Hausa NovelsMiskili Ne Hausa Novel

Miskili Ne 21-22

Sponsored Links

❤‍ *MISKILI NE*❤‍

*21&22*

 

…….what?? shariff yafad’a da k’arfi yana jin zuciyarsa na wani irin tsinkewa! fuskarsa da muryarsa bbu alamar rahama acikin su da wani irin tone yace”da gaske kakeyi abdallah?”daga d’ayan bangaren abdallah yace”wlh da gaske ne yaya….d’it! sheriff ya yanke wayar yana furzan da wani irin mugun huci me matuk’ar zafi daga bakinsa”meke faruwa kuma?”cewar mus’ab yana binsa da kallo”atak’aice shariff yasanar masa abinda ke faruwa”kafin yace”ayau zan kawo k’arshe alh yahaya da auresa da mahaifiyata, bayan na nunawa duniya da ammi wanene shi”yafad’a ahassale….cikin k’ank’anin lokaci shariff ya juye yakoma tamkar wani jan zaki”idanuwansa suka juye sukayi jajir”abinka game zafin zuciya”be tsaya sauraren driver yajasuba yafad’a cikin motar shida mus’ab “a haukace yaja motar cikin k’ank’anin lokaci suka iso gidan su”horn kawai shariff yaketa dannawa babu k’ak’k’atawa “tuni yakoma hassala”ana bud’e get d’in ya zuro kansa ta glass ya kalli get man agadarance yace”kaje na sallameka tunda baka san aikinka ba”yafad’a yana danna hancin motar cikin gidan”mus’ab kasa mgn yayi”tambayar kansa yakeyi shin duk sbd akan amaan d’in ne shariff ya canza haka ko kuwa?? be gama wannan tunanin ba sukaji k’arar shigowar text message acikin wayar shariff babba”lokacin kuma k’arfe 10:37 am”da sauri shariff daya gama parking zai fito yazaro wayar yafara dubawa kamar haka…. *kai d’an zafin kai! abinda mukeso dakai shine kayi gaggawar kamana duk wasu vedios dakasan kasamu game damu”basai mun maka dogon bayaniba”idan baka kawoba zamu kashe yarinyar nan bayan mutum 10 sunyi raping d’inta “bayan haka kuma zamu d’auki mahaifiyarka da k’aninka*…..k’aryane wlh! in har ban amso amaan ayau ba bancika d’an halak ba”cewar shariff cikin dakakkiyar muryarsa yana yin wurgi da wayar batare daya ida karanta text d’in ba har k’arshe”atake wayar taci screen “kallonsa kawai mus’ab keyi yanata huci”kafin ya d’auki wayar yaduba yagani”ya girgiza kansa yace”matsalar private number ce ,ba zamu iya kira ko tracking ba”tabbas duk sune suka sacesu”shariff beyi mgn ba yabud’e k’ofar yafito”shima mus’ab yafito rik’e da wayar yabi bayan shariff suka wuce interest d’in shiga cikin gidan…..tsaye carko carko yasami ammi da abdallah da jummai da laure masu aiki”suna ganin sheriff kowace tabar parlourn jiki na kirma”dan sun tabbatar da azuciye yake,ya koresu k’aramin aikinsa ne”kallonsa kawai ammi keyi aranta tana furta innalillahi wa inna ilaihir raju’un”sbd yadda taga fuskarsa ta tabbatar yana kan dokin zuciya”abdallah yayi saurin cewa yaya koka san inda taje ne?”banza shariff yamasa”ammi ta amsa gaisuwar mus’ab”duk suka zauna kan kujerah mus’ab yashiga yima ammi bayanin komai harda tashi matsalar”saidai besanar mata ga wand’anda suke zargi ba”kuma be fad’i turo text message ba”ammi! ibtihal na nan?”cewar shariff da k’yar yana kallonta da jajen idanuwansa “ah ah ta tafi skul”mahaifinta fa?”shima benan, dan tun asuba yafita be dawo ba har yanzun…sharif ya kalli mus’ab ya gyad’a masa kai kafin yace”pls ammi ki kira alh yahaya ki nuna damuwar kinga baya nan “daga nan zakiji zai dawo nan ko kuwa?”akan me zaka saka na masa hakan?”pls ammi zan miki bayani bayan kin kira d’in”batace komai ba ta d’auki waya ta nufi d’aki”shariff da mus’ab suka wuce upstairs”komai shariff ya had’a ahanzarce kafin ya kunnah laptop d’in”sai ga alh yahaya yana waya