nufi da ɗa namiji da alaƙar dake tsakaninsa da mace, karki sakankance yarinya ce bata san komai ba. Humm ƴar uwa a wannan zamanin babu wannan batun na sakankancewa game da shekaru ko wayon yaro, komai dolancinta ko ƙanƙanta zata iya baki mamaki wlhy. ALLAH ka shiryemu baki ɗaya, ka kare mana yaranmu da ga sharrin fasiƙan maza irin su JJ)_

Washe gari kamar yanda JJ ya buƙata haka Anoosh tayi, ta saka ƙananun kaya a ƙasa ta ɗora abaya da hijjab. Tana shiga mota ya sakata ta cire hijjabin da abayar. Tsabar yanda ya rikice baima san ya rungumeta ba. Duk yanda take kiciniyar ƙwacewa bai saketa ba sai da ya samu ƙaramar nutsuwa a haka. Bayan ya saketa ta hau masa kuka, sai ya shiga lallashinta cike da daɗin baki irin na mayaudara. Wai wlhy tsabar rikicewa da ƙyan da tayine. Amma ta yarda da shi shi ko hannun mace bai taɓa riƙewa ba sai a kanta, kuma itace ta ƙarshe. Nan fa ya kanainaye ta da zance harda su wa’azi. Dole ta haƙura, sai dai tunkan suje makaranta ta maida hijjab ɗinta. Daga ranar kuma saita ɗan fara ɗari-ɗari da shi. Ganin damar daya samu zata kufce masa ya sake sabuwar dabara.
Cikin weekend ya zo hira kamar yanda ya saba. Maimakon zama da Anoosh sai ya zauna da mamanta wai su tattauna akan kawo kuɗin aure. Hajiya Lailah taji daɗin wannan zance nashi. Bata ɓoye masa ba ta sanar masa zatama Gwaggo magana cikin dattawan layin nan mutum biyu su amshi kuɗin, dan bazata turashi wajen dangin mahaifin Anoosh ba saboda wasu dalilai da sai nan gaba zata sanar masa. Nunawa yay ai hakan babu komai, da yake shima zuciyarsa akwai tsatsa a ciki. Duk abinda suka tattauna Anoosh najinsu, sai taji ta samu matuƙar nutsuwa da sake jin ƙaunar JJ a ranta.
Kwana biyu dayin wannan magana iyayen JJ suka zo aka zauna. Sun kawo kuɗin gaisuwar farko har dubu ɗari cif, akan a sake basu lokaci suzo da sadaki da komai a saka rana. Ranar Hajiya Lailah ta kasance a cikin matuƙar farin ciki, sai dai abinda bata sani ba shine JJ iyayen ƙarya ya kawo musu, dan hatta su MB abokansa basu san ya cigaba da zuwa wajen Anoosh ba. Sannan Gwaggo alaƙarta da MB ta ɓangaren mahaifiyarsa ne, bata wani san iyayen JJ ba sosai musamman ma maza. Yarda datai da shi kuma yasa bata taɓa kawoma ranta zai aikata wani abu makamancin haka ba, ga shi kullum Hajiya Lailah cikin yabonsa take. Ga soyayyar da Anoosh ke masa. Ita kanta kusan duk juma’a idan ya shigo yakan kawo mata kayan marmari wani lokacin harda sabulai da omo, randa ALLAH ya cidata ma harda kayan shayi da nama. Gashi duk ƙwaƙwƙwafinka baka isa gane ainahin fuskar JJ ba, dan makirin mutum ne da ya iya takunsa, duk wani salo na cimma mace ya sanshi musamman irin su Anoosh salihan yara masu tarbiyya.
Kawo wannan kuɗi ya ƙara sakama Anoosh nutsuwa da JJ ita da mahaifiyarta, dan haka washe gari da yazo kaita makaranta koda ya rungumeta batai masa kuka ba, sai dai ta takure jikinta waje guda. Sai ca yay mata na murnar samuntane fa. Ko ita bata murna sun kusa zama ma’aurata. Cike da kunya tace tanayi. Hannunta ya kama ya sumbata, batare da ya bata damar sake cewa wani abu ba ya tada motar………✍️

‍Hummm

 

 

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*

Back to top button