Ni da Patient Dina Book 2 Page 40
Duka suna zaune afalo ummi tace ” son ina feena ?” Yana danna waya yace ” tana bedroom ” “okay jeka kirata ” tashi yayi tahaura upstairs din afalo yasameta tana yar goge_goge, kallonta yayi up and down kafin yace ” ummi nakiranki afalo ” cike da Al ajabi take bin bayanshi da kallo wato su ummin sundawo shine baze fada mata ba lallai Mr azaad. Dama doguwar rigar abayace goldin color ajikinta komawa bedroom tayi tasa gyale me girma tasauko.
Tun kafin ta iso gaba ki daya mutanen falon hankalinsu yakoma kanta ganin yanda lokaci daya tayi uwar rama sosai suke kallonta, tashi zeenat tayi suka rungume juna cike da murna tukun suka karasa falon duqawa tayi tagaishesu amsawa sukayi suna kallonta, zama tayi abinta akan lallausan carpet din falon , Abba ne yakalli Mr azaad yace ” meyake damun fatima? datayi wannan ramar haka azaad?” Kallonta shima yayi yana neman ramar da akace tayi bayan ko ina najikinta acike bulbul. Shuru yamusu dan besan amsan daze bayarba tunda shide bega wata rama ajikinta ba, girgiza Kai abba yayi yakalli fanan ” Fatima meyake damunki kika rame haka kode azaad yana miki wani abune bayan tafiyarmu?” Satan kallonshi tayi taga ko ajikinshi wayarsa ma yake latsawa abunshi , murmushin yaqe tayi tace ” Abba babu abinda yakemin kawai de kwana biyu ne nayi rashin lafiya ” ran ummi yabaci dajin haka domin kullum sesunyi waya da Mr azaad kuma seta tambayeshi ya fanan take yace mata” lafiyanta Klau” ashe baiwar Allah tana nan tana fama da ciwo amma dan bakin hali irin nashi yaki sanar da kowa.
Dago kai yayi suka hada ido da ummi dake doka mishi harara sunkuyar dakai yayi dan yasan dalili.
______ Rai abaci abba yafara magana ” yanzu kai azaad ka kyauta kenan matarka bata da lafiya kusan kwana biyu amma baka taba fadawa kowa ba! Sannan kabata wayarta ko kasiya mata wani abu yagagara kullum semun ce kahadamu da ita amma ka kasa to ka kiyayeni kaduba yarinya duk tabi ta lalace kamar ba itaba ” shide ko uffan bece musu ba saboda shibega abinda suke magana akai ba daga karshema tashi yayi yabar musu gidan , aranar kam fanan tahuta se lallabata sukeyi kamar kwai da dadin baki ummi take samu tama fanan wayo tasha magani har goma suna hira , jitayi kamar ta cewa ummi zata kwana apart dinta amma inta fadi haka zasuyi zargin wani abu tanaji tana gani sukayi sallama tawuce nasu part din.
Bari muleka Romeo and Juliet
Girki suhaima tayi mishi me ji da lafiya taci ado suna zaune suna sunashan hiran love Yanacin abinci se shagwaba takeyi mishi , bakaramin gigitashi takeyiba intana wannan shagwabar haka sukasha love dinsu ya ajiye mata tsarabanta tarakashi har bakin motar shi yatafi.
Komawa gida tayi tadauki fashion bag din daya ajiye mata tashiga dakin mama tanuna mata budewa tayi dogayen ruguna ne masu shegen kyau yan dubai da sarka da dankunne na gold se zobe, murmushi mama tayi tace ” ohhh su suhaima anyi saurayi ” kunya taji yarufeta tarufe ido suna dariya , ” tun jiya babanku yace inbada miki ki mishi magana inde da gaske yake auren zeyi yafito” cike da kunya tace ” to mama zan fada mishi”.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya yau yakama 1 month dayin auren fanan da Mr azaad, yana nan yana mata abinda yagadama wata rana yasata aiki wata rana kuma kota kanta bayabi, tun su ummi basu farga ba har suka fara fahimtan wani abu wani lokacin fanan setafi kwana biyu bata sauko downstairs ba kuma baya taba yarda wani yaje ciki ,sanda ze barta kuma se inzaayi dinner gaba daya tacanza, kuma komin tambayar dazasu mata amsa daya take basu shine ” bakomai bayamin komai” ummi ce ta siya waya iphone 14 pro max tabawa fanan da sim taloda mata kati da data aciki,tacewa Mr azaad saura kuma kar inganshi ahannunta, tanan ne fanan tafara samun saukin wasu kayan bakin cikin kullum setayi waya da yan gidansu, suhaima da amira,auta sunzo wajanta harso biyu suma sunyi mamakin yanda takoma wata shuru_shuru da ita .