bayan fitar shariff d’azun da asuba…. yallab’ai mun rabu jiya kuma yau kana son ganina kuma?”sai kuma yayi shiru”can yace”tabbas mahaifiyarsa nake aure sbd dukiyarsa da wacce suka gada wajen ubansu”dama na jima ina zaton kamar police ne, shine zai shiga gonarka?to karka damu zanzo muyi mgn yanzun”amma bana zaton zai saki vedio d’in dan yanzun”akwai wata yarinya danake zaton uwar zata had’ashi aure da ita “ita yaka mata asato atsoratar dashi koya kawo vedio d’in koku kasheta”kuma ko bayan yakawo vedio d’in zaku bibiyesa sbd zai iya seving d’inta ya ajiye”bara dai nazo yanzun…..kashe laptop d’in shariff yayi ya zaro k’aramar wayarsa yana huci yasaka kiran me gadi”bugu ukku ya d’auka yana magiyar ayi hak’uri bisaga laifin dayayi…tambayarka zanyi! kalmr da shariff yafad’a kenan atak’aice “to inaji yallab’ai “da asuba waye ya fita ,kuma waye yadawo?”to gaskiya alh yafita yadawo kuma”sannan bayan fitarka da safen nan yakoma fita”kashe wayar shariff yayi yabi mus’ab da kallo yana fad’in yadawo ammi bata saniba, anan kuma yayi dubarun yadda yayi yasace amaan”damuwata mus’ab kar y’ar mutane ta salwanta ko wani abu marar kyau yafaru da ita”bansan yazanyi ba idan hakan yafaru?”ban tab’a dana sanin shigowar ta rayuwataba sai yau….ya isa shariff karka zobe ladanka “karka manta haka allah yatsara tun kafin zuwan gudanmu duniya! shariff ya mik’e tsaye yana fad’in ina zuwa”fita yayi daga cikin parlourn ya sakko down stairs”ammi da abdallah na zaune da sauri tace”na kirashi yacemun yana kasuwa amma yanzun zai dawo yayi wanka” to shikenan ammi taso muje ciki kiga wani abu”kai kuma ka zauna anan koda ya shigo ka kirani”yafad’a yana kallon abdallah “dato ya amsa “ammi da shariff suka wuce upstairs……komai ammi ta gani da idanuwanta”salati kawai takeyi tana dafe da k’irjin ta”cikin wani yanayi tace”allah ya isa tsakanina da alh yahaya “dama abinda yake k’ullamun kenan batare dana saniba?”kinyi amfani da maganin ammi?”ah ah sbd ban yarda da maganin ba”yanzun damuwar, wane hali amaan take ciki….kiran abdallah daya shigo wayar shariff yasaka ammi tayi shiru”d’auka shariff yayi batare dayayi mgn ba”abdallah yace”yaya yadawo yana d’akinsa”kashe wayar shariff yayi yana kallon ammi yace”ammi muje”batace komaiba ta tashi ta fita cikin tausayin d’an nata”sai yanzun ta fahimci dalilinsa nak’in amincewa da aurenta da alh yahaya”shariff kuwa bed room d’in sa yakoma ya d’akko bindigogi guda biyu yasaka cikin aljihun wondonsa”sannan ya d’akko ankwa yafito”mik’ama mus’ab ankwa d’in yayi suka fito”abdallah dai na zaune yanata kallonsu”ammi kuma tayi tagumi”ammi kije kice yafito ina son mgn dashi”daga haka shariff yanufi bakin k’ofar fita shida mus’ab suka tsaya….. ammi na shigowa cikin bed room d’in ta samesa zaune da jallabiya ajikinsa da alama wanka zai shiga”yanayin yadda yaga fuskarta saida gabansa yafad’i”hjy lafiya dai ko?”yafad’a batare daya amsa sallamar taba”da sauk’i dai”amaan ce ta b’ata bamusan inda takeba”to shine shariff dukya tashi hankalinsa yana parlour muje kad’an taushesa dan allah”subahanallahi! ko wani wajen ta tafi ne? yafad’a hankalinsa nad’an kwanciya”ammi batayi mgn ba, ta masa wannan dubaran sbd ba gaskiya ce da shiba zai iya kiran miyagun yasanar musu ga shariff nan nason mgn dashi…”atare ita dashi suka shigo cikin parlourn……wani irin mummunan fad’uwa gaban alh yahaya yayi dayaga shariff tsaye da mus’ab suna jifarsa da mugun kallon da yasaka y’an hanjin cikinsa hautsinawa”shariff na huci yanufi gabansa”yaja baya da sauri yana fad’in lafiya dai?”shariff beyi mgn ba ya fincikosa yana bashi wasu punchers guda biyu gefen fuska”atake bakinsa yafashe! cikin azaba yace”hjy agabanki d’anki zai dakeni kina kallo?