Hausa NovelsNi da Patient Dina Book 2

Ni da Patient Dina Book 2 Page 39

Sponsored Links

Haka sukaci gaba da rayuwa acikin gidan daga ita seshi se yan aiki wahala babu irin wanda baya bata haka kurum zesata wankin manya_manyan bedsheets da blanket ga fada da tsawa gakuma maruka.

Ana gobe su ummi zasu dawo taje tasameshi yagama shiryawa zefita office ” Mr azaad inaso muyi magana ” okay kawai yace , tadaura da ” Mr azaad badanni ba kayiwa Allah daya halicceka kayi hakuri kasakeni bana kaunar zama dakai dede da dakika biyu banajin zanci gaba da zama dakai yanda ka tsaneni na tsaneka yanda baka sona haka nima bantaba sonka ba duk abubuwan dakamin na yafe maka ka sauwakemin intafi wajan iyayena sukadai ne nazama musu dole ” ko kadan kalamanta basu bata mishi rai ba, hasalima tunda tafara magana yake kallonta babu ko kyaftawa yakafeta da wayan nan mayun idon nashi , gyara tsayuwarshi yayi ajikin kofa hannayenshi na harde akirjinshi yana kallonta murmushin gefen baki yayi yace ” saurin mekikeyi haka base kinsake tunamin ba am aware kawai Jiran lokaci nakeyi ” besake sauraranta ba yafice zama tayi akan kujera tana tunanin rayuwa anrabata da gidansu yan uwanta da kowa nata gashi farin ciki yakaurace mata, haka ta yini jiki asanyaye jitakeyi kamar bata da wani lafiya, sosai takejin sanyi nan take jikinta yabara barin sanyi bedroom tasamu tashiga takwanta taja bargo tarufe jikinta.

Zazzabi me zafin gaske ne yariketa ko kwakwaran motsi bata iyayi tana kwance tun safe daya fita yabarta be dawo ba balle yasan halin datake ciki ko aikin dayasata bata samu tayi ba.

 

Kwance take adaki se sakin murmushi kawai takeyi waya na manne akunnenta lumshe ido tayi giyar soyayya na dibanta murya anarke tace ” hubby wallahi nayi missing dinka!katafi kabarni uhmm uhmm Allah inbaka dawo dawuri ba zanyita kuka kuma bazanci abinci ba haka zanbar kaina da yunwa” ajiyar zuciya fawwaz yasauke yana karajin tsananin kaunar suhaima nakara shiga ranshi besan wani irin so yake mata ba tariga da tazama wani bari na rayuwarshi yanzu sunriga dasun kamu da son juna, kara rungume pillow yayi yana fadin ” am sorry baby nima nayi missing dinki fiyeda yanda bakya zato gobe zamu dawo” ihu tasa seda yacire wayar akunnenshi ” hubby are you serious? ” Dariya yayi dan suhaima itama ba laifi akwai dan sauran yarinta yace ” in sha Allah baby gobe zamu dawo just pray for us kinji ” nutsuwa tayi ta shagwabe fuska kamar yana gabanta tace ” hubby kamin alkawarin kana dawuwa zakazo inganka ” murmushi yayi yace ” I promise Ina dawuwa ko gida bazan shigaba zanzo inga babynah ” rufe fuska tayi tana kyalkyalewa da dariya ” baby tsarabar me kikeso in kawo Miki?” Shuno baki tayi tace ” hubby i want nothing than you kai kadai kawai nakeso ” haka suka dinga zubawa junansu kalaman soyayya masu dadin gaske ( nida ba soyayya nakeyi ba gajiya nayi da hirar nayi gaba abuna karsusa in fusata)