Alhamdulillah su Abba da yan uwansu sunje sun tambayawa fawwaz auren suhaima kuma anbasu ansa date nan da wata hudu zaayi ( tom Romeo and Juliet ankusa angoncewa kenan Allah yakaimu musha biki)
Ayau ne ranar asabar akatashi da wani irin gagarumin tashin hankali agarin gombe sakamakon ganin gawawwakin yara da manya , maza da mata ancire wasu sassa najikinsu anyi ritual dashi( tsafi) ansamu gawawwaki kusan 30 lamarin yadagawa mutane hankali kowa yanutsu da iyalanshi agida , jami’an tsaro se bincike sukeyi akan case din daga zaran yaro yafita haka zaa daukeshi baze dawoba sede aji labarin antsinci gawanshi.
Wannan aikin bana kowa bane face kungiyar SATANIC and BAPHOMET dasuke ritual domin yakar junansu domin duk wanda yayi nasara akan daya shize kwaci jaaazana haka suka dinga tsafi da mutane da basuji ba basu gani ba ,babu ruwansu dakoma waye yafita kana yin waje zaa daukeka cakk shikenan kuma katafi, wannan dalilin yasa akasa lockdown agombe.
Duk suna gida suna jin abinda yake faruwa Abba yace karwanda yafita, dukkansu suna zaune afalo sunata kallon labaran da akeyi .
Bangaren mommy kuwa tun ana kwana biyu zaa fara ritual din abin duniya yadámeta gashi bahalin zuwa ayi da ita dan haryanzu bata warke ba tanata kan jinya dan tasan dataje anyi da ita tasan dole tanzarzar yakara mata matsayi.
Jikin fanan ne yafara wani irin kadawa kamar wacce akasawa shocking , nufanta sukayi cikin tashin hankali ,riqeta gam azaad yayi duk jijigan datakeyi tana jikinshi yaki saketa can kuma seta dawo normal, kallonsu tayi gabaki dayansu tana zubda kwalla tace ” shin akwai abinda ake boyemin ne daban sani ba? Kufadamin jinake kamar zanmutu yanzu inbanji ba wayyo Allah na” takarashe maganar da karfi tana rike kanta da yasara mata tabbas abu takeso ta tuno amma takasa sede yadinga mata flash, duk shuru sukayi sun rasa abin fada shin yau ne fanan zatasan ko ita wacece? Kokuma yau ne zatabar duniyarsu? gaba daya tambayar dasukewa kansu kenan.
Areef ne sukaga yaje gabanta yazube akan guiwowinshi kanshi akasa , nan ne jikinsu yasakeyin sanyi domin sunsan tabbas wannan ba areef bane.
Cike da mamaki takalleshi ganin yadúrkusa agabanta goge hawayen fuskanta tayi tace” ya areef Meye haka ?” Girgiza kai yayi cikin muryan daya manyanta ” yace sarauniya ba areef bane! Sunana abdud Shakur nine galadiman masarautar nasminaya! Nazo ne domin in amsa miki tambayoyinki sannan insanar dake ko kedin wacece…….
Hakikanin gaskiya inajin dadin adduah dakukemin dakuma comments dinku it means alot to me, wallahi ina matukar kaunar ku sosai Allah yabarmu tare daga nan har gidan aljanna , ku Kuma masu karantawa kuyi shuru ba sannu balle Allah ya isa kallonku nakeyi kawai kowa yayi dede yasani amma zaazo time dinda mutum in yaganshi awaje karyaga laifina domin nima mutum ce ba engine ba.
Se munhadu gobe inme duka yakaimu da Rai da lfy .
via- https://play.google.com/store/apps/details?id=com.happyverse.diarywithlock&referrer=utm_source%3DD
https://chat.whatsapp.com/Jo87gS6QxQF58XSV10dYL8
⚕️⚕️ NIDA PATIENT DINA
Story & Written by
MRS ISHAM
JARUMAI WRITERS ASSOCIATION ✍️✍️
Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhum iname mika sakon taaziyata ga alhalin anty hadiza salisu sharif dakuma marubuta da kowa gabaki daya, Allah Ubangiji yajikanta da rahama, Allah yasa tahuta , Allah yakai haske kabarinta ya yafe mata Allah yasa innamu yazo mucika da imani da kalman shahada , Allah yagafarta mata Ameen ya hayyu ya qayyum.
꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁꧂꧁