……da k’arfi shariff ke taune lip nasa na k’asa da yayi jajir “zuciyarsa takai mak’ura wajen fusata yace”gidan ubanwa kakaimun amaan?”da kuma matar mus’ab?”karma kanuna wani abu ko ki fad’in gaskiya” duk naji wayarku gara tun da sauk’i kasanar kona datse y’an yatsun hannunka yafad’a yana turashi da k’arfi, yafad’i kansa yabigi tayis”yazaro bindiga yadaki gefen kansa cikin karaji yace”baza kayi mgn ba?”suna get house d’in alh isah tafashiya dake can g r a layi na karshe”daga hannun haggu gida me red d’in get”idan kayi k’arya bazaka tsiraba”kuma haka idan gaskiya ka fad’a”inaso yanzun kasaki mahaifiyata kona harbe maka k’afa….. ammi na kuka ta karb’e zancen da cewa allah ya isa tsakanina dakai”kaci amana ta”da k’yar bakinsa na jini yace na sakeki saki biyu”mus’ab ya matso ya d’aura masa ankwa”shariff kuwa dr mansoor yafita yakira, yasanar masa yazo da wata allura…….(bazan fad’i sunan taba)bayan sun gama wayar yadawo yana bin alh yahaya da mugun kallo yace nafiku iya mugunta”muddin kamun k’aryar inda suke naga ba nan sukeba saina yanke maka harshe”ya kalli ammi yace”ammi kamun wayarsa”dato ta amsa taje ta d’akko”shariff yashiga phone”yaga number d’in da alh yahaya yayi waya da ita da k’arfe 5:48 am”d’aukar number d’in yayi awayarsa ,kafin yasaka wayar alh yahaya cikin aljihu”hakan yayi daidai da shigowar dr mansoor cikin parlourn “bayan sun gaisa da ammi shariff ya amshi alluran”bbu tausayi ya matsa ya dakama alh yahaya ita gefen kafad’arsa”yasaki k’arar azaba….cikin second 50 yakoma kamar gawa”mus’ab da shariff suka d’aukesa suka kaisa wani d’aki suka rufe da key”kafin su nufi side d’in shariff ta computer sukayi tracking number d’in da alh yahaya yayi waya da ita”sai gashi sunga inda daidai yafad’a musu me number yake… bayan sun fito ammin na tsaye tace”shariff miye amfanin yimasa haka kuma?kaida yaka mata ku makashi cell “karki damu ammi, ammasa hakane kafin muje mudawo”barinsa yana numfashi koda yana a cell akwai had’ari”wannan alluran zatayi kusan awa 6 zuwa 7 ajikinsa kafin yadawo hayyacinsa”to ina zakuje?”police station! (yamata k’arya)”mus’ab kuzo muje”abdallah ka zauna tare da ammi ko ina kasan akwai security bbu abinda zai faru”yafad’a yana k’arema parlourn kallo “be tab’a zaton yadamu da amaan ba sai yanzun”dan gaba d’aya wani iri yakeji,dabai gantaba ko yaji motsinta agidan ba “fatansa allah yasa basuyi mata komai ba”suna fitowa shariff ya kalli mus’ab yace”nifa can zanje yanzun komai zai faru saidai yafaru!ya fad’a yana huci” wai kai kad’ai shariff? ka bari musanar office aturo mana wasu police ko?”girgiza kansa sheriff yayi cikin wani yanayi yace”fad’uwar gaba asaran namiji! kuma har abada matsoraci bai tab’a zama gwani”bazan dogara da kowaba sai allah da kuma kaina”sbd haka bbu shegen danake shakka koda ta sanadin hakan zan rasa rayuwata bazan damuba”yafad’a batare daya jira cewar mus’ab ko dr mansoor ba yayi gaba kamar zai tashi sama”dr mansoor yayi mamaki”mus’ab kuwa beyiba sbd yasan fahad shariff kaifi d’aya ne”baya tsoro balle shakka”dukda shima ba tsoronsu yakeyiba,beso garin ceto ran iyalansu su duka su rasa nasu rayukan gaba d’aya “gara komai abishi ta sauk’i”acikin motar dr mansoor suka iso police station sukayi bayani”mota biyu