Yana zaune a office dinshi yana duba wasu files dinda sakatariya jamila takawo mai na sabobbin ma aikatan dazaa dauka ga faisal shima azaune yadukufa yana aiki a system, ringing wayarshi yayi yayi picking yasa akunne yana fadin ” my sweet mom kuna lafiya ?” Abangaren ummi ta amsa mai ” da lafiya Lau son yakuke ina fanan tunda mukazo kullum senace kahadamu amma abu yagagara! Kasiya mata waya kabata kasan badadi yan uwanta nason magana da ita sujita shuru” harga Allah seda ummi ta ambaci sunanta tukun yama tuna da ita dan kwata_kwata yamanta da lamarinta okay yacewa ummi sukaci gaba da hira kafin tayi hangup, system dinshi yakunna yashiga footage din gidan na CCTv camera, tun daga sa’ilin dayake gida be fitaba yashiga harzuwa lokacin datashiga daki takwanta around 10:00 besake ganin ta motsaba haryanzu duba time yayi yaga 4:00pm mamakine yakamashi ganin harzuwa time din tana kwance tunani yakeyi ko bacci takeyi sekuma yatuna duk baccin dazatayi seta tashi tayi sallah amma yau shuru ko breakfast batayi ba.
Basarwa yayi yaci gaba da aikinshi can kuma yamike yayi switching din system din daukan jacket din suit dinshi yayi. faisal ganin oganshi yatashi yasa yamike yadau briefcase dinshi suka fice tada motar driver yayi dayaga sunfito shiga sukayi suka nufi gida , direct bedroom dinta yashiga yasameta kudundune acikin bargo numfashinta nafita sama_sama batama san yaye blanket din yayi yasa hannu taba jikinta dasauri yacire jin zafin daya dauka daukanta yayi yakaita bedroom dinshi , lalubo wayarsa yayi yakira doctor ammar, within 20mnt doctor ammar yashigo shikanshi yasha mamaki ganin fanan awannan yanayin ga ciwo datake fama dashi , kallon Mr azaad yayi yace ” amma tadade tana ciwo ne Koh?” Amsa yabashi da ” I don’t know” jin haka yasa besake mishi magana ba yafara bata taimakon gaggawa yadaura mata drip yayi mata allurai ” ga magungu nanta tana farkawa tasamu tasha abu me dumi like tea setaci abinci kafin tasha magani Allah yabata lafiya ” yatabi yabarshi zama yayi agefenta yana kallon beauty face dinta dayayi fayau sa hannu yayi yana shafa gashin kanta daga bisani yakoma kan cusion yazauna.
______ karfe 8 ruwan yakare cire mata drip din yayi yana kokarin cire calular , ahankali tafara bude idonta dasuka mata nauyi dishi_dishi take kallon fuskanshi harta fara ganin komai clearly fisge hannunta tayi daga nashi takoma can kuryan gadon ta dukunkune awaje daya tana ” Mr azaad kayi hakuri dan Allah karka dakeni kaina ne yakemin ciwo amma yanzu zanyi aikin kayi hakuri kamin rai bazan sakeba” haka tadinga sambatu tana bashi hakuri, jikinshi ne yadanyi sanyi hawa gadon yayi yanufeta ganin tunkarota yakeyi duk tunaninta dukanta zeyi ko yamata tsawa yasa ba shiri tasauka akan gadon zata gudu jirine yafara dibanta tayi tangal_tangal zata fadi yatarota tafado jikinshi muryanta dabaya fita tace ” Mr azaad kabarni intafi dakina” tana magana manyan idonta na lumshewa dagata yayi yamaida ita kan bed din sannan yadanna line din gidan wanda in aka kira masu aiki zasu daga , dagawa abu me aiki tayi umarni yabata data shirya abinci da tea yanzu takawo part dinshi aikuwa haka akayi , bata jima ba tazo tayi sallama jin muryanta yasa yaje yakarbo tana zaune atsakiyar gado tana binshi da ido ita haryanzu gani take kamar ze mata wani abun dan batayi abinda yasata ba .
Sa tea yayi acikin cup yamika mata karba tayi tafara sha kadan_kadan hartasha fiyeda rabi taji dadin shan tea din sosai ajiye cup din tayi akan bedside table , food flask yabude jallof din arish potato ne dayasha kifi banda da vegetables diba yayi yadawo gabanta , zefara bata kai mata spoon din yayi zebata abaki taki bude bakin se kawai kallon mamaki datake binshi dashi tafara tunani aranta anya Mr azaad ba poison yasa mata acikin abincin ba kuwa abinda betaba mataba yau shiyake mata.
Ganin taki bude bakin yasashi kara tamke fuska yana watsa mata uwar harara bashiri tabude bakin haka yadinga feeding dinta hartace ta koshi maganinta yamiqa mata tasha nan take tabara bata fuska zatayi kuka , lura yayi da kwata_kwata bata kaunar magani hakan yasa yajika maganin a cup yamatseta kamar wata yar jaririya yamata dúre dakyar tasha kokarin amayar da maganin take fuska ahade yace kina amar dashi adaren nan zanbaki hakkinki , aikuwa ba shiri tamaidashi. Kara daukanta yayi yashiga toilet da ita yadireta akasa yafice ,cire rigar jikinta tayi tana kokarin hanging dinshi yafada acikin jacuzzi cireshi tayi ta ajiyeshi a gefe wanka tayi tare da alwala rasa yazatayi tafito tayi iya towel ne a toilet din gashi kayanta din ruwa yajiqashi tafi mint goma tana tunanin mafita daura towel din tayi tafito, godewa Allah tayi dataga baya dakin hanyar fita tanema, harta kusa bakin kofa yafito daga dressing room hannunshi narike da jallabiya.
Idonshi ne yasauka akan kyakyawar surar da Allah yamata , kasa motsawa yayi sebin shape dinta da kallo yake musamman hips dinta dasuke acike masha Allah mamaki yafarayi dama wannan yarinyar haka ainihinta surarta yake ga brest dinta da rabinsu suka fito waje aranshi yace” how could that be possible yarinya da jikin manya?” Ganin irin mayen kallon dayakebin jikinta dashine yasa tayi saurin murda handle din dakin tafice tafada bedroom dinta tasamu tasa doguwar riga da hijab ta tada sallah , duk sallolin da akebinta seda tayisu kafin tasa kayan bacci jikinta bawani karfi sosai ta kwanta.

Shikuwa gogan naku gaba daya kasala ce tarufeshi lokaci daya barinma inya rufe idonshi yahasko mishi hoton surarta ,haushin kanshi yafaraji taya zetsaya yana tunanin wannan karamar yarinyar da ko cikekken hankali bata gamayi ba.

 

Karfe 1:00 na rana jirgin su abba yayi landing,Mr azaad damasu tsaransu ne sukazo tarbansu fawwaz de car key kawai yakarba dan beda burin daya wuce yaje yacika alkawarin daya daukawa babynshi .

 

Back to top button