akayi ta police mus’ab yabisu suka tafi….. shariff kuwa yana isowa parking lot yashige mota yajata atsiyace”cikin y’an mintina ya isowa anguwar”kasancewar quarters ce anguwar,tsit take babu kowa sai masu wucewa kan abin hawa” wasu na wajen aiki….zuciyar shariff adake yayi parking yafito”yatura get d’in gidan gabansa gad’i”yana shigowa ya hango security guda biyu a bakin get da wani mutum da alama me gadi ne”suna ganinsa suka nufosa”yasaka hannunsa guda cikin aljihun wondonsa”beyi wata wataba ya zaro bindiga ya harbi secuty guda a gwiwar k’afa”gudan kuma yafara harbinsa yana gocewa”yana hango me gadin zai gudu shima ya harbesa a k’afa”kasancewar alh isa baya ciki sai yaransa ne kawai dasu amaan da bilkisu da ahmed”shiyasa babu wasu security aciki sosai sai masu gadin get”dan beyi zaton za’a iya zuwa aka musu farmaki ba”shiyasa yafita yanzun bada jumawa ba…saida bullet d’in bindigar security d’in ta k’are sannan yafara zare ido yana neman hanyar guduwa….kafad’amun ina matar da yarinyar da aka sato suke kona kasheka?….suna cikin lambun gidan”inane hanyar?”da hannu yanuna masa”shariff beyi mgn ba ya harbesa ga gwiwar k’afa yanufi hanyar daya nuna masa itace inda lambun gidan yake…..yana gudu da waige waige har ya iso bakin k’ofar shiga cikin lambun gidan “yana d’an lek’owa ya hango wasu k’atti majiya k’arfi ,da bbu d’igon imani ko tsoron allah azuk’atansu,sunfi su goma suna rik’e da manyan maka mai sunata zare ido”sai bushe bushen hayak’i sukeyi”can ya hango su amaan yashe ak’asa “sai zare ido takeyi ta takure jikinta waje guda”idanuwanta sunyi luhu luhu da alama taci kuka ta godema allah”itama bilkisu da damuwa saman fuskarta ,tana rik’e da ahmed dake atsorace ya b’oye fuskarsa ajikinta…..kai waye nan nake gani kamar mutum?”da sauri shariff yasako kansa ciki sbd ya lura basuda bindiga saidai makamai…. amaan kamar daga sama ta hangosa yana tunkarosu cikin izzah bbu alamar tsoro asaman kyakykyawar fuskarsa daya tsuke…..da sauri ta mik’e tsaye tana fad’in hamma nah! har cikin kansa yaji sunan”tunda take kiransa dashi be tab’a jin hakan ba sai yanzun”kallon cikin idon junansu kawai sukeyi”bilkisu ta fashe da kuka tana waigen ta inda zataga mus’ab yafito”kusan mutum 4 suka nufi shariff gadan gadan”yayinda sauran suka zayage su amaan”ta saki k’ara tana kiransa….tun kafin su iso yazura hannayensa duka cikin aljihun wondonsa yazaro bindugu guda buyu duk ya harbesu”hakan yayi daidai da shigowar police wajen”mus’ab shine daga gaba”kai tsaye wajen iyalansa yanufa”yayinda sauran k’attin ke kok’arin jan hannun amaan da ahmed zasu gudu dasu”tsalle guda shariff yayi yakaima k’aton daya rik’e amaan duka”ya juyo afusace sai soki shariff da wuk’a”cikin zafin nama ya kauce yakoma kok’arin kawo suka”duk amaan na tsaye gefe tana raba ido tana kuma kallon mus’ab dake kok’arin k’wato d’ansa wajen k’attin biyu”da taimakon harbin da sauran police d’in sukayi yasaka wasu suka tsere aka kama wasu”bilkisu ta fashe da kuka ta matsa ta rungume mus’ab”amaan azatonta hakan abin kirkine itama kawai saita fad’a jikin shariff dake tsaye yana kallonta ta rungumesa tana sakar masa k’aramin kuka….✍️

wannan book d’in na kudine ! idan kina buk’atar siya serious regular grp 300
vip grp 1000
via 2230373842 nabila aliyu uba bank

ki turo shaidar biyanki ta what’s app number d’ina 08100084251

idan kika karanta mun book baki biyani hakk’ina ba ko kika siya kika fitarmun Allah ya isa ban yafe miki ba

Back to top button